TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 44

4.5K 348 65
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

  Wattpad @ 68billygaladanchi.

                 44

Har suka isa masauki be k'arayin mata magana ba itama kuma haka, seda suka isa d'akin suka zauna sannan ta kallleshi

"Abu Hidar kace zaka kaini gunsu mom sekuma na ganmu anan?" Hancinta yaja

"Kisa rantsuwa kema bakifi son nan akan cen ba?" Rufe fuskar ta tae da tafukan hannayenta

"Allah ni inaso inga mom" Janyota yae jikin k'irjinsa

"To maza sanya hijab d'inki kizo muje na miyar dake gun mom" Kallon agogon hannunta tae

"Noo yanzu after 11 gobe da safe dai semuje ko" d'agata yae gabad'aya ya shiga zagayar d'akin da ita, dariya tashigayi ba k'akk'autawa, ita mamakin sa sosai takeyi wasu lokutan, yanzu yanzu zakagan shi fuska ba annuri yanzu yanzu kuma zakaga ya washe kaman ba shiba, seda ya gaji ya direta akan gadon yana shima ya kwanta yana mayar da numfarfashi

"Yarinya karki zama k'atuwa fa wannan nauyin haka, idan har kika k'ara bazan miki doki ba" Murmushi kurun tayi, Daganan kuma zance ya sauya suka shiga yin hidimar d'ebewa juna kewa, mu'az be gushe ba sedabya tabbatar ya saukarwa matarshi gajiyar daya tara mata, yau taji sauk'i kam ba laifi tayi garau da ita, seda ya tabbatar ya kimtsa ta da kanshi, taci ta k'oshi sannan suka kwanta b'acci, yau sun kasance cikin farin ciki dukkansu, meenal Anci kaza da me siyan kazar kuma anyi baccin dad'i.

**********
    Yauma kamar kullum toshe da hanci takecin chips d'in da plantain dukda bawani k'amshin dabanne dasu ba amma dazaran ta bari k'amshin ya haye mata kai toko tabbas setaga haza dan duk seta harar da abinda taci, kallonta yakeyi cikeda tausayi shidai ciki ba abinda baya zuwa dashi, ita kuma kalar nata laulayin kenan salma ba haka tayi ba sam duka haihuwar ta uku, ko wanne da salon sa amma bame wahala kamar Meenal, yakula cikin ma zallar sha'awa yake sanya mata, baiwar Allah gashi bata ma gama sanin kan abinba, sedabta gama cin abinci sannan ta kalleshi tana janye Pack d'in, murmushi ya sakar mata tace

"Kallon na miye?" Hannunta ya kamo

"Na kwad'ayi ne" batace masa komai ba se murmushin dai, seda ta wanke hannunta da bakinta sannan ta dawo ta nutsu yanayin sa ya nuna mata tsaf magana yake so suyi

"Meenaly zanje masarauta tare da Abbana da ummiena da yaranki, zamuje ne muyi gabatar da Abba amatsayin wanda ya b'ata kuma muka ganshi daga baya koda yake bazamu wa kowa wannan maganar ba ta yanda aka sameshi kamar dai yanda na gaya miki jiya, yin baya baya ko b'oyo akan abubuwa baze tab'a bamu nasara akan mak'iyan mu ba, harga Allah naso naje dake kema masarauta amma kuma ina tsoron kar wani abun cutarwa yazo miki, sabida haka na yanke shawarar ki zauna abinki agida gunsu mom,zan baki tsaro me yawa inshaa Allah kafin na tafi" kallon sa takeyi tunda ya fara magana seda taji yayi shiru alamar ya gama sannan tace

"Su Hidar, fa baka tsoron wani abu ya same su?" Murmushi yae

"To ai suma dan dole sesun je ne meenal, yanada kyau kowa nawa ya hallara"

"Niba koman ka bace kenan Takawa, rashin son da kakemun haryakai ace kana wareni acikin kowa naka? Kokana manta cewar nid'in nan matar ka ce ta sunna inada dukkan hakk'in daya dace akanka, awurina nidakai ya dace ace mu gudu tare mu kuma tsira tare" Nisawa yae

