TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

Od 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... Více

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

27

3.2K 292 26
Od 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad @ 68billygaladanchi
     
     27

Tsaye ya mik'ar da ita ya sake zabga mata marin daya haifar mata da soma yin hab'o kai tsaye jinin hancinta ya soma zubowa, kuka takeyi tana magiya amma ina basu saurareta ba

"Oga mu yanke harshen mana da yatsun muyi mubar nannpart d'in kar wani farka" tsaki yaja

"Wanda duk ya farka sena kasheshi, kumama maganin baze baiwa kowa damar tashiba se nan da awa sha biyar, ko yanzu kuma sunada awowi 11" D'an kwab'e fuska d'ayan yae 

"Oga to yanzu me zakayi?" Hararar sa yae

"Bakinta zaka d'auremun biyu suja kaf'a biyu suja hannayenta banson gaddamaa zan hau tane" Kallon sa

"Kana ganin oga wannan baze mata lokaci ba?" Cikin hargagi yae ihun daya farkar da Hidar Dake sama ya tashi ya lek'o, Tsoro ne ya kamashi dukda zamansa yaro ya koma sama ya lafe kurun....

**********
   Ihun da ogan yae ne ya mayar da hankalin sojan da Takawa yasaka zagayar part d'in na meenal cikin dare, dukda banan yake kwana ba amma yana zagayawa duk bayan d'aya seya koma part d'in takawa dase yayi tafiyar mns ma ze isa da k'afa dai, yazo zagaye an our ago yaga sunada barci amma seya koma ganin babu suspicious abu, yanzu time na dawowa ne yae.

  Baya yaja kad'an ya zaro wayarsa yakira ogansa

"Akwai matsala apart na Madam, kuzo da yawa", da sand'a shi kuma yashiga gidan bayan ya sanar dasu insunzo sushigo yana ciki, sojoji bakwai ne suka taso gaba d'ayansu zuwa wurin part d'in da gudun su, Kai tsaye ciki suka afka adaidai lokacin da suke rirriqeta suna shirin zare kayan jikinta, babu ruwan soja kai tsaye suka harbe hud'u daga cikinsu, dama kuma su basuda bundiga se makamai kurun, Suka daddam k'e sauran suka doma dukansu suna shurinsu da takalmin su masu shegen nauyin nan, duniya ba imani mazaje sunkai goma dukdan a cutar da mace d'aya! Daganan suka soma musu bayani, Meenal se hak'i takeyi tana mayar da numfarfashi, da hannu ta nuna musu sama, takasa magaba k'wak'wara, sojan ne yaje yasoma duddubawa bega komai ba, ana haka Hidar ya leqo daga sama, aikam ya sakko dashi ya soma rarrashinsa danyaga yana kuka, d'aure sauran b'arayin sukayi sannan suka nemi taimakon Madam, ita da kanta ta ciro Small meenal dukda sarawan da kanta keyi, sunso zuwa dasu part d'in oga amma akwai tafiya gashi darene, sun sani tabbas Meenal bazata iya tafiya ba kuma su bada mota suke ba, dole aka barta da sojoji guda biyu sauran suka juya donsu tado ogansu yazo yaga 'yan ta'addan da aka kama.
 
   Takawa yana bacci yajiyo knocking nasu yasha mamakin knocking cikin dare haka, haka yaje toilet yadan yi freshin up cikin wannan izzar yafito da singlet da gajeran wandonsa, Michael ne yace muryan sa yana rawa

"Oga ansmu wasu b'arayi sunje part d'in Madam har suna qoqarin suyi rape nta sanda mukaje..." Kanya k'arasama ya bankeshi aguje zuwa part d'in nata da k'afarsa...

