TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

173K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

38

3.5K 320 18
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad 68billygaladanchi.

      38

Harara sarauniya hassy tabi bayan Meenal dashi, har ita munafuka ce, gani take kamar tafi kowa wayo ita a zatonta cewar bata fara gano k'ulle k'ullen datake bane, waye ze yarda ya sauka daga kan mulki akan biyan buk'atar wani?, lallai zata nuna mata duk wanda ya rigaka kwana seya rigaka tashi kuwa, zata wayi daga ita har Takawan sun shek'a lahira, shirinta baze tafi akan gubar ba sabon zubi zatayi.

    Asha ta kira bayan sun zauna ta kalleta da kyau tace

"Asha, kin sani banida wata amintacciya sama dake afuk fad'in duniyar nan, sannan keda kanki bawai dad'in yanda aka wulak'antamu kikajiba tunda yake yanzu kema dole ki dawo baya, sannan kuma kinga dai yanda muke wulak'anta mutane a masarautar nan, daga haka fa baya zamuci kuma kowa ya kwaso kashin sa se a saman kanmu, dan haka aikine zamuyi na had'in kai matso kiji kawo kunnenki"......... Yanda zasuyi komai ta zayyane mata se jinjina kai takeyi alamar gamsuwa.

Meenl da dama yana cikin shirinsu tunkan a mayar da sarauniya hassy nan gidan ta sanya camera's ako ina banda ban d'aki, duk inda take da buk'atar sanya abun saurare kuma ta saka ako ina fa, kallon su takeyi acikin system nata tana nazarin maganganun Sarauniya hassy, ko shakka batayi sarauniya hassy ta sauya plan akan yanda suka tsara, matsalar batasan ko meye ba? Batasan metace d'inba ta dulmiye komai, cikin tashin hankali ta rufe laptoo d'inta ke gabanta ta mik'e tsaye tana zagayar d'akin, har yanzu akwai abubuwa da dama agabanta, ta aika katin gayyatawa wa Gimbiyar Rusau, tanaso suma tasan takunsu tunda hakane kuwa dole ta duba, k'ara janyo system d'inta tae bayan ta zauna ta kunna shi ta lalubo b'angaren datakeso, hannayenta duka biyu ta d'aura asaman hab'arta bayan data had'esu wuri d'aya

"Bana buk'atar komai se gawar sa wlhy, menene amfanin wannan yaron, ada nace bazanyi kisa ba amma a yanzu d'ayan biyu, idan ma kisan baze yiyu ba tokuwa tabbas a b'atar mun dashi daga doron k'asa bana buk'atar ganin sa" Murmushi Waziri yae

"Kidai bi a hankali gimbiyar Rusau, karki manta Takawa shine uban jikokin ki, idan dai kikai hak'uri ko wasu 'ya'yan ya haifa nan gaba Hidar fa shine magajinsa, sarki yanada tsaro ke kin sani, tun b'atan sarki jalal sarakunan masarautar nan sunada tsaro me tarin yawa tayaya kike ganin zamu b'ullowa wannan tafiyar? Idan kika koma b'angaren mulki, iko da jin sarauta gayamun acikin sarakuna goma dasuka gabaci sarki meci yanzu wane sarkin ne yakaishi jin mulki da hayak'insa akai? Wann nene ya kaishi Ilimin addini dana boko aciki? Wa yayyen mutum ne baze tab'a yadda yaje inda zamuga damar shisba, baze tab'a sakewa da tsofaffin kuyangin muba, suturu ma haka, boka ne kurun ze iya mana wannan aikin kuma kinji dai meya faru dashi wata masarautar yawa aiki akan sarkin su bincike yakai har kanshi aka kasheshi, banida wani gata bokan mu na Niger ma ya d'auki tsananin fushi sabida duk sanda yae magana se bokan Sarauniya Ameena ya k'aryata kuma ta zauna hakan shine yae fushi akan baze k'ara yi mana aiki ba, ki sani masarauta fa ta sub'uce mana sedai sabon shiri kuma dazamuyi akan dawowarta hannun mu kota halin yaya ne" Sauke nannauyan ajiyan zuciya tae cikeda takaici, seda ta kutsiri goron dake hannunta dan gani take shi kad'aine ze taimaka mata sannan tace

"Iskar Garin ma kwata kwata zafin ta nakeji wlhy, komai takaicin sa nakeji, babu ma wanda yafi bak'anta raina sama da Me martaba, in hanashi yin abu amma seyace dole se yayi nina tabbatar ba banza aka barmun shiba" Waziri yanaso yae magana game da wancen sarki dasuka had'u besan mekesa duk surutun sa ya kasa furta kalma game da wani abu daya shafi Sarki jalal ba watak'il madai mugun mafarki ne yae. Haka suka gama tattaunawa basu samu wata mafita ba har taron ya watse!

