🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 12-14

710 45 0
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

1⃣2⃣➖1⃣4⃣

Koh bayan mun isa gida sai na fara jin kewan kawaye na saboda wata irin sabo ne ya shiga tsakani mu farat daya toh dama chan ni ba kawayen gare ni ba Koh da muke Abadam daga ni sai kanwata ita kuma in banda shirmen da zata yi ta saka ni dariya ba na iya wani iya doguwar hira nake yi da ita ba dan bata san komai ba ga rayuwar kadaici da na taso a ciki babu uwa babu kawa mahaifi na ba zama yake yi ba tafiye tafiye in zai yi tafiyar shi  gidan wani amininshi shi yake kaimu kafin ya dawo toh shima aminin ya zo ya bar garin saboda yanayin rigingimun da ake yi barin shi garin da wasu yan watanni ne Mahaifin mu yayi tafiya  yana ta tunanin inda zai kaimu saboda gudun fadawa hannu mara kyau sai yayi ta jinkirta tafiyan har dai Allah ya kawo kanwar ummar mu da kaddara ya fada akan ta

Da kewar su na kwana na rungumo ummi sai ga hawayen da ban san dalilin shi ba saboda a lokacin ba wai gama sanin ciwon kai na na gama yi ba hawayen sai ya dinga saukowa kamar an balle kan abin ruwa ashe wai kadaici ne ni ban sani ban taba jin maraici ba irin na ranar koh me yasa hakan ban sani ba

Da muka tashi sallah da asuba sai kawai na juye ruwan wankan mu muka yi ni da ummi kafin muyi sallah hakan da nayi ya ma Abbu dadi ganin yar shi ta fara hankali da wayo har sai da ya furta da zai hada mana abin kari

Ni ko sai cewa nake ai Abbu kai ne kaki koya min yanda ake hada abinci sai ka ce wai ban gama wayo ba ga ya Ibrahim nan ka koya mishi kullum shi ke yi kuma in ya dawo daga makarantar ma shi zai cigaba da yi gashi in yana girkin har gwalo yake min ya ce ai ban iya komai ba nikuma na ce na mai alkawari in ya dawo yanzu ni zan fara yi mana abinci Abbu pls ka koya min wallahi zan mayar da hankali in koya da kyau na karashe maganar ina saka fuskar tausayi

Sosai Abbu yayi dariya ya ce eh lallai mamana kice gasa kuka dasa ke da yayan naki toh ai kuwa zan taimaka miki koh dan saboda  ki cinye gasar nan

Da murna na ce da gaske kake yi Abbu ya jijiga min kai alamu eh da gasken yake murna akan murna zan koyi girki kafin yaya Ibrahim ya dawo gidan kuma gashi salma ta ce min zata yiwa abban su magana a canza min Islamiya mu rinka yi tare

Tuna wannan abubuwan sai na yi ta washe baki ina gayama ummi ina ta murna matuka Abbu ya tausaya min ganin yanda nake ta murna akan zan koyi girki da ace mahaifiyar mu na nan yanzu ai da na kware kware fannin girki saboda mahaifiyar mu ta kasance gwana ce a fannin girke girke koh a zamanin da sukayi rayuwar su kafin ta rasu ita ke girkin ta da kanta bata yarda yan aiki su yi mata ga kyau da diri suman nan yalala babu ta inda ban daukota ba a jiki face no din dai ban da jikin da take dashi saboda yar dumaduma ce wanda a yanzu jikin yana son dawowa wun ummi ne dan mashaAllah tana da jikin hutu ga haske ba kamar ni ba da nake da duhu da surutun tsiya wanda aka rasa inda na gado shi

Yayin da ummi kam tun a lokacin miskilanci ne da ita kamar wata yar sarki dan wasu lokuta da dama in aka mata magana akan ta bar yin abin da take yi toh koh da ta bari din sai ta dauki lokaci kafin ta sake da kai koh wani irin magana zaka mata sai ta maka banza wannan hali nata yakan dan dami Abbu wani lokaci tunda shi babba ne ya rigada ya gama hasaso irin halin da zata yi a nan gaba in ta girma wanda shi kuma ba zai so hakan ta faru ba ya fi son ta kasance kazar kazar kamar yanda nake amma lokaci bai kure mishi ba zai san yanda zai tankwasa ta inshaAllah

