SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

120K 6.6K 88

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

BABI NA TARA

2.2K 124 0
By ZulayheartRano89

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

            *SANGARTA*

                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

     ''' Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah'''
  
                     *9*
Girgiza kai  ta yi tace

" Ayya Najeeb ai Ameesha bata soyayya, don bata iya wa da kayan takaicin da ke cikin soyayya."

Kasak'e ya yi yana kallonta, tare da mamakin furucin ta, in har hasashen da yake yi gaskiya ne, kenan Ameesha bata tab'a soyayya ba.

"Kayi hakuri Najeeb gaskiya ba zan iya amince maka ba, don ban son in jefa zuciya ta cikin halaka, shi yasa ko kadan bana ɓata wa kaina lokaci."

Tana gama faɗin haka ta yi waje.

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta tashi tafita, tabbas sai ya yi da gaske hak'an sa zai cimma ruwa, da wannan tunanin ya tashi jiki a sanyaye.

Ameesha na barin falon bak'in bedroom dinta ta shiga, hankalin ta ya tashi b'ata tab'a soyayya ba, haka kuma bata jin zata iya soyayya da wani, wayarta ta jawo ta dan nawa Meena kawarta kira.

Bayan sun gaisa ne Ameesha ke sanar mata da yadda sukayi da Najeeb din. Daga bangaren Meena ajiyar zuciya ta sauke ta ce

" Bai kamata kiyi saurin fada masa haka ba, kamata ya yi ki zauna kiyi dogon tunani akan maganar, musamman dai kin ga Najeeb ba wai mutumin banza ba ne."

" shi yasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'a yi? "

"  OK mu haɗu a school gobe. "

Daga haka sukayi sallama.

Bayan sunyi sallama ne, ta mike ta koma falo jin alamar shigowar Abbanta, ai ko shi ɗin ne yana zaune ga yayyenta suma a zaune kusa dashi, da sauri ta karasa tana fad'in
" oyo-yo Abbana welcome back."

Murmushin jin daɗi ya yi ya ce

" Thanks my daughter ya gida? "

"  Lafiya lau Abba, gaskiya nayi kewarka fa."

Ta karasa maganar cikin shagwaba.

" Zo zauna uwata, ayi min Afuwa nima ina can tunanin rashin ki kusa dani ya dameni."

Sai da ta zauna kusa da Abbanta, sannan ta gaida yayyenta, wanda suke zaune cikin jin daɗin ganin Abban nasu, a tare suka amsa cikin kulawa don suna matukar son Ameesha sosai, kasancewar ta ita ɗaya ce mace cikin su.

"Wai Abba waye naga kun tsaya da shi ɗazun da ka shigo? "

Jaheed ne ya yi tambayar.

" Najeeb ɗin ne kuma yau baka sani ba? "

Alhaji Taheer ya yi tambayar fuskar sa cike da mamaki.

Dan rufe baki Jaheed ya yi cikin dan mamaki ya ce
"  badai Najeeb din Alhaji Mansur ba?  Allah Abba ban gane shi ba, naga ya canza."

" Aiko shi ɗin ne, nima nayi mamakin ganin sa a gidan."

"yo Alhaji wajen Ameesha yake zuwa, Yau shi ne zuwansa na biyu. "

Ummi dake zuwa falon ta yi maganar. Ai Ameesha tana jin maganar Ummin ta kwasa a guje tayi stair, bata zama ko ina ba Sai bedroom ɗinta.

Da kallo suka rakata, Jaheed ya dan kada kai take ya fahimci in da maganar Ummi ta dosa, Kai kusan dukkan su sun fahimta, amma shi Jaheed tuni ya fahimci zuwan Najeeb din, don yasan ba abin da zai kawo shi wajen Ameesha sai soyayya.

Mikewa su ka yi gaba daya jin an soma kiraye kirayen sallar magriba.

Bayan an idar da sallar ne suka dawo falon, don cin abinci wannan al'adar su ce, da safe da dare tare ake cin abinci a dining. Suna gama cin abinci duk suka mike zasu tafi

"Kai Jaheed da Abdul ku tsaya, ku kuma kuna iya tafiya."

Alhaji Taheer ya yi maganar ba tare da ya ɗago ba, Ameesha ta mike zata wuce
"A'a uwata ke zauna, ai yau hira zamuyi da ke wacce muka daɗe ba muyi ba."

Zama tayi tare da jingina jikinta da kujera, lumshe ido tayi "ba don Abbanta bane babu abinda zai hana ta wuce wa, don so take ta kebe waje ɗaya, don ta yi dogon tunani akan maganar ta da Najeeb."

"Wai ku kuwa sai yaushe zaku girma? Zuwa wannan lokacin yaci a ce kuna da mata, kai fa Jaheed shekaran ka talatin (30)  kai Abdul kana da ashirin da takwas (28) shekarun ku kullum k'ara ja yake, me kuka nema kuka rasa? "

Shiru su ka yi suna sauraren mahaifin nasu, ci gaba da magana ya yi

" Duk kuna da aikin yin ku, kuna da karfin da zaku rike matan ku da ya'yan ku, to ku buɗe kunne kujini da kyau, na baku nan da sati biyu ku kawo min matan da zaku aura ko ya'yan waye ku tashi kuban waje."

Jaheed ya kuma sadda kansa k'asa ya ce

" Yi hakuri Abba wallahi dama tun satin da ya gabata, Abban Baderyeet yake ta ce min yana son ganin ka, to jira nayi zuwa da safe sai inyi maka bayani."

"Masha Allah kai amma naji daɗi da jin wannan furucin, insha Allah gobe zan tura su, Alhaji Isa da Alhaji Mansur don su tambayo."

"Kai fa? "

" Dan murmushi ya yi ya ce Abba nima mun dai dai ta, da Meena dama jira nake ka dawo sai in sanar maka."

Meena kawar Ameesha ita yake nufi.

To Alhamdulillah tunda hakane Allah ya sa Alhairi, duk gobe za'aje nema maku auren."

Farin ciki ne ya rufe Ummi da Ameesha, Ummi fatan Alhairi kawai takeyi a zuciyar ta, don sosai taji daɗin wannan maganar.

Da haka kowa ya wu ce, aka bar Ameesha da Abba da Ummi, wanda suke hira.

************************************
Bayan sati ɗaya komai ya dai dai ta, na maganar auren su Jaheed har an tsayar da ranar auren, wata biyu masu zuwa.

Kuma ya zuwa wannan lokacin, tuni an daɗe da sanya ranar auren Asmad da Aneesa, farin ciki wajen Aneesa ba'a magana, don wannan shi ne burinta ta mallaki Asmad a matsayin mijin aure, shi kuwa a nashi bangaren ba haushi ba haufi, wato kadaran kada han.

Ta fannin Ameesha kuwa, duk da dumbin shawarwarin da Aneesa ta bata, har yanzu bata yadda da Najeeb ɗin ba, sai ma garashi take kamar ball a fili, koda yaushe cikin zuwa gidan su yake, don Abban shi ya takura shi yana son jin gamsashshiyar amsa.

Yau ma kamar kullum, Najeeb din ne zaune a gaban Ameesha, yana ci gaba da jaddada mata irin son da yake mata.

" Zan yadda da buk'atar ka amma sai kayi min Alkawarin ba zaka ci amanata ba, ba zaka sa zuciya ta cikin damuwa ba, don kai kaɗai ta fara niyyar amincewa, sai dai ban baka wani babban waje ba, amma matukar kayi min Alkawari to ni kuma zan soma son da ban taɓa yiwa wani ba."

Kallon ta yayi gaban sa na dukan uku uku, da jin furucin ta lokaci ɗaya tunani kala uku ya yi cikin second goma, na farko ji ya yi zuciyar sa tana gargadin sa da karya cuci yar mutane, na biyu yana tunanin yadda zata kaya tsakanin sa da mahaifinsa, na uku kuwa shine take yaji zuciyar sa ta kamu da son Ameesha so na gaskiya ba irin wanda Abbansa ya turosa yi ba.

To kuma in haka ta faru tabbas akwai matsala babba.

Dago da kai ya yi ya dubi Ameesha dake ci gaba da matsa wayarta cikin sanyin murya ya ce

" ki yadda da ni princess, bada yaudara nazo gareki ba, da son gaskiya nazo wajen ki."

"Indai Alkawari ne nayi maki, ni Najeeb bazan ci amanar ki ba."

Gyada kai ta yi ta ce "Tom Allah ya sa haka, amma matukar dai ka yaudareni bazan taɓa yafe maka ba."

Wani farin ciki ya mamaye Najeeb don jin daɗin furucin Ameesha.

Soyayya suke gudanarwa, abin gwanin ban sha'awa hatta cikin gidan su Ameesha kowa yasan da maganar, Abba ya yi farin ciki sosai da jin wannan maganar, don yasan karfafa zumunci zaiyi da abokin nashi.

**********************************

Wata mahaukaciyar dariya Alhaji Mansur ya saki don jin Najeeb ɗin ya ce ai Ameesha ta amince, har ma Alhaji Taheer ɗin.

" Wayyo Taheer na kusa tarwatsa maka farin cikin ka, na kusa sanya maka takaici."

Girgiza kai Najeeb ya yi cikin takaici da dana sanin biye wa mahaifin nashi buɗe baki ya yi yace "Abba............"

_*Yar Mutan Rano*_

Continue Reading

You'll Also Like

22.2K 699 29
the story takes place in Nevermore where Wednesday meet a tribrid that is Hope's twin sister who was misplaced at birth. her name is Faith Mikaelson...
13.1K 1.2K 86
" දන්නවද අභී..! එයා හරියට වැස්සක් වගේ...!" " වැස්සක් !?...'' '' ඔව් වැස්සක්...එයාගෙ ආදරෙත් හරියට වැස්සක් වගේ...කාලයක් මාව ඒ වැස්සෙන් තෙම්මලා....එයා ය...
42.7K 995 6
Hiroki has recently discovered that the four women he once knew and loved, his girlfriend (Nao), sister (Kanoko), best friend (Ayumu), and mom (Kaede...
15.8K 1.6K 18
" ඇයි අයියෙ ඔයා කොයි වෙලෙත් මාව සුදු අරලිය මලකට සමාන කරන්නෙ.." මං අයියගෙ මූන දිහා බලන් අහනකොට එයා මගෙ ඇස් දෙක දිහා බැලුවා.. මගෙ අයියගෙ මූනෙ ඇඳිලා තිබ...