*************
      Lokacin duba system ne awurin meenal, bata buk'atar ranar walimar ta samu matsala koda k'waya d'aya ce kuwa, Zaman dirshan tayi akan gadon dukda tana fama da ciwon mara kwanakin nan aganinta period ne zezo mata dan haka bata wasu 'yan damu ba, dama kuma tanaso taje asibiti sabida ta wuce lokacin period d'inta da kusan sati biyu hakan kuma ba sabon ta bane ba sam, duk yandabtae 21 day's da gamawa to dawuya time d'in ya wuce batare data yi wani ba. Kamar kullum yauma b'angaren sarauniya hassy take lek'awa sabida tsaro, tana cikin rud'u ganin batasan me suka tattauna da kuyangar taba a wancen lokacin, tasha mugun takaici kam sabida bawai tagama yarda da hassy bane ba, mamakin ta be k'aruba seda taga sarauniya Daurama a gidan hassy suna tattaunawa

"Yanzu ke hassy da sauran jininki a jiki zaki yarda ki zama koma baya? Kinsani dai ba sabona bane ba zuwa gunki amma wannan abun tabbas ya tayarmun da hankali wanda naga dole inyi ruwa inyi tsaki akan shi" Kallon Nazari hassy ke mata secen ta nisa tace

"Matarshi ce babbar 'yar iska ai Ranki ya dad'e, bansan dalilin dayasa ta mayar dani wawiya ba, setazo guna da mugun dad'in bakinta ta gama yaudarana ta gudu, dayake ma tanada wani boka daya iya aiki shisa ban mammaka mata rashin mutunci ba har yanzu, yanzu tazo tace dani ranar walima a kasheshi ta hanyar poison amma wlhy se ranar tazo kiga ta canja komai ta kub'utar dashi, yanzu kuwa na sauya takuna akansu kwata kwata, ta hanyar dabata zata ba zan kashesu dukkansu har ita" Da gefen ido Daurana ta kalleta

"Karfa b'acin rai ya sanya ki aikata abinda zakizo kina masa dana sani nan gaba kad'an, bakya ganin kamar ranar walimar yayi sauri ki bada time mana, yanda bazama a zargeku ba amma hakan ai garaje ne" Murmushin dabe wuce labb'an taba tae mata

"Bazama a ce mu bane, gardawa ne nayi hayar su daga waje zasuzo su sacemun sarkin da kaf ahalin sa, se an shekara ana nemansu zan saka a hallakar dasu gaba d'ayansu ai idan sunsan wata basu san wata ba, wlhy sena ciyar dashi kashi tunda tak'amar sa jin kai, Hidar da Meenal kuma tun dama cen na shirya basu wani maganin baccin daze saka baza'a tafi dasu walimar dan kuwa bazan cutar da 'ya'yan 'yata ba, hatta gidan da zasu zauna na gama shirin komai na gidan tsaf, kuma har Amo tunda bata sona nima bawai sonta nake ba, ita kuma matar tasa agabansa zansa aimun raping d'inta" Murmushi irin na manya Daurama tayi

"Lallai kinada basira, Allah ya shige mana gaba to, idan kikai hakan kinyi daidai kuwa"  murnushi tayi ta waiga kad'an ta kalli gefen ta ba kowa sannan ta matso kusa da ita sosai ta rad'a mata wata maganar...Meenal bazata iya jiyo me aka ce ba amma tabbas taga yanda tshin hankali ya bayyana k'arara a fuskar Daurama! Murmushi Meenal tae sabida kanta ma ya dena gane komai zuwa yanzu, duk yanda take tunanin masarautar da munafurcinta abun yaci tura, abubuwa biyu ke damunta, na frko dai rashin sanin menene sarauniya hassy ta gayawa Asha da kuma wanda ta gayawa Daurama.

