TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

43

3.4K 329 34
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad 68billygaladanchi

       43

Bekosan wainar da akae tonawa ba, abokin tafiya ne ya kirashi a waya bayan yaga tafita da k'afa, dama yae wlcm back da wannan ma ya samu daman kiran Abokin tafiya dayike duka contact nashi suna nan acikin gmail nashi, Ringing wayar tayi harta yanke bejiba, se karo na biyu ya d'agota cikeda baccin daya masa nauyi, tsaki yaja ganin Abokin tafiya ne, ya k'ara kifar da wayar kurin batare daya d'aga ba, ganin hakan baze yiyu ba ya sanyashi bin bayanta, yana kallo tahau adaidaita da wannan yabi bayanta. Yana cikin tashan sanda tahau motar abuja kuma lokacin saura mutum biyu yana zaune a motarsa har suka cika suka tashi har lokacin yana k'ok'arin kiran Takawa amma baya d'agawa, dafe kanshi yae tunda yake yaga layin abuja tahau mota kuma motar abuja ce watak'il Takawan yasan da tafiyar amma kuma ze bari tahau motar kasuwa ne? Ya tambayi kanshi, watak'il kuma b'adda kama yakeso tayi shisa, da wannan tunanin shima ya koma masauki yaci gaba da sabgogin sa, Takawa be farka ba se 11, sannan kuma wankansa kurun yayi 40 mns, yasha  mamakin rashin ganin ta, amma tunawa da yae jiya ma ta fita ya sanya yae tunanin tafita ne ta siyo wani abun, order abincin yae yaci, bashi yabar d'akin ba se wuraren 1 bayan yayi alwala yafita domin gabatar da salla yakuma fita, a reception yabar key akan idan tashigo abata, haka yashiga sabgoginsa bayan idar da salla,abokin tafiya yanaso ya masa maganar ta amma seyaga tunda har aka d'auki wannan lokacin be tambayeta ba tokuwa tabbas yasan da zancen tafiyar da wannan ya gimtse bakinsa kurun sabida ko maganar msd col d'inma takawa be masa ba.

***********
   Tunda taje gidan Al-Ameen tak'i tayi magana, banda kuka babu abinda takewa matar sa, gashi baya gari kwata kwata,  maman humaira (matar Al-ameen) tashiga tashin hankali matuk'a, ga wayar gogan akashe, da k'yar ta lallab'a Meenal d'in take d'an tsakura mata dangane da alk'awarin dashi Takawan ya mata na saki sannan kuma ita bazata zauna dashiba danba sonta yake ba" Nisawa Maman humaira tai

"Waike meenal mesa bakyaji ne? Har se yaushe zaki san ciwon kanki, ke yanzu tsabar bakida hankali seki zubar da cikin ki akan wani shirmen mijinki baya sonki, ina ke kina sonsa?" Kallon ta tayi ta k'ara turo baki

"Yo anty dan ina sansa seya rik'amun wulak'anci?, yoko ina sansa ai zan iya hak'ura da shi tunda na hakura da yaa muh'd niba namijin daya kaimun dole" Murmushin takaici tayi

"Yanzu gayamun fushin menene ya kawoki nan gidan batare da izinin mijinki ba?" Share k'wallan daya zubo mata  tayi sannan cikin kunya tace

"Anty fa kullum dan yaga k'amshin jikinsa nakeso seya rik'a guduna, kuma seya zo ya dinga mun abubuwan iskanci seyaga nazo inaso, bazan iya hak'ura ba seya tashi ya k'yaleni kuma marana ya murd'emun bana ma iya tsayuwa yae fuska kaman be gani ba tsabar mugunta, jiya ma cemun yae wai idan bazan dena zancen zubda cikin ba haka zeyita horani, jiya shine naga zan mutu abanza sena tahowata inda baze ganni ba sam" Murmushi maman humaira tayi

