WAZEER!

By REAL-SMASHER

4.2K 343 53

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... More

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Wedding march
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mission
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Inexplicable
Strangerlike
Safwah
Adviceful
Thought pattern
Proposalist
Her wish!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Wedding bell!

121 6 0
By REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2024.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*


                               29

#Wedding bell!

*WAZEER*

        Tunda yazo duniya ko yace ya girma ya mallaki hankalin kansa,wani abu bai taɓa haɗa shi da wani ba,zagi ko cin mutunci ba'a taɓa masa ba saboda tsananin takatsan² da kamewa,yau da Safwa ta zageshi ta gaggaya masa magana gani yake kamar wani mummunan zunubi ya aikata,da ƙyar bayan ya tabbatar ta tafi and she'll never came back ya buɗe motarsa ya shiga tare da barin GRA ɗin. A hanya yana driving yana tunanin kalamanta da suke masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa,idan yace bai shiga damuwa da ruɗewa a sababin maganganunta ba,tabbas sai dai ya zama ya faɗi son ransa,kalamanta sun dakeshi da gasken²,tuhumar kansa yake me yasa yayi haka? Me yasa bai sanar da Safwa komai ba? Me yasa da Dad yace masa a'a ya yarda aka tafi a a'a? Me yasa bai sanar da Abba ba his granfa,ko yayi maganar da Mimi ya nemi shawararta? Wata zuciyar tace "wait Wazeer.. Ta ina za ka iya tunkarar wani da wannan al'amarin,bayan ba kowa ya san waye kai ba? In fact ba da kowa kake mu'amala ba.." Numfashi me zafi ya sauke,zuciyarsa na sake tuhumarsa abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa,maimakon ya wuce Galadanci haka kawai yaji bazai iya ba ya ɗauke hanya ya nufi Jambulo,Mimi yake son zuwa ya gani,ko da bazai ce mata komai ba,ko da kuma ba zai iya sharing damuwarsa da ita ba,yana ganin zuwan nasa kawai ya ganta zai sanyaya masa rai. Sanda ya iso line a waje yayi parking tare da sauka motar ya nufi masallacin unguwar,sallar ishaa da bai samu yi ba kasancewar yana hanya akai kira ya fara gabatarwa,bayan ya idar ya fito masjid ɗin ya wuce gidan da ƙafa,a bakin entrance ya tsaya yayi knocking,Kubra tazo ta buɗe tana tambayar "waye?" Bai ce mata ƙala ba sai fuskarsa da ya sake ɗaurewa,ganin wanda ke tsaye yasa ta bashi hanya tana faɗin "sannu da zuwa" a hankali kamar ba zai amsa ba yace "thanks!" Tare da wucewa ciki yana furta "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Jin muryarsa yasa Mimi dake aiki idanunta akan MacBook saurin ɗagowa tana zare glass dake kan fuskarta,Mama dake zaune tana kallon labarai wani lokaci suna hira da Mimi ta saki fuskarta tana faɗin "wa'alaikas salaam warahmatullah wabarkatuh.. A'ahh! Me gidana yau ka tuna da wannan matar taka ne?" Ɗan gyara yanayin fuskarsa yayi ya durƙusa kusa da ƙafar Mama zai zauna saman rug,da sauri Mama tace "tashi² ka zauna kusa da ni Abuu Turab" cikin girmamawa yace "Mama ki barni na zauna nan na gaji ne,ƙasan zai fi min daɗi" Mama tace "tohh shi kenan zauna tunda ka fi son nan ɗin" yayi ɗan murmushi me ciwo kafin ya shiga gaisheta "barka da dare Mama" Mama tace "barkanmu dai Abuu Turab,ya aiki da mutanen gidan naku?" Yace "alhamdulillah!" Mama tace "kamar ka san kwana biyun nan ina cigiyarka" yayi ɗan gajeran murmushi yace "aiki ya min yawa ne shi yasa ban samu zuwa ba" Mama tace "Allah sarki.. Toh Allah ya taimaka yayi kyakkyawan jagoranci" yace "ameen.." Idanunsa na kaiwa kan Mimi dake sauraron hirarsu,a hankali yace "Mimi barka da dare" Mimi da tun kallon farko da tayi masa ta fahimci yana da damuwa ta gyaɗa masa kai tace "barka dai,ya aiki da su Daada?" Yace "lafiya lau alhmdllh" tace "maa sha Allah" tana rufe MacBook dake gabanta. Tunda ya zauna bayan sun gaisa bai sake cewa komai ba yayi shiru yana ƴan tunane²,Mimi ta tashi da kanta ta tafi kitchen ta haɗo masa abinci ta kawo tare da ajiyewa gabansa tana faɗin "ci abinci" ɗaga idanunsa da suke cike da damuwa yayi ya kalleta,kafin yayi magana tace "ci maza u look somehow.. Daga ina kake ne ma?" A hankali ya sauke kansa ƙasa yace "na je wani unguwa ne" tace "Mmmm! Eat first to" ba don yana jin zai iya ci ba,sai don kada Mimi tayi saurin fahimtar akwai wani abu dake damunsa ya gyara zama tare da ɗaukan spoon yayi bismillah,bai wani ci da yawa can ba saboda har yanzun ba komai yake iya ci ba a abincin gargajiya ya ajiye ya sha ruwa. Jifa² da Mama suke hira ita da Mimi sosai ya ɗebe masa kewa,kuma ya rage masa damuwa da zafin da zuciyarsa ke yi,aƙalla ya samu good 2 hours a gidan kafin ya fara haramar tafiya,yana ɗaukan key ɗinsa da ya ajiye ƙasa tun shigowarsa yace "Mama zan tafi" Mama tace "toh Abuu Turab.. Mun gode sosai da zumunci,Allah ya mayar da kai gida lafiya,a gaida su Daadan naku da mutanen gidan" yace "za su ji in sha Allah.. Sai da safe" tace "Allah ya tashemu da alkhairi" ya amsa yana miƙewa tsaye,tashi Mimi tayi ta ɗauki hijab ɗinta tasa,suka jera tare zuwa waje,a balcony suna sauka take cewa "Zaki!" Yanda ta kirashi sai da sunan ya keta ƙirjinsa,a hankali tasa hannu ta riƙo nasa suka tsaya a gurin,tana masa kallon tsanaki tace "meke faruwa?" Shiru yayi da farko kafin ya girgiza mata kai yace "nothing.." Tayi shiru itama tana kallonsa da sake karantar yanayin dake kan fuskarsa,a hankali tana kwantar da murya irin na me rarrashi tace "ko dai baza ka iya sanar min ba?" Da sauri yace "Mimi babu fa" tace "are u sure babu komai?" Ya gyaɗa mata kai da sauri yace "absolutely" tace "ok! Allah yasa" yace "ameen.. Sai da safe" tace "uhumn! Allah ya tashemu lafiya.. Ka gaida gida" yace "na gode" cikin ɗan sauri ya wuce ya sauka yana tafiya,Mimi tayi tsaye tana kallonsa,tunani da yawa suna zuwa ƙwaƙwalwarta game da rayuwarta da ta ɗanta har ya fice gidan.