Abin mamaki sai ga Abbu na murmushi alokaci daya kuma yana hawaye ban san dalilin shi na hawayen ba sai na fara surutun fama ce min yayi ban ga yana dariya ba na ce eh yace toh ai saboda murmushin da yake yi ne yasa hawaye fito mai sai nace toh nima bari in gwada yi abin ya bashi dariya amma sai ya hana ni yace in yi in gama mu tafi kar mu makara da haka ya min wayo dan ya lura in yana biye min da yawan tambayoyi na watarana zai iya yin kuka a gaban mu kuma ba zai so hakan ta faru ba dan koh na tambaye shi ba zai san amsar da zai bani ba

Mun isa makaranta duk na matsu in ga su falmata ai koh babu dadewa sai ga motar su ya danno cikin makarantar da saukan su muka rungume juna mun jin dadi hasina ta yo wun ummi tana mata surutu kamar yanda suka saba in sun hadu muma sai muka wuce zuwa ajin mu jim kadan muka fito yin assembly a nan aka kara yiwa su salma ta'aziyar rashin da suka yi daga nan muka wuce zuwa ajin mu inda aka yi wata yar karamar drama dan salma fah kukewa ta yi akan safiya ta bar musu kujera zasu saka (ta manta cewa jiya jiyan nan ta je gidan su yi mata ta'aziyar rashin da suka yi yarinta abin dariya)

Allah sarki za tausayi ta mike zata bar kujerar  saboda duk wani abu da zai hada ta da salma toh tana gudun shi dan salma kiba ne da ita kamar me hannu kawai in ta danne mutum dashi sai mutumin ya ji ajikin shi yana daya daga cikin abin da yasa in ta kadawa mutum warning babu mai cigaba da yin abin nan in koh kaki toh kai ka jiyo

Sanin hakan ya sa babu mai shiga sabgar ta in dai ba ita ta kawo kan ta wurin ka ba a hakan ma in ka nuna zakewa sai ta mamake ka ta yi wucewar ta

Ta inda aka sami sabanin halayar su da falmata ke nan ita falmata akwai hakuri wanda ya hada da miskilanci da rashin son raini daga wun yan ajin su gata da da saurin hana salma yin abin da take son yi in dai ita bai mata ba shiyasa wasu lokutan har fada suke a tsakanin su salma ta yi ta ganin laifin falmata akan ta cika shiru shiru har a je a cuceta bazata yi magana ba amsar da take bata dai daya ne kuma shine
"Ni dai ki dinga yi a hankali kina ji kullum sai mommy ta hana mu neman rigima kuma ta ce duk Wanda ya neme mu kar mu amsa shi"
A duk lokacin da ta bata Wannan amsar ji take yi kamar ta bugeta ta huta da abin haushin falmata karshe in falmatan taga tana muzurai sai dai tayi mata dariya ita kuma ta cigaba da huhura hanci irin ranta ya bacin nan

Me yan aji zasu yi in ba dariya wa safiya ba sai suka fara yi mata gwalo wai ai jiya ita ce yar iyayi da ake neman masu zuwa gidan su ita ta fara fitowa toh gashi nan ai rashin mutuncin salmar ya sauka akan ta suna ta mata dariya da gwalo abin sai ya taba ni ganin saboda ni ake yiwa safiya haka sai na juya zan ma salmar magana sai ta riga ni tace

"Safiya zo ki zauna a nan ke da falmata ni kuma zamu zauna ni da Aisha a kujera daya"

Safiyar sai ta goge hawayen ta ta ce a'a bar shi kawai zan zauna a chan kujerar gaba tana kokarin daukar jakar ta da lunch box din ta ai ganin haka sai salma ta tunzura ta fara zazzagawa safiya wai tana mata yanga ganin ta ce tazo ta zauna da falmata toh ai dole sai ta zauna da falmatar

Ganin haka yasa safiya komawa ta zauna abin tausayi wannan ai shine a dake ka a hana ka kuka ta kore ta ta tafi kuma ta ce ta dawo ta zauna dole ya ta iya bata saba hayaniya ba koh da chan da yan ajin suka ga haka sai suka fara rage dariyar da suke yi kafin ta juyo ta fara da su suma (salma case)

