🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

SiyamaIbrahim által

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining Több

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 7

680 49 0
SiyamaIbrahim által

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

7⃣

      _Some days after_

 
   Buga ƙofar gidan na yi wanda yayi daidai da tsayawar wannan ɗan saurayin da muka dawo gidan tare da shi the other day wato islam kamar yanda naji hajiya rukayya ta kirashi da

  "Hlo young lady how may i help you"?

Na murmusa na juyo na ce

"Ina kwana"

Sai ya dan dakata kadan wondering a ina ya san fuskar

Gano hakan da na yi sai na yi interrupting short tunanin da ya faɗa yi by saying

"I was with you just 3days ago mu muka taho da wannan patient din tare da metron"

"Yauwa now i remember toh ya kike ya ayyuka""

"Alhamdulilah"

"Toh mu shiga ciki mana i thought kin dawo ne"??

"Eh mun yi da hajiya akan zuwa karshen satin nan zan dawo that is during the weekend"

Ya daga min kai ya ce
"Ok toh mu shiga"
Yana mai bude gate din gidan

  Ni na shiga da kafa shi kuma ya karasa shigowa da motar shi

  Tare muka jero muka shigo cikin apartment din da sallama a dauke da bakin mu
  Shi ya haura sama ni kuma ya ce min "pls seat and feel comfortable let me call her'"

"Thank u"

  Bayan wasu lokuta sai ga ta ta fito tana min murmushi tare da cewa
  "Ƴata ashe dai baki manta da assignment din naki ba"

Na dan yi dariya na ce
"Not at all ma'am ai i was very conscious of the date"

"Hmm that's nice to hear"

Ta karasa saukowa muka gaisa nake tambayar ta about the patient

"Ohh she's good toh ki bari a kawo miki abin motsa baki mana kafin mu yi maganar"

Na dan canza fuskata ina son yin magana

Tayi saurin katse ni da cewa
"Ohh wannan ƴar tawa na lura kamar baki da saurin sabo da mutani"

Sai na ji kunya ta kama ni after all this woman was nice to me tun ranar farko da muka hadu but why won't i be comfortable with her she's very nice

"Kin yi shiru"

"Ma'am toh babu damuwa a kawo tnx a lot"

"Know u are talking"

Wannan datijjuwar ta kira ta ce ta kawo min abin motsa baki

Bata wani dade ba sai gata dauke da tray shake da kayan cime-cime ta ajiye a center table din ta juya ta tafi

"Bismillah ƴata"
A ɗarare dai na taba wani abin na bar shi na ce mata na ƙoshi

"Hah are u for real me kika ci da zaki ce min kin ƙoshi koh dai duk a cikin zumudin jin labarin ne"?

Tana mai leƙo fuska na sai na yi murmushi na ce
"Eh toh kusan haka ne ma'am

  Jijiga kan ta tayi ta ce toh kafin mu shiga ganin ta akwai abin da nake son gaya miki

"Ok ina jin ki"

"Bayan kin tafi sai ga kiran dr Ladan toh bayan na dauka ne yake gaya min cewa ya tafi ward dina kuma ga abin da nurse Ahmad ta gaya mishi sai ya ke tambaya na koh me yasa nayi taking wannan risk din"

"Hmmm dr kenan a wurin ka ne hakan ke nufin risk amma ni a wuri na ba hakan bane saboda na gama lura kana so tausayin ahalin ka yayi overshadowing professional morals din ka shi yasa ni kuma na zare hannuwana a tafiyar ka"

"But Hajiya ina jiye miki matsalar da zai kai ya kawo kin san yanayin abin nan ke kadai na bama wannan labarin"

""A'a dr ka daina kirawo min matsala aimiscun farko na gaya maka yanda za'a yi amma me kayi you put a blind face to what i said har ka doɗe kunnuwar ka akan shawaran da na baka"
"Koh ba'a yi haka ba dr"??

"Jin labarin ka yasa na ce zan taimaka maka because na lura kana an saka ka a ethical delmar amma baka yi duba da hakan ba"

  ""Hajiya walahi ba haka bane ba kuma wai na yi ignoring shawarar ki bane i was hoping that abubuwa zasu lafa bayan na tura musu video clips din nan in yaso sai in yi involving security agents akan maganar but seeing what happened earlier i have to go into a hide ni da family di na"

"Hmm dr kenan toh ka ce ma asibitin me"??