"Gaskia nan kam yanada laifi anan, sam shikuwa ba'a yiwa mace haka musamman me ciki, wannan kawai aiseya b'arar da cikin kiyi hak'uri wasu mazan suna sani suke maka abu dan kawai suga k'arshen ka, kema kinyi kuskure mune muke d'aukar ciki musha wahalar shi irin wannan wahalar dakikesha yanzu komafi amma zakiga mazan wani zubin harse su fimu son 'ya'yan gani yake kamar k'arshen k'iyayya kenan ki nuna masa bakya buk'atar wani jini a tsakanin ku yazo duniya shiyasa nake ga yake miki horo irin wannan"  Sadda kanta tayi a k'asa zuciyar ta tana mata suya

"Nito bazan bari ma yasan ina nan d'in ba, kosu mom bazasu san inda nake ba, seya musu bayanin cewar latsani yakeyi na gudu dan kar ya kasheni" Dariya Maman humaira tae

"Ki nutsu mana Meenal, zaki tashi hankalin ki ne kawai ki tashi na iyayenki, rashin sanin inda kike aiba shi bane horo me kyau dazaki masa, horon dazamu masa aiba yanzu bama se nan gaba" B'ata fuska tayi

"Anty na rok'eki da Allah ki adana ni anan se bayan kwana biyu, kinga dai dukkanin abinda kikace inyi bana miki musu ko, to dan Allah ki taimaka mun da wannan bayan kwana biyu naje gidan" Jinjina kanta tae

"Toh shi kenan idan yayanki yazo kinsan dai halin fad'anshi, sekiyita hak'uri da abinda zece mun nidake, sannan zancen cikin nan karna k'arajin kina maganar zubar wa wlhy kinji na rantse ko a zuci karna k'araji" hawayen idanta ta d'auke da d'an yatsan ta

"Bazan k'ara ba Anty,har maganar sakin ma bazan k'araba, amma wlhy sena rama wannan wulakancin guda biyu, na farko wannan latsani dayake yana barina da ciwon ciki kuma wlhy senaci uban jakadiyar sa me mammatsa k'afa yana lumshe ido dan samun wuri" Dariya taso k'wacewa maman humaira tabbas kuruciya tana yawo akan wannan baiwar Allah, ga kishi amma batamasan meye ba, bazata iya cewa ga inda ke mata ciwo ba....

"Gaskia semun rama, har wata jakadiya ce dashi me masa tausa, lallai dani zataci gidan su, yanzu dai ki tashi kiyi wanka ki sauya kaya ki saka nawa kizo kici abinci se bacci ko?" Murmushi tayi tamike, haka tazo tana cin abincin tana toshe hanci batason warin shi anty tayi dariya lallai yau manya ne da ciki kenan🤣🤣🤣.

*************
    Beko waiwayi hotel d'inba se wuraren 5 na yamma likis, gashi ya gaji ba abinda yake buk'ata irin yaci ya kwanta tinda ya fita yake tsaye akan wasu harkokin sa, matar daya baiwa key tagama duty harta tashi ta barwa wanda ya karbi duty key nasu, beko tambaya ba yasan meenal na d'akin koda yaje ya tura a rufe, beyi mamakin komai ba ya soma knocking kusan 10 mns yana tsaye agun, ganin kamar kota k'ara fitane ya sanyashi juyawa zuwa reception d'in, karb'an key yae ya koma yana tunanin tafita ne bayan ta dawo amma mesa take yawo ne irin haka? Bata tsoron wani ya ganta mesa ne yanzu meenl bataji wai? Tsaki yaja yashige wanka, yanayin d'akin ya nuna masa bata dawo ba sam, har dusbing ya duba bega shirgin kayan takeaway na breakfast datayi ba kurn dai yaga na jiya da dare kenan cleaners ma basu zoba, to ina meenaly ta shiga ne? Ya tambayi kansa, dama rigar suit ce ajikinsa ita kawai ya cire ya juya zuwa reception da hanzarin sa, yayi tambaya akan meenal amma sunce basu ganta ba, yafa shiga rud'u lokaci d'aya ya tashi hankalin hotel d'in, ganin ze musu bori ya sanya manager yasa aka lalubo cctv, tu  wuraren 8 am data fita bata dawo ba sam babu ita acikin masu shigowa, idan ma wani abin ne to kuwa da k'afarta tafita kuma ba'a wurn su ya same taba. Abokin Tafiya yakira yazo shi kuma ya sameshi har d'akin sa, hannayensa ya zuba duka a aljihunsa beko cire madubin idan sa ba dake fari k'al ya k'urawa Abokin Tafiya ido ya kasa furta komai se kallonsa yake shikuma yana zaune asaman kujera k'waya d'aya jal dake d'akin shima kallon Takawa yake yana nazarin sa, ba abokin sa bane ba yaron sane amma tun suna yara yake masa hidima suke tare, yasan koda ya tambayeshi bawai amsa ze bashi ba dan bega dama ba, dan haka ya k'ura masa ido kurin yana nazarin yanayin sa har kusan mintun goma sha uku, harya cire tsammanin ze masa magana sekuma yaji yace