**********
   Tanaso tae magana da Sarki amma taga alamun abun dakamar wuya wai gurguwa da auren nesa, koda wane lokaci abubun fada kan tauye mata saduwa dashi, tasoma shiga damuwar rashin k'amshin sa, batasan taka maimai meyake sanya takeson k'amshin na jikin saba, Nusy tawa waya akan tana nemanta befi 30 mns ba nusyn ta karaso, muhimman abubuwa suka tattauna kan daga bisani ta mata sallama ta wuce, fitar dole zatayi dole ma taje gun mom d'inta, anzo gab'ar datake neman taimakon mom d'in da shawarwarin ta, zaman shiri tayi bayan ta fito wanka amma abun takaici duk kayan data d'akko ta sanya seya matseta yanda bazata wali acikiba, zama tae ta soma k'wallan takaici gata ba gwanar yin zani ba, bakuma zata iya fita a yanayin suturun masarauta ba sabida nauyin su, yanayin gaisuwar dataji na tashine ya tabbatar mata cewar Takawa ne yazo gunta watak'il labarin zuwa b'angarenshi a lokuta ma banbantane ya riskeshi datayi baya nan, Ko motsi ba taiba harya iso wurin datake, da idanta dake zubar da k'walla ta kalleshi

"Barka da zuwa" shine kad'ai abinda tace dashi ta kawar da kanta gefe, zama yae kusa da ya rik'o kafad'unta

"Sarauniyar Hankaka gaba d'aya ke kuka kuma? Ana zaune qalau lafiya kuwa?" Turo bakin nan tae

"Ni bansan mesa duk suturuna sun kama sun matseni ba, yanzu wai inaso zanje gun mom kuma shine dukkanin suturuna sun gagara shigana ni wlhy naji haushi" Dariya ta bashi amma seya danne karya k'ara b'ata ranta

"Ayyah swt hrt gaskia nima banji dad'i ba, inaga jikine ya k'ara bud'ewa kad'an kiyi hak'uri" Kwantar da kanta tai saman kafad'un shi

"Jallabiyuna ma duk sun matseni tunda dama sunada shap, kuma ni dama inaso zan gaya maka zanje asibiti banida lafiya" kallon tae k'irjinsa yae mugun dokawa bayaso tasan tanada juna biyu yanzu, danshi ya gama fahimtar cikinne da ita tuni

"Meke miki ciwo kuma?" Narai narai tae da ido

"Ciki nane ta k'asan seya murd'e sena had'a gumi secen ya sauka, kuma kaga nanma sunamun zugi sosai" ta nuna breast d'inta da hannunta

"Sekuma k'anshin jikinkan nan dayake hanani bacci idan bam tare shima inaso ingayawa Dr. Su bani magani ya dena, dan yanzu ya zamana kaina kemun ciwo idan na damu inaso inji, ga jiri danake yawan gani gakuma cin abincin nan kaman gara wlhy, abun haushi kuma sena toshe hanci nakecin sa banason warin sa, ina tsoron idan ba wani mugun ciwon bane, yanzu kuma nawuce time na period d'ina dakusan sati uku" Nisawa yae yarigada yasan baze yiyu yaci gaba da b'oye mata ba tunda take laulayi

"Kije ki gayawa mom kankije asibiti mana ko? Wataqil tamiki adu'a duk su den ciwon, zanjen suturu kuma dama nasan kina bin bashin kayan lefenki a hannu na, zan biyaki yanzu maza ki sanya kayan daze shugeki mu fita tare dama inada wannan shirin zamuje mu siya kayan walimar dazamu sanya kinga seki ebi jalllabiyu da wasu atamfofin inyaso zan kaiwa wani tailor na mata ya miki dogwayen riguna da wannan rigar dakuke me kaman babban riga seki wala abunki ko my queen?" D'an murmushibtae dole tae shirin sarakuna suka jeru, motoci sunkai goma da tsananin tsaro suka fita kai tsaye wurin siyayyar sukaje seda suka kammala komai sannan suka bi ta gidansu meenal, murna awurinta ba'a magana, sunsha hira da mahaifiyarta take gayawa mahaifiyar tata yanda suka tsara komai amma ga manufar su hassy, mom da kanta ta b'ullo da mafita me sauk'i wacce suke ganin kamar da ita zasuci nasara.