Haka aka yi zaman har malamar ajin ta zo ta kira sunayen mu muka amsa ta koya mana abin da zata koya mana ta yi gaba aka fito break duk a ajin muka yi break din mu wanda a yau har safiya ma ta hadu da mu saboda falmata ta ce ai ita yar uwar zaman ta ne dan haka a ajin zata na cin abinci itama daga yau koh uhum salma bata ce ba sai ma tambaya na da ta fara yi aka na koshi koh ta kara min da nata dan ita ta koshi na ce mata a'a nima na koshi daga haka muka fara maganar islamiyar mu a nan nake ce musu ni fah tsoron zuwa nake yi me zasu yi in ba dariya ba abin sai ya bani haushi na au dariya ma nake baku wallahi ina tsoro fah sai falmata ta ce

"Keh in zaki dage ki lakada musu duka ki dage dan wannan sanyi sanyin ba zai taimke ki ba"

Sai na ji abin wani banbarakwai wai in duke su ni dai akwai baki amma maganar duka ban taba yin shi tun da nake toh a chan maiduguri ma ba zuwa muke yi ba a gida ake zuwa yi mana ban taba yi ba kuma bana tsammanin zan fara dan ba dabi'ata ba ce

Na ce "no falmata bazan daki kowa ba so kike a kai kara na wun Abbu a ce mai fada nake yi a makarantar a'a gaskiya sai dai kawai in gayawa Abbu gaskiyar maganar in ya so sai a yi mai yiwuwa"

Salma Kala bata ce mana ba ita haushin kanta ma take ji da ta bari safiya ta zauna tare da falmata har ma da cin abinci tare da mu sai tayi kwafa kawai tace

"Aisha kina son islamiyar mu? "
na ce mata eh ina so amma Abbu ba zai bari ba kuma ai nasu islamiyar ta yi nisa da gidan mu"

Sai ta ce ke dai kina so na ce eh ta ce toh ai shikenan

Ban fahimce ta ba nima sai ban sake magana ba har aka dawo break muka cigaba da karatun mu ana kada karrarawa na tashi aka fara fitowa za'a wuce gida ciki kuwa har da mu amma abin da ya bani mamaki shine ganin motar su salma ya zo amma taki tafiya dan har falmata da hasina sun shige sai na ji mamaki na tambaye ta me yasa bazata tafi ba tace min wani take jira da mamaki na ce wani kamar ya ta ce ke dai kin cika tambaya Aisha nayi shiru suma yan motan sai basu tafi ba suka  jiran ta

Mintuna kadan sai ga Abbu ya zo daukan mu mu tafi gida sai naga salma ta fara matsar kwalla tana gaida Abbu shima da mamaki ya ce lafiya me ya faru take kuka

Duk a zaton shi nice na bata mata rai sai ya ce koh dai mamana ne da sauri ta juya kai alamun a'a ya ce toh menene kawai sai ta fara bayani

"Abbu ka ga Aisha bata sona ni da falmata nace mata tazo mu rinka yin Islamiya tare wai a'a bazata zo ba wai gidan su yayi nisa da islamiyar kuma fah na ce mata zan ce ma Abban mu ya rinka saka driver yana zuwa daukar ta amma ta ki yarda shine nace zan kawo karar ta wurin ka kace mata ta yarda mu rinka zuwa Islamiya tare Abbu"

  Wannan ai shi ake kira da daure ka da jijiyoyin jikin ka yanzu ya take so ya mata in ya ce a'a toh lallai bai kyauta ma yarinyar ba ganin yanda ta damu da nashi yar har take son hada alaka da ita mai karfi daga haduwar makarantar kwana uku kawai bata dau halin yayan masu kudi ba wandanda basu ganin wanda ba irinsu ba da kima kuma in ya ce eh toh bai yi aikin shi ba a matsayin shi na uba dan har yanzu su din yara ne basu san rayuwa ba har yanzu gashi Alhaji kasim wato baban falmata ya gaya mishi iyayen yarinyar sun yi tafiya idan suka dawo suka riske wannan labarin fah yaya zasu dau maganar shi a karan kanshi baya so ya amince