Cikin gidan ya afka tare dasu dasuka rufa masa baya da gudu cikin daren, kutsawa yae har cikin d'akin nata, acen yaganta itada yara ta ruqumqumesu tana kuka mara sauti, jini harya kwanta mata a idan nan, fuskar ta kumbura tayi wani iri, ga jinin hancinta har yanzu be tsaya ba se zuba yakeyi, dama yaran duk qaran bundiga ya tashesu basu bama har sauran part sunji wannan k'arar bundigar kowa dai ya lafe ne sabida tsaro.... Kansu yae ganin yaransa lapia lau ya lalubo wayarsa yake sanarwa amo had'e cewa zasu rako yaran yanzu, taso ya turo mata har Meenal amma yace noo ta barta ze kula da ita.

   Seda yaje yawa sojojin warning akan suje su binne wanda suka harba kuma su b'oye masa wanda suka kama batare da kowa ya saniba acikin masarautar ba, seya gama bincike tukunna" sannan ya dawo wurinta se kuka takeyi, har lokacin kuma k'walla be dena ambaliya daga idanta ba, ga jini duk ya b'ata mata jikinta wanda ya zubo daga hancinta, Toilet yaje ya tara ruwan d'umi sannan yazo ya zare rigar jikinta a hankali ya d'aura mata towel, itadai yaukam jitake bazata iya k'ara kwana d'aya a wannan masarautar ba, ta zubar da makaman yaqinta gun mommy da daddy zataje,  a tsorace take dankuwa wannan mugun anufinsa wannan k'atuwar abar ze tura mata, to ina? Kuma wai da gaske da cire 'yan yatsun nata zasuyi? Sautin kukan ta ta k'ara tunawa da masifar data  jefa kanta aciki, shikuma gogan komai bece da itaba har suka je ban d'akin, a ruwan ya zuba ta ta runtse idanta, haka seda ya mata, wanka sosai ya gaggasa mata fuskar nan,,D'aki ya kawo ta yaje ya d'akko wasu ruwan zafi da small towel ya gaggasa mata fuskar nan data kumbura, da k'ank'ara ya gasa mata idanta sannan ya gyara komai bayan yabar security a wajen har lokcin kuyangin suna bacci da bayi, sannan ya dawo ya rufe gidan da k'ofar d'akin zuciyar sa babu dad'i, zare singlet d'inshi yae yadawo iya boxers ne ajikin sa, batare daya sanya mata wasu kayan ba kota saka ya shige acikin duvet shida ita kansu ne kurun  waje, sumar kanta ya soma shafa a hankali bayan ya turata gaba d'aya ajikinsa hannunsa ya mik'ar ya d'aura mata kanta akai, cikin taushin murya yace

"Am so sorry my Meenaly, kidena kukan haka kanki zeyi ciwo kinji, Baccine ya saceni nasha maganin mura" Tabare fuskar nan tayi cikeda shagwaba ga jikinta se rawa yakeyi

"Bakai bane kake barina nini kad'ai kullum, yaa muhammad na baya mun haka, nice ma nake gudunsa, ni Allah gobe gun mommy zani tsoro nakeji" Tana maganar ne cikeda tsoro jikinta se rawa yakeyi, k'ara matseta yae jikinsa yace

"Bazan k'araba Meenaly, kullum zanna rik'a kwanciya wuri d'aya dake, bazan k'ara baiwa kowa damar cutar dake ba, kuma zan hukunta wanda suka nemi hallkar dake" Sautin kukanta ta k'arawa yawa

"Wanan mugun fa cewa yake zeyi raping d'ina, wlhy bazan zauna anan gidan ba, so yakeyi ya tonamun asiri, idan kuma ya dawo gobe fa" Jijjigata ya shigayi

"Meenly aishi aka Harbe a bayanin danaji, so baze dawo ba kinji" Itadai batada nutsuwa da alama sambatu ma takeyi

