KE NAKE SO

By ummyasmeen

177K 12.3K 4.3K

#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza m... More

RAYUWA.
BA'KO
Haduwa da Rabuwa...
BAZATA
RIKITACCIYAR ALAKA
IKIRARI
MAFARKI
AN YANKA TA TASHI...
BAIKO KO WARWARA?
KARSHEN TUKATIKI...
Tafiya...
SAKO...
ABDUL-AALI...
DAN KANO1
LAIFIN WA?
RIKITACCEN SAKO
DAN KANO 2
KE NAKE SO

BANKWANA

7.3K 603 132
By ummyasmeen


Assalamu alaikum

I'd like to dedicate this chapter to my first readers from Al'amarin zuci, through Amaren Bana to Ke nake so

ummu

ayeesh_chuchu

mamanmus

@sadiyaumar

NajahIM

lisco_

@fatimaumar

And all of you my lovelies, you all are important. I feel the love. It's ironical, but words can't be enough to express my gratitude to you my peeps.

*********


Bayan sun kammala karyawa ne. Abdul-Aali ya-cewa Mai-jidda. "Anjima zan kai Hamamatu gidan Sister dinta da ta haihu, zan ajiye su Ramla gidan Abba, za ki je ne, ko ki na gida?"

Ta yi shiru tana tunanin, idan suka watse, gidan zai mata shiru, don haka ta-ce. "Ba damuwa zan shirya, sai ka bar mu gidan Abban".

Suna fita gidan yar Hamamatu, suka fara zuwa ma mai haihuwa, dukan su suka shiga har da Abdul-Aali yayi mata gaisuwa. Zulfa'a tana da fara'a, kasancewar ta kan hadu da Mai-jidda a sunan yaran kanwarta, ko wata hidima, ba ta gwada mata wani canji ba.

Suka gaisa kamar koyaushe, yayin da Hamamatu take ta jin haushin yarta, wai yaya za ta washe baki, ta yi ta yiwa kishiyarta dariya.

Da suka zo tafiya ne. Mai-jidda ta bude jakarta ta fito da ledan zani, ta ba ta. "Ga wannan ba yawa ayi goyo. Allah kuma ya raya cikin addinin musulunci."

"A'a haba Anty Hauwa, kuma sai ki shiga dawainiya haka? Ki bar shi kawai, don Allah."

"A'a kar mu yi haka don Allah, ki karba, ai na riga na yi niyya."

"To shi kenan. Allah ya amfana. Allah ya bar zumunci."

"Ameen-Ameen. Mu za mu wuce kar Dadin su Mimie ya yi ta jiran mu."

Nan ta rike hannun Mimie ta daga Ramla a hannu. Hamamatu ta bi-ta da kallo. Suna fita, ta hau yiwa Zulfa'a bala'i.

"Haba ke kin faye daukar abu da zafi, tana da kirki sosai, ki ga yadda take da yaranki fa."

"Duk kinibibi ne, bari na fada miki, ke kuma dole ki fadi haka, tunda har zani aka kawo miki."

"Akan ba ni da su ko meye? Ke dadina dake rashin son gaskiya."

Ba abinda yake damun Hamamatu, illa yanzu haka Mai-jidda za ta je ta kame a gaban motar Abdul-Aali suna tafiya, suna hirar soyayya. Tamkar ta cewa Zulfa'a ta fasa wunin, don gaba daya ta kasa daina tunanin Abdul-Aali da Mai-jidda.

Sai da yamma ya dauko Hamama, suka taho gidan Abba, nan suka samu su Ramla sun sha kyau, saboda Mai-jidda zama ta yi ta rangada masu kitso, ta aika aka sayo mata Ribbons ta jera masu a kai.

"Mami kin ga kitson mu. Anty Hauwa tayi mana, kuma ba zafi".

Ganin Abdul-Aali a wurin, ba ta son ta nuna haushinta ta-ce. "Lallai kun ji dadinku, sannu Anty Hauwa, kun ce mata thank you?"

Nan Mimie ta kama baki, cikin alamar tuna abu. "La na manta, thank you Anty Hauwa."

Abdul-Aali ko dadi ne fal! A ransa ganin an samu canji tsakanin jiya da yau.

Mama ma farin-ciki ne ya cika zuciyarta, saboda ganin komai ya daidaita, sannan Danta yana cikin farin ciki. Daga gani dai, hala Hauwa ta sassauto ne.

*******

Tana zaune a falonta da dare ne, ta ga wayar Abdul-Aali, don haka ta daga. "Ki sameni a falo." Ya fada a takaice. Mayafi ta daura kan kayan barcinta, sannan ta shiga falon nasa, ta samu yana kallon labaru, don haka a kasa ta zauna nesa kadan da kafafun sa.

"Gani".

Mika mata wani kit ya yi da jarida, ta duba ta ga kayan yankan farce ne, da gyara kafa.

Ta dube shi, don neman karin bayani. "Bude mana, ko sai na gwada miki? Farce na sun fito, so na ke yi ki dan gyara min."

Wani kallo tayi masa, wanda ita kanta ba ta san iya ma'anar sa ba. "Ni zan yanke maka farce? Na fada maka fa, kar ka yi tunanin ko zan zama wata (Ideal wife) gareka, ka jira wacce ta saba maka, ta yanke maka."

"Ke nace ki yanke, ko kina da matsala?"

Cikin sanyin jiki ta matsa kusa da jakar, ta shimfida jaridar, sannan ta mika masa hannu alamar ya ba ta hannunsa. Fuskarta a murtuke ta fara masa gyaran farcen yana kallonta yana murmushi, ga hannayenta da suka faye laushi, tamkar ba ta aikin komai. Yana kallo har ta gama yanke na hannu cikin natsuwa da kula take aikin.

Bai ankara ba, yana cikin kallonta ne ya ji zafi har cikin kwakwalwarsa, saboda yanke matsa babban yatsar kafa da ta yi cikin kuskure, nan da nan kuwa jini ya hau bulbula, da sauri ta mike ta dauko Tissue ta danne wurin, tana fadin "Wai, sorry don Allah ka yi hakuri."

"Ba wanin nan, dama ba ki so yankan ba, da gangan ki ka yi ko?"

Ta tsume nan da nan, ta bar bare-baren da take yi na ganin jini a kafarsa. "Da da gangan ne, ai da guntule yatsar ma zan yi, ai dama na ce maka ban iya ba."

"Yatsata za ki guntule?"

"Eh".

"Bismillah." Ya fada hade da mika mata dayan ma. "Bayan yanka kadan ma kin fi-ni rudewa da ganin jinin, shegen tsoron tsiya, a hakan ne za ki guntule yatsa?"

"Ka kawo mana ka gani, kuma na gama kenan, daga yau ka rinka yankan farcenka da kanka".

"Ai aiki ya sameki, don kuwa ni ba abinda na ke yi, hatta wanka yi min ake yi, idan za ki koya to".

"Sai ka ce wani yaro karami, sai na tsaya yi maka komai? Lallai ma ka na da aiki ja gabanka".

"Shi kenan, ashe za a bar ki a baya kuwa. Don kin ganni. Ni Dan gata ne, sai abin da na ke so, za ayi min, idan kuwa ba kya min, to ni ma za ki sha mamaki."

"Kamar na damu." Ta fada hade da juya idanu.

Ta mike za ta tafi ya-ce. "Yau a dakina za mu kwana."

Ji ta yi kamar ta karbi rezar ta gutsure yatsar da gaske, don ya soma ba ta haushi. "Abdul-Aali sai da safe."

Bakin gyalenta ya rike ya-ce. "Ke haka ki ke son mu rabu, gobe kuma Hamama ce a nan. Kin san jibi fa za mu koma, ko kin fi son na yi ta tunaninki, na kasa aiki?"