Ganin shirun yayi yawa yasa salma kara muryar kukan ta sai yi take yi nikuwa gani a tsaye kamar hoto dan ta bani mamaki da irin abin da tayi ban taba zato ba koh tunani har zan ce wani abu Abbu ya riga ni

"Kina ji na salma ki bari har sai iyayen ki sun dawo sai muyi maganar kin san dai yanzu basu nan koh ba haka bane"?ta mai shiru

Ya cigaba toh kinga ai bai kamata a ce na bar Aisha na zuwa islamiyar ku ba tare da sanin baban ki ba koh still shirun ta mai sai ya ga kamar bai kyauta ma yarinyar ba

Kafin yayi magana ta ce

"Abbu wallahi koh Abba ya dawo babu abin da zai yi sai dai ya ce min na yi kokari kawai ni dai Abbu ka bari ta fara zuwa ka ji"? Ta ida tana turo baki ta son yin rigima

Sarai Abbu ya san ba kankanuwar yarinya bace da zai mata wayo in koh ya ce zai yi toh dole kallon makaryaci zata yi mai nan gaba kadan sai ya yanke shawarar amince mata da sharadin idan Abban su ya dawo zai zo suyi magana kafin Aishar ta fara zuwa ba haka ta so ba dan haka tasa kuka tana cewa

"Ni dai Abbu a'a kawai ka yarda mu fara zuwa tare yau"
Ganin da gaske take yi sai ya ce ya ji da murna ta share hawayen ta ce toh zasu bi mu zuwa gidan mu in mun shirya sai mu tafi gidan su da dai Abbu ki yayi amma ganin yarinyar na matukar Kaunar jinin shi sai ya amince

Motar su muka shiga sai gidan mu

Da isar mu gidan muka fito muka shiga gaba dayan mu a falon mu suka zauna na ce musu ina zuwa Abbu ya ce in kawo musu abin sha fridge din mu na bude na dauko lemon kwali kwali uku da kofuna na saka a tire da ruwa na kai musu na ce bari mu yi wanka mu chanza yanzu zamu zo da murmushi suka amsa muka yi gaba yayin da Abbu ya dumama mana taliyar da ya dafa mana lokacin da ya dawo gida kafin ya zo daukar mu a makarantar  har muka fito muka same su babu abin da suka taba sai ruwan da suka sha kawai na ce musu su yi sallah suka ce a'a sai sun tafi gida zasu yi nace toh

Zamana kenan cikin shirin Islamiya da jaka na sai ga Abbu da plate babba cike da taliya ga cokula har uku wai mu ci su ummi da hasina ma zasu ci nasu tare

Gyara zaman mu muka yi muka fara cin abincin

  Muna ci muna hira har muka gama sai salma ta fara min signa wai in tashi mu tafi na ce masu ina zuwa kitchen na maida kayan na fito na shige dakin Abbu na ce mai zamu tafi bai bar ni na fito ba har sai da ya hada da nasiha da jan kunne akan in tsaya amatsayi na kar in shishige musu haka dai yayi ta min nasiha iri daban daban kafin ya  bar ni in fito da na fito sai na same su a tsaye suna jira na da zuwa na muka fita suka yi wa Abbu sai anjima

A motar sai hira muke yi har muka iso gidan su saukowa muka yi daga motar daya bayan daya mun shiga tare har cikin dakin su salmar inda na tsaya jiran su su shirya su fito mu tafi makarantar

Bayan sun gama duk anubuwan da zasu yi ne suka ce muje mu gaidasu Mama wato iyayen falmata da muka shiga muka gaishe su da mamaki suka ce mana dama tare muka dawo shine salma tace eh dama sun fara zuwa gidan mu suka jira ni na shirya kafin mu zo sai abban falmata ya ce toh yanzu ya akayi muka zo nan dukkan mu sai falmata ta ce

"Abba akan maganar da ta fada mana jiya ne shine salma ta yi ma Abbu magana akan ya bar Aisha tana zuwa makarantar mu shiyasa ma ka gan mu tare"

Sun ji mamaki amma sun san basu da ikon hana salma yin abin da take so dan itace yar gidan kuma koh da a yau iyayen ta suka dawo bazasu yi fushi ba saboda haka su dama gudun kar a sami matsala yasa suke tambayar amma tunda sun ce da sanin mahaifin ta ai ba wani abu

