TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 24

2.8K 282 16
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

    Wattpad 68billygaladanchi

              24
Wata irin fusatace ta tasowa Sarauniya Hassy, lallai zata wulak'antar da wannan yarinyar ina ta samo wannan bayanan?, tayaya tasoma maganar sirrin daya shiga tsakaninta da waziri, wannan sirrine wanda babu wanda yasanshi daga ita se wasiri se kuma hajiyar Rusau se Allah, se sharce gumi takeyi a wannan daren bata runtsa ba, kanta ya dena ja kwata kwata, kodai da bak'ak'en aljanai take yawo ne? Da wannan ta yanke shawarar zuwa gun waziri domin su tattuna barin masarutar ya kamata, no where is safe yanzu acikin masarautar, shirinta tsaf tayi ta kama hanyar waje wuraren k'arfe 8 na dare, malmo ce ta walwalo da gudun ta ta zube a k'asa tana me baiwa Meenal girma tace

"Ranki ya dad'e Sawun Takawa Iska ta kad'a shanyar da kikayi zuwa wajen masarautar nan yanzu yanzun nan" Murmushi Meenal tae  Malmo akwai kaifin basira da saurin hadda akan nan, kallon sauran kuyangin ta tae  dake wurin sannan ta mayarda dubanta zuwaga Malmo

"Ba wani abu bane me muhimmanci tunda akwai ire irensu da dama anan, jeki kawai sabida binshi wajen msarautar ma rashin tsaro ne" K'ara duk'ewa Malmo tayi

"Zanje inci gaba da kulawa da sauran, gudun kada iskar ta k'ara watse mana su" jinjina kai kurun tae ita kuwa ta koma waje, kai tsaye Meenal Bed room d'inta ta shige ta masa key, sannan ta bazama danna Audio d'inda ke zuwa mata direct, shiru babu komai sabida bata isa wurinba, tafi one hour tana saurarenta harm ta sare sannan ta soma jiyo maganar su

*
"Waziri akan zancen damukayi daka kwana biyar data wuce, dawa kayi magnar ne? Kallonta yae cikin mamaki

"Haba mana hassy? Dawa to zanyi maganar ne e?  Ko tun shekaru sama da 30 da suk wuce mun tab'a yin maganar dakikajita a wani wurin?" Nisawa tayi

"Karkaji haushina waziri wannan sawun ce ta takawa take k'ok'arin wulak'antamu indai bakayi maganar nan da wani ba inaga to wlhy da bak'ak'en aljanu take aiki, Audio fa ta kawomun na maganar dukda muka tattauna dakai acikin sirri, kuma ciki hadda sharrin dana kulla mata nabaiwa wata guba ta zubawa takawa, dukkanin wasu sirruknmu da basu wuce wata d'aya ba wlhy tana sane dasu" da sauri ya kalleta

"Toko dai tana amfani da wasu abubuwan computer nan ne na zamani" girgiza kanta tayi

"Anan dajin kuma Waziri?, tayaya wata computer zata zo nan, aljanine dai tasaka yake bibiyata, kuma shiri zanyi inje Niger gobe, gun Mark'azuzu d'an tala, Zansa kai tsaye ya dakatar da aikinsu ya haukatar mun da ita kowa ya huta, batada labarin wuta ta tab'o, sabida ni wlhy ba'a wasa dani batada labarin gidan zaki ta kawo kanta da kanta, ni zakanya ce kuma bana wasa"  dariya suka kwashe dashi kanta kuma cewa

"Idan kuma mukayi wasa seta tona asirinmu akan Sarki Abduljalal, yin hakan kuma barazana ce agaremu babba"  HAKA suka gama tattaunawa sannan ta nufo masarautar.....

   Meenal kai tsaye ta mik'e ta shirya sosai shiga me tsadar gaske sannan ta shirya zuwa B'angaren sarauniya, lokcin k'arfe sha d'ayan dare yakusa yi, acen sarauniya ta sameta, kuma kowa ya kula da tsoratar da tayi sanda ta ganta, zubewa meenal tae ta gayar da  ita agaban kuyangin ta, amaimakon ta ansa seta kore duka kuyangin ta  ta mayar da dubanta zuwaga reta, mik'ewa tae ta tako har suna jiyo bugun zuciyar juna ta fuskanceta tace.

"Ina da ido k'waya dubu, kunnen k'waya dubu, k'afafu k'waya dubu, mjiya k'waya dubu, magana k'waya dubu, dukkanin jikina dakike ganinsa ido ne sunkai k'waya dubu, asaman idanuwa na dubu inada kunnaye guda biyu, kiyi kuskuren zuwa  Nigar jibi in kasheki tun a hanyar ki ta zuwa base kin isa ba, ki kira bokanki a waya kuma kiji labarin mutuwar shi zuwa gobe da safe, kiyi kuskuren sakawa a haukatani zan sanyaki mutane dubu su soma miki kallon mahaukaciya cikin second dubu, kina zata ke kad'ai Allah zeta baiwa sa'a a duniya? Ki kiyayeni wlhy, inji maganar zuwa Niger in sanar da inda tsohon sarki yake kuma in kashe mutum in kashe banza.....Abu na gaba kuma ki sani wlhy nasan cewar acikin yaranki akwki wanda ubansu ba sarki bane ciki kuwa hadda d'an fari...hahhhhh ta juya kawai ta barta a tsaye cikin tsananin fad'uwar gaba  da tashin hankali, seda ma taje tagaga zata fad'i ta rik'e kujerar dake kusa da ita, zufa se tsatsafo mata yakeyi tako ina.

**********
     Da sallamar sa ya shigo d'akin ya zauna kusa da ita sosai yanda zasuke fuskantar juna, narke fuska yae yace

"Ameena dan Allah badan  niba ki bani dama inmiki bayani idan har nagama bayanina be gamsar dake ba zan baki dam ki d'auki dukkanin wata mataki daya dace akaina" Kallonsa tae cikin dakewa tce

"Ina saura renka" gyran zaman sa yae

"Da farko dai sunana Mu'az Abduljlal Mu'az kaman yanda kika rigada kika sani, kuma ni haifaffen d'an wannan masarautar nan ne, kuma d'a d'aya tilo da sarki Abduljalal ya haifa shida matarsa Sarauniya Ameena Dazo ta wancen lokacin, mahaifiyata da sarauniyar yanzu ubansu d'aya, dukansu 'yan k'asar Nigar ne a masarautr agadez suke, mahaifinsu shine sarki a wancen lokacin yanzu haka yayansu ne sarki wanda suke uba d'aya da sarauniya hassy, kusan lokaci daya mahaifina da sarkin abdulra'uf suka so iyayenku suka kuma aura, bayan mutuwar mahaifinsu wato sarki mu'az se ya kasance shi aka d'aura akan sarautar wannan garin, dukda yake yanada yayyu amma mata ne, aciki ma akwai babba ma gimbiya sailuba wacce take aure a masarautar Barayar zaki, kuma ita tana da babban yaro dayake kusan sa'ana koma ya girmen, so mahaifiyata dai seda tayi shekaru goma kafin tasamu cikina, a wannan lokacin kuwa Yarima Fu'ad yanada shekaru kusan tara, gimbiya hassy ce ta haifesa kuma seda yae shekaru goma sannan aka haifen, a wannan lokacin kuwa mutane da dama sunyi bakin cikin haifata da akayi, musamman dayake basusan da wannan cikin ba  dawowa kawai akai dani, hankulnsu ya tashi ainun, inada watanni shida aka nemi me martaba mahaifina aka rasa, neman danake cewa dake har yanzu ba labarin shi, daganan rayuwa ta canjawa mamana haka muketa rayuwa cikeda bakin ciki, sarki na yanzu daga rik'on k'warya ya zarce sabida babu labarin mahaifina babu shi.

   Na taso acikin 'yan uwana cikin kyara da tsangwama, nikuwa se Allah ya d'uramun son mulki, izza da kuma jinkai sosai, tun ina k'arami nakeso in girm in karb'e mulkin mahaifina amma yarima fu'ad  seyake tabbatar mun akan bazan tab'a mulkar msarautar hankaka ba, haka na girma na tashi da shak'uwa me tsanani tsakanina da k'anwar Fu'ad wato Salma, bansan dalilin daya sanya bayan mun girma na bukaci auren taba Me martaba be hanani itaba, amma dai ban damuba tunda inawa salma son so fisabilillah.... Haka kafin nayi wannan girman mutane dasuke so su kasheni sunada yawa sosai, kingan ninan har guba ambani nasha, sannan an kuncemun burkin mota soba adadi, da yarana ma ake had'a baki ake kokarin kasheni, hka naje nayi karatun sojan kasa, bayan nan naje nayi karatun tuqin jirgi harna fara aikin na pilot.
  Haka akazo akai auren da salma, cikinta n frko aka had'e baki da kuyangrta aka zubar, haka na biyu ma, in tak'aice miki abinda baki saniba first born d'ina yanada shekara biyu aka kashe shi, idan nace kisa in nufin yankan rago, a wancen lokcin raini ya soma shiga tsakanina da me martaba sabida ina kallo zega anyi abu anma ya hana amun bincike agano su waye, harna fara zargin sa dukda yake nasani baze zauna zaman kashe jikokin saba, amma nasani ko raina da ake nema shine sabida zahiran nake nuna masa nifa mulkin kasar sena karb'a, da haka nazo na haifi Ameena yarinyr dataci sunan mahaifiyata, ana haka dai akazo itama aka so kasheta nasha mamaki ganinta mace amma haka na hakura ganin wannan time d'in sarki ya tashi tsaye anata bincike akan wanda yaso yae kisan. Ina nan aka haifi Aliyu Hidar, tun yana jinjiri ake nemn ransa, meenal ina k'aunar matan sedai ina zargin batada jituwa tsakanin ta da yan uwanta akaina, haka taketa hakuri, a gurguje dai accident aka saka tayi, tabaro masarauta zuwa cikin abuja itada excort ashe basuda burki an kwance shi, haka sukayi Accident k'afafunta duk biyu suka yanke, gaba d'aya... Nasha kuka nashiga tashin hankali sosai Meenal inaji ina kuma gani salma ta tafi ta barmu batare damun shirya rabuwa ba, nida yaranta bamuda zab'in daya wuce mana kuka, kullum kikag muke zuwa park....

Meenal bansan dalilin daya sanya yarana suke sankiba, ganinku kurun nae atare, banida wata masaniya akan dalilin soyayyar ku kokuma yaushe har kuka saba dasu dazasu soma miki wannan so har suna miki kallon uwar da kullum sesunmun kuka akan in kaisu gunta, bazan miki k'aryaba a zatona asiri aka had'a baki aka musu dan ki shigo rayuwata ku cutar dani, ya kasance ranar dasuka takurani akan kunyi zaku had'u nakaisu park aranar aka kusa kshemun meenal d'ina aka mata wannan eban karan mahaukaciyan da mota,  kin daigani jikin meenal har yanzu se'a hankali, baya ga haka kuma sekikazo sunan da Salma ke kirana dashi kema dashi kike kirana, mafiya yawancin kalamanki irin nata ne sak, da wannan na d'auki  dogon bincike aknki, nasani basonki yasanya na aureki akwai abinda nake tsammani shisa na aureki, akwai wacce kemun bincike aknki seta yawan mawomun saqonnin wayar dake shiga tsakaninki da wasu mugwaye acikin masarautar nan, wannan ya sanya nake saka ido sosai akanki, kowa so yakeyi ya kasheni meenal, mahaifiyata kurin ke qaunata wlhy, banda ita banida masoyi a rayuwa, dole ne in kasa yarda kowama an so akasheni tare da guards dina, fadawana, kuyangina, abokaina, k'anin mahaifina, k'anwar mahaifiyata, brother na cousine nawa ke kowama Meenal, yaya zan yarda dake? Abunda ya faru ranar shine yakaini ga zuwa mtn office na gano tabbas wacce nake baiwa aiki akanki tanamiki qage, haka duka ntwrk dakike using na zauna an nunamun baki taba alaqa da wata number a masarautar nan, ita ma sena soma tsoron ta nashiga ko kwanto a ranki, dan Allah  ki yafeni kinji" Nisawa tayi tanata kuka, labrinsa ya matuqar kashe mata jiki, tace cikin sanyin murya

"Akoda wane lokaci ana so mutum yake fauwalawa Allah lamuranka, haka marigayi mijina ya fad'amun, ana kuma so kayi amfani da basirarka wurin zartar da kowane hukunci, karasa wazaka yarda da ita se mace? Macen ma mutuniyar banza irin Nusy? Banga laifin kaba danka gagara yarda da kowa a msrautar nan dakewaye, amma shin amatsayinka na me ilimi baseka binciki abu da kan kaba?" Nisawa yae amma bece komai ba taci gaba

"Mesa kake neman gafara a guna? So kakeyi ince komai ya wuce?  Kome?" Murmushi yae

"Ea haka nakeso kice My meenal" wani murmushi tayi sannan tace

"Zan taimakeka Takawa, zan tsaya tsayin daka inga cewar nidakai mun nemowa matsalolinka maslaha ciki kuwa hadda gano inda mahaifinka ya shiga, amma da sharad'i d'aya?" Kallon ta yae yana jinjina kansa

"Ina jinki menene sharad'in" D'an murmushi tayi

"Idan na taimakeka, ka gano mahaifinka, ka gano masu munfuntarka ka karb'e sarautar ka hankalinka ya kwanta, zamu rabu, zaka sauwak'emun, dama inada wani abun danike ganinsa wajibi akaina daban aiwatr ba kuma aurenka baze barni in iya aikatashi ba, idan ka yarda kayimun alqawarin wannan zan nuna maka bubuwan ban mamaki dana samo na binciko agidannan, zan kuma tsaya tsayin daka inga cewar an hukunta masu laifi an kuma kmasu dumu dumu" k'ura mata ido amma shi ai a tsarinsa babu sakin mace har abada, kuma baze iya yaudarar meenal ba yaya kenan?.

Mom Nu'aiym

Continue Reading

You'll Also Like

77.4K 2.7K 72
I do not own any of the characters. Y/n are a supe. But not a famous one, that didn't work out. Now you are one of the sevens PAs. Maybe, briefly Th...
610K 1K 47
idk exactly what this is gonna be but 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️
250K 12.7K 92
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...