"Cewa sukeyi zasu yanke faratana duka gom na hannu harda harshe na, Takawa dafa Allah be kawo kuba da tuni nasan na zama tarihi kasheni sukeso suyi" Besan da wane bakin ze soma rarrashin taba wannan ya sanya ya shiga bubbuga bayanta kurun, se uban kuka datake rusa masa har kusan asuba batayi bacci ba kuka kurun takeyi,  zuwa wannan lokacin jikinta ya d'auki zafi sosai, se rawar sanyi takeyi, duk inda ze juya tare yake juyawa da ita tana jikinsa, tausayin ta ya hanashi koda raba jikinsa da nata, tunanin mafita yakeyi, Baya tsammanin mutanen masarautar hankalinsu har yakai akan Meenal tunda yake bata dad'e a masarautar ba, incident na food poison daya faru ya d'aukeshi akan cewar  shi aka so yiwa amma wannan abun daya faru ya sani sarai ita ake hari, zancen a datse 'yan yatsu dakuma  harshe wannan abune dayake nuni kai tsaye  cewar tasan wani babban sirrin su dabasa so aji, idan hakane meta sani?, kuma acikin masarautar su waye?, anya beyi sakaci ba kuwa? Daya kasance be sanya idanshi akan 'yar mutane daya kawo acikin fitiniba, sodayawa yake ganinta tana zagaye acikin mabanbantan sassan dake cikin masarautar be hanata bane sabida ya kula da k'warewar ta wurin furta kalamai a baud'e, yaga kuma yanda take zubewa take qasqantar da kanta agabansu...

    Shiya taimaka mata tae salla, sannan tayi wanka da kanta fuskar nan kam se a hankali ta canja matuk'a dan yau hadda wani bak'i tayi inda mari da naushi ya sauka sanda sukeso su riqata tasaha naushi, sannan banqarar ma dasuka mata duk jikinta ciwo yake mata, tashiga yanayi me ciwo....
   Yanzukam Takawan Bashida yarda da kowa dake b'angaren nata se kanshi, dan haka da kanshi ya soya mata k'wai da tea ya had'a ya kawo mata, da kanshi kuma ya bata, tana gama shansu se amai, zazzab'i sosai takeyi harta soma ganin jiri, Dr. Ayub ya kira aka mata allura sannan yae shirin gagggawa na barin fadar da ita batare da sanin kowa ba, haka zalika kuyanginta ma da fadawa masu tsaron kofar waje be tafi da kowa ba, koda yafita da excort kan hnya aka ajiyesu, iya wayoyinsu da system data buk'ata ya bari aka d'akko mata, shima ana ajiyesu kan hanya ya karb'a da kanshi ya rik'e wasu, batasan dalilin fitowar suba kurin dai tasan jiri takeji, wani hotel sukaje sukawa kansu masauki, suna zuwa ya kama d'aki babba, yaje ya kama d'akuna gudana 4 dukda sunan sa, seya zab'a d:aya yaje ya suka baje, da kanshi ko yanzu ya mata wanka sannan ya ordering abinci, k'inci tayi ta soma kuka, shikuwa ya hau aikin rarrashi

"Haba Meenaly, kukan nan baze k'are ba wai? Ehn? Kanki ze k'ara ciwo ne my baby ki dena kuka kinji, inshaa Allahu babu wani abinda ze k'ara samunki, yaranki ma da Ummi na sunacen na bada tsaro sosai a kansu" kallonshi tae da jajayen rinannun idanuwan ta tace

"Abul khair bazan iya ciba, banida appetite kuma kaga hak'orina ma ciwo yakemun tunda wannan ya makamun mari" Tallafota jikinsa yae

"Babyna sannu, idan bazaki iya tauna abincin ba nizan tauna sena baki ki had'iye" Kallonsa take ido cikin ido, Meenal tasan meye aure, tasan meye jima'i amma baka rabo sabon shiga da tsorata maganar shi ma ta bata mamaki, kawar da kanta tae gefe d'aya

"Abul khair, nizan iya ci da kaina, wannan ne bana so, ni dan Allah ka kaini gun mommy" Dafe kanshi yae da hannu d'aya

"Meenaly, kin cika Rigimafa, tayaya zan kaiki gun iyayenki a haka? Dan Allah ki nutsu me kikeso yanzu?" D'an turo Baki tayi

"Fura nakeso ko youghurt" Nisawa yae yakira reception, babu a hotel d'in se yaro suka turo masa yaje ya siyan masa a wajen wurin, youghurt d'inma da aka kawo seta ce ita se fura gashi basu samo furar ta, had'a fuskar nan yae tamkar be tab'a dariya ba, ya tsiyaya a cup ya mik'a mata

"Ungo shanye shi tas yanzun nan inba hakaba sena mareki, tun yaushe ake lallab'aki kici abinci kinawa mutane wawta bakida lapiya so kikeyi yunwar nan ta kasheki ga kuma ciwo" Seda ta turo baki sannan ta karrb'a tanasha tana yatsina fuska da gaske amai takeji sosai yana taso mata sabida batajin dad'in bakinta, haka ya tsaya seda tasha rabin robar aikam se amai, haka ta dingayi seda ta galabaita sannan tazo tayi bacci, ficeqa yae ya rufe d'akin, kai tsaye acc dakeda Sunan Hidar yaje ya ciri kud'i, kai tsaye mota yaje ya siya sannan ya siya mata new plate number, shi duka motocinsa TAKAWA ne a rubuce, dole ya b'atar da kama, yanzu kam baze saurarawa masu bibiyar matar saba dashi kansa seyaga k'arshen su ya gano zama ba nasa bane ba, wasa yakeyi shima. Hotel d'in ya koma,har lokacin bacci takeyi kusan 4 na yamma, wanka ya farayi yaje yae sallah sannan ya soma tashin ta, Da salatin annabi ta frka abakinta sannan tayi mik'a, ba laifi taji k'arfin jikinta sosai yanzu ba zazzab'in ma ba ciwon kai, dama wataqil rashin bacci ne

"Ki tashi kije kiyi sallah, har la'asar tayi" wara ido tae sannan ta sakko da hanzari sosai ta nufi ban d'akin, seda tae wanka sannan ta d'auro alwala tazo tayi sallolin har wanda taci bashin sa, waigowa tae ta kalleshi shi d'inma ita yake kallo matsawa tae kusa da gadon dayake sannan ta kwantar da kanta asaman cinyar sa

"Takawa zanje gun mommyna, ka taimakeni ka rabani da gidan sarautar nan wlhy basuda imani" Runtse idanshi yae sannan ya bud'e a hankali, hannunsa ya d'aura asaman kanta dakr cikin hijabinta yace

"Meenaly na tabbatar akwai abinda kika sani game da wannan masarautar dabasaso kisan dashi, gani kike kaman banaso in kaiki gida, toki sani gwara zamanki anan akan kije gidanku, ko kinaso a mawo hari a had'a har mommy da dad nki?" Da sauri ta girgiza masa kai

"Yauwa to ki nutsu ki saurareni ki gayamum abinda kika sani da inda kika san abun, da yanda kike gudanar da abubuwan, Meenal masarauta wurine dayake had'arin Gaske, yake kuma tattare da had'rurruka masu rikitarwa, ba komai kake yi kanka tsaye ba sekayi nazari akan abun, dakuma mezeje yazo, yanzu kinga akan garaje kin janyowa kanki, sauri ya haifi nawa wa gari ya waya kenan? Idan ma basuyi nasarar nak'asaki ba ai sunyi nasarar tsoratar dake dakuma firgitar dake ko? Kinga kuma dole ki dakatar acikin ku waye a sama kenan?" Sauke numfashi tayi tana nan har lokacin kanta a cinyarsa tace