Da haka suka ce mana toh muje mu shirya kar mu makara da murna muka tafi mu hudu dan dama ita ummi Abbu ya ce bazata bi ni ba ni kadai zan na zuwa ita kuma zata cigaba da tafiya wancan islamiyar tamu

Tsakanin islamiyar da gidan su tafiyar mintuna biyar ne zuwa shida bai da wani nisa a nan suke gayawa malamin su ai abban su in ya dawo zai zo yayi ma Aisha registration malamin bai wani damu ba ganin dama chan Alhaji Habib ya saba aikowa a kawo yara daga baya ya aiko a musu registration haka ma yanzu ya dau maganar

Da salma aka fara karatun kafin a zo kan falmata har aka zo kaina dai nima aka min karin karatun bayan na biya inda nake

da aka tashe haka salma ta cika alkawarin ta ta dawo da ni gida amma na lura tana son yi min wani tambaya amma ta kasa har na fito zan tafi sai na tsaya nace

"Wai salma me yafaru ne tun dazu naga kin yi shiru"

Sai tace min babu komai sai da na matsa mata kafin ta amsa min da

"In bazaki damu ba wata tambaya zan miki"
Da mamaki nace ina jin ki

"Aisha mamakin fah tun da muka hadu baki taba cewa maman ki ba kullum Abbu kike kira"
Ta karashe da dan damuwa akan fuskar ta

nima da damuwar a kan fuska ta na dago kamar zan yi kuka nace

"Salma umman mu ta rasu tun lokacin da aka haifi ummi Abbu ya ce min wai bata ma san ummi ba amma ni ta san ni"na karashe ina kuka

Ta kasa yi min magana sai ta fara kukan ita ma tana ce min toh ki dawo gidan mu mana mu zauna tare

Da sauri na dago na ce a'a bazan je ba kawai ta bar maganar ganin yanda nayi maganar sai tayi shiru ta ce toh shikenan

Haka na fito na wuce gida ina daga mata hannu suma suka wuce

Abbu ya ga changi a tattare da ni sai ya tambaye ni dan a tunanin shi abin da yake gudu ne ya faru wulakancin da baya so a min saboda haka ma shi ya yanke hukuncin zuwa gidan da kanshi ya sami abban falmata ya mai bayani toh kuma sai gashi na dawo a hargitse sabanin yanda na fita

Tambaya na yayi koh wani abin suka min na yi saurin girgiza kaina na ce basu min komai ba

"Toh me yasa kika yi kuka na ganki haka"

"Abbu dama salma ce ta tambaye ni wai ina umma take shine na gaya mata ai umma ta rasu sai ta ce in zo mu koma gidan su da zama amma na ki shine nikuma na fara kuka nima ban san me yasa ba Abbu" na karashe maganar ina kuka da ban san dalilin yin shi ba

Sai Abbu ya rungume ni shima yana share nashi hawayen dan kamar an tado mishi da mikin da ya dade ne a zuciyan shi sai kuma ya dago ya ce min

"Mamana kin san me yasa kike kukan"?
Na ce a'a

Sai ya ce min"kewa kike ji da rashi na uwa"

Gaskiya ban fahimci Abbu ba dan haka nayi shiru kawai shima ya san hakan zai faru sai yayi saurin share nashi hawayen dan kar in fara mai tambayoyin da na saba ya ce toh mamana zoki ci abinci tun dazu su ummi suka dawo sai ku ci tare ku yi sallah koh

Na amsa da toh na yi gaba abu na na tarda ummi ta na ta wasanta na chanza kayana na ce ta taso muci abinci

A daren ranar haka Abbu ya kulle kan shi yana ta kuka sosai yayi saboda a yau yake kara tausaya ma yayan shi gasu mata kuma kanana wasu matsalar su sai da uwa zasu iya magance shi sai gashi a yau babu uwar kuma babu wata da zata iya magance musu damuwar su sai shi shi kadai haka ya kusan kwana yana abu daya kafin daga baya ya fara salloli yana ma umman mu addu'a

Haka dai rayuwar mu ta cigaba da gudana har zuwa lokacin da muka fara shirye shiryen rubuta jarabawar mu ta karshen shekara wanda daga shine zamu chanza aji zuwa aji biyar yayin da shakuwa ta musamman ta ke shiga tsakanin mu ni da su falmata da salma