"Bangan taba fa, cctv ya nuna tun 8:am tafita daga nan" hannayen sarkin mota dake kan saman kujerar ya tattaro gu d'aya

"Wacece Ranka ya dad'e?"  Sajensa yakaiwa cafka zuwa gemunsa yaja gashin gemun da k'arfi kaman ze cirge shi kan yace

"Ameena mana sarauniya Ameena bansan ina taje ba wlhy" Cikin takaici yace

"Takawa kai d'inne nima idan abubuwan ka suka motsa seka rik'a tsoratani dajin ikon kan nan, nifa naga fitarta na dinga kiranka awaya kak'i d'aga wa, nazo nabita har tasha dataje batasan ina binta ba, naga tahau kotar abuja, tunkan motar ya tashi naci gaba da kiranka baka d'aga ba, haka na barta ta wuce abunta, bayan kafito ko maganar msd col bakamun ba banji kana neman taba, shine nayi tunanin kasan da fitar tata na kame bakina" Bangon dake kusa dashi yakaiwa mugun duka cikin k'araji

"Haba Auwal!!! Yaya kasan had'arin damuke ciki zakayi wasa da rayuwar meenal, sena d'auki waya ka tsayar da ita mana kokazo ka bubbga mun" Girgiza kanshi yae dama yasani haka zata faru

"Muje muje muje, tashi muje Abokin Tafiya" Ba halin tambayar inda zasu, seda suka hau titi sosai yace dashi
."Abuja" a tak'aice, beko ce masa komai ba shima ya d'auki hanyar abuja.

    Bayan isha sakaliya suka dira, kai tsaye gidan su meenal ya wuce, bayan gaishe gaishe yaje part d'in mahaifan shi dan har yanzu agidan suke b'uya, ya duba jikin mahaifiyarsa da yaransa, seda yajanyo yaransa waje yace da Hidar

"Hidare dare n mom, jeka part d'insu ka kiramun momynka" cikeda zak'uwa yaron ya kalleshi

"Dad mom ma kunzo tare ne?" Ya fahimci wata k'il yaron besan taxo ba

"Kaje mana kace ina neman ta, tana cikin gidan kaji" rugawa yayi da gudunsa yashiga yana neman ta, Mommyn meenal ce ta taress

'Hidar lafiya kuwa?" Kallonta yae

"Dad yace nakira masa mom d'ina wai tana ciki tazo" kallon sa mom keyi da mamaki "Tare sukazo ne ai bata shigoba tukun,wata k'il tana b'angaren su me martaba" Juyawa yaron yae kurun batare da yayi magana ba

"Dad wai inji granny tare kukazo?  Tace idan tare kukazo ma bata shiga ba kota tsaya nanne gunsu granny" Dafe kanshi yae cikin tashin hankali, mesa zata zab'i yi masa haka ne wai? Meke shirin faruwa ne haka? Be sanar da iyayen taba ya guntse bakin sa gudun karya tayar musu da hankali, se cewa mom yae yanawa hidar wayo karya masa rigima bezo da itaba.