"Karkice haka meenaly meyakawo zancen rashin so, nida bakina nace dake bana sonki, kinga ke kinada juna biyu ga cikin yanzu ne ma ya shiga satinsa na farko acikin watanni uku ko fad'uwar gaba ma wani abinne bamusan mezeje yazo ba koda bama fatan komai se Alheri" Turo bakinta tae cikin takaici

"Ehm nidai koma me zakace k'afata k'afarka" Murmushi yae

"To Naji amma banaso ki nunawa Nusy kin gane komai game da ita, k'aramar wayar dakika barmun ma tanata faman kira bandai d'agaba sabida bana buk'atar damuwar ta" jinjina masa kansa tae daga nan suka d'auki hanyar zuwa gidan mom.

***********
     Sojoji ne ke gaban motocin su Takawa yayinda tasun take tsakiya shida sawunsa, Abba kuwa yana cen tare da Ummie da jikokin sa yasha shiri irin na sarki yayi kyau matuk'a yayi k'iba sosai kaman bashi ba, dogon zama akeyi a fada ana maganar d'aura yarima fu'ad akan mulki tunda yake anji shiru, waziri ya kasa ya tsare akan hakan, wasu sun aminta da wannan wasu kuma suna ganin rashin dacewar yin hakan abinda ko sati d'aya ba'a gama rufawa da faruwar shi babu tabbacin baze dawo ba, Sarkin fada ne ya zube agaban Sarki me murabus

"Allah yabaka yawan rai yin hakan aiba laifi bane ba, sabida bama zauna ba jagora ba,kaikuma kace bazaka dawo ba, kuma ai rik'on K'warya ne idan Allah yasa ya dawo seya janye ya bashi wurin shi tunda game wuri yazo ai me tabarma dole ya nad'e ko?" Bece k'ala ba se madawaki ne ya k'ara cewa

"Kuma Ranka ya dad'e wannan masarautar ai bazamu bari tarihi ya maimaita kansa ba, haka akayi lokacin b'atan sarki jalal wata d'aya da akayi ba kowa akan mulki sega takardar gaggawa daga fadar sarkin musulmi akan adadin kwanakin daya bayar na gargad'i akan rad'a wani sarkin, yanzu kuwa bazamu zuba ido hakan ya faru ba". Har lokacin sarki meyi magana ba se magatakarda ne yace

"Bana tunanin akwai abinda ze tsayar dashi daga dawowa daya samu sake, tunda yake mahaifin sa wayar gari kurin mukayi bamu ganshi ba, shi kuma a idon duniya aka sace shi inaga wannan aikine na wasu miyagun cikinmu, kuma dazamu  bada lokaci da tabbas babu abinda ze hanawa Takawa bayyana inshaa Allah" Galadima ma seya wurga tashi maganar

"Allah ya baka yawan rai ina ga ai ko bayan Takawa sarki Jalal yanada yaro daya haifa da babbar kuyangar sa mariya me suna Ahmad, zamtowar sa d'an kuyanga tabbas ya hana masa gadar sarki na al'ada amma baze hana masa zama akan kujerar ba koda na rik'on k'warya ne tunda yake shine babba asaman Takawan ma" Kowa da abinda yake furtawa yayinda sarki yae k'us yana saurarar su, suna cikin xuba zantuttuka Tawagar Takawa da Sarki jalal suka bayyana a wanan babbar fad'a me girman gaske ciki kuwa hadda sojojin takawa, Babu wanda ya ankare da sarki Jalal se waziri, gumi ce ta fara tsatsafo masa ya soma zungurin Galadima dake kusa dashi, Sarki Ra'uf kuwa mik'ewa yae ya baiwa sarki Jalal kujera inda lokaci d'aya ya zauna yana murmushin manya, mik'ewa kowa yayi a fadar kowa ya gama shaidashi sannan suka k'ara zube cikeda mamaki, yau Takawa shigar sojoji ne ajikin sa fuskar nan babu annuri ko kad'an, bayan sun gama gaishe gaishen su sarki Ra'uf ya soma bayani kamar haka

"Kamar yanda kowanne dake wurin nan ya shaida yaya na Abduljalal shine sarkin wannan garin,haka zalika neman da akai masa aka rasa ne ya bani xama akan kujerar sa da sunan rik'on k'warya, da yawa daga cikinku sun shaida yanda nake neman sa har rana irin n tayau, to cikin ikon Allah watannin baya mun ganshi acikin wani mugun mawuyacin hali to dalilin daya sanya ban gayawa kowa ba gudun kada wanda suka cutar dashi a farko su k'ara yunk'urin cutar dashi yanzu kuwa ya samu lapia gashinan kaman yanda kuke gani, sabida haka me wuri yazo me tabarma dolen sane ya kwashe tabarmar sa" Kabbara wurin ya d'auka suka shiga zubo masa gaisuwa cikin mulki da isa kaman baya son magana ya furta

"Kamar yanda yae bayani hakan ce ta kasance, bin cike akan inda aka kaini sanda aka saceni dakuma sanya hannun waye da waye ze fara daga yanzu inshaa Allah" Shiru fadar ta d'auka kowa da abinda yake sak'awa a ranshi, fiye da rabin mambobin cabinet na sarki sun shiga rud'ani yayinda wasu ke matuk'ar farin cikim bayyanar sa musamman a wannan lokacin da azzaluman masarautar ke shirin aiwatar da mugun nufin su, kowa ya gama tofa albarkacin bakinsa kanya kuma cewa

"Na dakatar da waziri daga aikinsa,mulkinsa da muk'amin sa, ina kuma bada umarnin a sanyashi a kurkukun gidan sa har se sanda nida kaina nayi buk'atar ganinsa, Bugu da k'ari ban yarda kaiwa waziri ziyara ba ban kuma yarda shi ya kaiwa wani ba" Tsif fada tayi waziri se muzurai yake yana zare idonshi sekce wanda yae k'arya, haka suka kammala tattauna maganganu masu yawa kafin daga bisani fada ta tashi akan se washe gari.

************
     Tunda suka zauna meenal se faman cin dabino take abinta bata cewa nusy ci kanky ba, seda nusyn taga zaman shirun ya isheta ta kalli Meenal

"Ranki ya dad'e yau lafiya kuwa? Naga duk bakya cikin walwalarki" Tataccen ruwan kwakwar dake gaban ta a cup na glass ta d'auka ta kurb'a ta ajiye, yamutsa fuska tayi kanta ce

"Nusy ina cikin tashin hankali mara misaltuwa, ci bayan baya ya sameni na rasa inda zanbi inga haske" Cikin tausayi nusyn tace

"Subhanallah Ranki ya dad'e menene damuwarki haka?" sunkuyawa tae sosai kusa da Nusy

"Nusy dawowar wannan tsohon babban ci baya ne agareni wlhy, yanzu daga sarauniya kuma na kuma dawowa wani wai sawun takawa, yo wane takawan rayuwar da akeyi a furgice, kaida ka tsufa kyau ai daka dawo ka nutsu gefe d'aya kabarwa masu k'uruciya suyi mulki mana kome ke kike gani?" Nisawa nusaiba tayi

"Nima dai sabida kurun karna fad'a ne aga bekena, amma wlh nayi wannan tunanin, nace uwargidana kuma mulki yayi k'asa, shi wannan dattijon ya kyauta kenan ya dawo kuma da rana tsaka ya karb'e mulkin?" Tura d'ankwalin kanta baya tayi ta shafi goshin ta

"Nifa wlhy Nusaiba da inada yanda zanyi baze k'ara kwana koda d'aya bane ba aduniyar nan, kashe shi zansa ayi in koma kan muk'ami na daya dace dani kome kika ce" Murmushi Nusy tayi

"Akwai wanda ze taimaka mana in hakan shine buk'atar ki ranki ya dad'e" Murmushi tayi

"To waye wannan? Nifa bana son magana ta wuce tsakaninmu  sabida ban yarda da kowa ba idan bake ba, kinsan mutane fa" Murmushin mugunta tayi tace