Bayan jarabawar mu aka bamu hutu ta fannin islamiyar mu kuwa Alhamdulilahi muna kokari Abbu yana kokarin ganin ya koya min abinci saboda alkawarin da na yiwa yaya ibrahim

A wani asabar sai ga su salma sun zo wai in zo mu tafi gidan su Abban ta da umman ta sun dawo har da yaya Aqeeb ma ya dawo ni dama ban san su ba

Abbu na gayawa sai yace toh mu tafi tare da ummi kuma kar mu dade

Har yake cemin in gaya wa salmar gobe inshaAllah zai zo ya gaida iyayen nata ya kuma yi musu sannu da zuwa nace toh dama a lokacin Abbu ya sami masu mai zaman shago wasu matasa biyu yahaya da zakir kuma suna iya kikarin su na ganin sun kare mai kawuwancin sa wasu lokutan ma yakan kaimu shagon mu wuni tare a shagon in ba islamiya har mun saba da su sosai wanda hakan ya sa Abbu ya fara zargin wani abu daga wun yahaya sai dai yayi shiru yana jira ya ga iya gudun ruwan yahayan

Muna isa gidan su salma direct part din su muka je inda tun kafin mu shiga gabaday ta fara kwala kira tana Abba gata mun zo

Da dariyar shi ya karasa saukowa daga benen yana cewa

"Ohh salma yaushe zaki girma ne wai"

Kafin ta ce wani abu sai ga wani mai tsananin kama da salman ya fito yana cewa

"Ai Abba wannan autar shirmen ta yafi haka jiya ma sai da ta min haka gata katuwa amma ba wayo kina ji na koh toh wallahi in baki rage wannan kibar taki ba korar ki zamu yi daga gidan nan dan baza mu zauna da obessed girl a gidan mu ba"ya gama yana mata hararan wasa

Me salma zatayi sai ta fara raurau da idanun ta zata yi kuka da sauri Abban su ya ce

"Nooo auta kar ki mai kuka manta shi kawai ai dan yaga bana son shi ne shiyasa"

Ai ko da sauri ta goge hawayen da ya fara tsilalo mata tana cewa

"Ya aqeeb kaji ai abba yace baya son ka sai ni"tana ta jin dadi

Kawai sai ya fara dariya yana cewa

"Kun ji ta idon kuka kawai har ta fara toh ni me ya shafe ni ma da ke" ya sauko zai fita sai naga ya kira ta waje wai ta zo tace bata zuwa yace har da abin nan bakya so ai da jin haka sai ta yi saurin bin shi sai aka sa musu dariya har d wata matar da ke saukowa daga benen itama wanda nake kyautata zaton mahaifiyar salma ce

Jim kadan sai ta dawo tana cewa umma kin ga Aishan

Dariya suka yi gaba daya sai na durkusa na gaidasu suka amsa suna jinjina tarbiya irin na yarinyar suka ce
Dama kece Aishar da ta sa aka hana mu sakat tun dawowar mu jiya komai Aisha kawata toh gashi yau mun hadu ina kanwar taki

Na ce "suna tare da husna"

Sai ta ce ma salma ta kawo min ruwa bayan tafiyar salma ne take tambaya na ya su maman mu ashe salma ta manta bata gaya mata cewa ban da uwa ba sai ni ce ke gaya mata

Sai ta tausaya min take cemin yanzu wa ke kula da mu nace mata Abbu ne sosai ta kara tausaya mana

Da salma ta dawo sai ta ce me yasa baki gayamin cewa maman su ta rasu ba sai ta ce umma mantawa na yi wallahi

Abba da ke jin mu shima sai ya saka baki ya ce Allah sarki toh Allah ya jikan ta muka amsa da amin a nan nake ce musu ai Abbu yace in gaya musu zai zo ya musu sannu da zuwa

Da fara'a suka ce toh Allah ya kawo shi lafiya daga nan salma ta ja ni zuwa dakin ta dan dama inda muka saba zama gefen su falmata ne sai koh ga falmata ta shigo da masifar ta wai salma ta tafi gidan mu bata kira ta su je tare ba sai hakuri take bata tana mata dariya har dai ta hakura muka dasa hira a nan salma ke ce min ai dazu da ya aqeeb ya kira ta tambayar sunana yayi

