🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 21-22

571 44 0
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣1⃣➖2⃣2⃣


  A firgice yaya Aqeeb ya tashi tsaye yana nuna yaya Kb da hannu sai ya kasa cewa komai ya tsaya tana kallon shi shima da dariya a fuskar shi yace
"Yes today is Aisha's Birthday which rhymes with her graduation celebration so am happy to wish you a very big happy sweet 17 dear"

Tafi ne kawai ya kaure a hall din dama abu na yan boko yan duniya gasu yan Abuja da ketare hakan ba abin mamaki bane a gare su, gabaki dayan yayyen mu tasowa sukayi suna bawa yaya kabeer hannu tare da yi mai godiya ta musamman illah yaya Aqeeb da ya fita daga hall din ba tare da sanin kowa ba..

A nan fah sabuwar tattaunawa ya kaure tsakanin yan jaridu da mu ni da na rasa abin cewa dan shaf na sha'afa  da wai yau ne Birthday dina sai yanzu ban gama warwarewa daga murnar liyafar da aka haɗa mana ba ga wani gagarumin kyauta kyautar da koh Abbu da ke mahaifi na bai bani ba na rasa abin cewa kuka zan yi a'a godiya zan yi a'a koh rawar murna da jin dadi zan yi ganin irin wannan kyautar da ban taba tsammani ba nan kusa a rayuwa ta ba..

Tashi Abbu yayai ya zo gare mu ya rike hannun yaya kabeer tare da kiran sunan shi

"Kabeer wannan kyautar da ka yi bamu da abin cewa sai godiya da yi maka addua'a da fatar alkhairi amma kabeer wani hanzari ba gudu ba me zai hana ka ajiye wannan kyautar har sai Aisha ta kara girma da wayau tunda yanzu dai ka gani yau take cika 17 bata wani gama hankalin kanta ba ka bari har sai ta kai koh irin 20 years and above din nan ina ga kamar in har ban maka katsalandar ba tsakanin ka da kanwar ka ba ka yi amfani da na wa shawarar a gani na hakan zai fi" daga haka Abbu ya ja bakin shi yayi shiru already Abba da umma sun fara fahimtar wani abu game da wannan kyautar ta yaya Kb dan haka ƙalla basu ce ba suka zuba mai ido kawai yanda kowa ma ya zuba mana idanu..

  Juyowa yayi a hankali yana mai kallon Abbu kamar wanda ya nemi abu aka hana shi sai ya sunkuyar da kan shi ƙasa ya fara magana

"Abbu da farko dai ina so in nemi afuwar ka na yin kai tsaye akan ikon ka kuma dolen ka ba tare da na nemi izinin ka ba Abbu ka yafe ni amma ni a gani na yau ce ranar da ya kamata duk mu haɗu mu saka Aisha farinciki duba da ganin cewa marainiya ce bata da wanda zai bata irin kulawar da zamu bata a yanzu bata taso cikin mutani da yawa ga kadaici da ya ta dawainiya da ita in har zan iya tunatar da mu Aisha bata taba celebrating birthday din ta ba so yau ce ranar farko da ya kamata a haɗa mata duk wata farincikin da ta daɗe bata yi irin shi ba wannan shine dalilin da yasa na ce ni kuwa zan shiryawa Aisha babbar surprise da zata y farinciki a rayuwar ta ita ce dalilin da ya sa n haɗa wannan ƴar liyafar saboda ina ganin koh baka kusa ni mai iya yi ma Aisha komai ne a matsayi na na wan ta kuma kanwa a gare ni amma yin hakan ya bata maka rai ina mai baka hakuri da daɗa neman afuwar ka Abbu ka yafe ni""ya ida yana mai haɗa hannayen shi wuri ɗaya alamun roko

  Kamar ruwa ya cinye Abbu haka ya yi tsit a wurin shi abin da yake nufi daban ne kuma yana tsoron kar jama'a su zarge shi da son kanshi da yawa bayan ga kannen kabeer din nan bai basu kyautar kwatankwacin abin da ya bama bare ba shiyasa ya yi kokarin dakatar da shi sannan tunanin da shi bai yi ba tuntuni shi kabeer din yayi wato hada min kwaryakwaryar birthday koh da sau ɗaya ne a rayuwata amma bau taba qamnan tunanin ba daidai da rana daya sai gashi wannan ya haɗa wa ɗiyar shi da zuciya daya amma ta eaaa da me zai saka mishi sai disappointment hakan kamar bai dace ba sai Abbu ya kalle shi ya fara magana

"Kabeer kar ka min mummuna kokuma bahaguwar fahimta kyauta tsakanin ka da Aisha babu wanda ya ke da ikon hana ka yin shi ciki kuwa har da ni mahaifin ta hakan da nayi nayi ne dan ganin kamar kyautar tayi yawa amma ba wai dan ban yaba ba amma ni ma ina mai baka haƙurin yin kai tsaye a kan hukuncin ka tsakanin ka da kanwar ka kabeer da fatan za ka fahimci nufi na da kyakyawar fuska"

Murmushi kawai yaya kabeer ya yi yana mai yi wa Abbu godiya da ya yarda da shi wannan yardar ya sa yake da full confidence akan abin da yake da niyar yi ba tare da ya ji koh da ɗar ba..

Su Abba da umma ma godiya suka yiwa yaya kabeer da sanya mai albarka a yayin yin hakan ne umma ta kasa hakura ta ce mai

"Kabeer ina maka fatar samin nutsatsiya kamilaliyar mace ta gari wacce zata cigaba da ɗora ka akan hanyar alkhairan da kake yi"

Murmushi kawai ya mata ba tare da yace amin ba sai ya juyo gare ni ya kalle ni na wasu lokuta kaɗan next me zan gani sai kawai naga yaya kabeer ya zube a ƙasa yana kallon kwayar idanuna.tun kafin in yunkura ince wani abu sai naga haske ya dallare mu gabaki daya sai na tsinkayo muryar yay kabeer yana min magana

"Its been long da na haɗu da ke na fara ganin ki ne a gidan mu tun kafin ki gama sanin kanki na fada a soyayyar ki ne a lokacin da na fara ganin ki ba tare da nasan son da na kamu da shi a kan ki mai girma bane hakurin ki da hankalin ki su suka daɗa kara miki ƙima da daraja a wuri na kawaicin ki da kunyar ki su suka daɗa zurmani a soyayyar ki nayi rayuwata a wata kasar inda mata ke walagagi ta koh ina amma ban taɓa sha'awar koh da mace ɗaya a cikin su ba na dawo nan ƙasar na tarar da su iri kala kala amma basu taɓa burge ni ba koh daidai da second ɗaya na yi shekaru shida a kasar nan ana nuna min mata amma ban yarda na bude idanuwana na kalle su ba koh da na kwana daya ne farkon dawowa ta kasar nan a kwana na biyu da dawowa ta na gan ki a ranar a lokacin na fara jin wani abu da ban taba ji ba akan kowace mace na so in shashantar da abin amma yanayin yanda nake jin abin a rai na ya rinjaye ni da yawa koh da na zo na fahimci meke dami na na kasa furtawa kowq haka na yi ta jinyar abin har rana mai kamar ta yau da naga ya kamata in sanar da ke saboda mu yi maganin wannan abin da ya saka ni jinyar shekaru kusan shida da haka nake son nemar alfarma a gare ki da fatan zaki yi min wannan alfarmar...

Tsit hall ya dauka ni fargaba sauran jama'a fargaba tsoro ne ya kama ni dan ban san alfarmar me kuma yaya kabeer ke nema daga gare ni ba wanda har yake roko na ba amma koh ma menene wannan alfarmar bana jin zan iya hana shi dan so da kaunar da ya nuna min wani nawa na jiki na ma ba lallai bane ya nuna min bai kyamace ni ba bai nuna min banbanci ba hasali ma janyo ni yayi a jiki ya nuna kaunar shi a gareni akan zanen da nake so yake taya ni son abin da nake so amma ko ma menene zan yi mai wannan alfarmar koh da kuwa hakan na nufin bashi abu mafi soyuwa ne a gare ni

Yaya Aqeeb da ya daɗe da dawowa cikin hall din dan ganin fotar shi bai da amfani so yake ya ga iya gudun ruwar yayan nashi killa ba abin da yake tsammani bans hala ma ya sami ikon isar da sakon da zuciyar shi ke aiken shi tuntuni da haka ya dawo ciki da niyar sanar da ni abin da ke damin shi amma sai me sai kawai ya ga abin da yayan shi ke yi bai gama tsinkewa da lamarin shi ba sai lokacin da yayan nashi yayi wani abin da ya girgiza mu mu duka har da media wato

""Aisha Murad will you be my MTB for ever"??

Ban san lokacin da na zazzaro idanuna waje ba haka sauran jama'a ma suka zuba idanun su suna kallon mu in ban manta ba "Meant to be" yaya kabeer ke nufi wato so yake in zama matar shi kenan wannan tunanin ya sa na dago da sauri baki na na ɓari kamar ya san tunanin da nake yi sai ya tare ni da cewa

"Yes Aisha i mean what you were think will you please be my forever"?

Hawaye ne suka fara tsere akan fuskata dan wannan alfarmar kamar tana kokarin bin ƙarfi na amma fah nayi wa kaina alkawarin yi mai wannan alfarmar koh da kuwa hakan na nufin bashi abu mafi soyuwa ne a rayuwa ta dan haka in har shi bai ji kyashin yi min dawainiya ba toh nima kuwa bazan ki yi mai alfarmar nan ba juyawa  nayi muka haɗa ido da salma ta yi saurin jijiga min kai tana murna alamun in amince juyawa nayi zuwa ga ummi ai da sauri ta jijiga min kai itama Abbu kuwa murmushin manya yamin kawai alamun shima ya amince juyawa nayi na kalle yaya Ib da dariya akan fuskar shi daga min kai Umma kam baki har kunne ta ce min "yes dear" daga haka na maido da kallo na ga yaya Kb wanda yale tsugune tuntuni sai na rasa bakin magana kawai sai ga hawaye a fuskata

"Yes yes yess yaya kabeer i will be your MTB and your forever inshaAllah"

Ai tuni ya miki ya fara juye juye kamar me neman wani abu sai ya kuma durkusawa kasa ya fiddo da wata yar karamar akwati ya bude min yana mai cewa

"Aisha Murad will you be the wife of Kabeer Habib"?
Da sauri na ce mai
"Yess i will"ni sauri nake ma ya yi ya tashi daga tsugunon da yake dan na fara gajiya da ganin shi a ƙasa amma shi koh a jikin shi

Da sauri ya cire zoben da ke cikin akwatin zai saka min na yi saurin dakatar da shi na mika mai hannu na instead murmushi kawai ya min dan yasan dama hakan ne zata faru sai ya saka min akwatin a hannu na na karba ina mai murmushi nima hall din ya kuma ƙurewa sa tafin jama'a yan jaridu an sami abin bugawa da cewa sai dauka suke ta yi

A harzuke yaya Aqeeb ya bar hall din itama falmata da zafi da radadi ta fita batare da wani ya lura ba

Tasowa yayi ya tsaya yana ta faman yi min godiya da alƙawarurukan kula da ni har karshen rayuwar shi wanda hakan ya saka kowa yi mana kallon sha'awa abokan aikin shi da suka hallari wurin ma sun taya shi murnar samin mace ƴar yarinya a matsayin matar aure har da yi mai tsiyar ashe shiyasa baya kallon kowace irin mace duk kyawunta dama yana da yar beauty da ya ajiye yake musu wayyo..

Haka dai aka karaci liyafar dan labarin mu a baki kowa mun fita mun iso kenan zamu shiga mota muka duba bamu ga falmata ba dubawan duniyan nan mun yi bamu ganta ba dan haka aka koma cikin hall din neman ta an fito ba'a gan ta ba sai gashi ta bullo daga gefen mu tana murmushi da sauri muka nufe ta muna tambayar ta ina ta tafi dariya ta yi ta ce

"Kun ji ku kun shagala da karbar surprises din ku ina zaku lura da cewa bana kusa anyway congratulations and happy birthday to you dear Allah ya bamu aron rai muga ranar bikin ku ke da yayan mu" ta ida maganar ta tana rungume ni sai ta share hawayen ta tana kokarin danne kishin da ke taso mata dan ta san duk yadda zata yi bazata taba samin soyayyar da ta daɗe tana dakon shi ba har abada daga wun yaya kabeer din dan haka kawai sai ta yi kokarin rarashin kanta da ɗorawa kanta dangana da yin alƙawarin taya ƙawar ta aminiyar ta samo soyayyar yayan na su...

Jin ɗigar abu kamar hawaye a kafadana na yi saurin ɗagowa na kalle ta na ce

"falmata me haka na ke gani daga idanun ki kamar ruwa"

Dariya ta yi ta ce min
"Kin ji ki da irin halin taki koh a'a ba ruwa bane pampo ne aka buɗe"

Duk sai muka yi dariya dan maganar ta bamu dariya matuka a gatse ta faɗe shi da haka nima na rungume ta ina mai jin daɗi nace mata thanks sweetheart...

Zan shiga motar kenan yaya kabeer ya ce ai bai san zancen ba sai dai in bishi mu tafi amma nima kememe naki yarda nace sai dai mu shiga tare da su salma ya ya iya da ni haka ya amince muka shiga ni da shi a gaba salma da falmata a baya tun da muka shiga surutu salma ke yi amma falmata daga uhmm sa uhnm bata iya buɗe bakin ta dan ta san tana bude bakin nata kuka ne zai fallasa sirrin ta wanda ita kuwa baza ta so hakan ba ni kuma kunyar yaya kabeer din nake ji shiyasa na kasa ce mai komai sai zuba yake yi ƙarshe ma shi da salma suka koma suna hiran har muka dawo gida yayi dropping din su ni kuma ya ce toh yanzu sun tafi za'a yarda a bi ni mu tafi gidan koh sai an samo yan rakiya?

Rasa abin fada na yi kawai sai na juya fuskata zuwa gefen murfin motar ina kallon hanya abin ya burge shi dan ya lura kunyata a jini take shiyasa ya dage akan lallai sai ni zai aura dan yasan zai sami rayuwa mai dadi da ni a nan gaba..

"Mrs Kabeer kin min shiru should i consider that as a yes"?

Na daga kai na kawai shi kuma ya ja motar muka tafi akan gobe su salma zasu shigo gidan mu a hanya ya rinka ja na da hira tun ina shashare shi har na sake ƙaɗan in ya tambaye ni in dan amsa mai a nan ne yake tambayata a ina nake a islamiya nace mai duk wuri daya muke ni da su falmata muna izhu arba'in da shida yace min wow ashe har mun kusa saukewa kenan na ce muna fata haka dai hirar ta kasance har ya dawo da ni gida inda yaso ya kuma dasa wata hirar nace mai

"Yaya baka fah yi sallah ba tun dazu nima ban yi ba ga lokaci nata tafiya"

Sai ya dan yi dariya yace "tsab na gano ki yarinya so kike in tafi kawai dama kin gaji da surutu na na gane toh shikenan zan tafi"

Da sauri na ce "a'a fah ni ban ce ba kawai tuna maka nake yi yace na sani beauty  kar ki damu zan kira ki anjima ungo karɓa ya miko min wani pack waya ce a ciki full charged da sims biyu na rasa abin cewa dan yau ya min abubuwa da bazan taɓa mantawa da su a rayuwata ba godiyar zan yi ya hana ni ya ja motar shi yayi gaba na juya na shigo gida sai na ci karo da motar da le mallaki na ne yanzu na kalli motar in total admiration of the car na yi kissing din motar na shige cikin gidan mu

Tarar da kaya na yi kaca kaca a falon ga ummi da yaya ibrahim nan zaune ana dudduba gifts din da aka bamu saboda akwai wani mutum da ya ce ma Abbu ya cancanci kyautar Father of the year har ya bama Abbu kyautar wata yar medal da key da bamu san ko na menene ba sai shi da Abbun suka sani

"A'a masoyan asali soyayyar ce a tsakar falo haka babu koh kunyar kar wani ya gan ku"!!

Dagowa suka yi suka kalle ni ummi na murna ta nuna min wata yar kit tace 
"Yaya Aisha kalla wata yar dankune na gani me kyau ban san wa ya ba ki ba amma ni kam ya min kyau in dauka?

Na ce sis dauka in ban baki ba wa zan ba mawa da murna ta rungume ni ta ce tagode

Yaya Ib da ke kallon mu da farinciki a fuskar shi ya ce
"Mrs Kabeer har an gama hirar kenan"!?

Hararar shi na yi nace haba yaya Ib yaushe na zama wata mrs pls ka daina..

Sai da ya gama tsokana ta kafin ya min congrats ya ce toh me za'a mana a matsayin birthday pleasantries da mamaki na ce lallai yaya ba ni za'a bawa pleasantries din ba ni ce kuma zan bayar toh kar ka damu zan hada mana dinner mai rai da lafiya kar ka damu ai yau a cikin farinciki nake

Ya ce ba dole ba yad yarinya dake da mota dalleliya ga miji likita kin samu a free ga shi yau birthday din ki ai dole kiyi farinciki

Hmm na tafi yaya Ib dan na lura yau falmata ta raba muku rigimar ta ne yau dan haka ni na yi gaba ummi ki je ki fara haɗa min kayan miya kafin in fito da toh ta amsa min ni kuma na yi gaba abi na yaya Ib kuma ya nufi ɗakin shi yana tsokana ta ni dai ban ce mai komai ba...

Daga falon straight ɗakin Abvu na wuce na tsaya jiran shi dan baya nan da ya fito sai ya ce min
"A'ahh yanmatan Abbu har an dawo ne"?

Da kunya na dukar da kaina ina jin kunya nace Abbu ya gajiyan hidimomi yace min Alhamdulilah mamana ya gajiyan shagalin na amsa ya ce toh dama koh baki shigo ba zan zo neman ki Aisha

Sai na natsu ganin magana mai muhimmanci zai yi da ni

"Aisha dazu a wun liyafar ku na so in sanar da ke wani abu amma ganin yanda kike cikin farinciki sai na jinkirta har sai kin dawo gida dan kar in ɓata miki farincikin ki da ni da nake mahaifin ki ban baki ba"

Abbu ya daɗa dulmuya ni a duhu dan haka na kasa hakuri na ce "Abbu dan Allah ka sanar da ni menene dan na matsu in sani""..

"Wato Aisha kusan sama da shekaru shida Kenan da yahaya ya min maganar ki har yake neman in bashi izini ya fara zuwa wurin ki in kin gama makarantar ki ban rufe mai ba nace na amince amma bazan miki dole ba in ba kya son shi ya ce min ya amince amma a yau da na gan ki cikin annashuwa sai na rasa bakin magana na bar ki kika zaɓi abin da kike so dan kina cikin murna a yayin da kika amincewa kabeer da auren shi da zaki yi kin ji maganar me zaki ce akan maganar yahaya"??

Na dau lokaci ina tunani dan lallai in na ki yahaya toh dole ƙimar mahaifi na zai zuba a idanun shi wanda bazan so hakan ba in na amince mai kuma ba zai dauki mahaifi na a matsayin mai nuna banbanci ba a tsakanin talaka da mai kudi ba amma kuma ya zan yi da yaya kabeer da sabuwar kaunar sa da ya dasa min a yau din nan kawai ga sabon da ya shiga tsakanin mu duk na rasa da wani shawarar zan yi amfani karshe dai ce mai nayi Abbu wa kake ganin ya dace da ni sai ya min murmushi kawai ya ce mamana da wa kika fi son yin rayuwar ki tambayar ta min nauyi sai na ce Abbu duk wanda ka zaɓo min yayi a karo na biyu ya ce min mamana kamar hankalin ki ya fi kwanciya da kabeer koh ba haka bane sai kunya ta kama ni shirun da na yi shi ya nuna mai amincewa ta sai ya ce tashi ki tafi abin ki mamana Allah ya miki albarka na ce amin Abbu amma shi yahayan fah sai ya ce tafi abin ki wannan ba matsala bane kin ji na jijiga kai na na tashi na tafi dakin mu dan ina so in watsa ruwa..

*******************
Shigowar yaya kabeer gidan na su yayi daidai da fotowar da aka yi da falmata daga sashen su domin saka ta a mota zuwa asibiti dan tun da suka koma gidan take kukan fitan rai amma mama kadai ta sani tun tana kyaleta har ya kai abin ya bayyana dan kuwa tari ta ke yi mai firgitarwa daga karshe ta fadi ƙasa sumammiya shine mama tayi kiran Baban su falmata dan ya zo su kaita asibiti

Da sauri ya karasa ya buɗe motar shi aka saka ta ya ja a gurguje ya fita sai asibiti...........

  *_🍒S,Ibraheem🍒_*

Continue Reading

You'll Also Like

431K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...
541K 17.6K 157
Genre: Space, Doting, Farming, Time travel, Healing Synopsis: Xu Linyue from the 21st century crossing over with the heavenly space soul penetration...
441K 24.4K 166
Featured at Wattpad's Editor Picks list. Luna, an overworked Engineer, had an unfortunate end. Her spirit, feeling wronged, fights Death for a second...
1.9M 97.2K 38
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...