"Asirinki baze tab'a tonuwa ba har abada, ba wani bane zeyi aikin se mahaifina Galadiman garin nan, sabida tun farko su basa sonsa sunama da hannu acikin b'atan sa na farko, kuma kinji d'an latsin hammata cewa yake zeyi bincike akan su, Abbana yace dani zasu tabbatar sun kashe sa kafin ya tona musu asiri a masarautar nan, sabida haka dama kurun zaki bayar da hanyoyi masu sauk'i dazamu bi a aiwatar da nufin mu" Murmushin jin dad'i Meenal tayi

"Yaya za'ayi in gana da Galadiman inyaso sena san abinda suka shirya da yanda zamu b'ullowa al'amarin acikin hikima"

"Aibama shi kad'ai bane ingaya miki ranki ya dad'e, kinga sarkin Aska ma yana ciki, shikuma sarkin ya gano sharrin daya k'ullawa sarki mu'az kafin ya rasu na had'a baki da sarauniya daurama ana manna wa sauran matansa maganin hana d'aukar ciki har yae ik'irarin hukintashi dacin amanar masarauta da sarki bayan ya aminta dashi, wannan ne ya sanya ya shiga cikin masu neman ran sarkin gadan gadan, Sarkinne yanda kika san shiya haifeki ranki ya dad'e hikimominsa masu yawa ne" Dafe kai Meenal tae cikin jimami

"Kice kenan kowa wannan dawowar tashi bata mai dad'i ba kamar ni, to ni yanzu banda su se waye wanda ze taimaka mana ne wai?" Murmushi Nusy tayi

"Ranki ya dad'e zafin nema ai baya kawo samu, ki kwantar da hankalinki da sannu komai ze zama normal, zaki samu abinda kikeso, kowa ma ze samu yanda yakeso,masarautar nan ta Hankaka kowa da kika gani akwai wani mugun nufi a zuciyar sa, matsalar dakika samu tun farko shine tinkarar matsalokinta da gaggawa da kinbi a hankali harki gama sanin kowa da halayyar sa, dan yanzu Allah ne kad'ai yasan wanda kika yarda dashi  yake k'ok'arin cutar dake sedai kinyi taka tsantsan, shi kanshi sarki Jalal d'in wlhy idan kowa akan sa yake sannan bashida tabbacin kaiwa ko gobe ne daga yanzu" Jinjina kanta tayi alamar gamsuwa

"Hakane wani zubin sekaga kamar kanada wayo amma bakada labarin amfika, har yanzu ban kama wani dacin amanata ba amma gaf sosai nake da kamawa d'in dankuwa bazan lamunci iskanci ba" Wani mayaudarin murmushi Nusy tae

"Allah yasa ki samu damar ganewa kafin lokaci ya k'ure miki" kallon sosai meenal ta mata takula magana take mata me harshen damo, irin abin nan da bahaushe ke cewa kukan kurciya ma jawabine me hankali kan gane, wani malalacin murmushi ta sake

"Ban gane ba?" Ta furta tana kallonta ido cikin ido

"Ea mana Ranki ya dad'e, idan me nufin cutar dakai ya lafe baka ankare ba seda ya aikata b'arna agareka ai kinga anci  baya, fatan dai duk wani munafiki kisan da zaman sa kafin ya miki halin" Dariya yanzu kam meenal tayi med'an sauti

"Gaskia kam kinada gaskia, to Allah ya karemu baki d'aya, aini dake kad'ai na yarda bari kiji ko Takawa ban yadda dashi ba bare kowa yayi saura"  Mayaudarin murnushi Nusy tayi

"Allah yaja zamanin ki aike tawace, bazan tab'a cin amanar kiba har abada, kome zaki zama arayuwa ina bayan ki, niko nace wai ranki ya dad'e ina labarin sarauniya hassy? Nasan dai kece kika sace ta, to har yanzu shiru kakeji sekace malam yaci shirwa" Tab'e baki tayi

"Har yanzu har gobe bansake samun labari akan taba, kinsan Takawa shine ya karb'e ta a hannu na, toki sani be k'ara tashin mun maganar taba amma karki damu zan lalubo mana info akanta kinji" jinjina kanta tayi kafin ta mik'e tsaye

"Ranki ya dad'e nizan koma, akwai babban aiki agaban mu" Haka sukayi sallama meenal ta zauna tana kurb'ar lemun ta tana murmushin kinma raina ni, wato Nusy wata sokuwa take kallon ta ko, aiki sukewa juna na mugunta dan bazata yarda wannan karuwar ta kada ita akan komai ba seta wulak'anta Nusy fiye da tunanin masarautar ta hankaka. 