Da mamaki nace toh me zai yi da sunana ta ce oho nidai mu cigaba da hirar mu

A hasashe na ba zai wuce sa'an yaya ibrahim din mu ba na dai share maganar muka cigaba da hirar mu har yamma kafin in dawo gida wanda umman su salma suka cika mu da kayan tsaraba kalakal wai in gaida abba na na musu godiya aka kai mu gida a wannan karon har da falmata muka dawo bayan sun ajiye mu sai muka yi sallama akan gobe zamu hadu a islamiya

da mamaki na karasa shigowa ganin kofar yaya ibrahim a bude ai da gudu na shige dakin sai gashi yana cin abinci nace yaya ka dawo ne sai ya min dariyar shirme na gashi ina ganin shi wai amma ina tambayar shi koh ya dawo sai ya dago ya ce

"Raguwa na dawo ne mana gashi kina gani"

da murna na ce yaushe ka dawo yace min dazu ya dawo aka cemai ai na tafi Wun kawayen ki ashe har kawaye kika yi

Da murna na ce eh har na fara bashi labarin su yana ta jinjina kai a karshe yace toh Allah ya bar ku tare na ce Amin

Sai ya dago yace ina maganar alkawarin mu na yi dariya na ce yana nan kuma sai na baka mamaki yaya shima dariyar yayi yana mai cewa ummi wai kin ji yaya Aisha ta ce ta iya girki sai ta daga mai kai tana dariya da haka na bar su na karasa zuwa cika ina nuna wa Abbu abubuwan da na zo da shi ya ji dadi sosai

Yanda ya ce hakan ya faru saboda Abbu har gidan su salma ya je ya musu godiya suma suka mai godiyan taya su kulla alaka da yar su da yayi

Mun jima kafin mu tafi dan har Abban salma yana tambayar Abbu sana'ar sa bayan ya ji ne yake ce mai ai kuwa akwai wani babban company da suke buga kayan mata da na maza kuma na wani babban aminin shi ne harda ma dai ya rasu amma akwai wani dan shi da ke kula da wurin me zai hana Abbu ya na supplying masu row kayayakin su kuma suna amfani da shi ai hakan ma ya fi

Matuka Abbu ya yarda da nasabar wannan mutumi sosai dan haka ya mai godiya da nuna jin dadin shi a kan wannan taimako da ya mishi sun rabu akan duk yanda abin ya kasance zai mai magana da haka ya dawo gida

Lokaci ya dan ja har dai hutun yaya ibrahim ya kare ya koma muma muka koma makaranta

Haka lokaci ya rinka ja Abbu ya sami aikin a companyn da baban su salma ya mai magana shakuwa na kara shiga tsananin mu

A yanzu mun kai shekaru  10 a daidai lokacin ne kuma muka gama makaranta har result din mu ya fito an fara neman mana makarantar gaba da primary gabadayan mu

Wani rana muna gidan su falmata sai salma ta fito daga toilet tana ihu ta na kiran umma wai ta zo ta gani ta ji ciwo a wurin fitsarin ta koh da muka ji haka sai muka tashi tsaye muka bita muka fito falon tare umman a tsorace ta fito tana tambayar ta zata bude mata wandon ta ta ce ke dakata zo mu shiga ciki haka suka shiga a nan umma ke sanin ashe girma ne ya zo ma salma a nan tayi murmushi ta ke mata nasiha kafin ta gaya mata abin da ke faruwa sai kunya ya kamata da haka suka fito tare sai muka ga salma na susunne kai duk mun matsu mu ji me ya faru amma bamu sami damar yin tambayar ba haka muka bita zuwa dakin dan sanin me ke faruwa

*_🍒s,ibraheem🍒_*

Continue Reading

You'll Also Like

845K 29.2K 104
When Grace returns home from college, it doesn't go like she thought it would. With her past still haunting her everyday choices, she discovers a sid...
1.4K 423 36
A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishada...
4.6K 129 6
"'Daliba ta a makaranta ze aura" "......Se da na gama kwalliya na sa kaya fa, sannan na fita nayi kwaskwarima na 'dauraye qafa na da hannu na, ni br...
41.5K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah