TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 12

2.4K 252 15
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                  12

Tun jiya gaban Ameena ke yawan fad'uwa aduk sanda ta tuna hidar gashi kuma kwata kwata batada lambar wayan takawa, yau tana school kuma se 3 zata dawo, ana lecture amma sam hankalinta baya wurin lecture da akeyi, a gaggauce taga sha biyun rana tayi tabar school d'in, kai tsaye asibitin ta wuce inda ta taradda takawa a d'akin, seda ta wurga masa kallo na 'yan dak'ik'u kanta d'an russuna kad'an tace dashi

"Sannu Abu Haidar ina wuni" seda ya d'an ja fasali kanyace

"Lapia" bata kula da yanayin amsawar saba ta wuce gun Meenal, myrmushi tayi ta dafa goshin yarinyar ancire mata bandage dake kanta, ta furta

"Small meenal sannu, ashe kuna jiki yayi sauk'i" murmushi tayi sannan ta yunk'ura zata zauna, da kanta ta tayar da ita,yarinyar ta turo baki

"Mom kinga dad ko? Shine yace da Dr. Ya askemun suman kaina, kinga yanzu dukba rabin sumar"  rungumota tae

" karki damu, zamuje paris na siya miki man gashi me kyau, ze cicciko inshaa Allah"  murmushi tai batace komai ba....
Dubanta ta miyar gun TAKAWA tace "ranka ya dad'e dan Allah Haidar fa? Inaso na ganshi ina kewarsa sosai, kuma bana ganinsa anan, ko yana gun momyn sane?" k'ura mata ido yae yana tunanin maganar ta, batasan momynsu ta mutu ba kenan? Meenal ce ta katse tunaninsa da cewar

"Momynmu ta b'ata, tun randa ta b'ata  daddy kullum seyayi kuka, nima nida Haidar mukanyi kuka sosai, amma yanzu dakike nan na rage kukan, kuma rannan kikace zamu ganta inshaa Allah ko?" Shiru tana nazarin kalaman yarinyar ta kuma mayar da dubanta zuwaga TAKAWaa

"Inshaa Allah zamu ganta ne, karki damu kinji, daddyma zan bashi hakuri ya dena kuka, kina cewa Allah ya bayyanar mana da mommynki adu'a yanada kyau sosai, kuma idan kinawa mommynki adu'a zata dawo inshaa Allah indai tana raye, adu'ar yara karb'bbiyace" jinjina kanta tai  sanna ta qara cewa

"Kinga ranar da motar nan ya kad'eki, hadda rashin adu'a fitar daga gida, kinga idan da zakina karantawa kullum kafin ki fita  da babu abinda ze sameki inshaa Allah, idan ma an rubuto motan ze kad'eki sekiga sanadin adu'ar nan Allah ya kareki abun yazo da sauk'i, kinga amaimakon wannan karayar seki gurd'e kad'an, yanzun ma nasan adu'ar daddyn kine damu ya sanya ba'a goshi kikaji ciwo ba a baya, sumar kanan naki ze fitone inshaa Allah" Lafewa ajikinta yarinyar tayi

"Ni bansan wane adu'a bane ba mom"  koyar da ita tashigayi tana fad'a tana nanatawa, sunyi yakai so goma seda ta tabbatar ta hardace kannan ta mayar da dubanta zuwaga TAKAWA wannan yarinyar tana matuk'ar rikitar da   shi, me bibiyar ka da sharri baze tab'a cewa ka nemi kariyar Allah ba, danyasan ta shallake ta kowa, menene ainahin abinda ya had'ashi da wannan baiwar Allah ne wai? Maganar Ameenan ce ta katse masa tunanin sa

"Ranka ya dad'e yau haka kawai hankalina yake gun Hidar, dan Allah   ka kaini gun yaron nan na dubasa, kwana biyu kenan shiru ban ganshi ba" murmushi yae yanzu kam, betab'a ganin tayi irin saba yace

"Muje" rarrashin Meenal tae, sanda ta hakura sannan suka wuce akan zasuje su kuma dawo ba jimawa, da jakadiya suka barta sannan kai tsaye da kanshi yau yaja motar suka nufi gidansa, yanaso yakai k'arshen tunanin sa....baya fatan yawa mutum yankan hukunci ba bisa ga hakk'i ba....beko kalletaba, har suka isa a wurin wani tangamemen gate me asalin kyau zubin na turawa....tasha mamakin ganin duk girman filin gidan gidane very cute cen a laqe, ga korayen ciyayi dasuka farfajiyar gidan k'awanya yayi kyau matuk'a......fadawane da kuma securitie's tako ina, kai tsaye wani parking space ya tsaya suka fito, daganan batare da yayi magana ba yashige gaba tabisa a baya, a parlor suka taradda Hidar wanda a take ya rugo da gudun sa ya rungume mom d'insa, Murmushi TAKAWA yae yana mamakin yanda yaran ke tsananin son yarinyar, yama kula bazata wuce 17 yrs ba, ita kuwa meze kaita shiga dabgar daba nata ba?...... Wucewa yae a d'akinsa befi 12mns ba yafito  daga room d'in kai tsaye hanyar waje yae, sak'on Talented ne ya fito dashi d'akin a birkice

"Ranka ya dad'e sir akwai damuwa a asibiti, kaje da securitie's naku yanzu" Becewa Meenal k'alaba ya fice had'a kan securities d'in yae cikin k'araji suka bar gidan se iya masu gafi susu biyu.... Tajiyo ihunsa amma bata wasu 'yan damu ba  tazata haline kurun ya motsa, takula yanada jin kai sosai man d'in...

"Mom muje kitchen ki dafamun indomie, yunwa nakeji kuma suka dafamun rice & stew bana santa"

"Muje ka kaini kitchen din my Hidar zan dafa maka" Jakadiyar dake nanne ta matsa kusa da ita

"Ranki ya dad'e wannan aikin ba naku bane ba, namune ki bari kawai zan dafa masa da kaina" mik'ewa tai

"Na mom yakeso karki damu" Dole jakadiyar ta kame bakinta taja gefe tama bar d'akin gaba d'aya, su kuma suka je kitchen d'in.....

**********

  Babu kowa agidan inji Talented Nusy, tace camerar ta ya nuna mata wata mace daya shigo tare da ita, amma babu a waje bare ta gane ko tare suka fita, datai kula  yarinyar ma ta mik'e, bazeyi gangancin barin gidan tare da Hidar ba sabida kisansa zezo da sauk'i, dan kuwa babu  kowa agidan se mata, masu gadin na waje ma na bad'esu da powder sun gama suma" Bata fahimci zancen saba, kisa kuma? Hidar? Anya taji daidai kuwa? K'ara matsawa tayi kusada window d'in ta hango maza sunkai susu goma sun saka mask a fuskokinsu  d'aya daga cikknsu ne yake waya, lura datai na waje baya hango naciki ne ya bata damar k'are musu kallo sosai, wanda ke wayar yaci gaba

"Ea Hajiya, da Talented mukai magana fa, ba kowa se mata mazan an sumar dasu, kuma ni babu wanda ya sanni a masarauta sannan a shirye nake dana sadaukar da raina akan ki hajiya" bataji me aka ce masa ba, tadaiga ya katse kiran ya saka wayarsa a aljihunsa....juyawa tai ta kalli Hidar dake ta wasansa da kekensa daya d'akko, d'ankwalin kanta ta cire ta d'aure bkinsa, jikinta har rawa yakeyi tace

"Hidar kasan yanda ake kashe mutum a film?, to wasune sukesk su kashemu, karkayi magana zan sakaka a drower karkayi koda motsi, komai girman surutun dazakajiyo karka koda motsane kajini ba?" A firgice yake se d'aga mata kansa yae, ya rud'e sosai yaron, da durowa ta turasa ta kitchen d'in wacce ke manne da bango sannan ta tuttura masa kayan kitchen ta kkma ta rufe sa tanata k'ara masa k'aringwiwa shikuma se hawaye ga wurin zafi....

Fitowa tayi da sunan rufe k'ofar da gudun ta, anan tayi karo da jakadiya a sheme a wurin, ja tai da baya cikeda tsoro seji tayi tayi karo da mutum, cikin razani ta waigo, d'aya daga cikin mutanan nanne data gani a bayan gidan, wanka mata lafiyayyan mari yae yace

"Ina Aliyu Hidar?"   Dafe wurin tae

"Ni bak'uwace agidan bansan shiba" Harara ya wurgo mata dukda idanshine kurin a bud'e, ya shak'o wuyanta

"Zaki nuna mana yaron kose na kaiki lahira?" Jikknta har tsuma yakeyi

"Kayi hakuri ammma banga wani yaro ba sanda nazo nan" wani marin ya aika mata ya shureta a k'afa ta durk'usa ya ce

"Banida lokacin dazan baki ki b'atamun, zaki gayamun gaskia kosena  hallaka ki" roqon duniya tashiga yi musu akan su k'yaleta amma seda ya yanki hannunta ta saman dantsen ta, wani arnen deep cut ne ya bata seta ta k'ara, se k'ara yankanta wayarshi tae ruri...ya dakata ya kara a kunne , kallonsu yae

"Talented tace TAKAWA yana hanya mubar gidan yanzu" juyawa sukayi ita kuma ta dafe wurin se tsargar da jini yakeyi tamkar an yanka bijimin sa, sosai suka manta yankan wulaqanci, batasan hawa ba batasan sauka ba,, rerafawa tadomayi zuwa kitchen d'in bayan taji shiru, sabida k'afarta daya daka da takalmin nan masu kamada k'arfe, amma seta kasa tashi jan jikinma ya gagareta, kanta wani uban sara mata yakeyi har cikin idanta, gata dafe da hannu....a haka TAKAWA da wasu securitie's suka taddasu itada jakadiya dabatasan halin da ake cikiba sam!!!  Da sauri yaje ya rik'ota ita dayaga alamar rai a kanta

"Sannu, suwaye suka muku haka?" Cikin k'arfin Hali tace

"Haidar yana kitchen, akwai zafi ku kaini in fiddashi" mik'ar da ita yae yana cewa

"Sannu Kinji, inane yake?" Hanyar kitchen ta qara nuna masa sukai cen se d'ingishi takeyi tsabar azaba, fuskarnan tayi suntum sabida tafin k'ato, ga yatsunta sun kwanta sunyi k'uru k'uru....da k'yar ta janyoshi inda ubanshi ya kama mata, yayi zufa zufa, dukya jike sharkaf, amma murmushi ya sakrwa daddynshi yayi kan mommynshi da sauri, be fahimci komai ba, se cewa yae

"Mom nadena wasan b'uya dake kin dad'e baki zoba se gumi nakeyi" kallonsa takeyi amma bata gani sosai jiri sosai yake d'ibanta bibbiyu take gani, loooo ta tafi zata fad'i ya rik'ota sosai zuwa jikinsa, se asannan data saki hannunta ya kula da tsananin yanka da aka mata, da alama addace dan wannan abin yayi yawa har flesh nata kana hangowa

"Innalillahi wa inna ilahiraji'un" Itace kalmar daya furta a sarari,hidar ya saka masa kuka akan mommynsa, securities ne suka kamata zuwa mota dan kaita asibiti, shikuwa qarar shigowar message a wayar sa ya sanya yakai hannunshi ya zaro ya duba

"Dukkanin abinda ya faru agidanka shirine, wannan yarinyar da sani tayi wannan shrin, so take ka yarda da ita ka sanyata ajiki ta cuceka, bata taba cewa ka kaita gun Hidar na se yau?... Ta b'atar danine domin a waya sunyi magana ne akan kisan Meenal, ina record na komai....seka zo na baka!!!

Mom Nu'aiym

Continue Reading

You'll Also Like

333K 19.3K 41
You live in a different time zone Think I know what this is It's just the time's wrong
262K 39.9K 102
แ€•แ€ผแ€”แ€บแ€žแ€ฐแ€™แ€›แ€พแ€ญแ€แ€ฑแ€ฌแ€ทแ€˜แ€ฐแ€ธแ€†แ€ญแ€ฏแ€œแ€ญแ€ฏแ€ท แ€šแ€ฐแ€•แ€ผแ€”แ€บแ€œแ€ญแ€ฏแ€€แ€บแ€•แ€ผแ€ฎ แ€Ÿแ€ฎแ€ธแ€Ÿแ€ฎแ€ธ แ€–แ€แ€บแ€•แ€ฑแ€ธแ€€แ€ผแ€•แ€ซแ€ฅแ€ฎแ€ธ
152K 5.6K 26
ููŠุตู„ ุจุญุฏู‡ ูˆุนุตุจูŠู‡ ู†ุทู‚: ุงู† ู…ุงุฎุฐูŠุชูƒ ูˆุฑุจูŠุชูƒ ู…ุงูƒูˆู† ูˆู„ุฏ ู…ุญู…ุฏ ุงู„ูˆุฌุฏ ุจุจุฑูˆุฏ ูˆุนู†ุงุฏ : ุงู† ู…ุงุฑูุถุชูƒ ู…ุงูƒูˆู† ุจู†ุช ุชุฑูƒูŠ !
66K 3.7K 79
When shrivi goes home after a long time. Who doesn't have her parents' love and family's love for some reason. She had support from her grandmother...