TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

35

3.6K 311 20
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

  Wattpad 68billy galadanchi

*Mom sayyed and noor, Sainah tawa, Umm Ramlat son so fisabilillah*
      
35
Sa'a yae yazo ummie tana bacci tace kar wanda ya tasheta se sanda ta tashi dan kanta, d'akin dayake tsammanin nanne d'akin da Meenal take ya nufa kai tsaye. Babbarsu tasha gabanshi had'e da zubewa k'asa

"Kamun rai Takawa, Anyi hani gareka daka shiga d'akinnan" wani kallo ya wurga mata daya haddasa mata barin wurin ba shiri,shikuwa kai tsaye ya shige d'akin abinshi, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali sanye da riga doguwa ta tufke gashin kanta a tsakiya, ba komai a fuskar nan tayi fayau, zama yae bakin gadon yad'an bubbugashi a hankali, bud'e idanta tae dama baccin bawai ya mata nauyi bane ba ta sauke lumsassun idanuwan ta a kanshi, zabura tae ta mik'e zaune

"Takawa ummie ce tace kashigo nan? Dan Allah karufa asiri na kartace nice nace kazo" K'ura mata idanshi kurun yae batare da yayi magana, shise yaga tama masa fari sosai

"Naga kinyi fari, ko bakida lafiya ne" Juye fuskar ta tae zuwa d'ayan gefen tace

"Lafiya k'alau hutune kawai, dan Allah idan har ummie batasan da zuwanka ba ka tashi ka tafi" murmushi yanxu kam yae

"Naji zan tafi amma dole sekin mun kiss" wara idanta tae

"Wane irin kiss kuma? Haba mana Takawa ka tausayamun mana" Gyaran zaman shi yae alamun ba inda xani

"Sekiyi ai, ni idan har bakimun kiss ba tokuwa tabbas ki sani kwanciyata zanyi a d'akin nan in shaidawa ummie idan tazo kece kika saka aka kirani har nan" wara idanta tayi waje sannan ta matso kusa dashi

"Haba yayana, ka tausayamun kaji, kaga idan kamun ka zubar mun da k'imana awurrin ummie, ka tausayamun kaji" D'age kafad'un sa yae alamun kanki akeji

"U kiss me i lv, idan bakimun ba insha Zamana kuwa" matsowa ta k'arayi kusa dashi harta doma ruwan hawaye

"To kawo kuncin mana" Dariya ce taso kub'uce masa amma seya kintse yace

"Wane kunce kuma? Ai irin wanda nake mikin nan zaki mun,idan ba haka ba kuwa konan dacen bazaniba" wara idanta tae waje cikin yamutse fuskar nan har lokacin tana zubar hawaye

"Irin wannan na 'yan iskane fa Takawa, dan Allah ka ceceni, kajiyo muryan ummie ko, ka tafi dan Allah nasan yanzu nan zata shigo"

"Idan fa bazaki zo kimun ba senazo nikam na kwanta abuna anan" Matsowa tayi jin muryan ummie nata matsowa kusa ya sanya tazo daf dashi amma ta kasa komai

"Gani" shine abinda tace masa, da murmushi a fuskar sa yace

"Ni haka nake miki malama?, ai zuwa zak8yi ki bani asalin french kiss ki tsotsa ki lasa na mintuna biyar,koda yake ummie na nan mintuna biyu na rage" kasa yin komai tayi seda taga da gasken dai ba inda zashi, sannan ta kawo fuskart kusa da nashi ta runtse idanta,shiru beko motsa ba harta bud'e idanta

"To gani mana"

"Yarinya baki shiryaba kenan, ni ai ninake miki sekiyi hakan kema" Badan tasoba ta had'e bakinta da nashi cikin takaici, had'uwar bakinsu tayi daidai da shigowar ummie a d'akin da sauri ta koma da baya tana kalima, janye jikinta tae da sauri ta kalli k'ofan jin muryan ummie, k'ara sautin kukan ta tae shikuma ya mik'e yana murmushi abunshi, naushi tashiga kai masa k'irjinsa da duka hanna yenta biyu, beyi k'ok'arin hanataba se dariyar sa dayakeyi, matsowa yae sosai ya rungumota gaba d'aya se kuka takeyi

