TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

By 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... More

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 9

2.5K 251 12
By 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                09
"Waini meyake damunki ne lele? Anya bazaki wa kanki fad'a ba ki janye daga zancen auren  yusuf tunda yace kuma ya nuna bayayi dake, sekace bakida masoya? Dan Allah  kiwa kanki fad'a meenal"  kallon uwar tai

"Mom ni bafa akan shi bane ba nake damuwa, ni indai yusuf ne inshaa Allahu sena auresa, wata yarinyace mom suke sona a park muka had'u itada qaninta da dad d'insu, ni bnsan su waye badai bansan mezance miki ba akansu, kurun dai inasan yaran ne suma haka, to munyi alqawari akan zamu had'u wednesday last week shine banje a na shafa, ashe sunje garin nemana mota ya kad'e yarinyar, baki gantaba jiya naje asibitin sekin mata kuka, shine nakeso in koma dubota, abin yana raina wlhy a damu sosai" jinjina kai mom tae

"To Allah ya bata lapia, semuje tare da junior anjima, ki shirya musu wani abin" batae magana ba dai har mom ta fita.

*****************

    Shi kwata kwata ya manta da wayanta dake kan cinyarsa wannan ne ya sanya yana fitowa mota ta fad'o, glass d'in wayan yae dama dama, bakama iya tab'awa ya jujjuya wayan tsadar tane yafi bashi mamaki, yakula manya manyan wayoyi uku ne a hannunta ko akan me oho? Beso hakan na, sabida baya son wani alaqa me tsayi ya shiga tsakaninsa da wannan yarinyar yaga pics nata da yawa dani mutum dayake saka ran mijinta ne, bayaga haka shi haka kurun yarinyar batai masa, dandai su Hidar suna takurawa kansune a kanta, amma banta haka ko ganin yarinyar ji yakeyi beson yi, setake qoqarin kwaikwayar halayyar salma wurin yiwa yara abu, tana cikin prime suspect nashi akan salman sa, ina tasan sunan da salma ke kiran yaran dashi? Mesa dacen be tab'a zuwa gun shida salma ya ganta ba se yanzu da salma bata raye? Menene ya sanya aduk yawan matan dake wurin su Hidar suka nace mata fiye da kowa, hasalima basa zuwa gun kowa se ita, mesa suke kiranta mom? Ko asiri ta musune?, mesa tayi alqawarin zatazo musu tak'i zuwa kuma a ranar mota yaewa Meenal d'insa d'ibar karan mahaukaciya, idan tana daga cikin mutanen dake bibiyar akalar rayuwar sa ai ze ganene? Idan tunanin ta wayo takeyi tota makaro, tashige sahun gaba a mak'iyan sa, kuma a yau ze mata gargad'i akan ahalinsa, yaga me martaba se wani zancen banza yakeyi tazo tanawa mutane munafurcin kuka, yana sane da takun kowa, kuma ze d'auki k'wak'waran mataki akan yarinyar....yanzu ze kwantar mata kaman ba komai bari ya soma akan binciken mutumin daya gansu tare a hoto, tayi k'ank'anta ace tanada aure, amma wacece ita?!!!!! Babu wanda ya isa ya bashi wannan ansar se talented Nusy!!!!! Bari yabar ragamr komai a hannun ta...

******************
       Shirin komai Meenal tayi ta kimtsa acikin lace d'inta ruwan toka, anmasa ado da zanen pink colour yasha d'inkin bubu free har k'asa, siririn mayafi ta yafa pink color, se takalmin k'afarta shima pink, tayi kyau dukda ba makeup ko d'aya a fiskar ta, kwalli ne kurin a idanta wanda ya k'ara taimakawa kyawun fuskarta dakuma k'uruciyar ta, Junior tare da mommy ne 'ya rakiyar ta, haka suka d'unguma driver ne ya kaisu har asibitin inda suka jeru zuwa ward d'in.....tasha mamakin ganin an k'ara yawn masu tsaron k'ofar d'akin, sedai basu hanasu shiga ba,  koda suka isa d'akin ba kowa ba kaman jiya ba, se ita kad'ai tana wasa da hannunta me lafiyan...kai tsaye wurita Meenal tawa kanta masauki ta furta

"Sannu Name sake, yaya jikinki" shagwab'e fuska tae

"Mom fushi namiki ai, se yanzu kikazo?" Cikin tausayawa tace

"Karkiyi fushi my meenal, ba laifi na bane abubuwa ne suka sha kaina, kuma kinga banida lambar wayan daddynki aida na kirasa da kaina na sanar masa bazan samu zuwaba ko?" Murmushi yarinyar tai

"Ba komai mom, amma kinga yunwa nakeji tun d'azu kuma daddy be shigo ba" da murmushi tace

"Na kawo miki abinci my Meenal, kinga na kawo miki chicken da kuma fruits salad, har onion kabana rice Mommy ta miki, wanne kikeso kici emm my meenal?"

"Zanci chicken d'in zanci komai ma" ita ta tasheta ta bata taci abincin sosai, tunda ta kwanta yaune taci abinci mem yawa hakan, tana gamawa se bacci a hannun Meenal tai baccin.....haka suka zauna asibitin har kusan magrib sannan suke shirin tafiya, a lokacin ne kuma *TAKAWA* ya shigo d'akin, fuskar nan babu yabo babu fallasa, kwantar da Ameena tai ta mik'e tsaye, wadata fuskar ta tai da murmushi kan tace

"Sannu Abu Haidar yaya aiki?"  Da sauri ya miyar da dubansa zuwa gareta, wannan sunane da Salma kad'ai ke kiransa dashi, yaya wannan yarinyar tasan dazaman sunan ne? Kotasan Salma ne? Kai ina batasan Salma babu wani mahaluki a rayuwa dayasan Salma wanda be sani ba, tabbas wannan yarinyar tana da hannu acikin kisan salman sa, kokuma tanada alaqa da wanda sukayi kisan, kuma dasa hannunta ake k'ok'arin hallaka masa Ameenan sa, lallai tana wasa ne da rayuwarta a hannun sa.....yana tunanin harta kuma cewa

"Bismillah ga wuri koda yake Ameenan ma bacci takeyi" Bece komai ba yaje ya zauna a gefen gadon ya dafa hannunsa saman wuyanta, kannan ya miyarda dubansa akan kulolin abincin dake baje a wurin ga plate awurin dake nuni da angama cin abinci , cikeda tashin ya kalleta

"Wayaci wannan abincin?" Ya wurgo mata wannan tambayar cikin hargitsi

"Meenal ce taci, itane take jin yunwa, dama nazo mata dashi shine na bata, kuma alhamdulillah taci sosai" Wani yawu me d'acin gaske ya had'ya amma ya gagara furta komai, bayaso ta fahimci ya gano ta shisa yakeso ya basar, kallon mommyn meenal yae yace

"Sannu ina wuni? Yakuma d'awainiya" se a sannan ta saki ranta, da har taji haushinsa akan ya k'yaleta, data haihu da wuri aida ta haife kamar sa..

"Lafiya qalau ya me jikin?" Murmushi yae

"Kune kuke jinya ai, mu yanzu mukazo" Fara'arta ta fad'ad'a

"Ai minal da sauk'i sosai, Alhamdulillah da kanta fa tace tanajin yunwa shine mommynta ta bata abincin kuma taci sosai, se bacci kuma   ya biyo baya" k'arayin yak'e yae amma bece komai ba, suna nan jigum jigum har wani lokaci, mom ce tace zasu tafi, amma shi so yakeyi se meenal ta farka yaganta da rai tukunna ze bari su tafi,Meenal ce ta sharb'e zancen

"Mom nagan ba kowa a wurin  Small meenan nan, soku tafi driver ya mayar daku, ni idan akayi isha senai waya driver yazo ya d'auken mu tafi" mik'ewa mom tayi

"Hakane, zan gayawa daddynki inda kuke, yace zezo ya dubata shima, amma maybe se zuwa gobe zezo" rakiya tawa mamanta har waje sannan ta dawo da sallamarta.....

Bakyajin komai se k'arar AC da fan dake d'akin, se kuwa bugawar zuciyoyin su dake tafiya da sauri sauri alokaci d'aya kowa da abinda yake sak'awa a ransa, itadai k'warjininsa ne ya mata yawa har bata iya kallon sa, yayinda shi kuma ya kafe ta ido yana nazarin ta, ya kula sosai nauyin sa da kuma kunyar sa takeji, wai wacece wannan baiwar Allah ne? Yanaso yasan komai game da ita.... Hidar ne yashigo tare da Escort dakuma fadawan sa  kai tsaye jikin mom d'insa yafad'a

"Mommyna, yaushe kikazo anan? Shine baki kirani nazo ba" murmushi tayi

"My hidar kayi hakuri, inata   nemanka bansan wazan kiraba ya kawon kai ba" Lafewa yae ajikinta

"Daddyna ma yae tahowar sa yabarni agida ni kad'ai, yanzumma kuka na saka shine aka aikoni anan" tayi murmushi wowtarsa wai aikosa ma akayi

"Tom ka k'yale daddy, idan zamuje paris bazamu dashi ba" wannan kalmar ta paris ta k'ara rikita tunanin Takawa, ina kuma tasan best Country na Salma, haka take yawan fad'a duk sanda Hidar ko meenal sukace daddy ya musu kaza koya musu fad'a se Salman tace bazasu dashi paris ba, wannan wace irin macece wai?  Mesa take bibiyar iyalansa? Waye yake sakata?

Mom Nu'aiym

Continue Reading

You'll Also Like

186K 6.9K 13
2 tom dylogii ,,Agony"
154K 5.6K 26
فيصل بحده وعصبيه نطق: ان ماخذيتك وربيتك ماكون ولد محمد الوجد ببرود وعناد : ان مارفضتك ماكون بنت تركي !
84.4K 3K 72
I do not own any of the characters. Y/n are a supe. But not a famous one, that didn't work out. Now you are one of the sevens PAs. Maybe, briefly Th...
66.7K 3.7K 79
When shrivi goes home after a long time. Who doesn't have her parents' love and family's love for some reason. She had support from her grandmother...