🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 5

847 60 5
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

5⃣

 
    _"Dr me zai sa baza ka rubuta resignation letter ba tunda kaga kana da asibitin kanka da kake running which is under your control kana da NGO's da kake programs sosai haka nan kana da isashen kudin da zai ishe ka yin rayuwar ka har ma da yet to come family din ka..., ka ga idan har ka rubuta resignation letter din nan you can be able to stay away from those heartless men at same time fasten ur visa saboda ku yi ku bar kasar nan kamar yanda maman su khadi'atu ta gaya maka ka ga idan ka yi hakan babu wanda zai fuskanci wani abin hakazalika babu wanda zai zarge ka da cewa harda saka hannun ka a abduction case din nan balantana a yi ceasing license din ka akan cewa kayi wrong practice wa patient_
  _A yanda na lura your reputation can be ruined easily in har ka tsalake maganar su kokuma kayi yunkurin fallasa su kamar yanda suka gaya maka kuma gaskiya tsakani da Allah ba yanda za'a yi mu cigaba da ajiye wannan yarinyar a wurin nan ba tare da hospital authority din nan sun sani ba kai kan ka kasan ana sanin wannan issue din kashin mu ya bushe daga kai har ni da ban san da maganar ba sai yanzu hakazalika idan ka yi la'akari da suffar yarinyar nan zakaga cewa ba daga gidan wahala ta fito kuma babu sanin ahalin ta akan bacewar ta su kansu na san ba'a barsu haka nan ba if not da an fara neman ta tun jiyan duba da sunan familyn da take amfani da shi.._

  _Saboda haka likita ni dai in zaka bi nawa shawaran ka yi abin da na ce maka ni kaina zan fara annual leave di na in d next 5 days saboda sa'adatu zata dawo next week(deputy metron) kai kan ka kasan halin ta sarai bazata taba amincewa da wannan labarin naka na boge ba hasalima tana ji kara zata kai zuwa authority in ko haka ya faru mai kake tsammanin zai biyo baya??_

   _"Asirin da kake kokarin rufewa zai bayyana rayuwar family din ka zai kasance a tangarda kafin jami'an bincike su shigo lamarin killa ma sun cutar da ku before then"_

_Kuma kana sanne da cewa tana da ciki we can't commit such a hug crime by seducing her with toxins a jikin ta gaskiya am not a murderer so the earlier the better likita ni dai iya abin da zan iya gaya maka kenan a matsayi na na ƴar uwar ka a musulunci and not as a professional colleague_

_Ka yi tunani da kyau likita idan aka ce ƴar cikin ka ne hakan ya faru da ita ya zaka ji ya zaka yi reacting_




Tsawon mintuna bai iya min magana ba karshe dai tashi yayi yana share zufan da ke ta tsatsafo mai ya ce min zai yi tunani a kai

   Har ya kai kofar fita daga office din na dakatar da shi na ce

  "Likita da ka shigo wa ya bude maka gate kuma wa ka hadu da shi a harabar ajiye motoci"??

  Sai ya dakata ya juyo da dan mamaki yana duba na nace mishi "yes i need to know saboda mu rufe musu bakin su if not za'a sami matsala"

Ya kuma sharce zufan kan fuskar sa ya ce min

"Anthony ne ya bude min gate while na hadu da baballe a parking lot"

Na girgiza mai kai ina mai kafe shi da ido na
"And the diagnosis"???

  Daga kan shi sama yayi kafin ya bani amsa da

"They are all fake diagnosis Hajiya lafiya kalau aka kawota hasalima kamar daga bacci suka dauko ta"
Ya ida maganar yana juya fuskar shi zuwa gefe saboda sun riga da sun rikiɗe zuwa jajjaye "sai kuma ya ban tausayi
Wato idan kaddara zata sauko ma mutum haka Allah ke lamarin sa dole sai ya saukko maka just last week yake zagaye asibitin nan da family din shi kafin ƴaƴan shi su koma inda suke karatu amma sai gashi wai wannan mummunar kaddarar ta sauko mishi ba tareda ya shirya ba.. Al'amarin ubangiji kenan""

"Dr ka cigaba da addua'a Allah zai kawo maka mafita don't loss hope kaji? "

"Nagode hajiya i will think about what we discussed"

Na yi shaking kai na a haka muka rabu

  Bayan fitar shi ne nikuma na aiki daya daga cikin securities  din na ce  ya kirawo min baballe bayan baballe ya zo ne na sa ya kirawo min Anthony

Shi dama Anthony ya kware wurin raha da wasa yana shigowa ya fara "maman mu me zamu samu anshe kana kiran mu"cikin gurbatacciyar hausar sa wanda ya saka kowa darawa daga nan ya karasa shigowa office din yana mai cewa ""yannmatan mama kun ji wei likita zai yi releasing naku gobe koh..suka kara darawa domin sun san tony(anthony) da barkwanci though hausar bata zauna mishi ba

Mun gaisa da ba'a na nuna musu wurin zama suka zazzauna

dukka hadasu nayi na kalle su na wasu lokuta domin ni kaina ban san ta ina zan fara musu bayanin nan ba

  "Baballe nasana jiya ka ga shigowar dr Ladan asibitin nan wuraren karfe 3:00 na rana koh ba haka bane"?