Shiru yayi na dan wasu lokuta kafin ya ce

"I know what to da kar ki damu amma what about the patient? '

"Wannan ba abin damuwa bane i agreed to take the burden all alone ni kuma na san yanda zan yi da ita kar ka damu"

"Toh na gode hajiya zan miki magana duk yanda abin zai kasance"

Da haka muka rabu toh ko bayan kwana biyu that was Friday da ya kira ni sai yake gayamin ai presently yana Singapore tare da familyn shi ashe shima ya riga da yayi visa harda ita patient din akan zasu bar kasar har bayan komai ya lafa in yaso daga chan sai yayi informing security agents da hospital management din akan gaskiyar al'amarin da dalilin shi na yin hakan daga karshe ya sa a yi cigiyar family din patient din

Amma ganin na dauke ta sai kawai ya haɗa kan matarshi da autar shi suka bar ƙasar temporary ba tare da ya sanar da hospital management din ba

Toh a haka yake ce min idan na gama treating din ta ta dawo normal mun samu bayanai akan ta sai mu yi raising maganar zuwa ga hukuma

Muka yi sallama akan zamuna communicating time to time

"Kin ji yanda muka yi da dr"

_Wai wani cakwakiyar sai a ƙasar  wato kawai baka da ƴancin yin rayuwar farinciki idan kayi exposing hidden truth sai dai ka koma kana ɓoye ɓoye kamar kai ne marar gaskiyar saboda kana neman kan ka da lafiya_

  _Allah dai ya sa mu dace_

A cikin zuciya ta nake ayyana wadannan maganganun

"Are u with me"

Firgigit na juyo
"Ina tare da ke ma'am kawai ina tunani ne yanda duniyar ta zama especially a nan ƙasar mu Nigeria shikenan bazaka fadi gaskiya ka kwana lafiya ba sai an nemi salwantar da rayuwar mutum"?

"That is the present resection da muka tsinci kan mu a ciki wanda dole a  ƙara yawan tsaro a ƙasar har da tsatsaurar doka akan duk wanda aka kama da yin wannan act din wato blackmailing da treats to an innocent citizen"

"Haka yake kuma dole media su ƙara daura bambarar yaƙi da ire-iren wadannan mutanen by exposing any single misbehaviour da aka kama mutum nayi ba tare da cewa sai an tsaya samo wasu evidence ba by so doing wasu mutani har da wasu media presenters zasu falga su yi taka tsantsan da wannan da aka kama da misconduct

Da haka ta ce min taso mu haura tana nan na bar ta a zaune ma ba laifi muna samun great improvement

Haurawa muka yi tare da ita zuwa dakin


    *_THE MJ RESIDENT_*

  Horn yake dannanwa kamar wani sabon kamun hauka

  Da sauri mai gadin ya farfado daga ƴar karamar baccin da ya fara kusan mintina goma da suka wuce harda yayi ƙoƙarin gani baccin bai dauke shi ba gudun cin mutuncin da zai iya fuskanta daga wurin wannan ɗa marar ɗa'a da mutunta mutani

Sauri yayi ya bude gate din a daidai lokacinda aka yi horn din a karo marar adadi

Tun kafin baba mai gadi ya gama buɗe gate din ya matsa tuni ya danno kan motar da wani irin speed saura kaɗan ya ingiza baba mai gadin ba dan ya matsa ba toh tabbas da gadon asiti ya samu baƙo

A zuciye yayi parking motar ya fito yana dumfarar baba mai gadi wanda a lokacin har ya fara karkarwa domin kuwa zufa ya fara keto mai

Yana zuwa ya fara sauke mai kwandon masifa da bala'i ta inda ya shiga ba ta nan yake fita sai da ya dau lokaci yana zazzaga ma wannan tsohon da zai yi jikan jika da shi kafin ya ɗora da

"Matsiyaci ai bai iya samun wuri ba in ba haka ba har wani bacci kake da lokacin yi a matsayin ka na ƙasƙantacen mai gadin wannan gida iye?ka bani amsa koh dan ku talakawa baku iya samun wuri bane?

Wannan ya zama na farko kuma na ƙarahe da zan dawo gidan nan ina danna horn kana ɓanata min lokaci kafin ka zo ɓude min gate ka fahimce ni ko a'a? "

Abin tausayi wannan tsohon da yake ta faman bashi hakuri yana roƙan shi da ya yafe mai yayi saurin girgiza kai

"Ka ga tsiyar ya zaka jijiga min kai kamar wani zombie ka buɗe baki ka bani amsar abin da na tambaye ka"

Ya karasa faɗa yana daka mai tsawa

"E.. Eh..Ehhhhh na ji ranka ya daɗe"

"Nonsense illiterate coward mtsw"

Ya ja wani irin doguwar tsaki yayi gaba

Shi dai baba mai gadi bai san ma'anar abin da ya gaya mai da harshen nasara ba amma ya san ko ma dai menene abu ne marar kyawun ji duba da yanda ya ja tsaki kafin ya bar wurin

  Baba mai gadi ya koma post din shi ya zauna shiru za tausayi yana jinjina al'amari irin na gidan nan tun da yake bai taɓa aiki ya fuskanci irin wannan matsala da ƙasƙanci irin wannan ba daga ɗan ƙanƙanin yaro da yasan ya yi jika da shi ba

