🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀

By xinnee_smart1

49.3K 2.6K 41

Dan Allah kuyi mun rai garku lalatamun Rayuwa...... More

🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part.. 1
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 5
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 2
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 3
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 4
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 6
🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀Part 7
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺Part8
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part9
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 10
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part11
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 12
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 13
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 14
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 15
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 16
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 17
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 18
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 20
🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀Part 21
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 22
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 23
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 24
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 25
🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 26

🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 19

1.6K 92 0
By xinnee_smart1

🥀🌺🥀 *FAHIMTA*.... 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life......_

   *XINNEE SMART*

~In life nothing will surprise me~ ~any more~ 🤷🏻‍♀

*19* Rukayya, kam agurinta duniya sabuwa dan sossai take she'ke ayarta yadda takeso, a 'bangaren auren Ma"aruf, a cewarta sai ta more kafun takoma gidansa, ko bakomai lokacin, ya gyaru dan so take ya San mahimmancin ta,

   Dan haka ma takashe wayoyinta, daga London, California tabi wani saurayinta, suka wuce, dan haka nema mahaifiyarta batasamun ta dan duk wayoyinta datake amfani dasu layukan waje ne kuma bamai number gashi ita ba wanda takira,

A kwance take kan gado tayi d'ai d'ai da ita sai faman ajiyar numfashi take, dan yauma kamar ko yaushe, bokan nata yazo yagama wujijjigata,

   Saida tad'auki tsawon lokaci tana maida numfashi kafun tami'ke, tashiga bathroom, tayi wanka, normal wankan soso da sabulu, tafito, shiryawa tayi, tazauna wayar ta tad'auko Kai tsaye layin Ma"aruf, na Thailand ta kira, yayi ringing har yagaji ba'adauka ba, ranta ne ya'baci amma bata karayaba tasake kira yana fara ringing cikin sa'a yad'auka sallama yayi, kasa amsawa tayi dan tarasa mai zatace amma dayake batada kunya saitace hello"Ma"aruf, Rukayya ce..... shine tunda natafi ko kanemeni? katse ta yayi tahanyar yin tsaki batare dayace komai ba yayi hanging, shiru tayi tana kallon wayar cikin 'bacin ran katse mata waya da yayi, kawai sai tasake Kira aikuwa tana soma ringing aka katse, busy tagani, aikuwa ranta ya'baci kamar me, take tahau mita,

Tabd'i jam! lallai ma, Ma"aruf, Anya yanacikin hankalinsa kuwa,? lallai nayi sake, aikuwa yazamar mun dole inyi gaggawar komawa, dan bazai yu ba, cikin sauri tafita, shirin tafiya tashiga yi gadan gadan,
 

Yakama yau alhamis "dan haka yau jirginsu Rukayya yalula, zuwa gida Nigeria'  'karfe 8:45jirginsu yasauka, a filin jirgin Aminu kano, dake kanon Dabo,  taxi tad'auka zuwa, hotel, d'aki takama a hotel din,

          Gari nawaye wa, tai Airport, sai Niger state,

Kai tsaye gidan iyayenta tanufa dan sotake taji ko tunda ta tafi Ma"aruf yazo ko bai zo ba?
.......................................................

Rukayya, wannan wani irin shashanci ne? har yaushe zakiyi tafiya, kikasa Kiran Kowwa a gidanku, har Yan uwanki dakuka tafi tare sudawo ke baki dawoba? Uhmm saboda Allah fa?
Tunda mahaifiyarta tafara mata magana komai batace ba, sai faman zun'bura baki take tana guna guni,
   Au ina magana kina wani turo baki gaba ko?
to dan Allah Aunty (kasancewar haka suke Kiran mahaifiyar su) ni mai kikeso ince? Daga dawowa ta kinsakani agaba kinata mun fad'a... Au haka ma zaki ce, to ai shikenan, nayi shiru...., 

toto.... tooo.... nidai kiyi ha'kuri, dama sonake inji ko danatafi Ma"aruf yazo? Kallonta uwar take cike dajin haushin yadda Sam bata ganin girmanta, Koda dai laifin nasu ne itada mahaifinsu sun sagarta yayansu sossai, shiyasa basu da wata tarbiyya,

     Kinji?

maganarta tadawo da ita daga tunanin datake,

Shiru uwar tayi tana nazarin tafad'a matane kokuwa?

Sallamar yayarta Maryam ce tasa dukansu duban 'kofa, kuka take uwa wacce uwarta ta mutu,

     Take hankalinsu yatashi ganin halin datake ciki, lafiya mahaifiyarta ta tambaya, batace komai ba sai kuka datakecigaba dayi, da'kyar dai tasaurara da kukan, cikin sheshe'ka da tashin hankali, tace....

Aunty Umar, yacuce ni, yasake ni..... ta'karasa fad'a da kuka, saki?
Suka had'a baki gun tambaya, Rukayya tace.... Amma dai Umar yacika butulu, duk abunda daddy yaimasa ashe zai iya sakin ki? Ko dayake namiji ne, amma yanaga fuskarki da shacin hannu,
Cikin kuka tace Saida yadakeni kafun yasakeni,.....

Aunty ce tace.... towai mai kikai masa har dayaimiki wannan irin saki na wulaqanci,??

   Aunty wai mahaifiyarsa ce tace lallai ya'kara aure wai banida kirki, nikuwa nace bata isaba shine fa, yadinga dukana wai naiwa mahaifiyarsa rashin kunya,.... Shine yasakeni kuma wai wani sati Za a d'aura masa aure da yar uwarsa......
Kanbuuuu, cafd'i, kishiya? tunkafun tazo ma andake ki a kanta ansake ki akanta,... amma ke baki d'au mataki ba, nikam wlh bawanda ya isa yaimun wannan iskancin,

    Tunda tasoma magana Aunty ke Kallonta, Maryam ma dake kuka saurarawa tayi tazuba mata ido, zatayi magana Aunty taimata alama datayi shiru, haka suka zuba mata ido tana ta bambamin fad'a, dacin alwashi Kala Kala akan duk ranar da miji yayimata kishiya to saitayi kaza, magan ganu dai gasunan, daga 'karshe ma tace ni bari kugani ma intafi bazan iya jin wannan takaicin ba, mtss.... tasa'ba Jakarta taja trolley d'inta tatafi,....... Murmushin takaici mahaifiyarta tayi, tace kowa yace yace to Sai yace bai ce ba,.......

.......................................................
Kai tsaye gidansu Ma"aruf tanufa, tanazuwa bakin gate tacewa mai gadi,Ma"aruf na nan kuwa,?

a a bayanan,
tasan Sarai bayyanan, dama sotake kawai ta'kara tabbatar wa yadda zataji dad'in shirya masa gadar zare, saidai ko yana gidansa,Maganar mai gadi taimata dirar bazata,

gidansa?
tamaimaita.... Cike da mamakin dama yatashi ne? Eh gidansa dake can scorepion road ba,
        Cike da son tabbatar wa da gaske yake tace zaka iya kwatantamun? Kasancewar yasanta, shiyasa baiwani 'ki kwatanta mata ba,


Kwance take a parlour d'in ta, hannunta da remote control, tanacanza Channel zuwa channel d'in datafi so wato Saudi, wayarta dake charge ce tayi ringing, jin taken ringing d'in ne yasa tagane mai Kiran, dasauri ta tashi,

Assalamu"alaikum "y masoyi nah" tafad'a cikin zazzaqar muryarta, amsawa yayi a d'aya 'bangaren, yaci gaba dacewa, I hope, saheebar tawa tana lafiya? Uhmmmhmm lafiya qlu nake inafata kaima haka,? Uhhm to dasauqi dai amma gaskiya ina kewar ki da wannan warm body d'in ki, in fact Jina nake kamar inganni a jikin ki Abu nah.... ya fad'a dasigar tsokana, Uhmm... Uhmm kagani ko tsokanata ma kake, tafad'a a shagwa'be, dariya yayi, um um niba tsokanar ki nake ba, Shima ya fad'a yanayin yadda tafad'a,

Dariya tayi, inafata dai aiki baya wahalar mun dakai? Uhmmm tom dasauqi dai, still dai kece damuwata, kowani emotions dina to kece aciki, zainab bazan iya Rayuwa babu ke ba, musamman a daidai wannan lokacin da kike sake sanar dani wacece zainab....i can't hide it for you, yah I'm really enjoying been with you, bazan so wani abu yashiga tasakani nadake ba a daidai wannan lokacin dakike lasamun zumar ki,........badan makarantar ki ba da dake zantafi,........ Shhhhh tafad'a is OK, ya isa haka, kaifa mijina ne mijinma wanda nakeso yake sona, so wanda banta'ba jin labarinsa ba banta'ba kallonsa ba banta'ba karantashi ba....... Ha'ki'ka kai mijine d'an aljanna, wlh da dawani kulawar nadaban danayimaka da da abunda zanma, yabaka farinciki dawwamamme tabbas danayi ma,.... Saidai....... Akwai, yakatseta, tabbas akwai zainab, nasan zakiyi mamaki, kuma zaki so sanin meye shi to bakomai bane face kisoni so wanda bashida 'karshe kisoni har'karshen rayuwar ki, murmushi tayi.... Indai wannan ne kasamu mijina, nasoka ina sonka ina ci gaba da sonka ina kan sonka....... Nagode my happiness, u are my world&I love you so very much my Baby....... dariya tayi to nagode yakamata kayi aiki, ........ Dukan dataji anawa 'kofar gidan tane yasa tayi saurin duban'kofar,

     Inaga nayi ba'ki Darling husband, OK to saina kiraki anjima, take care of yourself for me please, I will insha'Allah,
Ngode sossai da kulawar ka, is my pleasure, byee ahha byeee, ummhhhwahh, dariya tayi thank you, byee d'if takashe wayar,

dan inba haka tayi ba tofa bazai kasheba, yadinga kawo wata magana kenan shiyasa idan dai tanada abunyi itace ke kashewa, dasauri tanufi 'kofar dasaifaman duka ake ba saurarawa, tana kama handle d'in taji gabanta yai wata mummunar fad'uwa, a sanyaye tabud'e'kofar........... Wacce tagani ce tasata kusan Suman tsaye dan saida tari'ke'kofar,

     Inna"lillahi, wa"inna ilaihim' raji"un, shitake ta maimai tawa, cike da faduwar gaba, Rukayya kam tamarasa maizatace tsabar rudewa datayi da ganin yarinyar agidan da akace na mijinta to mai wannan yarinyar take a gidan?

Sa... nn..u..dazuwa...zainab tafad'a a rud'e, cike da gadara ta bangaje ta, tai cikin parlour da kallo tabi parlourn, zainab kam duk tabi tarud'e,

          Ke"

tadaka mata wata uwar tsawar data dad'a rud'ar da ita, uban me kike anan gidan? shiru zainab batace komai ba sai hawaye dake bin fuskarta, gabanta Rukayya, ta matsa, ta wanketa da Mari lafiyayye, dan ubanki ba magana nake miki ba kinajina kikayi shiru?

Hannu tasake d'agawa zata mareta caraf taji anri'ke hannun, cikin jin zafin wanda yari'ke mata hannu tajuya dan taga waye mai wannan 'karfun halin?

     Nina"tagani 'kanwar Ma"aruf,
Lafiya zakiyi ta marinta mai tayi miki,? Ai ba ita takar zomon ba rataya aka bata dan kuwa ba ita ta auri kanta ba aurota akayi........ Ragwab Rukayya tasaki hannunta da Nina tasaki, zama tayi akan tiles d'in parlour, jin takeyi kanta na wani irin juyawa,

Nina kam hannun zainab, takama suka shiga d'akin zainab d'in,
Zaunar da ita Nina tayi yayinda itakam sai kuka takeyi, zama Nina tayi a gefenta, tadafa kafad'arta, banyi niyyar zuwa gidannan ba yau saidai bayan nafito zanje gidansu 'kawata umaima,sai nahangi mota tana barin'kofar gida shine nake tambayar mai gadi waye, sai yake fad'a mun matar Yaya Ma"aruf ce, nace zainab? dan nayi mamakin abunda yahanaki shigowa, sai yake cemun wai uwar gidan sa dai, nan na fahimci Rukayya yake nufi, nan natambayeshi ya sukayi bayan naji nataho, dan nasan bazaku kwashe lafiya ba,

To ga abunda na iske, a gskiya zainab, zanbaki shawara Kidaina zama kishiya na dukanki ai sai ta rainaki yanzun da banzo ba aida wata'kila sai tayi miki lilis, wlh Kidaina tsayawa, nagaya miki idan tafad'a miki cuta kifad'a mata mutuwa, Kidaina tsayawa tana dukanki kamar wata Yar ta, Kidaina jin tsoronta dan wlh rainaki zatayi, haba zainab, kema kizama macce mai fad'a a gidanta,

Kidaina wannan kukan, tun d'azu kike abu d'aya, sai kace kukan ne mafita, Uhmmm nibari ma kigani inkira yayan, tafad'a had'i da ciro wayarta daga hand bag d'in ta, ri'ke mata hannu zainab tayi,...... dan Allah garki kirashi wlh banaso hankalinsa yatashi kuma gashi suna tsaka da aiki, Kinga Thailand bakusa bace,
        Tom shikenan Juliette, anfasa Kiran romion naki, tafad'a da sigar tsokana, har zainab, tadan yi murmushi, to mai kike so inkawo miki? Zainab, tafad'a had'i da mi'kewa, a a nikam banason komai, dan a 'koshe nake, ajiyar zuciya tayi dan dama'karfun hali ne kawai zatayi tafita amma zuciyar ta cike take da tsoro,

     Zama tayi suna d'an ta'ba fira da Nina yayin datake sake nunamata cewa ta'kwatar wa kanta yanci, dan yadda Rukayya take mata itama haka zata dinga mata, itadai jinta kawai take dan tasan da wuya ta iya yin yadda tace, saidai tana amsa matane kawai, amma bawai dan zata iyaba,............. Zuwa yamma Nina tamike zata tafi zainab kamar tayi kuka tace... Ki kwana anan mana,....

          Cafdi "aikema kinsan bazan iya kwana a wani gida ba inacikin garin minna, ina bazai yu ba, dan Allah fa nace Nina... Au kindauka ma dawasa nake ko to bari kigani, vail d'in ta tadauka da hand bag, tabude 'kofa zainab ba yadda ta iya dan dole tafito tarakata,

Tana nan gunda suka barta, lokaci d'aya duk tayi wata iri da ita, ta'be baki Nina tayi, a ranta tace..... Aikin banza kenan shasha,
          Tom zainab kibarni anan ma sai munyi waya cewar Nina dake sake gyara Zaman vail d'in ta, to Nina kigaida mun mum, zataji insha'Allah, nan sukayi sallama ta tafi, cike da fargaba tashiga parlour, ganin still tana gunda suka barta ne yasa gabanta sake fad'uwa, da d'an sauri ta'karasa bedroom d'in ta ajiyar zuciya tasauke, taddanawa 'kofar key, kwanciya tayi akan gadonta tana tunani,.......

Shin a haka zamu tafi, gaskiyar Nina fa, bazai yu indinga jin tsoronta ba, lallai yazamar mun dole inkoyi kwatar kaina a hannunta, to amma ta Yaya?
   Tunanin datake kenan taji Kiran sallar magrib, mi'kewa tayi tashiga toilet domin d'aura alwala"...............

Rukayya ganin 'kwa'kwalwarta, na neman samun matsala ne yasa, ta tashi kamar zararriya tashiga wani bedroom d'in da batasan konawaye ba tayi sa'a komai akwai , danhaka tayarda trolley dinta a tsakar d'akin, huci tashiga yi kamar wata zakanya, akai akai kuma tana Kiran layin ma'aruf, baya shiga ranta ne yasake 'baci,

          Wata zuciyarta ce tace.... Kije ki ci uban yarinyar idan ki kaimata lahani dole yazo ai, take kuwa tadauki shawarar zuciyarta ta, tanazuwa afusace tamurda handle d'in bedroom d'in ta, taji shi a rufe, aikuwa cike da masifa tadinga dukan'kofar tana hadawa da ashariya, dan kutumar ubanki ki bud'e 'kofar nan, shegiya tsinanniya, ba'kar munafuka........ yau koni ko ke acikin gidannan,..... Haka taita mugayen lafazi, tamkar wacce kanta ya kwance lokaci d'aya kuma tana cigaba da dukan'kofar,

           Baiwar Allah zainab, kam lokacin tana azkar bayan magrib, taji tafara dukan 'kofa, hartagama tanajinta tana ta surfa mata zagi da iyayenta dake cikin'kasa, kuka kawai take tana ro' kon Allah yasassauta mata acikin wannan al'amari dan Rukayya kam tayi nisa...............
.......................................................







_Xinnee smart_ 😘😍😘💋

Continue Reading

You'll Also Like

35K 1K 46
ROMANTIC LOVE STORY,IS ALL ABOUT AN ORPHAN WHO SUFFERED ALOT FROM HER STEP MUM,BUT LATER HAVE A BETTER LIFE WITH THE HELP OF 3 PEOPLE,,JUST READ ND...
1.6K 106 14
Sanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.
2.6K 158 11
A fictional story from the track where RV is blamed by Monisha for molestation. What will happen when RV and his family will lose their everything? W...
140K 3.9K 27
✍︎ she wasn't the first priority, she was hurt and she was all alone. but the end made her to be his one and only, solely queen.