🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

Від SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining Більше

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 9-10

662 45 0
Від SiyamaIbrahim

SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

9⃣➖1⃣0⃣

_Asalin Labarin_

*ABADAM MAIDUGURI BORNO STATE*

  Shine ainihin sunan garin mu da yankin mu mai suna Abadam

A chan aka haife ni aka kuma haifi kanwata mai suna farida wanda muke kiranta da ummi saboda sunan mahaifiyar mu ne da ita

A tarihin gidan mu mahaifin mu ya kasance dan kasuwa ne wanda kasuwancin nasa bai tsaya a nan gida nigeria ba yakan tafi kasashe saboda saro kayayaki ya kawo nan kasan ya sayar ma yan kasuwa

Duk da haka arzikin shi bai taba saka shi yayi sakaci da kula da taebiyar mu ba a matsayin shi na uba mai rauni sakamakon rasa ummar mu da yayi tun lokacin da ta haifi farida.

Ina da shekaru biyar a duniya aka haifi farida rashin uwa yasa na zame mata komai na rayuwar ta ni da mahaifin mu

A wannan yanayin kula ta taso har lokacin da ta kai shekaru uku a duniya wanda ni kuma nake da shekaru takwas

A daidai wannan lokacin ne kuma iftila'i ya sauko mana saboda mahaifin mu ya yi tafiya zuwa Cotonou saro kaya ya bar mu a gida ni da Ummi tare da wata kanwar mahaifiyar mu da ta zo tun daga yobe domin kuma tuntubar mahaifin mu da maganar ya bar ta ta tafi da mu amma yaki sai ma yace mata ga amanar mu nan ya bar mata har ya dawo daga tafiyar kasuwancin sa..

Tafiyar shi da kwana daya fitina ta taso mu gaba a inda aka shigo gidan mu aka dauke komai sannan aka yi wa kanwar mahaifiyar mu fyade kafin su mata kisan gilla dan a zaton su ita din mahaifiyar mu ce saboda tsananin  kamanin da muke yi da ita da kuma yanda suka ga ta kasa ta tsare akan bata yarda a taba mu ba sai suka mata wannan rashin imanin

A dai dai lokacin ne kuma yan fashion suka tare mahaifin mu a hanyar sa ta dawowa daga Cotonou suka kwashe kayan suka ma yan motar duka duka ba na wasa ba har sai da wasu numfashin su yayi kokarin daukewa ciki har da mahaifin mu

Bayan sun gudu ne sai ga motocin yan sanda da suka zo zagaye suka tarar da ta'asar da aka yi a wurin toh su suka taimaki mutanin bayan sun yi bincike suka gano yan fashi ne suka yi aika aikar

Koh da aka gwada tambayar mahaifin mu addireshin gidan shi har ma da garin shi bai iya basu amsa ba saboda yanayin da yake ciki sai da aka share kwanaki uku kafin a samu yayi magana har ya bada shaidar abin da ya sani sannan aka dawo da shi gida

Mu kuma a chan gida bayan yan bindigar sun fita ne na shigo kwala kirar jama'a da su kawo mana agaji sai a lokacin mutani suka sami damar fitowa daga gidajen su saboda suma boyewa suka yi jama'a sosai suka shigo mana a nan suka san halin da muke ciki bayan sun tabbatar da cewa kanwar mahaifiyar mu ta rasu

Kuka sosai muka yi saboda yanayi na yarinta bamu gama sanin komai ba ilah abin da muka gane ma idanun mu

A washegarin da aka dawo da mahaifin mu ne ya tarar da wannan abin al'ajabi gashi babu kowa da take da shi a yobe face dan ta mai suna ibraheem dan shekaru goma shabiyu toh shima yana makarantar kwana na sakandire mijin ta ya dade da rasuwa kakannin mu ma bamu sansu ba saboda sun bar duniyar tun kafin a haife mu

Rashin babu wanda za'a kira a chan ya sa aka mata wanka aka kaita

Da jimami aka samu mahaifin mu ana mishi ta'aziyar rasuwar toh a nan ake sanin cewa ashe ga abin da ya faru da shi abubuwan da yawa suke

Jaje sukai masa kafin su tattafi mu da muka ga mahaifin mu ni da ummi duk sai muka je muka fada a jikin shi ni kuka ummi murnar taga baban ta saboda ya rigada ya saba mana da zama kusa da shi hakan ne ya sa sabo mai karfi ta shiga tsakanin mu da mahaifin mu

