TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Last Free Chapter

Chapter 18

74 3 0
By KhadeejaCandy

Ni dai tsoro ya kamani zuciyata na raya min ko dai cewa aka yi a samo mai irin soffofina. Sam zuciyata bata natsu da wannan ba. Saboda haka na yi amfani da Hana na saka ta ari wayar Ya Nabil da sunan wata yi ma kawarta flashing ta kawo min.

“Noor Allah yasa ba wani abun zaki yi ba”

Na karbi wayar ina dan turo baki.

“Ni me zan yi ba Hafix ne yace na ari wayar na kira shi ba, kuma kin san idan ni ce ba zai bani ba”

“To kina da numbershi a kai ne”

“Ina da shi a littafi dai”

“Kin san halin Yaya dai dan ana bikinki ba zai hana yayi miki dukan tsiya ba, kuma dan Allah karki kira Zafeer”

Na mata banza na tashi na dauko littafin na zauna a gafe daya kamar ina saka number alhalin number Kareem dake cikin wayar Yaya nake dauka. Sai da na gama na mika mata wayar

“Gashi na ma fasa kiran”

Ta karba ta duba sashen kiran ta ga ban kira ba ta sake miko min.

“Ni ban hana ko kira ba amman karki kira Zafeer da wayar Yaya kin san abu mai sauki ya hada mu yayi mana duka, kuma kowa ya ji ya san baki yi daidai ba”

“Ni fa ba Zafeer zan kira ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi magana da shi Wallahi ba shi zan kira ba, kuma ki bar shi zan ari wayar Gwaggo na kira da ita”

Duk yadda ta so na karbi wayar sai na ki saboda sanin halin Yaya da na yi kamar yadda ta fada. Sai da ta fita azuwan mayar masa da wayar sannan na fito na tsaya daga jikin kofa na ari wayar Anty Larai domin ita ce mai lafiya a cikin yan'uwan mahaifina. Har ta ba ni na juya sai kuma ta kira na juyo bata ce min komai ba sai da na matsa kusa da ita.

“Noor Allah yasa dai ba tsohon saurayinki zaki kira ba?”

“Wallahi ba shi zan kira ba Anty Larai ai Baba yace be yafe min ba idan na sake magana da shi”

“Toh, na san ai kina da hankali ba kamar yadda suke fada ba tafi ciki ki yi wayar”

Na shiga dakin na nufi littafin da na rubuta number Kareem jiki na kwashi number na saka a wayar Anty Larai sannan na fito daga dakin na faki idon mutane na shige bandaki na rufe sannan na aika masa da kira.

KAREEM POV.

Jikin Momy ne babu dadi kwana biyu, ciwon da take yawan fadar rayuwarta yake nema ya sake sallamo mata sai dai wannan zuwan be tsanannta kamar yadda yake tsanani idan aka bude file dinta ba. Tun daga ranar da take jin fever din yana zagoyo mata Yusura take ta zirga-zirga na zuwa dubata, idan ta gama abun da take Kareem zai wuce da ita ya sauke ta gidan Momy sai dare zai dauko ta. Kasancewar yau Jumma'a babu makarantar Allo da Yamma washe gari kuma Weekend ne babu boko sai ya kwasa har da yaransa suka tafi duba Momy, ba sabon abu ne ba a gurin yaran kusan ko wane yana kai su su wuni sai dare ya dawo da su domin Momy mace ce mai son yara kuma gidansa ma yana cike da yara a duk ranaku hutu na yayan da ta raina ta aurar ko na Abokiyar zamanta ko kuma na yan'uwana.

Kamar kullum yau ma sun tarar da jikokin dangi da kuma na kanwar Kareem dake aure a garin. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma yaransa ba domin suna fama da kadaici a gidansu da babu kowa sai kayan kallo. Yusura ta shiga dakin Momy da lullubinta da far'a tana yi mata ya jiki. Kareem ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana sauraren yadda take amsawa Yusura tana shi mata albarka.
Yusura ta kalli Mijinta fuska a sake kamar ba ita ba, ta ce.

“Abban Tine ba zaka matsa Momy ta koma asibitin nan ba? Yau kwana biyu jiki ya ki dadi fa”

“Akwai wasu magani da muka dora ta akai, kin san ciwon ya kan taso wani lokacin kwana biyu sai ya tafi, to daga yau zuwa gobe dai idan ba a samu sauyi ba dole asibiti zamu koma”

Ya fada ba tare da ya kalleta ba. Momy ta tashi zaune tana mika hannu ta dauko plate din zogalen da Khadija ta gyara mata.

“Ko zan koma asibiti ba ta garin nan zan zauna, ba zan sake fita wajen nan ba, na gaji da yawo nan na gaji da shan maganin nan, ko mutuwa ce dai kara na mutu cikin iyalina”

Zancen mutu ya daga hankalin Yusura sosai a take idanuwanta da fuskarta suka sauya.

“Momy kullum baki da magana sai ta mutuwa, mu kike karyawa guiwa musamman da ba ni da gata sai ke a duniyar nan, cuta ai ba mutuwa ba ce”

“Masu lafiyar ma tafiya suke balle kuma mu, kuma idan ka ga ciwo yaki ci ya ki cinye ko yana tafiya yana dawowa rayuwa yake nema, kuma karki sake fadin baki da gata a duniyar nan kina da gatan da ya wuce na mijinki? Ko bana raye Kareem ba sai bari ki yi kuka ba ina da wannan tabbacin”

Yusura ta daga ta kalleshi shi ma ya kalleta kamin ta yi saurin kawar da kanta.

“Haka ne, Allah ya ba ni ikon cigaba da yi masa biyayya”

“Ameen Allah ya miki albarka”

Kareem ya sauke ajiyar zuciya sannan shi ma ya amsa da Ameen a addu'ar da Momy ta yi musu. Sannan ya kai hannunsa fuskar Momy  yana fadin.

“Ba za ki tafi yanzu ba, sai nan da shekaru dari da hansin Momy na farincikina”

Sanin hancinta zai taba ya saka ta buge hannun

“Wai Kareem ka mayar da ni abokiyar wasar ka, gaba daya ka mayar da ni wata kakarka”

“Toh ya za'ayi babu kakar Momy ke ce makwafinsu, idan ban yi wasa da ke ba da waye zan yi a gurinki kadai nake samun farinciki”

Yusura ta kalleshi tana Fake dariya kamar yadda ta saba idan suka shiga mutane musamman ace gidan Momy ne.

“Abban Tine ka ji tsoron Allah, idan kana fadin haka ai Hajiya sai ta dauka ko wahalar da kai ba ne bana baka kulawa”

Kareem ya kalleta irin kallon da su kadai suka san manufarsa and then he smile.

“Duk farin da zaki ba ni ai be kai wanda Mahaifiya zata bawa danta ba”

Momy ta aje plate din zogalen da spoon biyu kawai ta yi ta kama kunnen Kareem ta ja da karfi.

“Kai ne babba amman kullum idan ka gan ni sai ka maida kanka wani karamin yaro, ka maida ni kakarka Shiyasa Hajiya Na'eema take cewa ita kullum ganin take kamar ba ni na haife ka ba, gaba daya ka maida ni abokiyar wasar ka sai idan bana kusa”

Yusura ta yi murmushi.

“Wannan kuma Momy wani abu ne da kuka saba yi tun kurciya, ko dai ko da na bude ido a gidan nan na yi wayo na san baki da abokin shawara abokin wasa kamar Kareem, Kareem kuma ba shi da abokiyar wasa irinki, yadda kuke mu'alama babu wanda zai zaci ke da shi uwa da ďa ne, kum fi kama da Yaya da kanwa ko Kaka da jikanta, kin fi shakuwa da Kareem fiye da sauran Yayanki, shi ma ya fi shakuwa da ke fiye da Daddy”

Momy ta saki kunnensa tana murmushi.

“Ni kaina na kan yi mamaki yadda kunyar nan ma ta uwa da da Allah be dora min ba tsakanina da Kareem tun ana gulma har an gaji an saka mana ido, kuma kin ga yadda nake wasa da Kareem bana iya sake jiki na yi da Aryam haka shi ma da yake na biyu bana fari ba, wata kila hakan yana da nasaba da yadda yake da tsakanin tausayina da so na tun yana karami”

Kareem ya mike tsaye yana murmushi.

“Haka Barrister Hafiz yake ce min wani lokacin, wai Momy ko dai tsinto ka ta yi, ki ji dan iska...”

Duk suka yi dariya har Yusura.

“Allah ya tsare a dawo lafiya”

Daf da zai fice Yusura ta yi masa addu'ar da bata saba yi masa ba idan suna gida, juyowa yayi ya kalleta ya san tana yin duk abun da take ne saboda suna a gaban Momy ne.

“Ameen”

Ya juya ya fice. Be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i exact time din da ya zaba zuwa daukar Yusura. Babu fadan da be yi ba a lokacin da shiga falon ya samu Aryam da Khadija ga Yusura suna kallon Momy na cin gassashiyar kaza.

“Miye amfanin zamanku a nan toh? Kun san matsalar da take ciki ba, shiyasa ciwon ko ya tafi yake dawowa”

“Doctor kamar baka san halin Momy ba, karamin abu ne ta fara fada idan muka hana ta cin abun da yake so”

Cewar Aryam, Kareem ya tashi daga inda yake zaune ya karasa ya dauke plate din ya koma ya zauna. 

“Wallahi ku bar ni na ci dadi na tun ina da rayuwa, kar sai na tafi ku yi ta nadama, musamman kai Kareem kana bakinciki ka ga ina cin nama ko wani abun dadi”

Kareem yayi dariya ya tashi ya shiga kitchen ya wanke hannunsa ya fito ya dauki naman ya fara ci, taunawa yake a hankali zuciyarsa na wani gurin hana tuna masa da wani abun da ya wanzar da murmushi da nishadi a fuskarsa.

“Momy halinku yayi kama da Noor, da ace ban san iyeyenta ba sai na ce ke kika haife ta, yarinyar nan Allah yayi mata rigima”

“Wace Noor?”

Momy ta tambaya yana murmushi. Sai ya kalleni Momy kamar dai ya manta da Momy ce kadai a falon ba. Sai dai hakan kuma ba zai hana shi karasa mata labarin da shaukin Zuciya ya debe shi ya fara furtawa ba.

“Yarinyar da Hafix zai aura yanzu...”

“Au Noor ne sunanta?”

“Eh... Noor”

Kusan sautin muryarsa da sautin shigowar kira a wayarsa a tare suka fita. Yarsa Tine ta zo da sauri ta ciro masa wayar daga aljihunsa ya amsa kiran ba tare da ya saka ta ba kuma ta saka hands-free saboda yayi masa sauki ganin ya bata hannayensa da maikon ferfesun kazar Momy da ya karbe. Ta matsa masa da wayar kusa da fuskarsa yana kallon bakuwar number ya furta.

“Hello”

“Kareem... Noor ce....”

Ta fashe masa da kuka, sai ya dago da sauri ya kalli Momy dake kallonsa ya kalli Aryam ya kalli Khadija ya Yusura ce ta karshe da ya kai dubansa a gareta kamar wani marar gaskiya gabansa sai bugawa yake da karfi.

“Kareem ni dai Wallahi bana son Hafiz din nan ko kadan ni dai ban taba jin ina son shi ba...”

Yayi saurin aje naman dake hannunsa ya taba wayar da maikom ya cire hands-free din ya mike tsaye ya fice daga falon da sauri kamar zai hada da gudu. Harabar gidan ya fita sai ga ya juya ko'ina ya ga babu mai ganinsa sannan ya kara wayar a kunnensa.

“Noor me yasa kika kirani? Ina kika samu Number? Wayar waye?”

Ta yi shiru.

“Wane zan fara amsawa?”

Ya juya ya kalli kofar falon Momy dake bude sannan ya juyo ya kalli gate din ya sauke ajiyar zuciya.

“Me kike yi ma kuka?”

Ta sake fashewa da kukan.

“Wallahi ni dai Allah ya gani bana son Hafiz din nan, kuma waya sani ko wani manufa yake da ita akaina ma? Duk kaine sila kuma”

“Me ya faru me Hafiz din yayi?”

“Matarshi ta yi min kirki da yawa ni abun ya ba ni tsoro shiyasa na kira na tambaya tsakani da Allah Hafiz mutumen kirki ne?”

Ya kai hannunsa ya rike goshinsa.

“Noor idan Hafiz ba mutumen kirki ba ne, ai ba zai aure ki ba, ya fi ni zama mutumen kirki, matarsa kuma halinta ne ni ma tana kyautata idan na je gidan”

“Na ji tsoro waya sani ko cewa aka a samo wata yarinya mai wadda ta rabu da saurayinta marar jiki fara mai saurin kuka ayi wani tsafin da ita? Taya za'ace mace bata kishin mijinta? Sai idan hada kai suka yi waya sani ko kudin da yake ta kashewa ni aka siye”

Murmushi yayi ya lumshe ido.

“Babu wani hadin kai, Wallahi Hafiz mutunen Kirki ne mai nagarta ba shi da matsala, wayar waye wannan?”

“Ta Gwaggo na ce”

“Ina kika samu number na?”

“Na sata a wayar Yaya Nabil”

Ya bude idonsa ya daure fuska kamar ance masa tana gabansa.

“Okay daga yau sai yau karki sake kira number na, karki sake tambaya wani abu game d Hafiz ko wani dabam duk abun da kike son sani ki bincike shi, gargadi ne wannan na karshe, kuma zan fadawa Nabik kin kira ni shi ma kuma zan gargade shi”

“Ai dole na kiraka kai ne ka yi ruwa ka yi tsaki ka kawo min abokinka ka raba ni da Zafeer, kuma yanzu kace na daina damuwa dole ne mu yi damuwa tare”

Ya yanke kiran ya saka number a blacklist.

“Da gaske fa yarinyar nan bata da hankali...!!!”

Yana rufe baki wani kiran ya shigo da wata number dabam ba wacan ba. Mamaki ya kara kama shi har zai yi rejecting sai kuma ya amsa da zimmar yi mata fada.

“Noor What?”

“Noor....”

Safeena ta furta sunan daga dayan bangaren sannan ta cigaba da magana da murya mai ban tausayi da lafazi mai karya zuciya.

“Yarinyar nan ta yi nasarar shiga tsakanina da kai Kareem, ina ji ina gani ka juya min baya hankalinka ya koma gurin wata karamar yarinya, ka mata soyayya da ke tsakaninmu, fada min ba zaka cutar da ni ba ashe karya ne? Cewa auren dole aka maka ma karya ne, domin gashi yanzu zuciyarka ta bude har ka fara son ta, ni kuma ka raya ni da soyayyarka irin rayuwar da yau zan iya aikata komai saboda kai, ka saba min da rabar jikinka, na saba da mu'amala da kai ina gamsuwa fiye da mijina, rashinka ya saka na auri Abdull amman son ka be bar ni na ga laifinka ba, kaunarka bata bari na samu salama ba har sai da na rabeka, yanzu kuma ka juya min baya a karo na biyu, tsawon wata bakwai ban samu kebancewa da kai ba Kareem gaba daya ka sauya min, baka daga kirana baka maida amsar sakona, idan ina son ganinka sai dai na kama hotonka ko kuma na shigo motata na zo na faka a restaurant dinka ina shiga ko fitarka, shin baka tunanin ka azabtar da Ni? Kana ganin hakkina ba zai bibiye ka ba? You don't care how bad it hurts, kanka kawai ka sani Kareem? Ka yi hakuri mana son ka ba zai bari na yi rayuwa mai tsawo a duniya ba zan tafi sai ka so wata sai ka auri wata amman ina raye? Abdull gangar jikina kawai yake aure amman ruhina yana tare da kai.. Kareem ina zaka kai hakkina? You broke me first...”

Gaba daya sai jikinsa ya mutu iska ya busar daga bakinsa zuwa sarari.

“Noor... Sorry Safeena abun ne yayi yawa, kina da yaya ni ma ina da su, kina da miji amman mun biyewa shedan muna jefa kanmu a halaka, tun da Momy ta kawo ni a duniya ban tana aikata zina ba, kawai na biye miki ne saboda na faranta miki rai, na san na cutar da ke da farko amman ba kudirina kenan ba, kaddara ce ta zo mana a haka kuma ba zan iya cewa Momy aa ba, kuma da ace na san tun farko Momy ba zata yarda na aure ki ba ba zan zurfafa a soyayyarki ba, balle har mu wahala da yanzu ba mu kawo a wannan matsayin ba, da za ki fara tunanin haihuwa da ni alhalin kina da aure...”

“Shi ne kawai matsalar? Ba zan sake yi ba, i need to see you now i miss you so much, zan zo gidanka yanzu”

Yayi saurin tariyar numfashinta.

“No karki fara ba mu taba haka dake ba, and ba mu gida ina gurin Momy”

“Zan zo gurin Momy din ko kuma ka zo k same ni a inda muka saba haduwa, ba zan iya bachi ba a yau sai na ganka Kareem...”

“Zan yi tunanin”

“Zan zo yanzu Wallahi ba zan bari wata macen ta karbe min kai ba...”

Ta yanke kiran, ya duba wayar ya sake kiran layi bata daga ba ya sake kira bata daga ba. Juyawa yayi ya koma cikin falon, be kalli kowa ya wuce kitchen ya wanke hannunsa ya zari tissue ya goge wayarsa ya goge hannunsa sannan ya fito, ba tare da ya zauna ba ya kalli Yusura ya ce.

“Tashi mu tafi gida”

“Lafiya?”

Ta bukaci sani. Ya daga mata kafadunsa.

“Lafiya mana, by this time muke tafiya gida i think?”

“Noor din ce ta kira?”

Momy ta tambaya, sai ya kalleta.

“Eh tsabani suka samu da Hafiz, ina son na sauke Yusura gida sai na je na yi magana da shi”

“Ya kamata kam, ana shirin daura aure gobe ne ko jibi kuma ace an fara samun tsabani, ai ba dadi”

“Allah ya kara sauki Momy sai na shigo gobe da safe”

Yana fada yana aikawa Safeena sakon cewar zai zo ya same ta a inda suka saba haduwa. Shi ya fara fitowa ya shiga motarsa yayi mata key sannan Yusura ta karaso yaranta na yi mata sai da safe ya shiga motar yaja yana daga musu hannu. Tun da suka shiga motar bata ce masa uffan ba shi ma kuma be kalli gafen da take zaune ba har suka isa gidan. A haraba ya faka ta bude ta fita yayi reverse ya sake ficewa daga gidan.
  Ya hau titi da zai kai shi guest house dinsa bangaren da ya fi kyau na zuciyarsa na nuna masa illar hakan yana sanyaya masa jiki. Sashen da ya fi muni na nuna masa halin da Safeena zata shiga idan be tafi ba, domin ta siye kwarin guiwarsa da kalamanta na dazun. Ya kasa zaba tsakanin daidai ta akasin haka shedan ya shiga ciki har dayan bangaren ya rinjaye dan'uwa ya faka a harabar gidan bayan mai gadi ya bude masa gate. Motarta ya fara kallo ya sauke ajiyar zuciya kana ya bude tasa motar ya fito ya rufe cikin rashin kuzari ya doshi kofar. Kamar an masa dole haka ya kai hannu ya murda kofar ya bude ya shiga, da wani irin fitinannen kamshi ta tarbe shi wani kalar sexy perfume ne mai daga hankalin namijin da ya amsa sunan Namiji. Kofin ruwan dake hannunta ta aje ta mike tsaye ta nufo inda yake cike da zumudi jikinta har rawa yake idanuwanta suna auna marmarin Kareem da ta yi. Kamin ta karasa ya zuba hannanyensa duka biyu aljihu a kokarinsa na hana kansa taba abun da ba halalinsa ba. Bata tsaya komai ba ta rumgume shi, daman ya san ba zai iya hana ta aikata hakan ba amman zai iya hana kansa taba jikin matar da ba tasa ba.

“Na yi marmarinka...”

Ta sumbance bayan ta dago daga jikinsa sannan ya sake rumgume shi wuyanta a kafarsa, har sai da ya runtse ido saboda fitinar da turarenta yake kaiwa hancinsa, ta san weakness dinsa turare da Physical touch, hakan ya saka ta sumbantar wuyansa har sai da tsigar jikinsa ta tashi. A karo na biyu da ta dago daga jikinsa sai ta zuba masa ido har sai da ya bude nasa idon ya kalleta. Sai ta cire dankwalin dake kanta kananan kitson dake kanta suka bayyana, numfashi ya sauke a hankali ya hade yawu slowly,  yana marmarin abun da ya kwashe wata 8 be hada numfashi da Yusura da nufin shi ba. Bakinta ta kai saitin sansa ta san ba zai hana ta ba kuma ba zai iya gujewa haka ba, in less than second he lost control again. Hannayensa ya cire daga aljihun ya rumgumeta ya fara mayar mata da martani tun suna tsaye har tsayin ya gagara suka zauna daga bisani suka canja musalli daga Sitting room to Bedroom...

NOOR POV.

Ban kwanta da nufin farkawa ba, fata na yi idan na kwanta kamin safiya Allah ya karbi rayuwa. Sanin yau ce ranar daurin aurena sai nake ji kamar ranar mutuwa zata fi min farinciki fiye da wannan ranar da za'a daure da igiyyoyin aure. Misalin karfe bakwai na safe Anty Larai ta kawo min wani kaza mai tsananin daci wai na cinye ni kadai kuma kar na rage ko kadan. Tana fita na na saka yara suka debo min ruwa a bota na na nade kazar a dankwali na shiga bandaki na jefa a shadda sannan na dawo dakin na zauna kamar na ci. Ba a jima ba aka sake zuwa da mota aka dauke ni zuwa gidan wata mai lallen. Ban dawo ba sai Azahar bata min da yawa ba amman yayi matukar kyau domin kwarariya ce mai yi ma mare kunshi.
A lokacin da na dawo gidan na tarar da yan'uwan mahaifiyata suka fara shigowa sai kewarta ta kama ni, na ji ina ma ace tana kusa da ni wata kila zan ji sanyi fiye da kuncin da nake ji a yanzu, a jikin Mama Shafa na kwanta kaina na ciwo sosai kamar zai rabe gida biyu, hakan kuma ba zai rasa nabasa da rashin samun bachi da kuma tunanin da ke kokarin fi karfin kwakwalwata. Ban damu da sanin yaushe daurin auren ba abun da kawai na sani shi ne yau za a daura auren ko ma aka daura. Domin ban dade da shigowa ba ina daga kwancen a cinyar Mama Shafa na hango shigowar Yaya da Baba da kuma wasu daga cikin iyayena maza cikin shiga ta manya kaya sai gabana ya fadi, kuka ya rufe ni na kasa rike kaina ina ta kuka sosai jikina ya fara rawa numfashi yana fita da karfi. Wai yau da wani aka daura aurena ba da Zafeer ba Wallahi ban taba tsammanin haka ba. Yan'uwan Mama suka yi ta rarrashina suna kwantar min da hankali har suka samu na yi shiru sai dai na ci kuka kuma kuka ya ci ni har idanuwa sun sauya kala.

Har aka ci aka cinye ni dai bana wani kwarran motsi kuma bana da walwala balle sakewa ga wani irin tsoro da fargaba da ya rufe ni. Ba yi wani wuni da na ga saurin karewarta irin ranar yau Assabar, kan kace kwabo har hudu ya fara shigowa ana maganar a tafi da ni na yi wanka na shirya kamin masu daukar amarya su ta iso. Wani gidan na makota aka tafi da ni, amman na kasa wanka haka na zauna a bandakin ina ta rusar kuka har aka gaji da jira aka shigo aka fita da ni. Haka na sake saka wasu tufafin ba tare da na yi wanka ba domin bana iya komai babu kuzari a tare ba. Na samu kaina cikin wani irin rashin hankali da bakinciki na rabuwa da wanda nake so da kuma auren wanda bana so! Ashe haka abun yake ashe haka ake ji, wata sabuwar rayuwa zan shiga wani matsayi zan taka amman ba da wanda nake mafarki ba.
  Wani ya zo ya mana shigar rago ya shafe tarihin da muka so kafawa,  ya rusa gina da muka fara, ya dauki ajiyar da ba ta shi ba.

Bakinciki be kara rufe ni ba, sai da Baba ya tsaya kai da fata akan cewar ba za tafi dani gurin Mama da sunan ta yi min huduwar aure ba, idan ba zata tako ta zo ba to be yarda akai ni, duk yadda dangin mahaifiyata da wasu daga danginsa suka so ya bari na tafi hakan ya ci tura, domin Baba murdadden mutum ne idan y tsaya kan abu baya sauya. Ina ji ina gani aka hana ni ganin uwata har yan'uwan Mama suka fusata suka yi fada da Baba kacha kacha babu dadi. Bayan sun tafi na koma jikin Hana ta rumgume ni ita kuka ni kuka. Yaya ya shigo dakin ya mika min wayar

“Ga Mama zata yi magana da ke”

Na karbi wayar na kara a kunne na saka hannu biyu na dafeta a kunnena na kwanta a kasa ina jin kamar ina kwance a jikinta ne...

“Mama... Mamma... Mma... Mmama... Ma”

Na fada cikin wani irin kuka mai sarke numfashi.

“Noor ki yi hakuri haka Allah ya kaddara, kuma ki yi biyayya ga mijinki ni na yafe miki duk abun da kika min, Allah ya miki albarka... Ki roki kowa yafiya haka ake idan za'ayi aure”

Daga karshe sai ta fashe da kuka ni ma na fashe da kuka ina kiran sunanta. Bayan ta kashe ya dago na mikawa Yaya wayarsa.

“Yaya dan Allah kai ma ka yafe min”

Ya rage tsawonsa ya rumgume ni.

“Na yafe miki Noor, na fi kowa son farincikinki, Allah ya auren wannan shi ne mafi alheri fiye da Zafeer shi kuma ya ba shi wata wadda ta fiki zama alheri a gareshi, ki yi hakuri Noor kin ji ki yi hakuri”

Na sha kuka a jikinsa sosai sannan ya sake ni ya fita, Hana kam kasa ce mata komai na yi ni da ita muka rika kuka kamar an mana mutuwa muna rumgume da juna. Har sai da Baba ya shigo ya fara min huduba tare da yan'uwansa shi ma na roke shi yafiya ya yafe ya saka min albarka da addu'ar Allah yasa gurin zamana ne. Manya motoci na alfarma aka jera daga kofar gidanmu zuwa gidansu Zainab, gurin fitowa da ni ne ya zama aiki na kama Hana na rike gam ita ma ta rike ni daker aka banbare ni a jikinta aka saka ni motar, kuka be barta ta bi ni ba sai Gwaggwani da suka shiga motar tare da ni suna min fada wai sai kace kaina farau aure ina wannan kukan na tashin hankali.
Daga gidanmu aka dauke ni zuwa gidan da za a rusa farincikin.

Continue Reading

You'll Also Like

1.5K 73 13
KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not worry, for it was all destined...at what...
15.6K 1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
127K 12.8K 32
Athulya Singhania has spent her entire life in solitude, yearning for the love of a family. Over the years, she mastered the art of concealing her em...
3.7K 85 15
Book #2 of my SpiderWitch series Placed during TASM2 " All I can say is it was, Enchanting to meet you.." " Please don't be in love with someone els...