"Eh hajiya na gan shi dan har tambaya na yayi akan ban tafi gida ba har yanzu na ce mai sai anjima kadan saboda Ina jiran wani aike ne da nayi"

Na juya zuwa ga anthony na mai same tambayar da na yi wa baballe shima amsa min yayi da eh shi ya budewa likita gate da zai shigo asibitin

  "Toh ku saurare ni da kyau ku ji abin da zan gaya muku bana son ku min bahaguwar fahimta kuna ji na"??

Suka jijiga kan su

    Tiryan-tiryan na fara musu bayanin abin da likita ya gaya min kafin in dora da ce musu
""Ina so wannan maganar ta zama sirri a tsakanin ni da ku kawai kar ku bari wani ya ji koh da nan gaba wani abu zai taso ku yi kokarin boye wannan sirrin kun dai ji yanda halin rayuwar familyn dr yake ciki koh"?
  Cikin jimami suka girgiza kai tare da yi min alkawarin zasu yi kokarin riƙe wannan amanar at any cost

  Hakan da suka yi ya sa na sami relieve at least i won't carry the whole burden all alone akwai wadanda zasu iya bayar da shaida koh da wani abin zai taso nan gaba wanda bana fatan hakan ya faru

Na sallame su tare da yi musu godiya mai yawa

"Toh koh da aka cigaba da injecting yarinyar nan da allurai iri kala daban daban hankali na baya kwanciya saboda a kullu yaumi kallon ƴar ciki na nake mata ban sani ba koh dan ban da ƴa mace ne shiyasa tausayin ta ya ninku sama da yanda nake ji akan sauran patients di na"..

Haka kullum birkicewar yarinyar nan ke canzawa kuma kullum sai dr Ladan ya dau videon ta ya tura musu
Duk wannan budirin nurses din mu are not aware of it saboda a nasu tunanin wata ce very close to dr Ladan shi yasa yayi abin gaba gaɗi (kun dai san halin wasu unethical nursea marasa passion ma aikin su da..... Hmmm ban karasa ba lolz)

""Until that faithful day that u came a ranar dama nayi niyyar fitar da yarinyar nan ko ma mai zai faru ya dade bai faru ba domin na ga dr is not ready to help this innocent girl kawai shi dai tsoron sa family din sa""

"Kin san me??"
Ta min wannan tambayar na girgiza mata kai na in total shock of labarin da naji

   Ta ce min a lokacin da kika shigo sai da Anthony wato wannan gateman din da ya tsare ki da tambaya
Na yi nodding kai na
  Ta cigaba
"Ya kira ni ya gaya min cewa wata matashiyar yarinyan ta zo wurin patient din da dr Ladan ya kawo kuma shi yayi yayi akan ta wuce amma samm taƙi gashi shi yana tsoron barin ki ki shigo ƙilla kin zo yin harming patient din ne

  Na yi murmushi na ce mai ya ce kin nuna mishi ID din ki yace min eh sai na ce ya bar ki ki shigo shine ya bar ki kika shigo din nan

   "Tana kaiwa nan ta dago kan ta ta kalle ni ta ce toh kin ji iya abin da na sani akan wannan patient nawa mai suna Aisha murad Abdulsalaam""

In total amusement nace lalai wannan labari da na ji ya nuna min a kwai babban labari behind all these problems

  Ta ce sosai sai dai su da sanin cikaken labarin sai a baki ta which will be very hard for now saboda she is still in shock

Sai na kara tambayar ta "but ma'am me yasa kika dauko ta  har gidan ki kuma naji dazu kina ce ma baballe zai ji ki anjima da dare??"I was so confused

   

"Hmmmm abubuwa da yawa suka saka ni dauko ta kuma ai kin ga harda ɗa na na saka a issue din""

 
Babban abin da yasa na daukota shine kin ga na gaya miki family name din ta wanda ya kasance shaharare ne kuma sunnan wani hamshakin mai kudi ne (Abdulsalaam) though ban san relationship dake tsakanin ta da shi mai sunan ba since akwai middle name kafin sunnan shi wannan shahararen family din(Murad)