*********
   K'ura mata ido yae yana nazarin ta tayi fari sosai, farin cikin idanta ma ya k'ara haske sosai yayinda bak'in ya k'ara duhu, tayi kyau matuk'a, kumatun nan ya ciko fam, yanda take ta faman shan chocolate d'in sekace wata k'aramar yarinya se tab'ara takeyi, wannan cikin Na meenaly ya sanyata shegen kwad'ayi dagani yaron se yayi k'wad'ayi sosai, jin alamun idanu suna yawo ajikinta ya sanya ta d'ago ta kallesa murmushi ta dire masa

"Malam yadai kabini da ido" murmushi shima yae

"My Meenaly naga kinyi b'ulb'ul ne se uban kwad'ayi, bakya tsoron chocolate ya sanya baby ya miki k'ato ne kisha wahalan haihuwa?" Tab'e baki tayi

"Canfi ne kawai, ina son abu bazan tab'a cutar da kai na, idan babu ne sena hak'ura amma akwai senaci iya cina ba ruwana" Murmushi yae shima

"Menene kika gano game da Nusy baki sanar dani ba?" Turo baki tayi

"Kai Allah kuwan Abu Hidar sena gayaka da ummi, baka tab'a mun magana me muhimmanci se inacin kayan dad'i na, yanzu kuma bazaka bari sena nutsu ba mui maganar" Girgiza kanshi yashigayi da murmushi d'auke a fuskar sa

"Meenaly Rigima, zanje gun me martaba ne, kuma kin sani anmai bayani akan ke zakiyi aikin ta hanyar Nusaiba, gwara inje masa da labari me dad'i kome kika gani?" Murmushi tayi ta ajiye chocolate d'in akan olate dake gabanta ta tashi ta wanko hannunta ta dawo, zaman nutsuwa tae tace

"Hasashen ka gaskia ne, mahaifin ta yana daga cikin masu so su kashe sarki tun farko, shida sarkin aska, tace suna da yawa amma iya kar wannan ta furta kanta tsaye, idan na matsa mata da tambaya zata harbo jirgin amma sena mata banza nadai buk'aci ganawa da galadiman kurun, dole zan ji ta bakin sa, amma tabbas susu biyun nan dasu aciki, sedai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba.

Kallonta ta yayi bece komai ba ganin haka taci gaba

"Nusy fa bala'i ce, wani auto recorder ta d'ana mun ajikin zoben hannu na, batasan nasan abun ba, a nufinta idan na gama zayyanewa waninta wasu muhimman infor setazo ta cire abunta se an sakashi a system akejin komai, ina kallonta sanda tayi komai, zoben a hannu na yake itama tayi wowta, nayi tunanin in cillar dashi amma kuma sena fasa, na zare shi na b'oye zoben a wani wuri daban, se yau nakeso in sakashi a hannu in zauna da malmo mu zanta kamar da gaske kisan na sarki zan saka ayi dan itama tana zargin wani abu game dani kamar kona fahimci munafurcin ta ko wani abu me kamada hakan, tana dai fita na cire zoben na b'oye" murmushi yae

"Nusy batada mutunci wlhy, bazaka tab'a kwashewa lafiya da itaba, yusuf ma ya gayamun cewar sun gama shiryawa da ita akan idan tasamu dama sharrin kisa zata lik'a miki a kasheki kowa ya huta" murmushi tayi

"Shima yousouf d'in ka yarda dashi kenan Takawa anya ba kuskure bane?" D'age kafad'un sa yae

"Meenal kenan, kinsan fa kowa da matsalar shi, yusuf kud'i ne matsalar sa ko ubnsa ze iya cutarwa akn kud'i da yarda nayi dashi ba aikin kud'i yakemun kuma 25% na bashi akan se komai yayi daidai zan bashi remaining 75% kinga kuwa yanda yafi son kud'i da ranshi baze tona mana asiri ba, idan ma ya tona tokuwa a kud'in shi, kuma ko b'ata wannan shirin yayi munada plan B, babu wanda ze iya wannan aikin meenaly se yusuf, Bincikena ya nunamun aduk duniyar nan babu wanda Nusy ta aminta dashi sama da yusuf, ko cikin data zubar aishine ya taimaketa akan shi" Nisawa tayi

