TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 23

2.7K 285 20
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA KARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂....Anyiwa me dami d'aya sata.....*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd(Slimxy).*

Wattpad @ 68billygaladanchi.

23

Lafiyayyen mari Sarauniya hassy ta dire akan kuncen malmo

"Dana baku abincin kukai shine kukaje kuka sanya guba aciki, wato meenal d'ince ta gaya muku hakan zakuyi ko? Tun yaushe kuke a masarautar nan da har zaku zab'i bare 'yar talakawa ku cutar da Takawa" Jikin Malmo na rawa itada Me sulhu suka hau rantse dan kuwa sune manya acikin kuyangin

"Wlhy Tallahi Ranki ya dad'e babu wani abunda Sawun Takawa ta bamu muka zuba a abincin, hasalima ita batasan da zancen abincin ba" k'afarta ta sanya ta shure Malmo

"Karki mayar dani k'ank'anuwar yarinya mana?, to idan ba Sawun Takawar ba waye ya baku izzinin saka gubar?" Me Sulhu ce ta karb'e zancen dace wa

"Allah ya taimaki sarauniya Wlhy nidai bansan komai ba, tun safe yau dai suketa k'usk'us itada malmo mu dama ba'a bari muke isa d'akin Sawun Takawa gyaranshi ma malmo ce keyi, sabida haka sedai ko ita aka saka, dan kuwa jiyama munje B'angaren Takawar akace damu wai Sawun sa ta masa girki ya bayar kyauta, ranki ya dad'e kuma wa 'yanda ya baiwa se suka baiwa kuliya, tanaci anan ta shure basu dai fad'a bane ba sabida gudun abinda kaje kazo, watak'in ganin batayi masara ba jiya shine yau ta b'ullo ta wannan hanyar" Wani murmushi Sarauniya tayi

"Lallai asirin Sawun takawa ya tonu, haba mana take ta cemun wai itafa bazataci abinci ba idan ankai ashe da biyu tayi" Raliya dake tsaye tana yatsina fuska itaga 'yar sarki tace cikeda izza

"Naji ance taci abincin sabida yaga asirinta ze tonu she's acting smart to prove her innocence, kuma ni na tabbtar itne tayi abun, ke malmo ki gayamun Gaskiya in sparing life d'inki, itace ta baki ki zuba?" Jikin Malmo se rawa yakeyi cikinta ya d'uri ruwa muryar ta na had'ewa da yawu da majina ta furta

"Inaga sedai bayan da aka kai aka ajie kanya shiga ta zuba amma wlhy tallahi nidai bata bani ba komai in zuba a abincin ba" Dama mafita suke nema dan haka sukace

"Tabbas da hannunta ta zuba d'in kuwa sabida nina tabbatr dan taga ya kamata ne take acting banza 'yar talakawa, shi kuma tunda yafita da gawarta tun daren jiya be dawoba, soko Allah yasa y gane gaskiya" Juyawa sarauniya tayi tana sanya murmushi akan face d'inta, koda takawa be mutuba aidai zasuyi Nasarar rabashi da Meenal na har abada.

*************
Dafe da kanshi yake yama rasa wane tunani zeyi, duniyar sa abar tausayi ce, rayuwarsa duhu yake gani tuni, waze yarda dashi? Mecece mafita agareshi? Yazamana rayuwar sa kenan ba komai aciki se fitina? Ya kasance kenan bashida wurin b'uya se lallai an kashe shi? Meyayiwa mutane ne arayuwa? Ina yaga hanyar bi yaga haske? Akan sarauta zasu tsaneshi? Akan abinda gadon abunsa yae zasu nuna mai iya karsa? Akan hakane shida iyalansa basu da zaman lafiya? Meyawa mutane ne? Tunaninsa ya tsaya cak, kwata kwata jijiyar dake harba saqonni zuwa kwalwar sa ta dena aiki ta tsaya cak!!! Hankalinsa ya tashi ainun, yanzu kwanansa d'aya da ita a sibitin amma har yanzu likitoci basu ce dashi komai ba, yayi tambayar yayi tambayar amma a banza, ya rasa sukuni gashi yau ko d'an kukan dayake lab'ewa yae ya gagara zuwar masa Banda Umminsa babu wanda ya kula y kirasa yaji ya ake ciki, gashi shi kuma y gagara kiran iyayen Meenal, yana nan zaune har wani Dr. Yazo kusa dashi

"Yallab'ai muna buk'atar yin magana dakai" D'agowa yae daga duk'en dayake ya k'ura masa ido kurun batare daya ce komai ba, seda likitn ya k'ara cewa

"Yalla6ai kai muke saurare" mik'ewa yae cikin mutuwar jiki yabi bayan sa har zuwa ofishing babban consultant nasu, kujera suka nuna masa ya zauna akai sannan ya kallesa ya bashi hannu sukai musabiha Dr. Dayake ba indiye ne ya tattare nutsuwarsa ya had'e hannayensa duka biyu gu d'aya ya d'aurasu asaman hab'arsa yace

"Amm Sir you wife ate a very deadly poison, it spread all over her body to the extend that one of her kidney got infected"
Mik'ewa yae tsaye jikinsa har rawa yakeyi ya gagara furta wata kalma se motsa labb'ansa yakeyi amma sam kalaman sa sun tsaya cak!! Meyasa duk macen data rab'esa seta shiga masifu iri iri? Yanzu yaya ze kalli iyayen wannan yarinyar? D'ayan dake kusa dashi ya rik'o hannunsa shikuma d'ayan yaci gaba...

" Don't worry sir its not a big deal, after all it can be cured if care hav bn taken" Nisawa yae sannan ya zauna

"How can we take care of it sir?"

Bayani ya masa me gamsarwa ya k'araasa bayani sosai akan ba wani abu bame infection ne kawai, se matsala ta biyu ya tab'a mata idanta duka biyu sedai shima infection ne wanda sedai a hankali idan Allah ya tashi kafad'unta zasu bata medicated glass take using" Sosai hankalin Takawa ya tashi jikinsa yayi matuk'ar sanyi ainun, be tab'a zata da gaske take ba sanda taci abincin nan yazata acting kurun takeyi seda yaga ta daddage takuma birkice lokac'i d'aya......dole haka yaje wurinta amma ya tarar she's still unconscious bata farfad'oba tun jiya hasalima ox aka sanya mata dashi take zuk'ar numfashi abunta, tabashi tausayi sosai tsakanin jiya da yau duk ta fyad'e tayi wani fari fat da ita, Tunawan da yayi za'a gwada jininsa domin a saka mata idan zeyi, a waya yawa mahaifinta bayani a taqaice, sedai ya sakaya cewan guba ce taci don kariyr kanta cewa yae shinkafar 6era taci a abinci bisa kuskure hankalin su ya tashi suka bazamo anan suke har yamma, jinin dai nashin yayi haka seda tayi sati d'aya tana ciwo tukunna ta farfad'o.

*Ina Labarin masarauta?*

Labari kam yagama zaga duniyar msarautar Hankaka akan Sawun takawa ta sakawa takawa guba a abunci darensu na farko kuma ya tirsasata taci watak'il ma ta mutu dan kuwa su basu k'araji daga wurinsa ba akanta, mahaifiyar sa tana jiyosu amma bata tanka ba, ta jima tana zargin Sarauniya hassy akan abubuwwan dasuka shafeta daketa faruwa amma tayi shiru ne sabida sarakuta dake tsakanin su a wancen lokacin gakuma uwa uba jini d'aya ke yawo ajikinsu!!! Ta bar me mata bita da k'ulli da Allah mabuwayi.

*****
"Amma kinsan idan yarinyar nan ta mutu ta cutar damu sosai? Dan shine ze gaje komai ba Nusy nikuma ko oho" hannunta ta d'aura tana shafar kanshi a hankali

"Haba gwarzo? Kana ganin yanzu koda ta mutu idan na auri takawa zan dena bibiyar kane? Ai yanzu ma aka soma dankuwa sena dinga mu'a malar sirri dakai kuma kasan dole in ding lodam kud'ad'en dazaka zama wani ko? Ko bayan sarauta kana dai kallon yanda takawa yakeda matsiyatan kud'in pilot ne fa kuma babba, a k'ark'ashin turawa fa yake aikinsa?"
"Kumafa hakane, dazan samu dama ma dana nemi wasu k'arti sun k'arisamun ita daga gadon asibitin, dan idan kika auri Takawa nina warke" murmushi ta masa sukaci gaba da shek'e ayarsu dasukeyi a hotel room.

***********
Cikin ikon Allah Meenal ta samu sauk'i acikin sati na uku, yanda taso tabi mahaifinta gida abin ba'a magana, sosai take kuka akan binsa amma a kafe akan lallai sedai dole tabi mujinta, takuma kiyaye abincin dazata ci nan gaba karta k'ara cin shinkfar b'era, haka bata tona asirin meya faruba ta hak'ur suka koma masarautar da alwashin harshi kanshi setaci k'aniyar sa, idan kuma iskanci 'yan masarautar ke tak'ama dashi da sannu sannu zata yi maganin dukkansu.

******
Tunda suka koma masarautr muna fukan masarauta ke zuwa yi mata sannu amma Sarauniya ko gezau bare tazo, shi kuwa takawa bata ko kulashi idan ze shekara yana mata magana kuwa, kwananta uku da dawowa sega Talented nusy gidanta, tarba me kyau ta mata sannan ta shiga ciki tafito tace tazo suje ciki, seda suka zauna sannan ta sanya mata kuka akan ta taimaketa sabida kowama yabi ya tsaneta, ita kad'ai take sonta agidan ita kad'ai ke zuwar mata,Meenal dai hadda rungume Nusy tana kuka, da k'yar Nusy ta rarrasheta sannan tayi shiru ta bata shawarwari tana me rok'on tayita hak'uri komai lokacine, haka sukayi sallama tare da exchange na lambobin wayar su. Talent Nusy tafita tana tsananin murnar yardar data k'ara samu awurin Meenal da wannan damar zatayi amfani ta shige mata ta cimma wata manufa tata.
A d'ayan b'angaren kuwa Meenal murna ce fal aranta, tana tsananin farin cikin samun damar d'anawa Nusaiba tarkun ta, Ta b'oye abubuwan ta na record Da Kamal ya bata ajikin wayoyinta duka biyu kana kuma ta mak'ala d'aya ajikin d'an kunnenta me taken N da ad'an had'uwarsu ta kula kullum yana wurin tana fatan idan zata kwanta ko zatayi wanka tan zare d'an kunnen gudun kada aikinta ya lalace.

Shiri tsaf Meenal tayi dukda bawai dad'in jikinta sosai takeji ba ta shirya kuyanginta ta kama hanyar B'angaren sarauniya hassy, itama ta had'o rashin mutuncin ta ayau ta shigo gidan, a saman kilisar ta ta sameta zaune tana cin Apples kamar kullum takul cin tufa d'in yazame mata al'ada, yaukam bata zube ba zaman tamatela tayi takai hannunta ta zari Apple d'aya kanta kaishi bkinta ta waigo tace da kuyangin

"Kai duk ku watse anan" Lokaci d'aya ta musu kwarjini dukknsu suka watse harnkuyangin Hassy, seda ta gutsiri Apple d'in sannan tana murmushi taceda Sarauniya

"Mama Hassy!!! Yaubako gaisuwa?" Zabura sarauniya hassy tae cikeda b'acin rai ta furta

"Ke 'yar Talakawa!! Harkin isa ki zauna haka inda nake, ni zaki ambata gatsai batare dakin sako ainahin sunana ba n sarauniya? Ko kinaso ko bakyaso nice sarauniyar Hankaka kuma ko matsiyacin ubanki be isa ya hana akirani da wannan sunan ba" murmushi tai

"Idan kuma wannan ya fita fa" ta kunna mata recording na komai da suke k'ullawa, bata fahimci komai ba dan gane da abinda taji, zaman ta ta gyara tana zare ido, murmushi Meenal tayi ta dawo dashi baya ta mik'a mata wayar, karb'a tae da sauri ta kara a kunne, mik'ewa tai bayan data gama jiyo bayanan sirri nata kala kala ciki kuwa hadda wanda sukayi da sarki, shak'o alkyabbar jikinta tae ta mik'ar da ita,hannu Meenal ta saka ta bige hannayenta data rik'ota dasu tace cikeda izzah

"Girma zaki rik'a bani kokuma ilahirin masarautar nan dama kewaye su d'auki baitukan makircin dakike shiryawa, cikin mintuna dabasu wuce biyu ba zan saka gaba d'aya masarautr nan da kewaye kalaman ki ma mugun aiki su zame musu tamkar baitukan wak'ar datai fice a gari" Cikin tsananin fusata da doka wayar da k'asa seda ta tarwatse, wata dariyar mugunta Meenal ta bushe dashi sannan tace

"Ki fasamun waya so dubu, inada basira so dubu, dazan yad'a abinda kika aikata wa mutane miliyan dubu acikin saqonni dubu dabazebwuce d'aukata second d'aya ba so dubu" cikin fusata Sarauniya ta soma kumfan baki, tsaki ta daka

"Ki kuskure umarnina d'aya zan fallasa har tsakanin ki da waziri!!""" Da sauri sarauniya ta wurga mata kallo, wata dariyar ta kwashe da ita

"Shak'yanci kam nafikishi, danni nan dakike ganina da abu k'alilan zan iya tarwatsa sharrin mutum dubu acikin second d'aya so dubu, in girzaza zukatan mutum dubu, in anfana da abu dubu acikin lokacin dabaze wuce second dubu do dubu ba" murmushi ta k'arayi, ta nuna sarauniya da d'an yatsanta tana me bada wani sauti da yatsunta guda biyu

"Karkice zaki shiga hurumun me dubu, dan wlhy bala'inany shallake naki so dubu, kiyi biyayya so dubu ki binne sirrinki so dubu, se kinji sak'on sharad'ina sarauniyar Hankaka, yanzu kam kinada uwar gida a masarautar nan" Ta juya bayan ta tattare gawar wayarta tanar sarauniya tsaye agun tamkar wata statue.

Continue Reading

You'll Also Like

83.1K 2.9K 72
I do not own any of the characters. Y/n are a supe. But not a famous one, that didn't work out. Now you are one of the sevens PAs. Maybe, briefly Th...
153K 5.6K 26
فيصل بحده وعصبيه نطق: ان ماخذيتك وربيتك ماكون ولد محمد الوجد ببرود وعناد : ان مارفضتك ماكون بنت تركي !
5.3M 46.3K 57
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...
63.4K 1.1K 96
Continuation of Modesto story who happens to intercourse with friends,mature,classmates,strangers and even family...