   "Yauwa mom nifa banida lafiya?" Murmushi mom tae

"Kurun kice mun shagwab'ar ta motsa banda haka yaushe kike ciwo gakinan kinyi b'ul b'ul abunki" B'ata fuska tae sannan ta soma zayyano mata abubuwan dayake damunta, lallai ta yarda duk shekarunka sekawa cikin fari wowta, bata mantawa ko ita dataja shekaru batai ciki ba haka tayita k'uruciya  akan cikin bata fahimci komai ba seda aka ankarar da ita, Da fara'arta ta washe bakinta

"Masha Allahu my Baby, ai wannan ciwon na alkhairi ne, kikace sati nawa bakiyi al'ada ba?" Kallon uwar tae tunkan ta gaya mata cikine ta harbo bakin zaren to yaya akayi bata kawo zancen ciki aranta ba? To dama dan an d'anyi abu so biyu koso d'aya se ciki, idanta lokaci d'aya ya kawo ruwa jikinta se rawa yakeyi

"Sati kusan bakwai dana gama wancen kenan" Gud'a mom ta rangad'a ta rungumeta

"Inshaa Allahu juna biyu ne dake shalelen momy Allah dai ya raba lafiya amma fa ki kame bakinki kinsan bakin mutane ba kyau, kai nagode wa Allah rabbu ya tallafeki, laulayin ciki kuma sekinyi hak'uri da haka yazo miki" Tama gagara furta wata kalmar seda mom ta k'ara cewa

"Kunyar ce duk haka bazaki nunan murna anan ba" ☺

murmushin yak'e tayi

"Kai mom bafa haka bane ba, Dr. Be fad'a bane zamu yarda da hakan" B'ata fuska tai

"Dr. Allah ne? Nace Dr. Allah ne dazakice waibe fad'aba, kowane me hankalin yaji wannan halin dakike ciki yasan cikine" Murmushin dai ta k'arayi batare datace k'alaba haka tai mata sallama gwiwa a sace ta baro gidan hankalinta a matuk'ar tashe tashiga motar da aka tanada dama cen domin su, gidan baya ta zauna inda yake zaune shima ya sauke abun bayan ya d'aura hannunshi, a d'ayan b'arin ta juyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci takan share k'wallan dake zubo mata da wani k'yallen dake hannunta, dare ya rigada yayi dama sabida haka bawai lallai ya ganta ba amma yanayin saukar numfashin ta kurun ya isa ya samar dame sauraronta cewar kuka takeyi hannunsa ya mik'a ya rik'o hannunta bata waigo ba bare ya sakaran zega fuskarta ya tabbatar da zarginsa tunda yake akwai k'arfe tsakanin sa dame tuk'in motar seya samu damar furta sunanta a hankali

"Ameena?" Amaimakon ta waigo ta kalleshi setace "EHMM" kawai

"Menene ya faru kin shiga cikin gida kina fara'a kin zomun da kuka yanzu, wani abunne ya faru ban sani ba?" Duk'ar da kanta tae a k'asa ta k'ak'alo murmushi tana k'ok'arin b'oye damuwarta kantace

"Bafa komai kurun dai senaji ina kewar gidanne kamar abarni gun mommy in kwana" Be yarda da maganar taba amma be musa ba musmushin kurun yae yace

"Wataran zan kawoki ki wuni mata amma ba zancen kwana kin girmi wannan kuma yanzu" Murmushin ta k'arayi

"Nagode Ranka ya dad'e" Tunanin takeyi yanda zata zubar da cikin batare daya ankare dashi ba sam, bata maso wani yasan dashi bare Takawa bazata tab'a haihuwa da mutumin da baya sontaba,kumama akan me? Shida yake cewa ze saketa, wanda ya maka alk'awarin saki me ya rage kuma? Bayaga haka ma bazata zuba zuri'arta acikin wannan gidan ba me cikeda rud'anin tsiya, gwara tace tayi auren kwanciyar hankali inda zama ta manta da wani Takawa da mulkin sa. Shirunta kurun ya tabbatar masa cewar tagano cikin yanayin zurfin tunanin data afka kasan dogon nazari take akan abinda yake da muhimmanci agareta, Hannunsu dake sark'e dana juna ya matse seda tae k'ara ta waigo tana kallonsa acikin haske street lights dasuka haske street d'in

"Ba yau zamu koma fada ba, kinga tafiya ce takusan awanni biyu sannan kuma duk yawan masu tsaron nan gwara dai muje gida inyaso da safe semu tafi tunda yake akwai kuyangi sosai a tare damu dazasu kula dake" Batace masa k'ala ba har suka isa gidansu na garin, Kowa D'akinsa ya nufa tunda yake sunada komai na buk'ata.

   Tajima sosai acikin toilet d'in tana kuka, a k'alla tafi sa'a d'aya, ciki kuma ita Ameena? Tayi yaya dashi? Cikin ma waida Takawa kai ina, amma wlhy ya cuceta, bazama tabar abuja ba seta zubar wlhy, bazama ta bari ya sani ba.

    Bayan ta idar da sallah isha seta sakko neman abinci, sanye take da kayan baccin ta Riga da wando dogo har k'asa, ta tufke gashin kanta a tsakiya kana ganin fuskar ta kasan tasha kuka, a parlor ta taradda babbar jakadiyar sarki tana Wanke masa k'afa a wani bahon ruwa masu k'amshi sosai, d'auke kanta tayi zuciyar ta tana mata suya meye haka kuma? Dama haka akeyine kome? A kitchen ma tea kurun ta iya had'awa ta juyo koda ta dawo an d'aura k'afafunsa asaman timtim ga wani farin k'yalle akai jakadiyar tanata faman mammatsa masa, takaici ne da bak'in ciki ya tarnak'e meenal ganin yanda ya lumshe ido ya kwantar da kanshi asaman kujera, jekadiyar shekarunta be wuce 23 ba, da kad'anne zata girmi Meenal, cikin k'uluwa tace

"Ke meye haka?" Se a sannan ma Yasan da fitowarta ta farko da yanzu bekosan ta wuce da farko ba idanshi a lumshe suke, Bata saki k'afarba tana ci gaba da mammatsa masa tace

"Ranki ya dad'e ina gab'ar aikina ne, Me martaba ze kwanta" K'ugunta ta kaiwa cafko ta tattaro masifa hadda k'ank'ance ido

"Kina kan aikin ki ma kike gayamun? Dawaye ya sanyaki" Bata saki k'afar ba har lokacin tace

"Ki hafarce ni ranki ya dad'e al'adace tace haka inshaa Allah nanda mintuna qalilan zamu gama, sekuma na gyara mas shinfid'ar sa da tsintsinyar share dattin tsiya" Wurgar da mug d'in hannunta tacin fusata tace

"Idan baki sake mai k'afansa ba kin tashi awurin sena faffala miki mari wlhy" Bata sake k'afarba bata kuma fasa aninda takeyi ba, dan al'ada se idan Sarki ne da kanshi yace ta dakata kuma shi yasan hakan tun yana k'arami so tari akanyiwa me martaba na safe suna gunshi, kallonshi jakadiyar keyi shikuma yau mulkin ne a kansa hannu ya d'agata mata akan ta dakata sannan ta sake k'afar tasa ta janye timtim d'in ta turo masa takalmin sa da sauri, k'afarsa ta kama ta tura d'ayar ta dama acikin takalmin sannan ta janyo tabiyu zata zura kurun taji saukar lafiyayyen marin daya kusa gigita mata duniyar ta

"Zaki dena lagudar masa jikinsa kokuwa? Banza tambad'add'iya ni sa'ankice zanzo ina miki magana kina mayar dani wawiya, maza b'acemun da gani anan" shidai yau sarakin ko gezau beba balantana ka saka ran zece wani abu fuskar nan yasha mur sosai. Jakadiyar mik'ewa tae tabar wurin seda ma ta taka kwalba agarin masifa yau 'yan matan halin akeji ta juya batare data damu da jinin da k'afarta keyi ba bayan data zare k'aramar kwalbar, juyawa tayi zuwa d'akin ranta babu dad'i tarasa dalilin jin haushin wannan abu daya faru, ina amfani  kana namiji musulmi matar daba muharramar kaba tana lagudar ma jiki, bakasan me zakacewa Allah ya sanyaka kake yiba, jin mulki ne da sarauta? Sarakuna nawane suka komawa mahalicci kafin kai? Mesa wasu mutanen giyar mulki take d'ebar su suna aikata abunda suke so, kenan dama duk kwanan datakeyi a b'angarenta tana kwana ne kurin suna mata hansari, wannan shine anyi ba'ayi ba ai, kuma har yake baiwa jakadiyar damar rainata ita bazata umarni ba seshi ya bata, wannan ai shed'an ya shiga wata rana k'arfe goma gina tare da wani namiji gardi shegiyar yarinyar ma gata kyakyawa, a yanda taji ma yarinyar waccen jakadiyar ce dakewa sarki me murabus bauta, zataci ubanta a hannunta wlhy.

***********
    Washe gari kuwa dajin haushin sa ta tashi, ga takaicin ko kanzil bece mata ba kuma beko nemeta ba, watak'il son yarinyar yakeyi banda haka meye ma nawani mik'a masa jikinsa yana laguda? K'wafa tayi ita kad'ai ta gyara zamanta akan kujerar tana kanne idanta d'aya cikin jin zafin Takawa, da shirin sa tsaf ya fito yana tafiya ana take masa bayansa jakadiyar ce ko yanzu take take masa bayansa, da k'yar ta had'iyi wani yawu me mugun d'aci ta kawar da kanta, da hannu yawa jakadiya alama data bar wurin seda ta gayar da Meenal sannan tabar wurin, kallonsa ya maida gun Meenal yaudai bilhaq tak'i gayar dashi, wata izza taga yana tak'ama dashi halinsa ne ya dawo dashi nada najin kai,izza da rashin magana, gyaran murya yae kan yace

"Meenaly kin tashi lafiya?" D'auke kanta ta k'arayi gefe d'aya kantace

"Lapia" kurun murmushi yae wanda ko kakai meye wurin ganin k'wak'waf bazaka gane yayi shi ba

"Harna kimtsa baki shirya ba ke, kuma kinsan tafiyar da nisa ga abubuwan dazamuyi acen dasuke jiranmu walimar ma babu abinda muka shirya" Cikin k'ufula tace

"Niba yau zanje ba katafi abunka inada  wata sabgar yi,baga jakadiya ba ai bakada matsala" Dariyar data taso masa haik'an yai k'ok'arin mayarwa, juyawa yae d'akin daya fito ya rufoshi bazaka san yanada dariyar mugunta ba se ranar, dariya yae hadda k'wallan shi seda yae me isarsa sannan ya gyara fuskar sa ya fito, mamaki yake irin kishin yarinyar batasan ta gano tanada ciki ba se kishi kurun ta sani, tunda shine na, had'e fuskar nan yae sosai ya fito

"Idan kika wuce mintuna goma baki kimtsa kin fito mun wuce ba zan sassab'a miki fa, wace sabgar ce dake datafi abubuwan dazamuyi acen muhimmanci?" Turo baki tayi dama kuka takeso tayi yau ko Kuyangarta bata jira ba ta kimtsa da kanta ta fito suka kama hanya, shima mur yasha har suka isa be kuma kulata ba, itama kuma se cika takeyi tana batsewa.....

*Bayan kwana uku*

    Yauce ranar walima kuma har yau d'in meenal bata kula sarakin ta, ko b'angaren sa bata zuwa shima kuma yae biris da ita, ga azaba tanasha na neman sonjin k'amshin sa takawa, kazar ma da akeji shima anje yajin cinshi😀😀😀. Tasha gyara sosai makeup kaman ba gobe tayi shigarta ta alfarma hadda head a kanta, kishi ya hanata gayawa mijinta abinda taji ana tattaunawa game dasu da yanda akeso a kashe su, babu abu mafi bata haushi irin idan ta tuna yanda yake lumshe ido ana matsa mai k'afa shiga sarki haka fuskar nan babu annuri se Hall d'in daza'a gudanar da walimar suka had'u sabida gaba yae shima ya gama shak'ar yanda ta mai d'in beko nemeta ba, a bakin hall  d'in aka tilas ta mata jiranshi dole taja tunga ta tsaya seda ya iso haka suka jeru akai musu rakiya har ciki, Kai tsaye zama sukai wurin da aka tanada domin su.