*MUNIBA*

          Kallon Lieut Muniba take kamar yau ne ta fara saninsa a rayuwarta,haka nan tunda ya sanar mata zai yi tafiya Porthercourt take jin wani abu na mata yawo a jiki da jininta,tsigar jikinta na wani irin tashi,ƙofofin gashin jikinta suna buɗewa,hankalinta sam bai kansa saboda zurfin da tayi a tunanin da bata san ko na mene ne ba,Lieut dake sauraron tayi magana tunda ya fara mata sallama zai tafi,ya ɗan shafi gefen fuskarsa yana sakin lallausan murmushi,can ƙasa yace "ohh hello! Baby za ki barni na tafi kuwa? Idan kina kallona haka za ki sa na tsaya nan and hakan will lead me to na rasa flight.." Ajiyar numfashi me nauyi Muniba tayi da yasa tsigar jikinta sake tashi,cikin ƙasa² da murya ta furta "Allah ya tsare hanya,yasa yanda za ka tafi ka dawo lafiya.. Allah ya bada nasarar abunda za'a je nema,ya ƙara buɗe ƙofofin arziki na halal,ya rabaka da haram,Allah ya rabaka da dukkanin tsautsayi,ya kareka daga sharrin abun halitta,jinn wal-ins.." Fuskarsa cike da murmushin jin daɗi yace "ameen yaa arhamur-rahimiiyn.. Na gode sosai da addu'ah Madam" ɓata rai tayi kaɗan idanunta sun yi rau kamar za tayi kuka tace "godiyar na mene ne?" Yace "na jin daɗin addu'ar Mata ta ne,uwar ƴaƴana in sha Allah nan ba da jimawa ba.." A ɗan kunyace ta kauda kanta gefe tace "Allah ya amince" yace "ameen.. So zan iya tafiya an bani dama?" A hankali tace "um'um!" Yace "please Favorite zan je na sallami ƙannenki,ba na so na ɓata lokaci saboda a daren nan za mu tashi" a hankali jikinta ya ɗan saki tace "ok!" Yace "an amince min zan iya tafiya yanzu?" Sanda ta ɗago idanunta ta aika masa wani narkakken kallo da babu komai cikinsa face shagwaɓa,maganarta a sanyaye cike da barkwanci tace "permission granted.." Buɗe ido yayi sosai akanta yace "wow! Thanks Madam.. Sai mun yi waya?" Tace "in sha Allah" yace "ok! But kada na kira kin yi bacci" tace "zan jira kiranka in sha Allah" yace "na gode sosai,a gaida Mami.. And in sha Allah,idan na dawo zan zo gaisheta" murmushi ta saki tace "idan kana da lokaci ko?" Yace "i'll squeeze nazo" tace "Allah ya kaimu" yace "ameen.. Uhumn! Maganar event da whatever kuke shiri idan na sauka sai naji,and Hammad will take care of it,sai ku tsara komai da wuri ko?" Tace "in sha Allah" yace "tohh! I'm going Bee" tana fesar da numfashi tace "um'um! Kace dai sai ka dawo" yace "ok! Sai Allah ya sake sadamu" tace "Allah ya sadamu da alkhairi" yace "ameen.." Sun yi sallama sun ƙara kamar baza su rabu ba,kafin da ƙyar ya samu ya iya wucewa,Muniba da jikinta ke sake yin sanyi a duk lokacin da ta tuna tafiyar dake gabansa sai taji kamar tace masa kada yaje ko'ina ya tsaya,motarsa na fita gidan ta juya a hankali tana sauke ajiyar zuciya ta shige cikin gida.

*SAFWA*

         Radhiya dake sauraren maganar Safwa through voice call da suke yi tace "why Safwa? Da kin masa bayani ta lalama ina ganin zai fi,tunda dai na tabbatar Aley yana da ilimi,bazai kasa fahimtar ki ba.. A gaskiya ban ji daɗin yadda kikai masa ba,ɗan Adam yana da daraja,kuma kowa da kika ganshi a duniyar nan Allah kaɗai yasan matsayinsa,ko don gaba ki kiyaye harshenki da faɗin maganganu barkatai,mutane iri² ne a duniyar nan,akwai wanda za ki masa abu ya yi haƙuri ya kauda kai saboda ƙana'a,akwai kuma wanda ko yaya kika ɓata masa wallahi sai ya nemi damar da zai rama.. Don haka ina baki shawara wallahi da wasa kada ki bari irin haka ta sake haɗaki da wani,kawai dai tunda kin sanar masa aure za kiyi,fine.. Hakan ya wadatar,Allah yasa ya fahimceki kuma ya miki uzuri" Safwa tace "kada ma Allah yasa ya fahimta ɗin,ni da shi ai kuma yanzu ta ƙare,don wallahi na tabbatar na masa nisa irin nisan dake tsakanin sama da ƙasa,ni ba ajin irinsu bace.. Yawwa! Kin ma san wani abu kuwa?" Radhiya tace "uhumn! Safwa baza ki yarda dani ba,amma dai mene ne?" Safwa tace "saboda tsabar ƙarya irinta Aley yau a mota yazo ƙofar gidanmu,mutumin da ke fama da talauci,ke in ban manta ba a yadda ya taɓa faɗa min kamar fa jinin bayi ne ma,to kinga kuwa ni danginmu ba bayi bane,me zai kaini auren bawa? Kai Allah na gode maka daka rabani da alaƙaƙai" Radhiya tace "shi Aliyun ne yace miki haka?" Safwa tace "wallahi haka ya taɓa sanar min da jimawa" Radhiya dai ta yi shiru tana tunani,Safwa tace "whatever! Ni kinga bari na amsa waya,Hamood Waziri na kira,i think zai ce min ya iso" Radhiya tace "alright! Ace ina gaishesa" Safwa tayi dariya tace "zai ji.. Sai kin jini" tana faɗan haka ta katse kiran ta ɗauki wanda ya shigo mata,maganarta a tausashe tace "hello! Ur Excellency" daga can gefen Hamood Waziri yace "i'm outside" cikin sauri tace "i'm coming ranka ya daɗe" yace "ok!" Tana ajiye wayar hannunta ta ɗauki turaruka ta shiga fesawa,sanda ɗakin ya turare da ƙamshi kafin ta ajiye ta ɗauki mayafin abayar dake jikinta kalar sky blue ta nufi waje.