Oh duniya yanzu neman halalin kan ka ya zama hanya da za'a yi amfani da shi a ci mutuncin ka a ƙasƙanta ka ciki har da wadanda basu kai yi maka kallon banza ba amma saboda Allah ya haskaka tauraron su sai su wulaƙanta ka

Allah ya shige mana gaba ya tsirar da mu da mutuncin mu

Yana shiga cikin babbar parlorn ya fara ƙwala kiran ma'aikatan gidan yana faman basu order

"Martha marthaaaaa"
Ta fito da sauri har tana tuntuɓe ta iso gare shi tana haki ta ce

"Ye...yeess sir" har numfashin ta na sama sama

"You disgusting fish where were you that you couldn't answer me on time you made me strain my voice in calling your ugly name? Huhh?

Tana ɓari ta ce mai
"Am so sorry sir i was trying to clean up the restroom i didn't hear you sir pls forgive me"
  Ta ƙarashe tana durƙusar da kanta ƙasa

  "Idiot" ya cigaba da tafiya yana bata order

"" go get my stuffs and call barde to come and clean that car"
"Ok sir"

Ya wuce zuwa sama yana sake kiran wata mai suna Tina yana mai bata dokar ta saka mama hari ta hado mai coffee ta kawo mai

Ya haura zuwa dakin shi da zuwan shi ya tuɓe ya yi cikin toilet din shi da ke cike da kayan more rayuwa ya shige cikin bathtub ya yi kwanciyar shi yana hararo irin farin cikin da mahaifin shi zai yi in har ya ji abin arziƙin da yayi ya murmusa yana ƙara jinjina ma kanshi da alfahari da ilimin shi

Wayar shi da ke gefen bathtub din ya dauka ya danna wasu numbers ya yi dialing ya saka a kunnen shi

Bayan wasu ƴan seconds sai aka ɗauka sai ya saka wayar a handsfree ya ajiye a saman bathtub din saboda ya samu damar expressing farin cikin sa da kyau

"My boy how are you i thought you were angry with me because i stopped you from going to close the deal"

Sai da ya dan yi murmushi kafin ya magantu ya ce

"Nahh dad ai hana ni tafiyar da ka yi shi ne daidai saboda akwai surprise mai girma da na tanadar maka"ya kai karshen maganar yana wani murmushi da lumshe idon shi

  Cikin mamaki baban ya ce

"Wow my boy wani irin surprise kenan ka tanadar min"

"Ohh dad ka cika wayo da yawa ana gaya ma mutum surprise ne"?

"Well if you are that eager to tell me you can just say it ai ba wani abu am your dad"

"Nooo dad bazaka min dadin bakin da ka saba min ba am now a big man remember"

"Hmmm i see"

"Dad how did it went"

"Ahh smoothly mun gama komai i was able to convince them to sign all the papers kuma sun yi sun amince da mu haɗa hannu mu yi aikin tare kuma sun siyar min da wani share daga cikin investment din su,, ka ga tafiya na yayi amfani shi ya sa ma na hana ka zuwa because i know had it been na bar ka ka tafi da Bp di na ya tashi because you will easily give in a yanda suke da tsauri din nan gashi kuma kai ba ka da ilimin tafiyar da mutani a siyasance har ka sami abin da kake so nevertheless it was successful""

Already ya fara harzuƙa da maganar dad din shi amma wani zuciyar ta ce mai chill MJ ai yana haka ne saboda bai ji abin farin cikin da ka mai ba ƙara haƙuri har ya gama sai ka sanar da shi

Da wannan shawarar ya yi calming kan sa har dai ya gama sauraron mahaifin na shi kafin ya fara magana

"Am happy for the success dad am proud of you yaushe zaka dawo saboda in fara shiyawa dawowar ka"

  Da mamaki baban na shi ya cire wayar a kunnen shi ya duba sunnan ya gani eh fah shi din ne ba wani ba but how comes bai yi reacting ba shi ya dauka yana gama faɗa mai maganar zai mai halin da ya saba ne amma sai ya ga akasin haka instead har tambayar yake yi yaushe zai dawo.. So strange

"Next week my boy"

"Oh dad but next week yayi nisa da yawa surprise din might not trill you yanda ya kamata"

Dama ya sani in dai shi ne haka yake da gajin haƙuri duk kannen shi sun fi shi hangen nesa shi yasa in har abu irin haka ya taso is either ya tura kannen shi kokuma shi ya tafi da kan shi saboda in har ya biye ma wannan toh lallai da ya daɗe da fuskantar ci baya a al'amurar shi gashi Allah ya ɗora mai son shi a zuciyar shi being the first son after 15 years of marriage kafin Allah ya basu shi duk abin da yake yi yana sane kuma da taimakon shi ya taɓarɓare saboda komai yake ɓukata ana mishi shi tun da ya taso bai san a'a ba bai san ba yanzu ba bai san babu ba komai yace yana so yakan same shi immediately tun uwar shi na hanawa har ta barsu shi da mahaifin shi ta zuba musu na mujiya kawai saboda duk abin da yayi uban praising din shi yake yi shiyasa har yanzu da yake dan kimanin shekaru talatin da uku 33 bai da wayon ko sisi bai iya komai ba sai taɓara abin da yasa uban baya bashi ragamar yi mai businesses din shi kenan

"My boy you can just give the heading sai in ga cikaken surprise din when am back koh ya ka gani"

"Dad ka dai yi nasarar kamo ni toh shikenan"

"Dad guess what"
 
Baban yayi dariyar manya yace
"My boy ka mayar da ni karamin yaro kenan toh ina dai jin ka carry on"

Sai da ya dan tsaya yayi murmushi shi kaɗai kafin ya ce

"Finally i was able to plug the unwanted flower in my garden dad"

Da mamaki baban ya ce
"Unwanted flower in your garden? ban gane ba"

Sai da ya dara ganin dad din shi is interested in the surprise

"Dad ciwon idon mu na samo mana maganin shi cikin ruwan sanyi"

Again an incomplete sentence

Yace "my boy go straight to the point am getting fed up already"

"""Hmmmm dad i know that you will be proud of me kuma daga yanzu komai naka zaka na involving di na a ciki saboda ban taɓa yi maka abin farin ciki ba kamar wannan"
Ya cigaba

"Abdulrahman Abdulsalaam has been captured for the past 6 days by me"

"Yaron da yake takura mana rayuwar mu yake hana mu rawar gaban hantsi yake saka ka comparing di na da shi mai shegen girman kan tsiya da alfahari mai jin kan shi kamar wani sarki is now under my feet kuma sai na take shi son rai na dad i wanted you to return and see him da kanka amma gashi ka min wayo har na baka headline din but ai bai ɓaci ba dad na san yanzu ka matsu ka gan shi da kaji shine surprise din koh dad"?

Tsit kamar ruwa ya cinye shi yayi kafin ya ce
"Wani Abdukrahman Abdulsalaam din"?

Ya wani dara irin an yi abun kai din nan yace
"Dad shekaru sun fara ja jin ka ya fara raguwa i mean Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor""

Ai a 360 ya tashi sai jin fashewar abu yayi ta wayar kafin ya ce A ya ji wani irin mummunar tsawar da tun da yake dad din shi bai taba mai irin shi ba

"Majeeeeeeeed"
Ai shima a 360 ya mike tsaye rike da wayar a hannun shi

"When have you become a mentally ill patient yaushe ka fara zama mashayin da shaye-shayen shi ya fara nuna musu karya yaushe zaka daina wargaza min lissafi ne kai wani irin dakikin yaro ne ni a matsayi na na uban ka ban taba yin gigin gwada wannan abin ba sai kai da kake dan fitsitsi da kai kai da baka san komai ba sai abin da ka tsinta a sama?? Har yaushe zaka san da shashancin ka ake cinye mu a abubuwa na sauka gatan da na maka ya isa ya sa ka ka zamo abin alfahari a gare ni mai share min hawaye na wanda zai kwato min abubuwan da na rasa a rayuwa na amma i was wrong you always bring me down am telling you today Majeed Muhammad Ja'afar nayi danasanin haihuwar ka you have never bring any good to me kullum sai disappointment turrr da halin ka kuma ka san yanda zaka yi ka yi releasing din shi ba tare da yasan ni mahaifin ka bane kafin in dawo useless boy kawai""

Kitt ya kashe wayar shi

Ai bai san lokacin da ya fada cikin bathtub din ba yana tariyo maganganun dad din shi wanda suka mai bugun dalma tundaga kan shi har kafafun shi

Rike wayar yayi da kyau ya yi dialing wani number ringing biyu a na uku aka dauka

Bai tsaya jin komai ba ya fara magana

"Duk inda kika kai YARINYAR NAN ki je ki fito da ita na baki nan da awa arba'in dad biyu"

  Dif ya kashe wayar tare da mai wani irin muguwar wurgi

Wayar ta tarwatse a tiles din toilet din ya koma ya kwanta yana nishi,,,,,,..


  _Toh fah "ta fito da YARINYAR NAN duka inda ta kai ta in the next 42hours" waccece wannan kuma... Domin jin koh waccece ita mu hadu a next page_

_*🍒s,ibraheem🍒*_

Olvasás folytatása

You'll Also Like

40.4K 901 9
I am Elizabeth Swann's older sister. I was the only one who ever fell for Norrington. This is the story of how we came to be. Our story is one of lov...
41.6K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah
26.9K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
660K 23.7K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...