   Tunda mc d'in ya soma magana take rarraba idonta acikin hall d'in, tabbas taga fuskokin dabata aminta dasu ba awurin, taso tayi gate pass a baiwa iya mutanen da sukes suzo amma kishin tsiya dabatama san tanayi ba ya hanata, shikuma girman kai shiga sarki be nemi komai a wurin taba dukda sanin shirin su da yae, duk wanda take buk'atar gani ta ganshi abu d'ayane ya dameta rashin ganin Ummie da Meenal dakuma Hidar, ganin anci k'arfin programe ga kowa da aka gayyata har members na Tafaru ta k'are fan's, Taskar billy galadanchi, pherty zahra novels, Billy galadanchi's novels, haske fan's group, kundin haske novel group, Haske writers members, Zauren sanah s matazu, Da dai sauran groups duk na novels sun hallara, yan Kundin haske sunfi kowa qauyanci se zare ido sukeyi yau gasu ga sarki Takawa, Slimzy novels ma ba'a barsu a baya ba kai dukkanin me muhimmanci agun yazo banda Su Hidar, kasa hak'uri tae ta kamo hannun takawa beko juyo ba bare ta saka ran ze kalleta, haushin sa ya taso mata ga damuwar rashin ganinsu, kusa da kunnen shi taje

"Takawa ba ummiena ba yarana anan gun ka bincika kaji mana" waigowa yae sekuma ya basar kamar beji ba, wayarta ta zaro kurin ta kira waya fada, an tabbatar mata convoy na sarki suka biyo motarsuce ma k'arshe dan anmusu nisa, Kasa nutsuwa tae ta kira malmo a waya hayaniya be barta tajiyo k'arar wayarta ba, lokaci d'aya idanta ya kawo ruwa ta kuma rik'o hannun sa

"Ranka ya dad'e babu yarana babu ummiena, d'aukacin masarautar nan suna wurin nan me hakan yake nufi wai?" Kallon sosai ya mata acikin rawanin sa kanya zaro wayar sa shima ya hau kiran waya, kusan mintuna biyar aka k'ara kiranshi motar su tafito da Haris driver amma bata k'araso hotel d'inba, nanfa hankalinsu ya tashi aka hau shela!

Ko ina ummie da Hidar wa lameen suka shiga oho! Kota sauya zanine? Allah ne masani kurun!

Mom Nu'aiym.

Continue Reading

You'll Also Like

255K 1K 30
Just some AO3 shots not mine credit to owner โค๏ธ
23K 1.4K 30
แž–แŸ’แžšแŸ„แŸ‡แžแŸ‚แž€แžถแžšแž™แž›แŸ‹แž…แŸ’แžšแžกแŸ†แž˜แžฝแž™ แž‘แžพแž”แž’แŸ’แžœแžพแžขแŸ„แž™แž€แŸ’แž˜แŸแž„แž”แŸ’แžšแžปแžŸแžŸแŸ’แž›แžผแžแžแŸ’แžšแž„แŸ‹แž˜แŸ’แž“แžถแž€แŸ‹ แž แŸŠแžถแž“แž’แŸ’แžœแžพแž‚แŸ’แžšแž”แŸ‹แž™แŸ‰แžถแž„แžŠแžพแž˜แŸ’แž”แžธ แžŸแž„แžŸแžนแž€ แž‚แŸแžœแžทแž‰แžขแŸ„แž™แž”แžถแž“.....!!! แžแŸแž แŸ’แž™แžปแž„ แž‡แžปแž„แž แŸ’แž‚แžปแž€
69.1K 5.6K 16
๐—ฆ๐—ต๐—ฒ ๐—œ๐˜€ ๐—ง๐—ผ๐—ผ ๐——๐—ฒ๐—น๐—ถ๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ฒ ๐—™๐—ผ๐—ฟ His ๐——๐—ฒ๐˜€๐—ถ๐—ฟ๐—ฒ "Fuck, whenever you're in my arms, I feel like I might crush you. You're so delicate," he...
45K 1K 23
Isang groupo Ng kalalakihan na tagapag mana Ng ari-arian Ng mga magulang nito at groupo Ng kababaihan na anak Ng mayayamang political at may Isang da...