"To kiyi hak'uri a8 bansan ummmie da gaske zatazo ba, kuma watak'il ma bata ganki ba kinji" Doddka k'afa tashiga yi

"Wlhy najiyo muryanta tana salallami, nika jazamun kuma Allah yana kallon ka"

"Shine kuma zaki mammaqalemun ajiki hajiya? Seki cikani haka" janye jikinta tae takoma bakin gadon ta zauna tana kukan, shi kuma yae waje murmushi d'auke a fuskar sa, a palor ya tarar da ummie duk'awa yae ya gaidata ta amsa kaman ba komai seda ya mata sallama sannan tace

"Ina zaka?" Waigowa yae

"Na'am ummie"

"Cewa nayi ka tsaya kajira matarka tafito ku tafi danni bazakuzo kunamun rashin kunyaba anan" sosa kanshi yae

"Ummie dakin barta ta k'ara mirmijewa kwana biyu"

"Kaga d'aukar matarka fa zakayi ku tafi, mirmijewa kam ai naga zahiri ta mirmije, maza ka dakata ke Babbarsu jeki ki had'o sawun takawa ya wuce da abarsa bazan iyaba" haka badan yasoba ya tsaya seda ta shirya tsaf tama kasa had'a fuskarta data ummie aka rakasu zuwa b'angaren sa se kukanta take.

********
    Zaman dirshan sukayi akan carpet dake tsakiyar d'akin suna wasu shirye shirye dasu kad'ai sukasan ma'anar shi itada takawa,dukda tana cikin fushi akan kunyar daya bata agun ummie hakan be hanata ci gaba da taimakon saba akan mahaifin sa, kirane ya shigo a wayarta daga gimbiya zainab,  d'aukar kiran tae suka gaisa

"Nazo so biyu B'angaren ki bakya nan, a hannun kuyangarki na karb'i lambar wayarki, ina sone zan ganki idan babu damuwa" Murmushi ya sub'uce mata tace tana kallonsa

"Mezai hana Gimbiya zainab, ina b'angaren Takawa idan zaki iya zuwa nan d'in"

"Ba damuwa sena zo" kallonta takawwa keyi

"Anya Meenal bakiyi gaggawa ba kuwa?"

"Gaggawa akan me? Naga abubuwa sun fara birkicewa ne a tsakanin mu, gwara muy8 mu kammala in k'ara gaba abuna😏" yafahimci maganar ta amma bece mata komai ba, danshi yanzu idan akwai abinda xe rabashi da ita shine wanda ya rabashi da salma shid'inma dan babu yanda zeyi ne.....

Hannayen gimbiya zainab duka a baya suke, ta hard'esu tana kai kawo acikin d'akin, kallo d'aya zaka mata kasan cewar tana cikin tashin hankali, kallonta meenal tayi ta dafa kafa'arta

"Ki kwantar da hankalin ki gimbiya, yanzu abubuwan rayuwa ai sauk'i ne dasu idan hakk'in ki kikeso abi miki wlhy semun samu yanda zamuyi, munada kud'ad'en dazamu iya zuwa asibiti amana DNA test aga jinin waye yake yawo ajikinki, technology meya bari gimbiya? Ki kwantar da hankalinki nime sonki ce wlhy" Nisawa tae

"Nasani Meenal, nasan duk duniya ke kad'ai kike sona, yanzu so nakeyi ki rakani gun me martaba mu masa bayanin abinda muka sani, shi kad'aine ze iya tasa k'eyar Sarauniya gayin wannan test d'in da kika ce, hankalina ya tashi meenal, ina neman taimako, nayi sati biyu ina sak'awa da kuncewa akan maganganun dakika gayamun amma abubuwan sunci tura" Nisawa tayi

"Zanyi shirin zuwanmu agun me martaba d'in yau da dare, sedai fa akwai k'alubale agaremu, abu na gaba kuma shine sekinyi taka tsantsan, masarauta akwai idanuwa fiye da wanda ke kike gani, akwai kunnuwa sama da wanda ke kike gani sabida haka ki iya takunki sosai, labaran sarauta abun rud'u ne sosai, wasu har yaransu suke bayarwa akashe akan mulki, ya kamata kisan wannan, idan kikayi garaje zaki rasa rayuwarki asanda baki tsammana ba" Nisawa tae

"Nagode sosai Sawun Takawa, zan jira signal d'inki zuwa daren".

Meenal yau kuma shirin yammacin ziyarar Sarauniyar daurama akayi, inda kai tsaye ta wuce K'ofar ta yamma, ganin da sarauniya Daurama ta mata ba k'aramin tayar mata da hankali yae ba, bayan sun zauna ta kalleta sosai

"Meke tafe dake yau?" Murmushi meenal tae

"Haba kakus ni shikenan bazanzo ziyara ba seda wani abun, yaudai gulma kawai na kawo miki" Murmushin manya sarauniya daurama tayi

"Gulmar me kuma" Murmushi meenal tayi

"Wannan babbar masarautar ai baze yuyu ka kasa son jin gulma ba, ni kuwa wata magana naji Sarauniyar sarauniyoyi, cewa akayi wai gimbiya zainab 'yar waziri ana zargin 'yace awurin sarauniya hassy tayi juyenta zuwaga waziri yabata d'ansa fu'ad, a yanda naji kune manya a wancen lokaci kunsan komai, tunda yake ita hassyn da kuyangarta Asha hana jinjirin da aka haifa sukayi akan be lafiya, sefa da matar waziri ta haihu sannan ne aka fito dashi abin mamaki kuma har ance matar waziri ta haifi namiji aka dawo akace mace, sekuma akace ma kece ta farkon da aka gayama cewar namijine kuma ubansa ya gaya miki, amma acikin muntuna kad'an kurun se komai ya juye aka dawo akace mace, nidai kam ina tantama tunda gashi Fu'ad d'in tatas da Waziri yake kama gimbiya zainab kuwa ko makaho ya lakuba zega tsananin kamanin ta da hassy dakuma ahalin hassy" Tashi Zaune Daurama tayi

"Wane bokan ne yake miki aikine wai Ameena? Ke komai kin sani, yaushe kika shigo masarautar dahar kikasan dayawa haka" dariya tayi

"Yo yabazan saniba tunda d'aukacin 'yan masarautar nan idon su nakan mijina, nifa har wani labari nake dashi, wai acikin K'warorin sarki mu'az akwai masu 'ya'ya a yanda naji ma wasu 'ya'yan ba'asan me kike dasuba tun suna jinjiraye, da zaran an gano mace tanada ciki sarki baze k'ara ganin taba kin kaita wani d'akin kenan kin ajiye sekuma ta haihu ki korata arasa ina jariran ke zuwa" Wata iriyar gumi ce ta fad'owa Sarauniya daurama cikin tsoro tace

"Meenal waime na miki ne? Mesa zaki sanya mun ido da yawane?" Dariya Meenal tayi

"Kinfi kowa yawan bayi maza da mata agidannan, wasu arasa daga ina kike samun su, mu kuma munsan cewar 'ya'yan sarki ne kike dank'wararwa zuwa bayi, wannan maganar idan tafita tabbas banan masarautar ba har maqotan ta se sunyi shari'a dake, zab'ine agareki ki shirya muje gun sarki bayan magrib ki fad'a masa gaskia game da zainab da fu'ad yasan me ake ciki kona fallasa wannan, abin tsoron ma shine kimun wani mugun abu mutanena ko ina a masarautar nan su tona asirinki a banza" Allah sarki 'yar tsohuwar nan take jikinta ya soma b'ari

"Niba hannuna aciki sun nemi kurin in rufa musu asiri ne, kuma idan fad'ar gaskiyar kikeso mezai hana in fad'a, da yaushe zamuje?" Murmushi tae

"Kakus kina burgeni, bayan isha zamuje idan k'afa ta d'auke ko? Banaso kowa yasan munje, sirri ne kunno wutar kurun zamuyi muja baya mu kalli yanda za'a kashe wutar kome kika gani" murmushi ita tsohuwar tayi

"Naso sosai ace acikin tsatsona kikazo, irin wannan fasahar haka" Murmushi tayi ta mik'e

"Naji anata k'aryata zuwana budurwa awurin takawa, ku zurfafa bincike har gyaran sati biyu nasha, dandai kun hanashi ya gane komai na budurci akan salma shine akaina ma kuke tunanin hakan lallai ma, sabuwa dal nazo hajiyata kuma shiya b'are kayansa, dakuka k'wace wancen yae hak'uri ni kuma se Allah ya hanawa tsohon mijina ikon tarawa dani harya mutu yazo ya fanshe hakurin sa, kinga shisa ake cewa me hak'uri shiya dafa dutse harya sha romon sa" Mik'ewa itama tayi

"Waye yace munmaji wannan maganar bare har mu k'aryata

"Keda me kawo miki rahoto adila kuyangar ki Rahmu kune kuka tsegunta da kanku nakuma ji, acikin ku biyu dai dole wani ya fad'a mun kin kuma san ke ban magana dake ba, so ki binciki amintacciyar kuyangar ki, matsalar ku shine baku yadda da kowa ba se wa d'annan kuyangin su kuma sam basu da wanda suke kushewa seku kad'ai, kina kallonta buri ne tana miki kallon nunanniyar ayaba agabanta se a kiyaye"  mutuwar tsaye tayi ita dai sarauniya Daurama ita kum tabar b'angaren jiki ba k'wari dayike a 'yan kwanakin nan batada lapia ma, kanta ake rik'a k'wank'watsar mata sosai ga abinci kuma dazaran taci se bacci kaman kasa, da farko a b'angaren ummie tazata rashin abinyi ne amma yanzu ta fahimci indai muddin tanaso ta aikata wani abu tokuwa sedai kartaci dan komai muhummancin abu tanaci zata kwanta bacci.

***********
   A B'angaren sarki suka sameshi inda jakadiya ta musu iso ba b'ata lokaci kuwa yabada izinin su shiga parlor bak'i na b'angaren sa... Dukkanin su sunyi shiru har xuwa lokacinda sarkin ya iso ganin Uwarshi wato Sarauniya Daurama ya sanyashi gayar da ita cikin girmamawa, seda ya gama gaisawa da ita samnan su kuma suka gayar dashi, ya saki jiki sosai suka gaisa kaman ba sarki ba, kan daga nisani Sarauniya daurama tace dashi

"Abdulra'uf kasani a shekarun baya na tab'a zuwa maka da zance akan Yarima fu'ad akan ina ganin cewar shi d'in waziri ne ka kasa fahimta na, gani kakeyi kamar ina jifan matarka da zargin zina ni kuma ba nufina kenan ba, baka tsaya kayi bincike ba ka mayar dani masarautar k'ofar yamma na kame bakina kurun yanzu gashi allura ta tono garma, zainab yar gidan waziri ta kafe akan lallai ita kaine ubanta, da wannan taje tayi bincike takeso kuma lallai aje asibiti ai gwajin jini tsakanin kai sarauniyar ka dakuma waziri da se kuma ita, acewarsu ma har yarimma fu'ad za'aje dankuwa wannan gwajin shine ze kawo k'arshen duk wani zargi" Kallon hikima sarki yawa sarauniya daurama

"Menene haujjar zainaba na ganin nine ubanta da har take ik'irarin ayi wannan gwajin, inaga DNA test take magana akai ko? Wane dalilin ne ya sanya kina zaman lafiya a masarautar ki zaki kwaso wannan rigimar kwad'ayin mulki kike kome?" Sadda kanta tayi a k'asa kantace murya na rawa

"Kayi mun rai yakai wannan sarki me adalci, hujjojina suna k'arfi sosai, da ace nini kad'aice  nake kamanni da sarauniya hasssy lallai daban takuraba kamar yanzu daya kasance yarima Fu'ad ma yana kamanni sosai da waziri ba, ga kuma k'ananun maganganu suna tashi akan yanayin haihuwar tamu, bayaga haka kuma ga kusancin zuciya danakeji game daku kaida ita da sauran 'yan uwana, dan Allah ina nemn alfarma na tabbatar wannan baze gagara ba amun wannan gwajin in cire ko kwanto a raina" Nisawa sarki yae, shida kanshi yanzu tsoron matar sa yakeyi

"Inaso insani dawa dawa yasan wannan maganar?" 

"Iya mu kad'aine babu wanda muka tunkara daga kai se sarauniya Daurama" Nisawa yae

"Ke zainaba kije Abuja zan had'aki da wani k'wararren likitana akan yin test d'in kiyimun waya nasan yanda zan shirya komai, waziri ma da Hassy zance suzo muje checup ciki zan had'a da fu'ad, sarauniya Daurama seki shirya zanyi basaja ince dake zamuje, zan d'auki mahaifiyata idan yaso acikin sirri wancen likitan ze mana wacce ake buk'ata d'in kukuma seya muku 'yan wanda suka dace da tsufa kinga bazasu ganeba bare su hana, in rokon duk wanda kenan saya rufa asirina karya bari hassy taji harse komai ya kammala acikin sirri" Daurama ma wani nadama ne yake zuwar mata akan abubuwa da yawa aciki kuwa hadda kisan salma yanzu abun yafi danunta fiye da da, wannan ya sanya ta kud'irta ba wanda zeji a k'alla kafim ta mutu ta aikata  wani alkhairi dabaza'a manta da itaba a masarautar koda an tuna sharrin ta....haka ya basu izinin tafiya suka bar wurin.

**********
     Shirin kwanciya tae har yanzu dai fushi akewa takawa dazaran dare yae gashi ya kasa ya tsare yace shi lallai bazata koma part d'inta ba, ita ta kasa gane me yake nufi yabi ya takurawa rayuwar ta, yanzu kashi ma idan zatayi ta dinga dubawa kenan idan bayanan kartayi me wari girma ya fad'i🤣, yaje rabin kaynta ya kwaso su ala dole shiwai game mata, tagama takura sosai ita kam.

Tura d'akinta tae bayan ta gama baje kayan data aiki d'an asabe siya ya kawo mata su se murna takeyi tamkar bata tab'a gani tsire da kaza gashashiya ba ta rasa dalilin wannan jarababben kwad'ayin ga ubn youghurt me sanyi da robar coke an dire mata se washe baki takeyi tamkar gonar auduga, ta zauna se cin naman take inta yagi wannan ta yagi wancen, a d'aura da coke, da sallamar sa ya shigo ya zauna yana kallonta banda  taunar k'ashin kaza ba abinda take, setayi masa rugu rugu take ajiyewa, shi mamakinta yake yanzu dankuwa ada bata tab'a sakin jikinta taci abinci agabanshi amma yanzu seta take uwar gashashiyar kaza d'aya agabanshi har k'asusuwanta se wani ja takeyi ko ina nata ya cicciko, nonuwanta yakwai kallo dasuka cicciko sukayo wajen rigar baccin cotton din material dake jikinta, kallon cikinta yae duk uban abin da zataci yana nan alafe luff, girgiza kanshi yae yana mamakin Meenal

"Ke hajiya bako gaisuwa" kallo shi tae

"Au ashe bamu gaisaba ya gida takawa, ina wuni? Karma kace zakaci kaga tsiren ba yawa nagama cinye kazar a fridge zan saka sauran tsiren gobe asubar fari shizan warming naci dan da yunwa zan tashi nama sani, cox dama ulcer na idan ya tashimun haka yakeyi" Murmushi yae

"Kekuma ulcer da kowa ke gudun maik'o ke taki maik'on takeso ko, kullum kaza da tsire sekace kura kuma se zaki kwanta ki d'are kan kaza d'aya hadda youghurt wlhy sekin zama orobo ba ruwana" Tab'e baki tae

"Yo dama ninace da ruwan ka ne, nidai ba ruwanka dacin kazana" Bece komai ba harta kammala taje ta wanko bakinta da hannunta ta dawo ta sanya chewing gum abakinta me k'amshi

"Kaje d'akinka zan kwanta"

"Bacci nazo tayaki malama" kawar da kanta gefe tayi" jiya se k'aunar k'amshin jikinka nake tayi, daka rungumeni na kwasa cikin dare seda na d'akko wannan rigar na sanya saman hancina sannan nayi bacci , idan zaka saka wannan turaren kazo ka kwana mun d'in" Murmushi yae shidai be fahimci komai ba, haka ya shirya kwanciyarsa ya d'qre kan gadon indan turaren sane ai kullum yana tare dashi base yaje sakawa ba, rungumeshi tai tashige a qirjin sa ta shak'o k'amshin har tana lumshe idanta

"Kasan yanda nakeso k'amshin jikin kannan kuwa? tab bazaka gane ba" Be wasu yan damu ba dai yabiyewa shirmenta tanata masa hira har zancen ya sauya, yayi matuk'ar mamakin ganin batai masa musuba kai tsaye komai ya wakana cikin ruwan sanyi kuma bataji zafi ba, seda komai ya lafa sannan sukai wanka kuma haka ta k'ara rungumeshi itafa bilhaq k'amshin jikinsa takeso.

******
  Washe gari yarigata tashi tunda yaje salan asuba be dawo ba, haka kurun takejin ba abinda takeso se k'amshin jikin sa, ganin har 9 be shigoba ya sanya tae wanka taje d'akin sa ta shafa turaren sa takula baya mu'ala da wani kalan turare seshi, body splash d'insa, sure spray da perfume duk na kamfanin ne, tana dawowa d'akinta suka soma hawa mata kai, kan kace meye ta soma kwarara amai, tun tana iya tashima harta kasa, malmo ke taimaka mata koda ya dawo taji gata.

"Meya sameki mekikaci ne da cikinki baya so?" Cikin wahala tace
"Turaren ka ne nakan mirro na shafa  shine yake hawa mun kai" da mamaki ya kalleta

"Turaren kuma dakikeso yanzu bakyaso?"

"Ajikinka yafi d'ad'i, ko yanzu amai zanyi tayani cire kayan nan indena jin kamshim sa dan Allah" be musa mataba, ya sallami malmo ya cire mata har wanka ya mata da kanshi ya sanya mata wasu kayan, ya kwantar da ita da nufin zeje ya dawo tunda ta dena aman ta rik'o hannun sa

"K'amshin jikinka nakeso, ka sakani ajikinka inyi bacci kaji" kallonta yae cikeda tausayawa

"Kekam kin cika rigima idan kuma kika k'arayin aman fa" turo baki tae

"Nidai kaxo bazanyiba" haka ba yanda ya iya ya rufo d'akin yazo ya kwanta, ranar yaga al'ajabi dankuwa shinshina yashashi fuskarta acikin k'irjin sa tae bacci... Yana tausaya mata? Kodai cikine da meenal? Idan hakane idan ta gano babu zaman lafiya dan haka idan ma hakanne baze gaya mata ba seya nuna kam, amma idan cikinne yanada aiki shikenan bazena fita ba? Zaman shinshinar shi zata zauna yi, tun dawowar ta daga gidan ummie ya kula da hakan, duk fushin datake baya tab'a hanata zaman shinshinar sa.

Mom Nu'aiym.

Continue Reading

You'll Also Like

5.3M 46.3K 57
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...
339K 9.3K 70
Everybody knows the Dutton Family but none of them have made a name for themselves quite like the youngest, Mae Evelyn Dutton. She's a force to be re...
37.8K 2.5K 61
𝐭𝐡𝐞 𝟐𝐧𝐝 𝐛𝐨𝐨𝐤 𝐨𝐟 𝐬𝐡𝐨𝐫𝐭 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢𝐞𝐬 𝐚𝐛𝐨𝐮𝐭 𝐨𝐥𝐢𝐯𝐢𝐚 𝐫𝐨𝐝𝐫𝐢𝐠𝐨 𝐚𝐧𝐝 𝐲/𝐧'𝐬 𝐦𝐞𝐞𝐭-𝐜𝐮𝐭𝐞𝐬/𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢�...
63.8K 1.1K 96
Continuation of Modesto story who happens to intercourse with friends,mature,classmates,strangers and even family...