"Ina maka fatan Alheri aduk inda kake Takawa, Allah ya d'auraka akan mak'iyan ka Mijina, Allah ya baka fikafikai masu tashi kai musu zarra, mak'iyanka fadawan ka Mijina, ina hango haske acikin al'amuranka Alkhairin Allah ya bika a duk inda kake mijina" Hannunta ya kamo ya zauna yanzu kam kusa da ita sosai

"My meenal yau ina wannan lip glose d'in me dad'i, a shafa mun mana in lashe" Murmushi tayi cikeda jin kunyar kalmar sa ta k'arshe wai ze lashe tace

"Bakajin kunyana ma kake cewa haka, kuma ni naqi wayon yanda kakeyi idan na saka kaman zaka tafi da lips d'ina, sedai idan kai na shafa maka a naka lips kayita lasa" Dariya yae wacce bata tab'a ganin yayi irin taba, ita fa harga Allah mamakin sa take wai dama yana dariya irin haka yadda k'wallan sa, yafi 1 mnt kafin ya tsagaita da dariyar ya kalleta

"My Meenal kinsan Allah ina sonki so bana wasaba, wasu lokutan ko bama tare idan na tunaki senayita dariya, ke d'innan character ce ta sosai sosai d'innan, yanzu dan Allah idan na barki seki sakamun a baki da gaske?" Murmushi tayi

"Wlhy shafama zanyi niba ruwana, ina zak'in kakeso kayita lasa?" Ya tsansa yakai ya shafi lips d'inta

"To ai babyna taste d'in daga nan yake, sirrin yana daga wannan kyawawan lips naki masu laushi da kyau, ni bana ta wani shi kurun k'amshin sa na mint flavor idan ya had'e da k'amshin bakin kinnan me dad'i seya kusa sumar dani ma" Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskar ta tana murmushi, hannunsa ya sanya ya janye hannunta data rufe fuskar ta dashi

"Wayaga 'yan matan Mu'az wai nan kunyar she haka" tabare fuska tayi

"Allah Takawa kaikam kana bani kunya, dan Allah ni kazoma ka tafi abunka" rungumarta yae dama kuma dukkansu a k'asa suke zaune a carpet, kwanta yae tana jikinsa, ta dawo saman sa shi yana kwance a k'asa, hannunsa ya sanya yana jan tsinin hancinta

"Wata ta rantse batafiso mu kwana mu wuni a haka ba, ni ake nunawa ko oho bayan nasan cewar  har zazzab'in rashin ganina kike" K'irjinsa ta kaiwa duka sannan ta cura fuskar ta aciki

"Allah kuwan ni bance ba" cakulkuli ya hau yi mata suka shiga kwasar dariya suna mulmula akan carpet d'in.

~kuci gaba da bibiyar alqalamina donjin yanda zamu gano mu kuma magance mugwayen masarautar hankaka, insha Allah daga nan tafiyar bame tsawo bace ba, takusa zuwa k'arshe da yardar Allah~.

Mom Nu'aiym.

Continue Reading

You'll Also Like

153K 5.6K 26
فيصل بحده وعصبيه نطق: ان ماخذيتك وربيتك ماكون ولد محمد الوجد ببرود وعناد : ان مارفضتك ماكون بنت تركي !
5.3M 46.3K 57
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...
82.8K 2.9K 72
I do not own any of the characters. Y/n are a supe. But not a famous one, that didn't work out. Now you are one of the sevens PAs. Maybe, briefly Th...
149K 14.8K 30
"သူက သူစိမ်းမှ မဟုတ်တာ..." "..............." "အဟင်း..ငယ်သူငယ်ချင်းလို့ပြောရမလား..အတန်းတူတက်ခဲ့ဖူးတဲ့ အတန်းဖော်လို့ ပြောရမလား...ဒါမှမဟုတ်..ရန်သူတွေလို...