*HAMOOD WAZIRI*

        Yana zaune cikin motarsa da driver ya tuƙoshi Safwa ta fito tare da yin knocking glass ɗin motar,ajiye iPad ɗin hannunsa yayi saurin yi tare da buɗe motar ya sauko,idanunsa akan Safwa yana sakar mata kyakkyawan murmushinsa,tace "barka da zuwa Yallaɓai" yayi ɗan gajeran murmushi kafin yace "um'um! Ba na son wannan sunan,Yallaɓai kamar wani jami'in tsaro?" Safwa tayi ƴar dariya tace "ok! Wanne kake so?" Yace "suna me daɗi haka na masoya nake so a kirani da shi" Safwa ta ware idanunta tana dariya tace "toh kamar wanne?" Yace "a'ahh! I'm not sure wanne zai fi dacewa da ni,a knife and meat is in ur hand princes,sai wanda aka yi ra'ayin saka min" tace "shi kenan zan duba me daɗi" yace "stunning!" Ɗan waigawa tayi ta kalli get ɗin gidansu tace "mu ƙarasa ciki Ur highness" yace "ok!" Suka jera suna tafiya suna magana,sam kai baza kace Hamood ya haifi ƴa kamarta ba saboda yadda yake jin ƙuruciya. A compound suka zauna saman kujerun da tasa Bilal ya fito musu da shi,Hamood na sauke numfashi kaɗan yace "ni kam ina friend ne,kwana biyu bana ganinsa" Safwa tace "yana nan kuma,Allah dai baisa kun haɗu bane,amma yanzu ma shi nace ya kawo min chairs" yace "ohh! Allah sarki.. Ina son ganinsa kuwa" Safwa tace "in kirashi yanzun?" Hamood yace "yeah!" Safwa ta tashi tana cewa "ok! I'm coming" yace "baki ji ba" ta ɗan tsaya kaɗan tana kallonsa right in the eyes,yace "idan kin sanar masa ki jiramu kaɗan mu gama magana" ta gyaɗa masa kai tare da yin murmushi,yace "and.." Ta sake tsayawa tare da zubo masa idanunta,yace "did u make a list of abunda nace before?" Gyaɗa masa kai tayi tace "Mmm!" Yace "good.. Ki fito min da shi" tace "alright!" Not too long da shigarta ciki Bilal ya fito,sanda ya iso yayi sallama,Hamood Waziri ya amsa masa yana cewa "have a seat friend" Bilal ya zauna kujerar da Safwa ta tashi yana gaida Hamood "good evening Uncle" Hamood yace "wait.. Am i ur Uncle? Just call me In-law.. Ai mu surukunai ne ko?" Bilal yayi dariya yace "mene ne surukunai?" Hamood yace "what!? Baka san mene ne surukunta ba?" Bilal yace "i'm not sure" Hamood yace "ok! Ka san In-laws ai?" Bilal yace "ehh na sani" Hamood yace "toh abunda yake nufi kenan da Hausa.. And! Kaje waje ka samu driver ya baka saƙon da na bari a mota" Bilal yace "toh!" Ya tashi ya fita,bai jima sosai ba ya shigo da manyan paper bags a hannu biyu,yana ajiyewa ƙasa yace "ga shi Uncle" Hamood yace "ka kai cikin gida,kowa ya duba nasa akwai suna ciki.. And kace ma Addanka ina jiranta" Bilal ya ɗauki paper bags ɗin yana cewa "an gode Uncle,Allah ya saka da alkhairi,ya ƙara buɗi" Hamood yayi masa murmushi yace "ameen.. And idan zan tafi zan kiraka" Bilal yace "toh Uncle" daga haka ya wuce ciki,haka nan Allah ya dasawa Hamood son Bilal a rai,bai sani ba ko nutsuwar yaron ne da kamewarsa da yayi kama da na Wazeer ɗinsa suka sa yake bala'in burgeshi oho. Fitowar Safwa yasa shi yin murmushi,saman kujerar data tashi ta koma ta zauna,ya miƙa mata hannu yana faɗin "ba ni muga" a ɗan yangance me gauraye da kunyar irin mahaukacin abunda ta rubuta ta miƙa masa ya karɓa tare warware takardar ya shiga dubawa,murmushi kawai yayi kafin ya kalleta yace "shi kenan abunda kike buƙata ko akwai wani abun bayan nan?" Zaro idanunta tayi cikin mamaki tace "a'a shi kenan" yace "um'um! Think sosai ki sanar min" tana girgiza masa kai tace "a'a shi kenan" yayi murmushi yace "ok! Ni zan duba idan akwai abunda bai ba sai a canja.. Let's go to the next point" Safwa dai mamakinsa ya hanata cewa komai,yace "Safwa!" Ya kirata da cikakken sunanta,a hankali tana yakice tunanin da ke ranta ta amsa "na'am" yace "kamar yadda kika sanni,cikakken suna na da asalina,har ma da tarihin rayuwata duka,ciki har da labarin rasuwar yarinyata da rabuwar da nayi da Mata ta,kin san ban ɓoye miki komai ba,right?" Ta gyaɗa kanta a hankali tace "ehh!" Yace "alhamdulillah! So abunda nake fata daga gareki shi ne,ni mutum ne da ba na son sakaci da any abunda yake mallakina,ina son yin mu'amala da mutum me takatsan² da kulawa akan komai na rayuwa,ina girmama duk mutumin da nake tare da shi,ina ɗaukan komai masa da muhimmanci.. Ina fatan zai zama haka a gareki kema!?" Safwa tace "in sha Allah" yace "maa sha Allah.. Sai abu na biyu" ta gyaɗa masa kai tana sauraronsa,yace "ba wani abu bane illa maganar inda za mu zauna bayan mun yi aure,kin san na faɗa miki gidanmu dukanmu ni da ƴan uwana a Family house namu muke zama ko?" Safwa tace "ehh!" Yace "so! This time around na ji ba na sha'awar zama can,saboda wasu dalilai nawa,amma me kike gani a naki gefen? Za mu iya zama baki da matsala ko na kaiki sabon gidan dana tanada zan zauna da iyalina?" A hankali ta ɗago kanta zuciyarta na bugawa da faɗin "kice masa kema kin fi son ku zauna guri daban ba'a family house ba" idanunta ta ɗan runtse muryarta ya shiga ɗan karkarwa,maimakon ta faɗi abunda zuciyarta ke mata huɗuba,bata san sanda bakinta ya suɓuce ta furta "ni ba ni da zaɓi,duk abunda kaga ya dace it's fine" yace "um'um! Gara dai na sani idan kina da zaɓi please" wannan karon shiru tayi ta kasa cewa komai,sai wasan da take da fingers ɗinta,yace "ok! Zan duba abunda yafi dacewa da mu,sai na sanar miki daga baya,haka ya yi?" Ta gyaɗa masa kai tace "ehh" yace "uhumn! Lastly sai Maganar *SADAKI..* Nawa kike ganin ya yi miki na biya sadakin ki?" Safwa dai yau Hamood ya gama kashe mata baki,sam ta kasa furta komai,sanda ya sake maimaitawa,tace "Mmmm! Ni dai ban san me zance ba,amma duk yanda yayi maka ka bayar" yana girgiza mata kai fuskarsa da murmushi akai yace "addini ya baku dama ku yankewa masu neman aurenku sadaki,besides ni na tambayeki da kaina,ina so ki sanar min nawa kika yanke? Daga kan 1M har zuwa 100M i'll pay for it.." Ido waje Safwa da gabanta ke faɗuwa ta dunga kallon ƙasa ta kasa magana,al'amarin Hamood kuma fa ya fara ba ta tsoro gaskiya,lissafin kuɗaɗen nan da yake yi sun fara wuce tunaninta,a hankali muryarta na gargada tace "1M!" Yace "1M ɗin ya yi miki,ko na bari kiyi shawara da Mom?" Tace "ya yi" yace "um'um! Zan baki lokaci kuyi shawara,sai ki sanar min ko?" Tace "toh!" Jikinta a mace,yace "so! Ina ganin wannan su ne major maganganun da nace za muyi,and alhamdulillah duka mun samu matsaya.. Ɗan abunda yayi saura daga baya sai muga yadda za'ayi" tace "Allah ya kaimu" yace "ameen.. And! Na san ku mata ba'a rabaku da son hidima,don haka ina so ki samu wata cikin friends ɗinki,ku tsara komai da kuke buƙata,including ashobe kuke cewa ko anko?" Tayi ƴar dariya tace "anko" yace "yes anko.. So due to yanda aka tsayar da lokaci a gajarce,ina so ku fitar da ankon but kada ya wuce this week please,idan kun gama ki sanar min,akwai yaron da zansa ya kawo sai a rabawa ƴan uwa kafin lokaci ya ƙure" wannan karon Safwa couldn't help it da sauri tace "gaskiya hidimar ya yi maka yawa,ina ganin batun ankon ka barshi kawai kowa yayi da kansa,and tunda bikin na farko ne a gurin Babanmu kowa zai so yi,idan akace kai za kayi komai abun zai yi yawa gaskiya" Hamood na sakin murmushi saboda hankalinta da ya gani a nan,yace "um'um dear! Sanin hakan da ƙarfin aljihuna yasa nace zan yi,saboda haka kada ki damu,idan nace zan yi abu na san zan iya ne,ke dai kiyi abunda nace kawai" Safwa tace "amma.." Yace "no any amma a nan,just do it kamar yadda nace,and leave the rest to me" a hankali ta gyaɗa masa kai tace "ok!" After then bai jima ba yayi mata sallama saboda wasu ƴan ayyukan da zai gabatar,sanda ta rakashi bakin mota ya shiga,yana zaune back seat yana kallonta yace "shiga gida.. Ina jiran Bilal" ta buɗe idonta sosai tace "Bilal kuma?" Yace "sure" ta gyaɗa kanta a hankali tace "ok! Allah ya tsare.." Daga nan ta wuce ciki kamar ta ɗan ji babu daɗi.

*SAFWA*

      Cikin compound ɗinsu ta wuce,sanda take shigowa suka haɗu da Bilal da ya fito zai je kiran da Hamood yayi masa,fuskarsa a sake da fara'a yace "Yaa Safwa guess what!?" Ta girgiza masa kai tace "u know i'm not good in guessing.. What's it?" Yace "mun yi sabuwar waya iPhone 11 pro max,MacBook,i-watch and ear pods Uncle ya siya mana" tana kallonsa da mamaki tace "kai da wa?" Yace "dukanmu har Asim.. Bari nayi sauri na dawo yana kirana,akwai labari sosai yau" tace "ok!" Da sauri ta wuce har tana ɗan haɗawa da gudu saboda abunda taji,tana shigowa parlour ta samu Umma zaune tare da su Zunnurain da Asim sai murna suke sun saka kayan a gaba kowa yana ɗaga nasa happily,Safwa ta dunga binsu da kallo cike da mamaki tace "Umma wannan kayan fa?" Umma na ganinta ta kama hanci ta rangaɗa guɗa,sanda tayi me isarta kafin ta tsagaita tace "kayan arziki ne Hamood ya aiko mana,zo ki gani sabbin wayoyi ne kowa da nasa har Babanku,ni da shi kam ma har da key ɗin mota wallahi,abun dai ba'a cewa komai,Allah ya kashe ya bamu" a tsorace Safwa tace "mota!?" Umma tace "wallahi nima ga nawa a ciki" Safwa ta dunga kallon kayan da Umma ke nuna mata a tsorace zuciyarta na bugawa da sauri²,lokaci ɗaya hankalinta ya tashi ta shiga waige² a parlon kamar tana neman wani abu,can kamar zararriya tace "Umma kuma kin amince a karɓa? Kayan nan basu yi yawa ba? Kin ma san ya muka yi da shi yanzu nima a waje?" Lokaci ɗaya Umma ta haɗe rai cikin faɗa tace "ke ban son shirmen banza da shashanci,da ce miki akayi za'a mayar? Wa ya faɗa miki idan irinsu Hamood sun yi kyauta ana cewa su barshi? Ai gidan arziki da mulki basa gajiya da cewa ungo.. Don haka ahir naji kin furta min maganar da bata gamsheni ba wallahi zan saɓa miki fiye da zatonki,tun wuri idan za ki tayamu murna ki yi,in baza kiyi ba kuma ke kika sani,amma wallahi babu mai hana ni karɓar kyautar mota da duk abunda Allah ya tsaga rabona ne a jikinsa" jagwaf Safwa ta faɗa saman kujera ta zube,idan hankalinta ya kai dubu a yanzu duk a tashe yake,ta fara jin shakku da tsoron al'amarin Hamood,me yasa zai zo da irin wannan fuskar a lokacin da ta riga ta karɓeshi? Idan yana jin yana da arziki ai sai ya jira idan ta shiga gidansa ya yi mata duk abunda ya dace,amma kafin aure abun zai zama wani iri,duk da bai nuna mata any alama da zata sa tayi zargisa ba,amma ko da take kwaɗayin mu'amala da auren wani mai kuɗi,bata taɓa kawowa za ta haɗu da irin Hamood ba sam. Shigowar Bilal da Awwal da suke magana Bilal na bashi labarin abunda ke faruwa yasa Safwa ɗaga kai ta kallesu,ajiye babban kwalin da suka shigo da shi suka yi a gabanta,Bilal na cewa "Yaa Safwa gashi ya ce a kawo miki" Safwa da hankalinta bai jikinta sam jinsu kawai take tana kallonsu,kafin ta buɗe baki tace wani abu,Umma da duka ƴan uwanta hankalinsu ya dawo kanta tace "gaskiya na jinjinawa ƙoƙarin Hamood Waziri.. Irin wannan hidima haka,to ke uwar gayyar ma kinga ga naki nan ya biyo sahunki,yi maza ki buɗe mana mu ga mene ne a ciki.. Ke kam ai sai motoci ba dai ɗaya ba Safwa ta kalli Bilal tace "buɗe muku ku gani" Awwal yai saurin cewa "bari na buɗe" Safwa dai bata ce komai ba bayan binsu da ido da take,key ɗin ɗakinsu Awwal yasa a bakin kwalin ya yaga,Umma da duka ƴan uwanta kowa sai jira yake yaga mene ne a cikin nata gift ɗin,yana fara buɗewa wani irin baƙon ƙamshi ya musu sallama,hannu yasa ya wangale kwalin yadda kowa zai iya ganin abunda ke ciki,kallon manyan greeting cards da chocolates masu tsadar gaske da suke sama Safwa tayi tare da sauke wani bayyanannar ajiyar zuciya,Umma tace "kaiii tubarkalla maa sha Allah.. Fito da duka kayan muga" Awwal ya dunga ɗebowa yana zubewa gaban Umma,wani kwalin da ya gani da paper bag a ciki ya ɗauki hankalinsa,yasa hannu ya ɗauko tare da buɗe kwalin,cake ne well decorated daga samansa an rubuta *FOR MY FEATURE WIFE.. SAFWAH!* Yanda aka ƙawata cake ɗin da girmansa kaɗai ya isa abun kallo,nan suka shiga surutu kowa na faɗan albarkacin bakinsa,Umma tace "Awwal bani cake ɗin nan ka ji muci rabonmu ne ya tsaga" ya ɗauka tare da miƙa mata,Umma na magana ta shiga yankawa tana faɗin "yau ba sai mun ci komai ba in muka ci wannan garar,da na san za'a kawo mana kayan arziki haka ai banga abunda zai sa na wahala gurin yin girkin dare ba.. Amma yanzuma bata ɓaci ba,Awwal leƙa idan ka samu almajirai ka kirasu su amshi abinci sadaka daga cikin irin falalar da Allah ya yi mana" Awwal yace "an gama Umma.." Kafin kace me sun shiga ciye²,su ne ci wannan koma wannan,cikin ɗan lokaci gaba ɗaya sun hautsina parlon,banda hayaniya babu abunda suke. Shigowar Baba da sallamarsa yasa su ɗan tsagaitawa suka amsa masa,yaran duka suka yi masa sannu da zuwa ya amsa su ɗaya bayan ɗaya,yana musu kallo cike da tuhuma yace "hayaniyar me kuke haka ina ta horn tun ɗazu babu wanda yazo ya buɗe min ƙofa?" Cikin zumuɗi Umma dake tsakiyar kaya dumu² tace "sannu da zuwa Engr" Baba yace "yauwa.. Ina tambayar hayaniyar me kuke nace?" Umma tace "wallahi surukinka ne yazo ya kawo mana kayan gara,shi ne muka baje a nan muna kwasar daɗi" Baba ya kalleta kawai jin abunda tace,lokaci ɗaya ya juya yana cewa "tohh! Azo a buɗe min gidan zan shigo da mota" Umma tace "tohh ranka ya daɗe.. Bilal tashi maza ka buɗema Babanku gida ya shigo ayi da shi shima" da sauri Bilal ya tashi,inda ake ajiye mukulli saman fridge yaje ya ɗauko yabi bayan Baba da bai tsaya ba,yana buɗe get Baba ya shigo da motarsa yayi parking tare da saukowa,sanda ya jira Baba suka ɗebo ledojin cefanen da yayo musu na breakfast sannan suka shiga ciki. A parlour sanda suka shigo Baba ya kalli tarin kayan da suke ajiye,lokacin yaran kowa ya shiga ƙoƙarin nuna masa irin kyautar da Hamood yayi masa,bai ce komai ba kuma bai nuna yabawarsa ba ya wuce sama ransa kamar a ɓace yana kiran Umma "ki sameni yanzun nan" yanayin maganarsa yasa dukansu a kokwanto,Umma ta daure ta miƙe da ƙyar tana ɗaukan paper bag da duk wani abu data fitar nasa ta biyoshi da su ɗakinsa,tana yin sallama Baba dake tsaye yana jifanta da wani irin kallo yace "Murjanatu! Mene ne duka wannan abun da nake ji da gani?" Umma tayi sak tana kallonsa,lokaci ɗaya tace "ranka ya daɗe me ya faru? Me aka yi?" Cikin ɓacin rai Baba yace "auu! Tambayata ma kike me ya faru? Ke baki san dai² da rashinsa ba? Akan wane dalili daga bashi yarinya zai kama yiwa iyalina hidima kamar wani ƙaramin yaro? Shin siyar masa da ƴar nace zan yi? Wallahi kada ya janyo abunda zaisa nace na fasa yazo ya amshi kuɗinsa,don har ga Allah ina jin shakku akan al'amurin nan,dama maganar ba wai na gama amincewa da shi bane 💯 percent" cikin tashin hankali Umma ta dafe ƙirji tare da furta "a'uzhubillahi minash'shaiɗanir rajiim.. Baban Safwa wannan wane irin magana ce haka? Daga abun alkhairi sai kuma zargi ya shigo ciki?" Cikin ɓacin rai duk da Baba bai so suyi hayaniya yace "ni kike yima ta'awizhi saboda na ce don me za'a yima iyalina abu without my knowledge? Ni kike kira shaiɗani ko kuwa?" Umma tace "toh ai na ga kamar ka ɗauki zafi ne akan abunda bai kai ya kawo ba" Baba yana jifanta da wani disgust kallo yace "wannan abun kike kira abunda bai kai ya kawo ba Umman Safwa? Do u have any idea akan irin kuɗaɗen da ya kashe ya muku irin kyautar nan?" Umma tace "amma a ganina don yana da shi ne yayi,idan bai da shi me zai sa ya ɗaukarwa kansa dala babu gammo?" Baba yace "ok! Baki ga komai ba kika ce?" Umma tace "wallahi ni banga komai ba,bayan alkhairi da Allah yake nufinmu da shi ta dalilin haihuwa da ƴarmu" Baba yana gyaɗa kansa cikin kausassar murya yace "ko ki gani,ko ki ƙi gani.. Lallai² umarni na bayar ba shawara ba,ku tattara all that goods daya aiko ku mayar masa,idan ba haka ba wallahi ran kowa sai ya ɓaci" sake da baki Umma take kallon Baba kamar wacce akai pausing,Baba yace "ina fatan kin ji me nace,ni ban siyama yarana wayoyi da laptop ba,ba kuma halin siyan ne ba ni da shi ba,sai don ina so suyi karatu,and bana so wani abu ya taɓa tarbiyya da mutuncin iyalina,saboda haka ban amince wani a waje ya siya ya basu ba,ba zai yiwu ina gini wani mutum yayi ƙoƙarin rusa min foundation ba.. Na ce a mayar da komai,idan ana son zaman lafiya da ni a tattara komai a mayar masa,mun gode" Umma tace "Engr. Har fa da key ɗin Mota uku kake cewa a mayar.." Cikin fushi Baba ya kwaɗa ihun "ba mota ba Allah yasa mukullin jirgin sama ne a ciki" Umma tana jinjina kai tace "danƙari! Toh dai gaskiya Engr sai dai in baka haƙuri,don Allah ya sani ni dai banga dalilin da zaisa na mayar da kyautar nan da akai min ba,in kai ba ka so ba'a burgeka ba,ni da yara muna buƙata" Baba ya juyo a fusace yace "ni kike yiwa jayayya akan maganar nan Murjanatu?" Umma tace "a'a ai maganar gaskiya kenan,ya duk muna cikin farin ciki lokaci guda kace a tattara a mayar fisabilillahi? Gaskiya idan akai haka mutuncinmu zai zube,wannan ai nuna ƙaranta ne da gidadanci" Baba yayi sak yana kallon Umma,ba tare da ya sake cewa komai ba ya girgiza kansa ya wuce toilet ya barta tana ƴan ƙananan maganganu,don kanta data gaji da tsaiwarta ta zube kayan ta fice tana sababi da mita. Tana saukowa parlour ta tarar da su Awwal kowa cikinsu ya canja fuska,Umma ta kallesu da kyau tace "lafiya kukai jigum² kamar gidan makoki?" Awwal yace "Umma wai me Baba yake cewa?" Umma tayi ƙwafa tace "auu! Kun jiyomu da shi?" Awwal yace "ehh! Ai babu abunda bamu ji ba.. Don Allah taya ma za'ayi yace wai a mayar da kayan nan? Ni wallahi idan ba ya son motar ya bani,dama guy kamata ai yaci ace ina da ɗan abun hawa ko da ba mai tsada ba,batu na Allah abokaina duk babu wanda bai da motar hawa iyayensu suna musu hidima suna basu abunda suke so,nima ina so ma shigo gari nayi abunda raina yake so kamar ƴaƴan kowa" Umma ta sake yin ƙwafa tace "kaii ku sha kuruminku babu abunda zai shigo gidan nan ya fita,wallahi sai dai in ba suna na Murja ba.. Ai zai ga kalar taurin kaina yau da bai taɓa gani ba.." Tana faɗan haka ta koma ta zauna cikinsu suka ɗora daga inda suka tsaya tana mitar zancen Baba. Da safe ko da Baba zai fita jin da dare bai kuma maganar ba ko even yace ta kwashe kayan da ta kai ɗakinsa,Umma ta yi tunanin maganar ya mutu kenan,sanda yake saukowa ya tarar duk yaran sun wuce school sai ita kawai a parlour,har Safwa yau bata nan kasancewar lectures ɗin safe gareta tuni ta tsufa a school,Baba yana kallon Umma da tai kicin² ya ɗan tsaya yace "zan fita" bata kalleshi ba tace "Allah ya tsare hanya" ya amsa yana sake kallonta da mamakin sauyin da ya gani lokaci ɗaya,har ya juya zai fita ya dakata yace "arghm! Maganar da muka yi da dare,lallai² a tattara kayan nan a mayar" idan Umma ta tanka Baba to appliances da suke cikin parlon sun amsa,Baba ya gyaɗa kai ya wuce abunsa ya bar gidan. A hanya yana tafiya ya shiga kiran Hamood,ba'a ɗauki lokaci ba Hamood ya amsa suka gaisa a mutunce,cikin ɗan dakewa Baba yace "afwaan fa Alh na kira ban sani ba ko kana aiki.." Hamood yayi murmushi yace "a'a babu komai" cikin hikima Baba ya shiga throwing up abunda ke damunshi dangane da irin kyautar da ya yiwa iyalinsa daren jiya,Hamood na saurarenshi yana murmushi da sake ganin girman Baban Safwa,sanda Baba yake cewa "don Allah kayi haƙuri ka aiko a karɓi kayan,don gaskiya baza mu iya amsa ba,kyautar ta wuce hankali ya ɗauka,besides dalilin da ya hana ni siyawa yara irin wannan kayan more rayuwar saboda ina so su tsaya suyi karatu ne,kai kanka ka san irin zamanin da muke ciki yanzu,baka bawa yaro iri²n waɗannan abubuwan ba ya gani a wani waje wani abu mara daɗi ya faru bare ka yi da kanka,saboda haka idan babu damuwa don Allah ina son dawo da duk wani abu,ba don komai ba kuma ba don na raina ba,sai saboda kare martaba da tarbiyyar iyalina.. Ita dai Safwa ban hana ka yi mata ba,amma itanma in son samu ne,ka jinkirta har a kawota gidanka,in ka yi mata a wannan lokacin bazan ce maka don me ba,saboda na san ka fini iko da ita.." Hamood yace "Alh ai ba sai anyi haka ba,a ganina we are one yanzu,tsakanina da ku bai dace nayi abu ace min don me ba,saboda Allah ya haɗa zumunci tsakaninmu,sannan idan kace lallai sai an dawo da kyautar da na riga nayi,gaskiya bazan ɓoye maka ba bazan ji daɗi ba.. Ayi haƙuri don Allah na yi abu ba tare da na nemi shawara ba,amma haka bazai sake faruwa ba in sha Allah.." Duk yadda Baba yaso Hamood ya fahimceshi a mayar da kayan Hamood bai amince ba,saima nuna masa da yayi babu abunda zai faru da iyalinsa bare ya janyo gurɓacewar tarbiyya,haka nan dai jikin Baba a mace kuma ba don ya so ba ya yi masa sallama ya katse wayarsa. Kwanakin da suka biyo baya basu yiwa duk wani rai dake gidansu Safwa daɗi ba,don yadda Baba ya ɗauke wuta,ganin bai sake maganar mayar da kayan ba kuma yasa daga baya kowa ya sauko aka koma kamar yadda ake a gidan tare da fara shiri tuƙuru. Abunka da kuɗi ke magana,cikin satin maganar bikin Safwa ya gama bazuwa ciki da wajen GRA,al'amarin da ya bawa mutane da yawa mamaki,har ya janyo wasu daga dangi suka fara cecekucen dalilin da yasa akasa ranar bikin haka a taƙaice,Baba dai haƙuri ya bawa ƴan uwansa kawai don shi kansa ya so asa bikin ya kai ko da 1 month ne,amma ganin yanda Umma ta dage ita lallai sai a bar bikin haka,hakan kuwa aka yi don dole ta sha kansa yayi shiru aka shiga hidimar biki gadan²,don Hamood ya sake musu bakin account yadda suka so kawai Umma suke yi da dukiyarsa...

         '''#Shin me za ku iya cewa game da halin Umma da abunda take aikatawa? Baba ya yi abunda ya dace as uba ko bai ba?'''

             _#Wow anjad! That sleepy writing spirit in me had wake-up Habibaatiiy.. Kuyi min addu'ah kada ya sake komawa baccin nan har mu kai book ɗin nan inda ya dace.. U know akwai book ɗinku na *MAƘUNSHIN GISHIRI!* Da kuke jira right? Da mun sauke wannan in sha Allah zai dawo gareku,and zai zo muku da nasa salon,bazan kwaɗaita muku alƙamina ba,wanda suka sani sun san salon kowane labarina yana zuwa ne daban. Right?_



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Continue Reading

You'll Also Like

20.2K 321 30
She has the cutest daughter and perfect, caring boyfriend. Until he cheated on her and her life collapses. She lost faith and trust. But she soon get...
36.8K 1.6K 21
In this ff,Kaira love eachother alot....but suddenly due to some reason naira lied to Kartik that she betrayed him.......what will happen now....read...
76.7K 11.7K 74
~BOOK 3 IN THE DESIRES SERIES~ STARTED. ON 20-JANUARY-2021 FINISHED. ON 15-OCTOBER-2021 #1 in mothers. On. 7-08-2021 #1 in introvert...