"Abu Haidar kayi hakuri ban sanar dakai akan abubuwan danake tayiba, kai d'inne kamar anmaka dole a aure na, baka bani kusancin daya dace dani kodan kasancewar ni akawa auren na dole, sannan kuma ni ina gani ana cutar dakai se zuciyata bazata iya hak'ura ba.
  Tun ina k'ank'anuwar yarinyar na tashi agidan mu ake kawomun ababen wasa dasuka shafi computer komai nawa na school zakaga daddy daga waje yake kawomun wasu abubuwan senayi da kaina, sannan kuma munzo generation na computer, tin a primary nake guruwar gaske a computer akwai wani ma class mate d'ina tun primary tare muke takara tun a wancen lokacin ana ce dashi khamal system ya bala'in san kan computer nima haka nake, bayan nan a secondry schol na ma haka nake indai computer ne da ita abubuwa, akazo aka bani waya itama haka na k'ware sosai wurin iya aikinta, harya kasance daddy yana bani ayyukansa sosai na office, ya zamana friends nawa dayawa suna cemun Meenal computer guru, wasu lokutan ma zakaga wasu Meenal Guru kurun suke ambata na dashi, naso karatun b'angaren computer sanda na kammala secondry school amma bansan mesa daddy ya kafe akan baya so ba, haka da k'yar kanmu samu adm yabarni naje computer school, zuwana computer school ya k'aramun abubuwa da yawa akan wanda na iya a harkar computer, ciki hadda hacking acount da wasu abubuwan dasuka shafi yahoo! Acen muka k'ara had'ewa da khamal system kuma Talent Nusy itace malamar mu a wancen lokacin, nasani duk kaiwata da k'warewa akan computer nusy uwatace kuma ubanace a wannan harkar muguwar mugunta ta mata yawa dason kud'in tsiya bana manta dana k'ara mata 200k setakemun Extra clases inda na k'ara sanin kan abun fiye da da, hakan ya sanya bayan na gama na 6 month na k'arayin wani, nasha mamakin ma dabata ganeniba  sanda muka had'u amma na share, har sata mukewa networks na recharge card nida qawayena nice oga, babu abinda ban saniba akan system, haka muka had'e jami'a da khamal system shi yana karantar computer zalla, haka nake nanuk'e masa har wasu lokutan mukayi fad'a da yaa muhammad akan banida abokin zama se namiji kullum wayar mun dakai yake akan system, sannan kuma yana nunamun harkar d'ana camera's, mugun professional ne a b'an garen nan, a kwai wani zubin daya nunamun wani abin recording daduka k'irk'ira da kansu shida wani friend dinshi dake karantar mechanical engineering, sedai yana complain akan yayi girma, daze samu tallafi dayaje k'asar waje qarin ilmi idan ya gama jami'a, har nake cewa zanwa dad mgana yace zeyi sponsorin nashi zuwa America idan ya kammala, ganin abubuwan da Nusy keyi maka gashi ka yarda da ita ya tilastani dole naje gun khamal, to my greatest surprise friend d'inshi yana America haryake musu wannan abun dasuka k'irk'ira kuma suke amfani dashi sunma bashi aiki, yana tura masa su anan, to sena karbi sunkai hamsin gasu k'anana ne baka ma ganewa sedai kuma basson ruwa ya tab'asu, da wannan nasamu damar dasasu a b'angaren sarauniya hassy harm ajikinta, Hajiyar rusau ma nakai mata nakuma kaiwa Sarauniya daurama, so anan nake samun infor akan sharrin dasuke shirin k'ulla maka ciki kuwa harda zancen mahaifin ka da suka b'oye a wani wuri danake da yak'inin acikin masarautar nan, suke kuma bashi wani mugun abun dake mantar dashi komai duk bayan wata shida, ya zama kamar wagili ma yana underground ma a yanda naji sun kira sunan wurin wai Hak'on d'an Adam!" Da sauri Mu'az ya mik'e yana nanata kalmar ta k'arshe "Hak'on D'an adam?" Wurin satunda ya tashi yaji ance an hana kowa zuwa wurin sabida wai aljanaine sukawa gun katutu wani kurkukune da aka fasa dutse da k'asa aka ginashi acikin k'asa, a zamanin da idan ka dad'e aciki akace inka fito mahan cewa kakeyi!! Dafe kanshi yae ya dawo ya zauna ya k'ara mayar mata da kanta inda yake

"A ina kikaji wannan Meenal?" Mik'ewabtae ta had'a computer da wayarta ma, ta soma kunna masa Audio dataji suna maganar, aciki yaji suna zancen Shak'iyancin su itada waziri, ashe yarima Fu'ad ma d'an sane, sannan aciki yaji suna zancen wai mahaifinsa baida lafiya idan ma ya mutu anan zasu binneshi ko sallah bazasu masa ba, dalilin tado maganar ma akan waziri yazone ya sanar wa Gimbiyar rusau akan ciwon na tsohon sarki, duk wasu abubuwa harda na talented Nusy yajisu yakuma sha jinin jikinsa, kansa ya matuk'ar d'aure, kurun kuka ya saka wa meenal wiwi Tashi tayi ta zauna kusa dashi ta soma rarrashin sa seda yae sannan yace.

"Yanzu abinda zamu fara shine sace mahaifin daga wannan mugun wurin, ninasan wurin a masarautar kudu yake, amma ban tab'a shigaba, bana kuma son na shiga d'in, amma ya zamemun dole naje, sedai a asirce zamu shiga wurin dan idan suka sani akwai matsala, so ya kike ganin zamuyi?"  Nisawa tayi

"Zan soma duba girman masarautar, zan lalubo hanyar shiga da fita wurin, zan binciko yanda ake gadin wurin zan sak ido akan masu ziyartar wurin duk a cikin kwana biyu jal✌🏻?" kallonta yae

"Tayaya zakiyi wannan aikin Meenaly? Muda bama cikin masrautar ma, kuma dawa kika yarda ne?" Murmushi tayi tace, "zan jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya, me sulhu itace me neman kasheka, konince kashe yaranka dan kuwa itace babbar yarinyar Talented, inada record na komai akanta, sabida aikin hatsari zan sanyata zanyi threatening nata da audio's danake da akanta na k'ulla makirci akan ka, tuni na d'ana mata kayan aikina, ba jahila bace tanada iliminta sosai kuma tazone danta cutar damu baki d'aya... Itace zata kwana a tsaye neman yaushe ake shiga yaushe kuma ake fita a wannan wurin, bata isa tak'iyiba ko kuma na nuna maka ka kasheta takumasan tsaf har ita har nusaiban sun cancanci kisa, bayan ta gama mana wannan kuma setayi aiki akan Talented, dankuwa tanawa Sarauniya daurama aiki akanka ma!!!" Da sauri ya kalleta

"Ita nusyn?" Ya tambaya cikin mamaki, murmushi tayi

"Itafa,aida sanya hannun Nusy akisan Salma" Idanshi lokaci d'aya ya kad'a, nan take ta nuna masa audio sanda suke hirar da komai, ita sarauniya da kuma Yarta me zawarcin nan, akan ko yanzu Nusy zasu saka ta kasheni sufa Hajiyar Kilisa ce bazasu bari zuri'arta tayi yawa ba sabida sun tsaneta, Sarauniya Daurama ita keso ta kashe yaranka ma, shisa kaga koda wane lokaci se Nusy tayi amfani da yardar dakai da ita ta d'aukek daga wurin da wani abu ze samesu kafin  ka ankare ta k'are, da wayarta nayi amfani da number ta na gano abubuwan dasuka aikata sosai, trough phone conversation da chat na message, inada record na komai, matsala d'aya dana nunawa su waziri nasan komai shisa sukeso su kasheni, amma ko yanzu ka barni dasu, yanda nayi b'arnata ni nasan yanda zanyi gyaran abata" Mamakin kaifin basirar yarinyar yakeyi, jinjina kansa kurun yake.

"Yanzu yaya zamu aiwatar da duk wannan tunda yake kinga cewar bama cikin masarautar" Mik'ewa tsaye tayi ta mayarda hannayenta a bayanta ta hard'esu tace

"Mu'az wannan fa ba lokacin gudun makashin ka bane, lokaci ne dazamuyi gaba da gaba dasu amma cikin hikima, yau bazamu kwana anan ba masarautar zamu koma, ni nasan mena shirya a raina yanzun nan, kuma inshaa Allahu komai yanda ya dace ze tafi, ka kwantar hankalinka,nima kaina na cire wani tsoron su, akwai acikin yaran nan namu kuyangi memun aiki, itama da akwai kayan bincikena ajikinta bantaba ji ta gayawa kowa ba, sabida haka inada wacce na aminta da ita, ita kemun girki ma sunanta Malmo, so karka damu, idan muka kimtsa zan maka bayanin koma" rik'o hannunta yae ta juyo suka kalli juna

"Are u sure?" Ya tambayeta murmushi ta sakar masa

"Trust me Allah yana tare damu, sabida mune da gaskiya kuma Nasara tana tare da masu gaskia, trust in God and u'll never regret it" Murmushi yayi yanzu kam ya rungumet gaba d'aya

"Alhamdulillah ya Allah for blessing me with a good wife, da farko na dauka rashin salma duhu ne arayuwa ta, ashe naso shiga hurumin daba nawa ba nayiwa Allah butulci, yanzu ya sakamun da mafi alkhairi na tabbatar ke alheri ce agareni meenal" Murmushi tae yayinda ya d'ago kanta ya rik'e da hannayensa guda biyu, sumba ya manna mata a baki, sannan yae agoshinta yana murmushi yace

"Me kumatu a kumbure, kinga yanda kikai muni kuwa, Allah kaman ba Beautiful Meenlyn Mu'az ba, anya kuwa ba canje aka mun ba" Cikin shagwab'a da dire masa hannayenta duka biya a k'irji bayan data jimk'e su tana dukanshi cikeda shagwab'a

"Allah ni bana so Ka dena" rik'e hannayentanta kwace sannan ya saketa ya d'agata sama tawurin k'ugunta ya soma zagaye d'akin da ita, dariya suke dukansu tana cilli da k'afafuwanta a sama, direta yae bayan d'an lokaci shima ya kwanta akan gadon suna mayar da numfarfashi a tare suna dariya.

*Tafiyar nan dukkanmu se munyi hak'uri, kusan ba sabona bane yin littafi me tsayi amma wannan da haka yazo, zeje da yawa amma kad'an*

Mom Nu'aiym.

Pokračovat ve čtení

Mohlo by se ti líbit

113K 293 25
here are some of my horny thoughts as a trans man with a pussy. snap if you wanna sext ;)
594K 988 22
Smexy One shots😘 Got deleted twice 3rd times a charm🤦🏻‍♀️😭
262K 39.9K 102
ပြန်သူမရှိတော့ဘူးဆိုလို့ ယူပြန်လိုက်ပြီ ဟီးဟီး ဖတ်ပေးကြပါဦး
37.6K 2.5K 61
𝐭𝐡𝐞 𝟐𝐧𝐝 𝐛𝐨𝐨𝐤 𝐨𝐟 𝐬𝐡𝐨𝐫𝐭 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢𝐞𝐬 𝐚𝐛𝐨𝐮𝐭 𝐨𝐥𝐢𝐯𝐢𝐚 𝐫𝐨𝐝𝐫𝐢𝐠𝐨 𝐚𝐧𝐝 𝐲/𝐧'𝐬 𝐦𝐞𝐞𝐭-𝐜𝐮𝐭𝐞𝐬/𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢�...