*Bayan kwana biyu*

Cikin tashin hankali takawa yae kwana biyu yana neman Meenal amma ba labarin ta, yacika rud'ani sosai, ita kuwa meenaly tanacen hankalinta kwance ta samu nutsuwa rashin jin k'amshin jikinsa kurun ne damuwar ta kuma tana samun ragewar abun ma yanzu!, kamar yanda ta saba jin dad'in ta tana kewaye ko ina agidan yauma haka take shirin zuwa babban parlor d'in gidan domin tayi kallon wata drama da akeyi a zeeworld ta indiyawa me kyau, ya kasance parlor antyn nata Startimes ce se babban parlor d'inne da dstv inda zata kalli shirin, tasan cewar mijin matar baya nan kuma tare da antyn suke kallon series d'in, yau batasan mesa antyn tace bazatajeba ita dai taje kawai, Bata wani takurata ba tunda tace bata ra'ayi ta kama hanyar daze sadata da parlor d'in, tun a d'an walkway daze sadata da parlor d'in takejin wani kalar k'amshi wanda koma a inane tasanshi kuma tabbas k'amshi ne datakeso fiye da kowane k'amshi a duniya, lumshe idanta tae tare da jan dogon numfashi tana mejin dad'in k'amshin datake ji....lumshe da idanu ta shiga cikin parlor sedai mutumin datai tozali dashine ya sanyata gigicewa da har ta nemi lumshewar idan ta rasashi, seda ta dafe bango sabida ganin datai kaman gizo yake mata, kallon dayake mata cikin fuskar nan babu walwala kurun ya isa ya saukar mata da murd'awar ciki, take ta shiga kelayo gumi, hannunta ta sanya ta share goshinta sannan ta shiga lalubo nutsuwar ta data rasa, amma da k'yar ta samo wani kaso dabefi cikin cokali ba,yawu me d'acin gaske ta had'iya kafin tayi yunk'urin komawa da baya, juyawar dazatayi taci karo da yaa Al-ameen shi d'inma babu alamar wasa a tattare da fuskar sa, Waigawa tae ta kalli Takawa zaune yake k'afarsa d'aya akan d'aya ya zura hannayensa duka biyu a aljihun wandon suit dake jikinsa kalar k'asa k'asa ya murtuk'e fuskar nan, girar shi harta had'e gu d'aya sabida yanda yasha mur, k'ara mayar da kallonta tae zuwaga Yaa Al-ameen

"Sannu yaa Al-amen ina wuni, bansan ka dawo ba wlhy, anty bata fad'amun ba" D'an guntun murmushi yae

"Me martaba ne ya dawo dani nemanki muke ai, kuma tunda kina gidan sekije ku gaisa" Tabare fuska tayi, danma takula yayan nata baya wasa tsoron sa ake har matarsa tana shakkar sa

"Yaa Al-ameen ni wlhy bazanje wurin shiba" Tsawa ya daka mata daya sanyata shiga taitayinta

"Meenal yaushe muka soma wasa dake ne, maza k8 wuce ki gayar da Takawa" Cikin turo baki taje ta zauna kujerar dake nesa dashi, cikin takaici tace

"Barka da wuni Takawa" gogan ko kanzil bece ba bare ta sanya ran ze amsa mata abin mamaki kuma ya kafe ta da ido ko k'iftawa bayayi, dukta tsawwala takuma shiga tsoron sa me tsanani, sunfi 30mns yana kallonta ko k'iftawa bayayi, duk son datayi ta had'a courage ta basar abin ya faskara danya kama ya tsatsare ta da manyan idanuwan sa ko k'iftawa bayayi, duk yanda ta sadda kanta k'asa ji take idanuwan sa suna mata yawo ajiki tako ina, tasoma k'osawa da zaman kanta yana k'asa tana wasa da 'yan yatsunta, kusa da ita kurun k'amshin sa yazo ya manne mata sosai, d'agowa tae domin ganin waye idansu ya sark'e da juna, hannunsa ya sanya ya zagaye kafad'arta har bayan wuyanta yana wani k'asaitaccen murmushi ya furta

"My meenal mesa hana ehmm?" Mamakin shine ya dask'arar da ita auu duk wannan iskancin daya gama yi mata kuma yanzu washewa yake shirin yi, had'a fuskar nan tayi sosai ta kawar da ita d'ayan b'angaren, hannun sa ya sanya ya juyo fuskar tana kallon sa, yace

"Haba my Meenal, mesa ne kikeso ki rik'a tayar mun da hankali ne wai? Abu kad'an kawai sekiyi fushi ki gujeni, kinsan kuwa tashin hankalin dana shiga na kwana biyunnan dan Allah kiyi hak'uri kinji" Se yanzu ta d'ago ta kalleshi d'an guntun k'wallan datake taso ha adana ya silalo mata, cikin takaici tace

"Nidai dan Allah ka barni anan kaji, karkace zaka tafi dani" Rik'e hab'arta yae

"In rayu dawa nikuma bayan ga rayuwata anan ehn? Dawa kikeso na rayu? Ina zanbi inga haske ehm my meenal, hak'uri zakiyi bazan k'araba"

"Kana sani kenan kake sakani ciwon ciki da ganganko?" Dariyar sa ya gimtse

"Dama ni nake sanya cikinki yake ciwo, kodai ciye ciyen kine?" Wani Takaici ya bata gashi bazata iya furta masa abinda take nufi ba, kuka me k'arfi ya k'wace mata tashiga rero masa kuwa, sororo yae yana kallonta hadda shesheka sekace wacce ka daka shi mamakinta ma ya kashe masa jiki ya daskarar dashi a wurin, k'ara rungumota yae jikinsa

"Ki dena kukan mana, gayamun meye bakyaso inshaa Allah zan dena kinji"bata kulashiba ki kanshi yasan seyasha fama da meenal tunda ya kula ta iya fushi kuma kusa dashi yakeso ta zauna

"Meenal ki gayamun mana" nanma koci kanka batace masa ba, d'ago da fuskarta yae ya jona mata bakinsa anata tana faman kukan, se damben k'wace kanta takeyi amma ta kasa, tayi iya yinta yak'i ya dena dole ta sakar masa akalar ta yaja ragamar ta har lokacin kuka takeyi, yafi 15 mns yana abu d'aya ita kuma bata fasa kukan ba, musamman dataji mararta ta murd'e mata gu d'aya babu abinda takeso se saukar wannan abun datakeji, saketa yae gaba d'aya dan kanshi, ita kuma ta kwantar da kanta saman cinyarsa tana meci gaba da rusa kukan ta

"Dan Allah ka dena inda nake wlhy kasheni zakayi, ka tausayamun ban maka komai ba se alheri tun zamana dakai, mesa zaka rik'a cutar dani da saninka kuma? Meye arayuwa akeyi ban maka ba?" Tausayinta ya kamashi yace

"Meenal idn akan wannan ne zan dena aina gaya miki na dena duk abinda bakya so"

"Me kenan kayi yanzu? Cutar wa kome? Ina zaman zamana ka rik'a tayarmun da sha'awa kana barina da murd'ewar mara, na kula bani bace meson in b'arar da cikin nan wlhy kaine, kasan kuwa me nakeji, na tab'a zuwa gunka nace ka saukemun wata buk'ata tawa? To mesa kake son tayarmun da abinda Allah me tayar mun kakuma barni da tsananin ciwon mara" Bubbuga nayanata yashigayi a hankali

"Wlhy bansan yana saka miki wani illah ba, yaya zanso mutuwar gudan jinina wlhy banida masaniya akan hakan ze iya haifar da matsala agareki ko cikin jikinki, kiyi hakuri" batace komai ba ya hau aikin rarrashi haka seda yaga yabkwantar mata da hankali sosai sannan yace ta shirya su taci gidan su mom ta kwana acen gobe zasu koma akwai babban shiri agabansu, anan yake gaya mata dukkaini shirin sa na shiga masarauta gobe inda nan take tayi na'am da hakan ta k'ara da shawarwarin dazata iya bayarwa wanda take ganin ya dace ta bada.

Har wani lokaci me tsayi suka d'auka suna tattaunawa akan abubuwan dasuka shafi fadar da abinda zeje yazo gobe, kan daga bisani yabata izinin zuwa ta kimtsa akan zasu tafi.

*********
    Sarkin tsaro banaso kayi sakacin da kai ko matarka zaku gayawa meenal ainahin alak'a ta daku, daga ranar datasan nine jigon komai zata dena tsoron ka kai, zakuma ta dena gayawa  matarka abubuwan dake damunta, tausayinta nakeyi batada yaya ko anty dazata gayawa matsalar ta gata da tarin k'uru ciya, ka kimtsa sosai gobe banason abinsa ze kawo mana matsala ko d'aya a fada" Nisawa yae

"Amma ranka ya dad'e bazaka bar sawun Takawa anan ba? Baka tsoron abinda zeje yazo a fada gobe? Bafa ziyara bace ba ta dad'i kokuma wacce za'ayi cikin kwanciyar hankali, kar azo ayi wata fitinar daze tab'a lafiyar ta ya kuma tab'a babyn cikinta" Murmushin takaici yae ya shafi gefen sajensa da hannu d'aya

"Yanzu dai zanje da ita, zuwa gobe zansan abinyi banaso tamun nisa wani yazo ya cutar da ita batare da sanina ba, tunda yake harine zamuje dashi" Murmushi yae

"Tabbas k'anwata tayi sa'ar sarki, tafi mata fada Allah yabaka yawan rai lallai kanaji da meenaly" ko cikanka bece masa ba, ya fad'a mota yaci gaba da jiran meenal, seda ta fito tashiga gidan baya itama sannan Abokin Tafiya yaja suka tafi, hannunta ya kamo ya rik'e yana murmushi cikin isa yace

"Emerald hotel zamuje" Abokin tafiya dai se lallab'ashi yake

"To Ranka ya dad'e" kallon sa tayi tace

"Takawa Emerald kuma ba gidan mom zamuje ba dare fa yay...." Bata k'arisa maganar ba taji bakin sa anata, k'ok'arin k'wacewa take tana nuna masa Abokin Tafiya amma sema sanya hannunsa yae ya janyo kunkurunta ta matso daf dashi, kunyace dabatasan dana dashiba ya dabaibayeta arayuwa Takawa bashi kunya wlhy, seda dan kanshi ya gaji sannan ya sake ta yace yana lasar lips d'inshi

"Mint flavour wooo what a nice flavor, ina so ki rik'a sakawa" sarai ta gano lip glose data saka ne da wannan flavor d'in dama zak'ine dashi, tace aranta idan na kuma sakawa sena nemi bakin nawa kacire gaba d'aya bazan sakaba😑😑🙄🙄" .

Mom Nu'aiym.

Continue Reading

You'll Also Like

95K 2.4K 35
A little AU where Lucifer and Alastor secretly loves eachother and doesn't tell anyone about it, and also Alastor has a secret identity no one else k...
264K 40.1K 103
ပြန်သူမရှိတော့ဘူးဆိုလို့ ယူပြန်လိုက်ပြီ ဟီးဟီး ဖတ်ပေးကြပါဦး
37.9K 2.5K 61
𝐭𝐡𝐞 𝟐𝐧𝐝 𝐛𝐨𝐨𝐤 𝐨𝐟 𝐬𝐡𝐨𝐫𝐭 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢𝐞𝐬 𝐚𝐛𝐨𝐮𝐭 𝐨𝐥𝐢𝐯𝐢𝐚 𝐫𝐨𝐝𝐫𝐢𝐠𝐨 𝐚𝐧𝐝 𝐲/𝐧'𝐬 𝐦𝐞𝐞𝐭-𝐜𝐮𝐭𝐞𝐬/𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢�...
5.3M 46.3K 57
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...