"Allah ya bada sa'a. Na fada maka jiya ma kuskure ne, kuma ya daina faruwa, sannan ai ba mu zauna mun yi magana da Mamin Mimie akan yawan kwanaki ba".

"Ke kuma haka kawai ki ke neman fushin Allah a kanki ko?"

Jin maganarsa, sai ta koma gefensa ta zauna. "To, ka yi hakuri, ba haka bane nufi na."

"To meye ne nufinki?"

"Kawai dai, kayi min bazata ne, shi ya sa. Amma ni ban ce maka dama ina so ba".

"Oh, sai kin so ne, za ki farantawa mijinki rai? Shi kenan tashi ki tafi."

Jikinta ya yi sanyi kuma bayan ya fadi haka, ya saki gyalenta cikin jin haushi. Ta bar falon ba tare da ta sake kallon inda yake ba.

Ya rasa me ya sa Jidda take masa wasa da hankali, jiya sai ya rantse ba ta da wanda take so irin sa, ganin yadda ta saki jikinta da shi, amma yau tun da safe ta wani canza, sai ka ce Hawainiya sarkin canjin launi.

Ya san duk kora kunya take yi, amma kuma hakan ba karamin bata masa rai ya yi ba, su yara kanana ne da za ta tsaya tana masa wasa? Ya so ya bi bayanta. Amma bacin rai, ya hana shi, sai dai ya mutu akan ya je, dole ta gane kuskurenta.

Ko da ta koma daki, banda juyi, ba abin da take yi ta kasa barci, haka nan ta ji rashin dadin abin da ta yiwa Abdul-Aali, ta san lallaba ta yake yi, amma kuma ita ba za ta iya ba. Sai dai ba abinda take ji a kunnenta, irin tambayar da yayi mata ko ta fi son fushin Allah a kanta?

Don haka ta mike ta kashe wutan dakinta, ta koma sashinsa, ta samu ya kashe wutan falon, don haka ta san yana cikin daki.

A hankali ta kwankwasa kofar dakin, ya taso yana tunanin ko waye? Bude kofarsa, sai ya ganta a tsaye kanta ba Dan-kwali, ta sako gashin ta, ta gefen wuyanta.

Sannan gyalen dazu yana yafe iya kafadunta, sabanin dazu da ta rufe kanta da shi, sai wani sansanyar kamshi da take yi. Amma ya daure ya maida kofar zai rufe.

Da sauri ta sa hannu ta tare, idanunta sun yi narai-narai! Ta-ce. "Ka yi hakuri, Abdul-Aali." A hankali ta sa hannu ta rike hannun sa. Ajiyar zuciya yayi, ya ja ta jikinsa ya turo kofar.

**********

Tana goge-gogen Side dinta ne. Hamamatu ta shigo, hakan ya sa ta mamaki, saboda tun zuwansu ba ta shigo Side din nata ba, sai yanzu. "Mamin Mimie? Ina kwana?"

"Lafiya kalau."

"Bismillah! Ki zauna mana".

A bakin hannun kujera ta zauna, tana karewa falon kallo kafin ta-ce. "Na ga har kin yanke iya kwanakin da ki ke so mu diba, ko tukuna ba ki gama diba ba?"

Kan Mai-jidda ya kulle, amma ta yi murmushi ta-ce "Kwanaki?"

"Eh mana, ko jiya ba ke ki ka yankewa sweety farce ba? Na ga dai cewa ya yi mu yi shawara akan kwanakin da ya dace mu yi."

"Gani na yi ya kirani, shi ya sa na je, saboda dacewar hakan, a zatona ke ki ka fada masa hakan yayi miki".

Hamama ta hadiye wani abu, wato namiji ma sai a bar shi, bayan ya-ce su yi shawara. Shi ne har da kiran Hauwa. Daman ya san meye a ransa kenan. "Da shi muka yi za mu yi shawara ko da ke?"

"Yanzu dai magana ta kare, ki yi hakuri, ke me ki ke ganin ya fi? Kwanaki nawa suka yi miki?"

"Tunda kin yi kwana biyu, shi kenan, da yamma sai na karba, kwana bibbiyu kenan."

"To shi kenan, hakan ya yi." Mai-jidda ta fada. Hamama na fita, ta bi-ta da kallo, tana murmushi. Abdul-Aali kenan. Sarkin hada wuri.

Ranar ita kadai ta wuni a gidan kasancewar Hamama ta kwashi yaran sun tafi gidansu. Hakan ya sa bayan ta gama abinci, ta shiga daki don rama barci.

Ranar da za su tafi ne. Ta ji wani iri, don da safe ya shigo ya sameta. "Jidda, ni ban ga amfanin zamanki ke kadai ba anan, ki shirya mu tafi kawai."

Tayi shiru kafin ta-ce. "Kai ba ka san ance wai gida biyu , maganin gobara ba? Ni na fi son zama nan kusa da Mama da su Umma, ka ga idan an kwana biyu, zan dubo Muhammad, amma idan na yi nisa fa?"

Kallonta yakeyi kaman yayi yaya da rashinta da zai yi a ganganshi "Muhammad ne dai damuwar ko? Ina ce sun kusa yin hutu?"

"Eh sun kusa."

"To shi kenan. Ki zauna cikin shirinki, yana hutu duka za mu koma can."

Za ta yi magana ya-ce. "Kar ki fara." Riketa ya yi a jikinsa, sannan ya-ce. "Ba na son gardama."

"Allah ya kai mu lafiya, shi kenan?"

"Yauwa, ko ke fa? Ameen. Jiya na je wurin su Umma, suna gaisheki".

Ta daga idanu ta dube shi cikin tuhuma, har yanzu bai sake rikon da yayi mata ba. "Shi ne ba ka fada min za ka je ba, mu tafi tare, na zauna gidan nan ni kadai, ba abin da na ke yi."

"Idan nace ki min rakiya, ki na yi ne? uhmm?"

"Kai ma ka san da zan je, ka fadi wurin zuwan mana ka gani."

Dariya yayi, ya sumbaci saman goshinta sannan ya-ce. "Zo mu tafi Breakfast. Hamama na jiran mu." Lokacin ne ya saketa daga jikinsa.

Mayafinta ta dauka, sannan ta bi bayansa zuwa bangaren sa. Anan suka sameta ta gama cika, saboda ta kusa minti ashirin tana jiran fitowarsu, daga bari ya yi mata magana su ci abinci, shi kenan.

Haka suka gama cin abincin, ba wata kwakkwarar hira. Sai yara ke ta shirmen su. Lokaci-lokaci Mai-jidda na hada ido da Abdul-Aali, amma sai ta kawar da kai. A karo na uku ne ya sakar mata da murmushi.


Daidai kuwa a kan idanun Hamama, ranta ya baci. Haka ta hakura da abincin da ta bata lokaci tana hadawa. Mai-jidda dai ta ji wani iri, da yaran suka tafi. Sai gidan yayi mata shiru sosai.

*************

Ranar Asabar kawai, sai ga Walida da mijinta sun zo Kano, suna shigowa ta kira Mai-jidda a waya. "Haba don Allah?"

"Kawai abin da za ayi, ku je gidan Abba zan yi waya. Kasim kanin Abdul-Aali sai ya kawo ku."

"To shi kenan."

Tana ajiye waya. Kasim ta nema ta fada masa, saboda Sulaiman ya tafi Kaduna. Nan ta hau shirya kayan tarbarsu, masu saukin yi, kamar su zobo mai dadi irin wanda take hadawa a Dutse, don ta san Walida da son zobonta, musamman take sawa ta tafi masu da shi wurin aiki.

Ta fito da sauran samosan da ta saya, ta soya masu, sannan ta dan kara da wani abin da ba a rasa ba, ta kammala komai. Dai ga su Walida, sai da ta sa mayafinta ta bude masu falon Abdul-Aali. Can ta yi masu masauki.

"Kai Uncle ka kyauta min yau din nan raina fari kal!"

"Ko? To lallai ya yi kyau, tun ba yau ba ta matsa min, ita dai tun tafiyarki ba ki je ba, tana son ganin ki".

"To mun gode kwarai. Yaya mutanen gidan, duk suna lafiya ko?"

"Lafiya kalau. Alhamdulillahi."

Nan ya tafi ya bar Walida, bayan sun ci abubuwan da Mai-jidda ta tanadar masu. Mai-jidda ta-ce. "Ba ki san yadda ki ka taimaken ba yau, da ki ka zo, gidan nan shiru ba kowa".

"Haba ni nace ko saboda hutu ma hala na samu Injiniya?".

"Ran Talata suka koma, kin san yanayin aikin nasu da matsi."

"Ayya! Lallai ke kadai a cikin gidan nan? To wai me ya sa ba ki tafi ba ke?"

Mai-jidda ta yatsina fuska. "Ban gane ba, ki na bata fuska, kar ki ce min har yanzu ki na wahalar da Abdul-Aali bawan Allah?"

"Kin daina tayani tsanarsa ma kenan?"

"A yanzu kam kuma ai za mu wuce gona da iri, idan mun tsani Mai-gida guda, maganar gaskiya dai Mai-jidda."

"Don Allah ki bar maganar Abdul-Aali, damuwarsa sai shi, nan wai so yake yi idan na dauko Muhammad mu koma Portharcourt, ni da zai bar mu, mu yi zaman mu anan, ba komai na ke yi ba.

Zan rinka kai shi makaranta da kaina, na dauko shi, tunda anan yake barin motarsa. Can yana amfani da ta Mamin Mimie ne."

Walida ta zare idanu ta-ce. "Shi kuma mijin sai ki yi yaya da shi. Ko ba shi a lissafinki ma kwata-kwata?"

"Ke wa yake ta shi, ki na ga zuwan shin nan ma, ya takura min ga matarsa da har yanzu take daukar abubuwa da zafi, don ma an dan samu sauki kadan.

Dan yayi mana nasiha zuwan su. Gaba daya na fi son na yi zamana anan hankali na a kwance, wai tsumma a randa. Ya fiye min."

"Oh daman ya auro ki, don ya sa miki idanu ne?"

"Ni na rasa ma me ya sa mutane suke wani zafafa wannan abin, aure dai na yi shi, ba shi kenan ba".

"Ai ba daga auren bane sauke hakkin auren fa? Bare ke da ki ke da abokiyar zama, dole sai kin dage kan ki dasa wuri a zuciyar mijinki, domin kuwa kin riga kin samu suna rayuwarsu.

Zai yi wuya kan ki saba da yadda ake masa, ki bar ganin wai don yana sonki. Wallahi a ja ajin a hankali, kada ga-rin neman kiba, a samo rama ".

Jidda murmushi tayi. "Ni na fada masa, kar ma ya tsammanci komai daga gareni, har ya fara cewa shi ba haka matarsa take masa ba".

"You see! Which means Yana so ki gyara, kuma idan ki ka bari ku ka yi nisa a haka, ba ki dau gyara ba, to Wallahi kan ki gyarota, sai kin yi da gaske."

Mai-jidda ta jinjina kai, yanzu kam yaya ta iya ta riga ta aure shi. "Haka ne kam."

"Yaya su Yaya Maryam?"

"Suna nan lafiya, jiya aka kawo min A'isha da Nabil ma wuni". Nan suka sha hirar su, sai da dare Mai-gidanta ya zo daukarta, za su wuce gidan yarsa.

