🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

40.3K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 17-18

615 45 0
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

*_HAPPY EID EL MUBARAK TO THE ENTIRE MUSLIM UMMAH IN AND ACROSS THE UNIVERSE WISH U A VERY SWEET CELEBRATION_*

*PLS KAR A MANTA DA NAMAN SALLAH NA INA JIRAN KU AGAIN A AJIYE FLAGYL KUSA SABODA IN AN YI BUDA BAKI CIKIN YA HAUTSINE SAI A SHA A SAWWAKE*😄😄



1⃣7⃣➖1⃣8⃣

Rayuwar mu ta kasance rayuwa ce ta yan boko da wayewa ba wai wayewar tanbaɗaɗu ba wayewa irin ta fahimtar juna da karantar halayar juna hade da kau da kai akan abububuwan da bai shafe mu ba girman kai ba namu bane amma miskilanci ga duk wanda yake mana gani gani ba abu ne mai wuya a wurin mu ba

Kwatsam sai na fara bayyana wasu halayya wadanda da bani da su abu na farko shine yawan kyaliya abun da a da har tsoron tambaya na ake yi akan magana daya sai in yi tambayoyi sama da goma har guje ma tambaya ta ake yi a baya ce min ake yi aikin jarida zai fi dacewa da ni saboda yawan tambayoyi na amma yanzu da muka kai wannan marakin na aji uku a makaranta sai kuma na fara jajan aji maganar ma sai na ga daman yi koh tambaya na aka yi in bai min ba toh bana wani bayar da amsa sai na ji ra'ayin yin hakan wannan sabuwar hali na wa ya na damin kawaye na matuka dan har su abin bai musu dadi abu na biyu kuma shine tunda muka shiga aji na biyu nake mayar da hankali na akan zane wato painting abu kamar wasa tun suna min dariya wai aikin maza nake son yi har dai suka daina suka zubama sarautar Allah ido dan kuwa sun ga ni da sukewa dariyar abin baya dami na toh shigan mu aji na uku wanda yayi daidai da shigan mu shekara sha hudu (14yrs) a lokacin ne na fito da ainihim kaunar da nake yiwa harkar zane a gida koh da su falmata suka gayawa iyayen mu sun matukar jin dadin haka ganin ga ni mace amma ina da sha'awar zane zane kuma ban damu da duk wani kalubalen da nake fuskanta daga wun jama'a ba

Yayin da na tsunduma a harkar zane zane yaya kabeer na dada fitomin da manufar sa karara da farko ban gane ba gani nake yi duk saboda zanen da nake yi ne dan yana daya daga cikin mutanin da ke nuna jin dadin su akan abin da nake yi amma koh da wasa baya bari in gane wani abu dangane da kulawar shi a gare ni falmata so ne take mai kamar zata hallaka kanta amma alkunya da kama kai baya bari ta nuna mai koh kadan duk yanda zata yi ta danne feelings dinta in ta gan mu tare tana yi saidai in ta koma daki takan ci kuka ne kamar ba gobe tun mama na mata fada akan kukan da takeyi har ta zo ta fara rarrashin ta dan kuwa bata taba gaya mata sirrin zuciyar ta ba itama bata takura mata tsoronta daya ne kar ta rasa ƴar ta dan tana gani kamar falmata tana boye mata wani abu ne babba wanda ta rasa yanda zata yi ta gano wannan sirrin

Yaya kabeer a yanzu ya fara aikin shi a National Hospital dake cikin garin Abuja a matsayin gynaecologist(likitan mata)

Alhamdulilah yana jin dadin aikin shi kuma yana kokarin kare mutuncin shi baya bari aikin shi ya jayo mai raini daga wun patients din sa koh colleagues din sa ya zaɓi aiki a nan ne farko dan ya kware ya kuma kara samin ilimi kafin ya fara a asibitin shi wanda ake kan gina shi saura kiris a gama koh da Abba ya ajiye shi ya tuntuɓe shi akan batun aure sai ya ce ai ya kusa ne kar ya damu baba ma sai da ya mai maganar amma amsar shine ai ya kusa ne abin na damin umma ganin shine fah babba nan gaba kaɗan za'a fara maganar aurar da su salma dan ita bata so salma ta ƙara wasu shekaru masu yawa a gida dan girman jikin ta ya wuce misali ga tsayin ƙafa a duk sanda ta tuno wannan abin takan nutsar da shi ta gaya mai duniya fah ba wurin zama bane kuma ya bar ganin shi wai shi dan boko dan mai kuɗi a duk ranar da aka ce ya fadi ya mutu to lallai wadannan abubuwa basu da amfani a gare shi illa abin da ya bari wandanda su zasu kasance masu yi masa addua'a wadannan kuwa ba komai bane face sadakatul jariya wato sadaka mai gudana,auilmul yantafa'u bihi wato ilimin da aka amfana da shi,auwwaladul sahle wato ƴaƴa na gani masu kokarin yi mai addua'a wannan nasiha nata yakan sake mai jiki dan ya san da a yau zai zauna da ita ya gaya mata ga wacce yake so tsab zata amince ta taimaka mai dan ya aure ta amma matsalar shine shi so yake ya sami soyayyar ta da kanshi ya wahala da kanshi a wun nemo soyayya ta so yake muyi *soyayya mai garɗi* kafin mu yi aure dan hakan ne kadai zai samo mishi zaman har abada da yake son yi shi da iyalin shi a nan gaba..
fannin soyayyar da yake min kuwa yana nan babu abin da ya canza amma shi har a lokacin jira yake wai in na daɗa girma sai ya fito min da manufar sa

  Yaya ibrahim ya sami admission a university of kano wato Bayero university a inda yake karantar mass communication(aikin jarida) a lokacin da zai tafi kuka sosai ummi ta yi har da ƴar guntuwar zazzabin ta haka dai aka rabasu tana ji tana gani da farko ta saka abin a ran ta amma daga baya sai tazo ta ma manta sha'anin yara saboda shekarun ta tara kuma suma suna aji biyar kenan a makarantar primary kawancen su ita da  husna na nan sai ma abin da ya karu sun zamo kamar wasu ƴan uwan jini kusancin su yasa ake kiran su yan biyun umma koh da kuwa a chan gidan mu ne haka ake kiran su shi Abbu bai ma san irin godiyar da zai yi wa Alhaji Habib mustafa da matar sa Hajiya Amina haɗe da Alhaji Amodu da matarsa dan suna matukar kular mishi da rayuwar ƴar shi da yanda suka mishi kokari a rayuwa har ya kai wannan matakin ba tare da sun mai hassada koh kyashi ba

  Yaya umar ya mayar da hankali sosai a karatun shi yayi kokarin danne abin da ke ran shi dan ya san da karatun nan kadai zai iya aiwatar da abin da yake da niyar yi ba tare da an mai barazana ba bai cika shiga sabgar da ba nashi ba kullum kokarin shi shine ya kai matakin da ya dade yana kwadayin kaiwa a rayuwar shi dan haka neme nemen mata ba nashi bane rashin ji da kin mayar da hankali a karatu duk ba nashi ba ne hutun sati da yake zuwa yi ma ya rage ya mayar duk bayan wata saboda yanayin karatun shi yana buƙatar natsuwa

Akwai wani rana a makaranta ina zaune ina karanta wani magazine da falmata ta zo da shi na ga wani painting da aka rubuta inda aka yi shi a kasa abin ya burge ni harda ma dai painting din kamar zanen kaya ne na mata da na maza kafin a buga din nan

Kura wa magazine din ido na yi kamar na ga aljannah ta ganin na daɗe ya sa falmata matsowa ta wufce magazine din a tsorace na juyo na saka fuskar tausayi ina magana kamar ba zan yi ba na ce

"Haba babbar sister-in-law ya zaki min haka kih kin manta ke din matar yaya na ne to be pls ki ba ni magazine din nan in karanta wallahi da na gama zan dawo miki da shi"sai rokon ta nake kamar uwata.

Zugum tayi tana kallo na kamar taga talabijin kafin ta dora da

"Wai shin in tambaye ki mana Aisho"kasancewar sunan da take kira na da shi kenan a duk lokacin da zata min tsiya

Sai na ce mata ina jin ta

"Aisho wai ba kya jin wani iri ne da rayuwar da kika dorawa kanki akan abin da bai dace da ke ba  matsayin ki ba ƴa mace ace baki da abin yi sai zane zane da karance karancen kayan zane kamar wata namiji ni fah abin nan ya ishe ni kawai zuba miki ido na yi dan ban da yanda zan yi da ke ne in ba haka ba wallahi babu abin da zai saka ni barin ki ki mayar da hankali akan wanan shirmen sai ka ce kina namiji"ta ida maganar tana haki dan abin na ƙular da ita ganin ga ni mace amma sha'awar zane zane ne kawai a gaba na

Abin mamaki madaɗin ta ga nayi fushi koh na masife ta kamar yanda na saba sai ta ga akasin haka sai ma murmushi da na mata na ce

"Toh baaba falmata yanzu faɗa kike min ne koh da nasiha koh shawara kike ba ni"ina mai dage mata gira ɗaya sama
Ai ganin ban masife ta ba sai ta matso kusa da ni da sauri ta ce yawwa yar gari kin ga abin da nake so da ke shine ki duba lamarin nan da kyau ki gani kina kyakyawa maman Abbu guda yayan ummi kuma matar babban yayan mu watarana ai bai kamata ace ki zabi zane zane ba a matsayin ambition din ki bayan kin san wannan kwakwalwar taki zata iya daukar karatun alƙali koh likita koh dan jarida gasu nan da dama amma kice sai wannan aikin mazan ai sai babban yaya ya fasa koh kib fi son haka ne?

Da mamaki na ce hala kin manta da cewa shi babban yayan ne ke supporting di na kuma me halaƙa ta da shi da zaki zauna kina kirawo min shi a matsayin wanda zan zama matar sa watarana??

Sai kuma ta yi shiru tana kokarin daidaita kanta dan ta manta cewa ta so yin suɓul da baka saboda shi kan shi yaya kabeer din bai fito ya faɗa ba kawai ita ce ta hango hakan sai ta yi shiru kafin ta fara magana

"Kin ga ni dai ki daina wannan abin wallahi bana ganin wani alkhairi a tattare da wannan mafarkin naki sai ma matsala a matsayi na na babbar kawar ki kuma ƴar uwar ki pls ki daina wannan abubuwan bai ma yi fitting din ki ba"..

Salma da ke jin mu dan shigowar ta kenan ta karaso ta zauna kusa da ni ta ce

"Pls Aisha ki ji maganar falmata wallahi koh ni nan bana son ki da aikin nan kawai ki fitar da ran ki akan shi kawai kin ji"?

Ganin da gaske so suke su gusar min da tunani na sai na nuna musu na amince dan kawai su bar ni ai ko sun yi murna sosai har da yar bushasha muka yi tuni falmata ta cire fegin da aka yi rubutu akan zane zanen da sunan kamfanin ta yage bayan ta faki idanuna na yi niman na yi haka na hakura na bari amma ƙudiri na na nan ban canza ba wato ƙudirin zamowa mai zane zane(painter)


Lokaci na ta tafiya a kwana a tashi babu wuya a wurin mai rai a yau ne aka haɗa gangamin taro na gani na faɗa inda ya tara da manyan masu faɗa a ji kama daga masu karamin karfi har izuwa manyan makarantar cike yake maƙil da jama'a ta kowani bangare ka juya jama'a ne ko ina sai hayaniya kasancewar ranar ce ranar ake yin taron yaye ɗalibai waɗanda suka kammala karatun su.

Ni,falmata da salma duk mun yi kyau dan in ka kalla sai ka ƙar

Yau din ba wata rana bace face ranar farin cikin mu ranar da tarihi ya dasu a rayuwar mu ranar da na ke wa laƙabi da ranar abubuwan mamaki domin kuwa a ranar da aka yaye mu muka karɓi kyaututukan mu a ranar ne na fuskanci abubuwan ban mamaki da na daɗe ina shawagi ban san da zaman su ba.

Bayan mun gama shagulgulan mu a makaranta a ranar muka rankayo muka dawo gida gabadaya daga mu har iyayen mu da yayyen mu illa yaya aqeeb da bai sami damar zuwa ba dan a ranar zai dawo daga ƙasar da yake karatu wato cyprus inda yake karantar psychiatrist(wato karatun kwakwalwa) wanda a yanzu yake mataki na uku toh shine yake cewa in har ya dawo toh zai haɗa mana wani yar liyafar gama makaranta wannan ne dalilin da ya sa muka mai uziri muka amince amma duk su yaya umar yaya kabeer da yaya ibrahim sun zo har ma da su ƴan matan gidan mu su hasina da ummi farida yan rigima da iyayi koh da suka zo sai wani rigima ake mana a dole ga ƴan matan sakandire dan ajin su biyu a lokacin yayin da suke shekaru goma shabiyu an cancaɗa ado kamar za'a gasar kyau tun da suka zo da su yaya ibrahim bata bari ya sake da falmata ba sai jan ra'ayin shi take yi tunda a yanzu ta fara gane cewa so ta ke yi ma yayan nata wanda hakan ya sa bata son kowa ya raɓe shi saboda tsananin kishin sa da take yi Abbu dai ido ya zuba mata dan yana matukar saka mata dokoki idan ba dan haka ba toh lallai da tuni ta daɗe da gaya mai cewa tana son shi dan har yanzu tunanin nata bai gama nuna ba

Mun dawo gida lafiya a inda aka ƙara ware mana lokaci akan mu ƙara shiryawa zuwa goba za'a mana liyafa wannan kuma dawainiyar yaya kabeer ne a cewar shi gudumuwar shi kenan mun yi farin ciki sosai yanda su salma suka so shine in zauna a gidan mu sha hiran mu tare amma nima a'a nace musu dan kuwa ga Abbu da nake so in zauna da shi mu sha hiran mu yau sosai ga su yaya ibrahim abokin taokana na da ummi ƴar kanwata da na lura tana tashen ƴanmatanci ina so mu zauna tare mu yi hira sosai kafin su koma makaranta ina so in karantar da ita abubuwa da dama game da rayuwar ta na ƴa mace da umma ta koya min a lokacin da nake kamar ta haka dai suka bar ni muka tafi gida muna ta zuba hira yayin da yaya ibrahim ke jan mu a motar ummi na daga gefen shi ni kuma da Abbu muna bayan su suna ta hirar su mukuma muna namu ni da Abbu

Isar mu gida na wuce na yi wanka ummi kuma ta dafa mana fast food ita da yayan nata da take ji da shi muka fito muka baje a saman wani babbar darduma muna ci muna hirar bayan rabuwa a nan ne nake jin Abbu ya canza mana gida ya gina wani gidan a can wuse zone 2 inda kuma bayan sati biyu zamu koma sabuwar gidan mu dan dama yaki sanar da ni ne saboda yana so sai na dawo sai ya kaini in gani murna na ya kasa boyuwa sosai na taya Abbu murna da samuwar alkhairi na ce Allah ya kaimu gobe sai mu tafi kafin mu tafi wurin liyafar da za'a shirya mana a gidan su falmata.

Haka muka raba daren muna ta hira kafin su Abbu da yaya ibrahim su tafi wurin bacci mu kuma muka cigaba da hirar mu har shabiyun dare kafin mu koma cikin dakin mu ni da ummi inda muka kara buɗe sabuwar babin hira ni da ita a inda nake tambayar ta ya karatun take ce min kalau

"Yaya Aisha kin san wani abu? "
Na ce mata a'a sai kin faɗa

"Yaya Aisha wani abu ke damu na a duk lokacin da naga yaya ibrahim da Yaya falmata suna hira wallahi ji nake kamar in shake ta in kuma ban yi hakan ba toh ranar kuka nake zama a ɗaki in yi tayi koh Husna ta tambaye ni bana sanin me zam gaya mata shi yasa na ce ke kadai zaki san abin da ke dami na yaya Aisha koh kin san me ke dami na? "

Na ji mamaki ban kuma ji mamaki na dan a ganina ummi tayi kankanuwa a ce har ta san wani abu mai suna so har ta zurfafa a ciki wanda kishin abin da take son yana kokarin fallasa a fili ba tare da kawaicin komai ba ta daya gefen ban ji mamaki ba saboda shakuwar da suka yi babba ne kuma shakuwa ce sa duk wanda ya gani zai yi tsammanin bayan ƴanuwantaka akwai wani abin amma rashin fallasa abin da ke damin ta yasa duk yanda zaka yi dan gano gaskiyar lamarin toh bazaka gano komai ba bayan shakuwar ƴanuwantakan.

Shirya kayana nake yi a wardrobe amma sai na dakata na zo kusa da ita na zauna ina kallon ta na wasu mintuna kafin in dangana da rike hannunta cikim nawa ina kallon ta ido cikin ido

"Hmmm ummi idan na fahimce ki da kyau so kike kice min a duk lokacin da yaya ibrahim da falmata suke tare haushin su kike ji? "

Ta yi saurin daga min kai cikin zakuwa

"Ummi tun yaushe hakan ya fara"?

Dan ƙasake ta yi kafin ta ce tun tana primary school

Waro idanuwana na yi sosai na ce

"Kina nufin tun kina yar ficikan ki kenan"sai na bata kunya sai ta sunkuyar da kai tace eh

Sai kuma ta bani tausayi ganin tun tana ƴar kankanuwar ta har ta faɗa a tafkin soyayya wanda ni kaina da nake yayar ta ban taɓa yi ba koh da wasa

Rungume ta nayi na ce
  "Ummi da wa kike son ganin yaya ibrahim"

A hanzarce ta ce in ban da ke bana son ganin shi da kowa

Sai ta bani dariya har na dara ganin wautar ta ƙarara nace ummi koh dai kishi kike yi!?

"Yaya Aisha ni ban sani ba shiyasa nake tambayar ki"

Dama na san bazata sanin ba shi yasa na mata tambayar amma saboda ina so hankalin ta ya kwanta ta daina wannan shirmen sai na ce kar ki damu ƙanwata daga ke sai yaya ibrahim kin ji?

Da murna ta dago ta ce min da gaske yaya Aisha?

"Uhumm na taɓa gaya miki karya ne"?ta girgiza kan ta nace toh kin gani yanzu dare ya ja ki bari har gobe sai mu cigaba da hirar mu koh?

"Toh yaya Aisha good night" na yi kissing cheeks din t kafin in kashe mana fitila ta rigani bacci saboda na kasa rintsawa ina tunanin ƙurar da zai tashi in ummi ta fi haka girma da wayo anya kishi bazai janyo mata matsala ba kuwa ga shi ina tunanin yanda zan yi da soyayyar kawata da yaya na dan kuwa sun yi nisa har iyaye sun sani ga kanwata tana neman janyo mana wani abin ohh y salam da wanne zan ji kanwata zan taimaka ko kuma kawata zan bari ta mallaki abin da kanwata mafi soyuwa agare ni ta ke burin soda kauna!!!juye juye nake ta yi na kasa bacci na kasa nemo mafita......

  *_🍒S,Ibraheem🍒_*

Continue Reading

You'll Also Like

65.7K 5.1K 40
Dad! Mi... ji.. n... UMAIMAH.. ne! ****ta Yaya musaki yasan soyayyah? Wannan wani salon munafurcin ne!
1M 22.4K 58
A 'slut' of a 21 year old Nidhi is married to the disabled thakur, who is paralysed below his waist. What will happen when her sexual frustration wil...
178K 2.3K 30
mikha and aiah found out na mag tita sila!!
194M 4.6M 100
[COMPLETE][EDITING] Ace Hernandez, the Mafia King, known as the Devil. Sofia Diaz, known as an angel. The two are arranged to be married, forced by...