  Toh a gaskiya idan har na bari aka san cewa a facility din mu aka yi treating dinta harda seducing din ta zamu jawo ɓatanci ne ma wannan asibitin wanda sai dai wani ikon Allah both ni da nayi admitting din ta da shi dr Ladan din da ya kawo ta kin san mutani da son zuciya baza su yi reasoning da condition din shi ba da wanda family din shi suka shiga ba zasuyi denying ne saboda kar a ɓata musu suna a ƙasar da wajen ƙasar ba ki ɗaya kuma in kin duba ai babu wanda zai so a shafa mishi kashi koh ba haka ba
Ta karashe tana mai juyo da tambayar ta kaina
  Jijiga kai na nayi na ce haka ne gaskiya

 
Cikin gamsuwa ta daga kan ta tace min

"Toh kin ji dalili na na farko
"Dalili na na biyu shine tana da danyen ciki wanda in har na barta aka cigaba da ɗura mata allurai marasa dalili zai iya ɓarar da cikin yin haka kuma tamkar taimakawa ne koh ma bayar da gudunmuwa wurin yin kisan kai"

Dalili na na karshe kuwa shine tana matuƙar bani tausayi ita da iyayen ta.. Alƙawari na dauka koh bazan cika gabadaya ba zan kwatanta cikawa wato in ga cewa ta samu lafiya na taimaka mata ta koma gurin iyayyen ta saboda ta shiga min rai ji nake yi kamar ƴar da na haifa ne da kai na maybe is as result of Allah bai taɓa bani ɗiya mace bane kuma duk ƴaƴana biyu maza ne""
  Kaiwa nan sai ta share kwalla ni ma sai ta bani tausayi saboda na lura ta na da son ƴaƴa mata

  "Shi kuma baballe da na ce mishi zamu hadu anjima abin da ya faru shi ne bayan na yi dr maganar yarinyar har na gaji sai kawai na yi shawara da zuciya na akan kawai in dauke ta duk abin da zai faru ya farun
A lokacin ne na kira baballe na nuna mishi nufi na kuma na ce mai in har dr bai yi responding ma maganar da muka yi da shi ba then ya kasance cikin shiri a kowani lokaci ina iya neman shi in ya so ni da kaina zan taimaka mishi ya bar garin shi da iyalan shi har dai lokacin da komai zai lafa
Ni nabashi shawaran zuwa authorityn asibitin ya sanar da su zai yi wani tafiya kuma zai dade kafin ya dawo in yaso sai suyi replacing din shi da wani temporary kafin ya dawo tunda ya dade a wurin kuma an amince da shi sosai ni kuma zan ba shi abin da zai dasa wani ɗan sana'a da zai kula da iyalin shi kafin ya dawo bakin aikin shi

  sai da nakara yi mishi wata ƴar karamar nasiha na nuna mishi cewa wannan aikin ya dauka a matsayin jihadi ne zamuyi daga ni har shi

"Ranki ya ɗaɗe ai ba sai kin min komai tunda na fara aikin tuƙa ma'aikatan asibitin nan ban taɓa samun matsala da ke ba koh daidai da rana ɗaya ne hasalima ban taɓa jin an yi wani magana akan ki na ɓatanci ba saboda haka ni na miki alƙawarin inshaAllagmhu zan taimaka miki mu yi wannan jihadin tare Allahu ya bamu ladan yin shi ranki ya daɗe""
Amsar da ya bani kenan wanda ya sa na ƙara samun ƙarfin gwiwar yin abin da nayi niyar yi

 
   "Toh fah da haka muka rabu bayan kamar kwana biyu sai ya same ni akan cewa sun yi maganar an barshi ya tafi amma da ƙyar dan sai da ya rubuta a paper aka yi printing kafin su barshi akan zai sanar da su ranar da zai tafi saboda wanda zai yi replacing din shi ya yi resuming

Abin ya min dadi sosai na mai godiya

"Toh a ranar da abin ya faru shine nace mai ya kasance cikin shiri saboda su yi saurin barin ƙasar kafin maganar ya yaɗu""

"Kin ji dalilin koh",,,,
  "Eh na ji kuma na jinjina ma ƙoƙarin ki amma one more question ma'am
"Ina jin ki"

"Me kika gaya ma colleagues din ki about the issue"?

"Nurse Ahmad na wa bayanin komai na dora da ce mata ta bawa dr paper da na ajiye a cikin drawer dina
Abin da ke paper kuwa ba komai bane illah tunatar da shi akan maganar da muka yi da shi 4days ago da kuma plan di na na dauke ta..

Na ƙara da ce mai idan wannan saƙon ya riske shi toh ya tabbtar da ya san nayi shi da ahalin shi coz ni babu abin da ya shafe ni dan ba da ni aka kawo ta asibitin ba kuma babu wanda ya isa ya titsiye ni akan abin da ban sani ba

"Hmmmm (wani kayan sai amale) abin da na fada a zuciya na kenan kafin in numfasa"

Ta juyo ta ce min "ɗazu da na kai ta sama na amsa wani kira wanda nurse Ahmad ne ta min"
  Sai ta dakata kafin ta dora

"Koh kin san me ta ce min"??
Nace "a'a

"Ce min ta yi bayan mun bar asibitin da wasu mintuna sai ga dr Ladan ya shigo duba patient din sai ta kira shi cikin office din kafin ya karasa bed din
Bayan ya shiga ta nuna mai papern da kuma sanar da shi ta san komai in fact dukkan su sun san komai
  Ta ce min he was shocked for some minutes kafin ya bar ward din

"Toh har yanzu ban ji komai ba daga gare shi jiran kiranshi kawai nake yi""

"" Iya abin da na sani kenan akan wannan patient mai suna Aisha Murad Abdulsalaam""

"Amma in kina son sanin cikaken labarin ta kina iya dawowa koh da cikin weekend ne sai mu gani if there is improvement a lafiyar ta da har zata iya baki wani abin toh"

"Amma dakata wani hanzari ba gudu ba kin gaya min inda kika sami labarin bacewar wannan patient din amma baki gaya Mon yanda akayi kika san tana nan wurin ba??

Na dan numfasa kadan kafin in dora da cewa

"Nurse Ahmad"

Cikin wani irin kallon ina neman karin bayani tace min

"Nurse Ahmad"? How?

"Well kinga mun dade muna communicating da ita tun lokacin da ta karanta wani article da na rubuta sai ta kira ni ta min magana tace min ta ji dadin article din kuma she is proud of my writing

Toh tundaga lokacin muke waya lokaci lokaci

Koh da wannan abin ya faru kamar wasa sai ta kira ni take gaya min akwai fah wata patient da aka kawo facility din su kuma daga dukkan alamu tana zargin matar da aka ce ta bace ne a shekaranjiya case din da ya fito daga Abuja kuma ita ta duba file din ta taga history din ta kuma tana ganin kamar illegal case ne saboda dr da ya kawota shi kadai yake treating din ta daga shi sai metron din su

Ta ce min if am interested ina iya zuwa in duba da kaina sai in fito da labarin ya bi ko ina

Ni kuma a lokacin ban ma ji labarin ba sai na shashantar da maganar kawai na ce mata ta bar shi kawai
She insisted amma na ki

Mun gama wayar da ita kenan na shiga shafin sada zumunta sai na fara cin karo da labarin bacewar wadannan mutanin  sai na fara ganin Newsline harda news paper akan issue din kuma ana maganar ba'a san inda suke ba

Ai ban kai karshen karatun ba na fara tracing labarai da suka gudana a kwanakin a nan ne na fara hada yanda zan  ɓillowa lamarin

Sai na kirata nake kara tambayar ta akan ta ƙara bani labarin case din
Ta labarta min kuma ta ɗora da cewa are you interested in the case

Na ce mata eh but sai na kara wasu kwanaki saboda idan na zo in tattaro cikaken rahoto

Na ce mata ta taimaka min da monitoring patient din ta ce min toh

Ana haka ne har na kai kwanaki uku kafin in iso asibitin bayan ta min kwatance

Ita ce ta ce min in nazo in nace ma gateman din har sai ya bar ni na shigo tamin kwatance ward din har ma da bed number din

Toh koh da na zo ban gane ta ba saboda dama can ban santa ba itace ta san ni so ita ce ta gane ni har ta min signal ta ce min ai itace nurse din nan da muke magana

"Kin ji yanda na san cewa barnawa aka kawo missing patient din"

   cikin gamsuwa da bayanin da na mata ta ce

"ki ce dai nurse Ahmad tana cikin team din mu amma bata gaya min ba hala tsoro ta ke ji"

Na yi dariya na ce "ma'am har kin ba ni dariya walahi"

  Na mayar da littafi da biro na cikin handbag din da nazo da shi tare da stopping recorder di na duk na mayar a jakan na tashi ina mai gyara rolling di na

"Nagode sosai hajiya da kika bani time din ki har ma da full attention din ki kuma ina mai ƙara jinjina ma namijin ƙoƙarin da kika yi Allah ya baki lada inshaAllah zaki ji ni zuwa weekend din"

Ta rako ni har zuwa gate din gidan ta danna wasu numbers karamin kofar gate din ya buɗu

Muka yi sallama na tafi itakuma ta koma cikin gidan,,,,,,,,.......

  _*🍒s,ibraheem🍒*_

Continue Reading

You'll Also Like

41.6K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah
158K 9.9K 45
Elizabeth has been ruling her kingdom for 3 years now. She's gone through countless advisors in those 3 years. When she's finally ready to give up on...
83.2K 6K 67
a love story, this is a love triangle between 4 lover's.
433K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...