A haka aka share kwanaki bakwai ana zuwa gaisuwa a nan ne kuma mahaifin mu ya yanke hukuncin zuwa ya dauko yaya Ibrahim daga makaranta saboda saura kwanaki biyu suyi hutun zangon akan in sun dawo nan Abadam sai mu bar garin baki daya

Hakan ta kasance bayan ya dauko shi ya mai bayanin abin da ya faru da kuma barin garin da zamuyi

Makota da abokan arziki su suka ma mahaifin mu addu'oi da fatan alkhairi akan Allah ya bashi sa'a a inda zai zauna

Abubuwan da mahaifin mu ya tsira da shi shine gidajen da ya mallaka wanda ya sayar ya karbi kudadensa ya hada muka bar garin a nufin in mun kai inda zamu je sai ya fara kasuwancin sa tunda shi din dan kasuwa ne bazai iya zama haka nan ba

Bamu tsaya ko ina ba sai wani gari da ake kira da birnin tarayya wato Abuja a wani gari mai suna kubuwa

A ranar mahaifin mu ya fara cigiyar inda zamu zauna aka ce mishi sai dai zuwa gobe

Rasa wurin kwana ya sa dilalin da aka hada shi da shi ya bamu aron wani daki cikin dakunan shi na gida akan mu kwana zuwa gobe

Mahaifin da yaya Ibrahim ne suka mai godiya ya gayawa matan shi a nan suka kawo mana abinci ba laifi sun tarbe mu sosai

Su suka ce ni da ummi mu shigo mu kwana tare da su saboda bai kamata a ce mun hadu duka mu hudu a daki daya ba ga namiji da ya girma sosai

Mahaifin mu ya musu godiya da haka muka kwana bayan sun saka mu mun yi wanka sai tausayin ummi suke yi saboda a shirmen labarin da n basu sun gano cewa bamu da uwa

Washegari ma haka suka mana hidima Kamar dai sun san mu a yayin da mahaifin mu da yaya Ibrahim tare da dillalin suka bar gidan domin zuwa nemo gidan  da zamu zauna

Sun dan sha wahala duba da irin garin da mutanin da ke rayuwa a cikin ta sai da rana ta fado kafin su dawo gida

A nan nake jin wai sun sami gidan ne a wani wuri mai suna federal housing a cikin 2/1 market

Toh a ranar muka bar gidan duk da rokon da sukayi akan mu tsaya har gobe mahaifin mu ya ki ya ce wahalar da suka yi da mu daga jiya zuwa yau ai ko naka iya abin da zai maka kenan  da haka muka rabu dama ba wasu kayayaki muka zo da su ba face kayan sakawar mu

Muka dau taxi zuwa 2/1 market a inda gidan mu yake muka tsaya mahaifin mu ya sallame shi mukuma muka shige ciki a inda muka tarar da wani daki mai kyau wanda yaya Ibrahim ya ce mana mu shiga ciki nan ne namu ni da ummi dakin Alhamdulilah komai mai kyau shima yaya Ibrahim akwai dakin shi daban kafin a shigo falon inda namu yake mahaifin mu kuma nashi a bayan namu yake sai wani dakin da babu komai a ciki

Ashe bayan sun sami gidan sai da suka tsaya suka dan mana sayayya suka saka a gidan kafin su dawo chan gidan

A bakin yaya Ibrahim nake jin komai toh dama mahaifin mu ya saka shi yi mana abinci daidai mu kafin ya sayo mana abin da zamuci shine ya kira ni wai in shigo in koyi yanda ake yin girki gani katuwa amma babu abin da na iya kasancewar shi makarantar kwana yake ni kuma ina yar primary

Sai da muka dau Kwanki hudu kafin abubuwa su yi mana daidai saboda an samo mana makarantar da zamu na zuwa yaya Ibrahim ma an samo mai makarantar da zai tafi ya cigaba da karatun shi dan har ummi an saka ta makarantar itama mahaifin mu ya samu wani karamar shago ya kama haya akan zai fara sayar da abubuwa irin na maza da mata shaddoji da yadi da atamfuna

Ranar da zamu fara zuwa makaranta a ranar ne shima zai fara zuwa kasuwancin sa shi yaya Ibrahim har an kai shi makarantar tun ranar lahadi.

"Mamana.. Mamana"
"Na'ama Abbu ina zuwa"

"Amma dai kin san kun fara makara koh'"
"Abbu ummi nake shiryawa yanzu zan fito"

Shiru ya mana har lokacin da muka fito ni da ummi sanye cikin sabbin kayan makarantar mu wanda yake riga ce iya gwiwa sai doguwar safar da muka saka ya zo mana har gwiwa sai sabbin takalman mu bakake muka kafa hulunan mu na makarantar(Barrett) da abin sunan mu (name tag) goye da jakan mu da lunch box din mu muka fito dama Abbun mu ya saba yi mana girki tun bayan rasuwar ummar mu toh koh a yau din shi ya hada mana abin kari da wanda zamu tafi da shi makaranta

Sai da Abbu ya tsaya ya kalle mu saboda kyau da muka yi cikin kayan dama sabbin kaya kyau suke ma mutum sai kuma muka ga yana share hawaye yana murmushi

"Abbu ka yi hakuri bazamu kara yin latti ba"
A tunani na bata lokacin da muka yi ne ya saka shi kuka kun ji shirme a madadin mu da muka yi lattin mune da kukan wai amma Abbun mu mukewa kallon shine ke kukan lattin da muka yi

Sai yayi yar dariya yace

"Mamana wai baki san kin girma bane wannan shirmen ai sai kanwar ki ummi amma katuwa da ke a ce kina irin wannan wawtar"

"Ba kukan lattin ku nake yi ba mamana"

Yarinta dangin hauka sai na Kara tambayar shi

"Toh Abbu in ba kukan lattin mu kake yi ba kukan me kake yi"
"Oh mamana ina yanzu na gama miki magana akan wawtar nan"yana kallo na

"Toh ni Abbu ka gaya min mai ya saka ka kuka toh"'na yi maganar ina dadaga kafafu na Kamar wata ummi

"Mamana kuka nake yi saboda kun min kyau"a nan ya tsaya bai karasa maganar ba saboda yasan koh ya karasa ba lallai bane mu fahimce shi toh nima ban fahimta ba bare ummi da ke kanwar baya na

Sai na ce

"Abbu toh wa...
Yayi saurin dakatar da ni mamana zo mu tafi saboda kun kure lokaci kar a dakar min ku

Da haka muka fita muka kullo kofar gidan mu ya kai mu sabon makarantar mu ya wuce kasuwa

Bayan Abbu ya tafi ne muka fito domin yin assembly inda ajujuwa daban daban aka firfito mun gama komai za'a koma aji layi layi ake bi da aka kai na su ummi sai na yi hanzarin zuwa gareta na tsareta

"Ummi kar kiyi kuka kin ji Abbu zai zo ya dauke mu in an tashi ki yi karatu sosai kin ji"

Ita dai yarinya ba damun ta maganar tawa tayi ba hasalima murna take yi akan ta samu abokan wasa irin ta koh da na kara ce mata kin ji koh ummi kar fah kiyi kuka sai ta daga min kai ta wuce saboda an kai wurin ta da haka na koma layin mu

Akwai wasu masu min dariya wai ina wani gaya ma yarinya magana kamar wata babba wasu yara biyu ne wanda bazasu wuce sa'oi na ba suka ce eh din ina ruwan su sai kuma masu magana suka yi tsit ni dama ba ce musu komai ba domin a matsayi na na sabuwar daliba bana so a shede ni da rigima saboda ba laifi nima ana ce min kule zan ce cass

Toh har muka kai aji duk mai gulma akai na wadannan yaran ne ke tsawatar musu koh a ajin ma kujerar kusa da nasu na zauna bayan an tafi break ne muka zauna a ajin suka rinka ja na da hira saboda surutu ne da su Kamar me basu san nima din duk kanwar ja ba ce anan nake sanin sunayen su ita dayar mai tsananin haske da kyau itace salma habib dayar kuma wace take da haske kusan irin nawa sai dai ta fi ni dan haske ita ce falmata amodu

Ni ma sai na sanar da su sunan nawa wato Aisha Murad

Kafin a tashi daga makaranta a ranar har mun kulla kawance mai karfi in baka sani ba sai ka dauka mun dade ne tare koh da aka tashi karfe biyu sai na yi saurin tafiya zuwa ajin su ummi saboda hirar mu da sabbin kawaye na ya rinjaye ni sai da aka tashi na tuna cewa ina da wata kanwa

Da shiga na sai tazo ta rungume ni tana min labari wai ga kawar ta sunan ta hasina da mamaki na ce

"Inyee kanwata tayi kawa kenan"da murnar ta ta ce min eh yaya Aisha

Sai na ga kawata salma ta shigo wai ta taho daukar kanwar ta ashe hasinar ce kanwar tata ban sani ba sai ita ke gaya min

Tare muka fito ni,ummi,salma da hasina da falmata babu dadewa da fitowar mu sai ga mota ta tsaya ta gaban mu a nan na san cewa salma  aka zo dauka sai naga sun shige harda falmata wai tare ake kawo su a mayar da su gida kasancewar su din makwafta ne kuma mahaifin falmata kamar ma'aikaci ne a karkashin mahaifin salma kenan salma ita ce yar gidan masu kudin

Sun yi sun yi mu bisu su sauke mu a gida na kiya nace musu ai mu bamu san hanyar gidan ba sai dai Abbun mu ne zai zo ya dauke mu (kunsan in mutum na yaro akwai shi da jin magana ba karya kuma in akace tsaya a nan toh a nan zai tsaya)

Haka suka tafi suka bar mu a tsaye har da ce min gobe in zo makaranta da wuri zasu kori safiya yar kujerar su sai in dawo mu zauna tare mu uku

Na yi dariyar yarinta nace toh amma in aunty ta tambaya fah sai suka ce ai ba za ma ta tambayan ba ai ta san su da rashin ji

Wato na lura da wani abu tun da na je makarantar a yau ita salma fitinar ta har tana so ta fi ta falmata ita falmata nata masifar a ruwan sanyi take yin shi dan koh ana surutu inta kalli mutum ta makamai harara da idanuwan nan nata sai kiji an yi shiru ita kuwa salma baka zo bama bin ka take yi ta cakalkala maka kuma baka isa ka ce a ba kana fadan wani abu toh sai ta nemi ta cakume maka kwalar riga koh ita safiyar da ke zaune tare da su saboda falmata take zaune don ta taba tare mata wani dambe da aka so yi da ita wani rana da aka laka mata sharrin ta yi Satan chocolates din wani yaron yarbawa mai suna Abdulwasi'u Adebolaji toh shine fah yaron ya zo da bala'i akan sai ta biya shi chocolates din shi kokuma ya kai karar ta toh sun ci sa'ar salma bata zo ba a ranar saboda kwana tayi da zafin jiki sakamakon haka sai aka ce ta yi fashin  zuwa makarantar ranar shi yasa har adebola kamar yanda suke kiran shi ya samu damar yin fada da falmata toh ashe ita kuma safiya tana kallo lokacin da aka saka ma falmata chocolates din a jakar ta toh shine fah ta fadi gaskiyar lamrin dan ita falmata a lokacin miskilancin sun motsa tunda ta ce mai ba ita ta dauka ba sai ta mai banza duk abin da yake fada koh kala bata kuma cewa ba

Washegari da salma ta ji shine ta fara masifa har ya kai ta da yin dambe da adebola suka ma juna duka a nan ne ita falmata ke gaya ma salma ai safiya ce ta fadi gaskiya toh tun daga ranar ta ce mata ta zo su na zama a kujera daya domin a tarihi tare suka taso tun yarinta haka ma rayuwar su tare suke komai wanda ya kai da har a makarantar ma kujerar su daya su biyu ne kadai zuwan safiya ne ya sa wasu abubuwan da salmar ke yi ya ragu amma bata so hakan ba sai dan kar ta batawa falmata rai zuwana kuma a yau sai taji tana so na shine take ce min zata kori safiya a kujerar

Duk wadannan labarun a wurin falmata nake ji

Bayan sun wuce kamar da yan mintuna kadan sai ga Abbu ya zo daukar mu da murna muka rungume shi ni uwar surutu koh gaishe shi ban yi ba na fara sana'a wato surutu

Sai da ya ce
"Haba mamana yau ko yar gaisuwar babu sai surutu"

Na dan ji kunya saboda duk surutu na bana manta gaisar da mahaifin mu da safe rana da dare amma sai gashi yau kawai kawaye sun saka ni manta abin da ya zame min jiki

Na dan rufe ido na nace
"Abbu yi hakuri ina yini"

Murmushi ya min ya amsa sai ya janyo ummi yana autar Abbu yau ba magana ne

Da yake yarinyar bata cika kiriniya ba sai ta ce mai

"Abbu kawa,Hasina"tana ta jin dadi tana dariya

Muma dariyar ta bamu wai ita a nufin ta kawa ta yi sunan ta hasina amma da yake babu isashiyar hausar sai ta ke gwalangwalo

Gida muka nufa Abbun mu yace muje muyi sallah kafin mu ci abinci hakan ta kasance mun yi sallar kenan ya bamu abinci ya ce mu yi maza mu gama akwai wani islamiyar da zai kai mu kusa da shagon sa ne a kasuwan in ya so kafe shida in muka taso sai mu dawo gida tare

Mun gama cin abinci da naga bai ce mu zo mu tafi ba sai na yi mana wanka na saka ma ummi hijabin ta nima na saka nawa ai kuwa sai ga kiran shi muka fito muka rufe kofar gidan mu muka wuce

A chan islamiyar kuwa kin yarda nayi a raba mu aji da kanwata sai da abbu ya dan min jan ido kafin in amince

Karatun mu muka yi yanda aka saba yi toh ni dai koh da aka tashemu sallar la'asar sai na ga wasu yara suna ta surutu har ya kaure musu da fada suka zo suna ce min keh ai kina kallo tun dazu koh wai kin ga lokacin da na zage ta

Shiru na musu dan sun bani tsoro yanda suke maganar kamar da ni suke yi dan dayar har kamar zata buge ni toh ni surutu kawai na iya ban iya fadan ba kokarin tashi a wurin na fara yi sai suka hana ni wai walahi sai na yi magana haka fah suka taso ni gaba danaga ba sarki sai Allah kawai ina hango wani malami da sharbebiyar bulala na saka ihu sai kuwa ya juyo ya zo wurin mu yana tambayar ba'asi tun kafin su ce wani abu tuni na riga su na bayar da bayani na dora da cewa

"Kuma fah mallam walahi ban gan su ba koh jin su ban yi ba"na kai karshen maganar ina haki

Ai kuwa ya ce gaskiya ne suka so yin taurin kai sai da aka fara zane su suka ce eh gaskiya ne

Zana sosai aka musu kafin malamin ya ce min in wuce ajin mu kuma duk wacce ta min wani irin kallo in kawo karar ta da toh na amsa

Sauri sauri nayi alwala na na shige wurin sallah daga nan na koma ajin mu ai kuwa ile Sai gasu sun shigo suna ta famar banka min harara ni dai sunne kai na nake yi kamar marar gaskiya ana tashin mu na je na dauko ummi a ajin su muka fito jiran Abbu kafin ya zo wadannan yaran suka zo kusa da ni suka kashe min warning akan in muka hadu gobe Sai na gane kure na

Dayar ce me dan mutuncin ta ke gaya min kawai kar in zo gobe saboda in nazo toh wallahi sai sun min dukan tsiya

Da wannan tunanin a zuciya na Abbun mu ya zo ya dauke mu muka wuce gida

Har dare yayi lokacin bacci yayi na rasa yanda zan yi in ki zuwa makarantar islamiyar mu gobe gashi ban gaya ma Abbu ba har ummi tayi bacci na tashi kamar zan je in gaya ma Abbu amma sai na kasa haka dai na kwana dan yanayin yanda na dauki maganar har mafarki nayi da shi wai sun min dukan tsiya har da rufe ni a wani aji suka bar ni

A sittin na tashi na fara kuka ina cewa ni wallahi bazan koma makarantar nan ba gobe

Da asuba Abbu ya tashe mu muka tafi muka yi alwala muka yi sallah muka yi wanka kafin mu yi breakfast mu shirya muka fito da Abbu kamar jiya haka yau ma ya kai mu makarantar

Allah Allah nake yi mu hadu da su falmata da salma in gaya musu abin da ya faru jiya.....

_*🍒s,Ibraheem🍒*_

Продовжити читання

Вам також сподобається

1.4M 96.7K 24
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...
184K 9K 51
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...
41.5K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah
541K 17.6K 157
Genre: Space, Doting, Farming, Time travel, Healing Synopsis: Xu Linyue from the 21st century crossing over with the heavenly space soul penetration...