********

Tana zaune kamar kullum. Yau ma ya kirata a waya, ta daga, gaba daya sai ta ji ta tsargu, musamman yadda suka tattauna da Walida, ta ba ta shawarwari, daga yanayin amsar wayar tata yau. Abdul-Aali ya ji bambanci, don da tamkar wuta haka take Allah-Allah take ya gama magana, ta ajiye. Amma yau cikin kwanciyar hankali take masa magana.

"Jidda, yau na ji wani nishadi ki ke ciki me ya faru?"

"Wa, ni din ce?"

"Eh mana, tunda muka fara magana, ba ki nemi fada ba, dole da wani abin."

"Don ni ce Sarkin masifa, sai na yi ta fada koyaushe, abin naka ma na ga har da sharri ciki".

Dariya ya yi sannan ya-ce. "Mai hali dai, baya barin halinsa".

"Hmm! Kai dai ka fada kai tsaye, ka na tunzurani, sai kuma ka ce ni ce marar hakurin".

"To na ji ki yi hakuri, ban labarin me ya sa ki farin-ciki yau?"

"Walida ta zo min, muka wuni, sai dazu suka tafi ita da Mai-gidanta".

"Allah Sarki. Yaya take? Wai na ji dadin zuwan tan nan, ko ba komai na san ita 'yar gari ce, tunda ta fara sa matata yi min fara'a."

"Da ba ka ganin fara'ata ne?"

"Wai wani kallon idan an yi min. Tamkar zai kifar da Kano gaba daya, ke dai ba a cewa komai. An cuci na dawa".

Dariya ta yi a karo kadan da za ta iya tunawa, tun fara nemanta da Abdul-Aali ta-ce. "Dadin Mimie kenan, na ji tunda haka ka daukeni. Daman ina son na ma maganar zuwa na Dutse Next week.

Idan na je, sai na jira hutun Muhammad, tunda nan zaman haka ya min shiru da yawa."

"To ba komai, zan yi Making arrangements Insha-Allah. Kin ga amfanin tahowarki ko? Da yanzu ki na da abokin hira."

Murmushi ta yi sannan ta-ce. "Bayan zan je na ga Ummata, ina ruwana da kai."

"Haka ki ka ce ko? Ba zan ce miki komai ba."

"Ka gayar min da Mimie da Ramla".

"Banda Mamin su?"

"Ka iya hada fada, ba ka jira na karasa ba, za kayi min fassara, ka gaisheta ita ma. Dan hadin rigima".

Yana dariya. "Ga ta nan ma, ko za ku gaisa?"

Gaban Mai-jidda ya fadi, daman Hamama tana wurin yake waya da ita? "Abdul-Aali dama tana wurin ka ke magana?"

"A'a yanzu ta shigo."

"Sai da safe to."

"Tsaya. Jidda kar ki kashe wayar. Yaya muna hira za ki kashe min waya?"

"Yaya zan yi magana da kai, bayan tana nan?" Ta fada hade da rage murya, tamkar tana wurin ita ma.

"Zolayarki na ke yi, kin faye kishi. Menene, don ta ji hirar mu?"

"Wannan sirrin mu ne, akan me ya sa za ta ji, ni na ji nata ne? Sannan ni ba na kishin ka. Maganar abin da ya dace ne da wanda bai dace ba".

"Jidda Sarkin fada, to Allah ya ba mu alkhairi, bari na shiga, kafin na yi wani laifin."

Mai-jidda ta kashe wayar cikin jin haushi, har ma Allah-Allah wato yake yi ya gama waya da ita, ai daman ba ta iya magana ba, matarsa ta fita iya komai.

****

Hmmm our Jiddo 😂

What do you think?😜

Continue Reading

You'll Also Like

177K 12.3K 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za...
1.2M 91.5K 126
credit to original author Shui Qian Cheng. This story belongs to Rosy0513 . I am just a translator. This cover photo is not belong to me.
1.3M 45.5K 61
Myanmar × BL Uni/Zaw [ 2 ] Warning..... Start Date: 29.9.2023 End Date: 20.11.2023 Photo Crd
355K 27.7K 56
Kaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar...