TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter 1

723 46 3
By KhadeejaCandy

*©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠*

SHIMFIDA...

“Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min liyi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi...
Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna...”

TA ƘI ZAMAN AURE...
Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da daure kai. Wata kalar kaddara ce mai rikitarwa, shimfida ce dake lalaye tafiyar wasu daidaikun mata....

Tafiya ce ta irin matan da duniya ta canja musu zane, suke da wani rufaffen sirri a zuciya! Sai dai kadan daga masu ilmi ke fahimta. A cikin rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa shim kun ankara da haka?

Mabudin kowace kofa makulli ne sai dai wannan kofar a balleta ne ta kasa, sai shigar cikinta ta kasa yi ma mai dakin dadi.
Al'umma sun kasa yi mata uzuri iyayenta  sun kasa fahimta, mazajen kuma sun kasa riko...! Uba na gari jigo, sai dai ita bata dace ba, miji na gari gimshiki a nan din ma dai bata dace ba, kuma duka laifin yana komawa zuwa gareta ne.... Duniya ta yi mata juyin masa, ta yadda ta kasa banbance fari da baki, ji da gani sun mata nisa,  albishin daya take jira... mutuwa...!

Masoyana Assalamu Alaikum Khadeeja Candy ke muku sallama tare da fatan na same ku cikin aminci da kwanciyar hankali.
         Gani dauke da wani sabon labari kuma ina fatan zai kayatar da ku fiye da sauran. Labari ne akan NOOR da rayuwarta da iyalan gidanta.
Labarin nan kirkiren labari ne idan yayi daidai da rayuwar wasu ko wata to arashi aka samu. Za ku fi samunsa a AREWABOOKS @KhadeejaCandy

Ranakun posting. Monday - Friday

Chapter 1

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

Tasss muka ji sautin saukar mari, irin marin da zai iya kurmantar da mutum a take. Na kai hannuna da sauri na dafe kuncina hawaye na sauko min. Hana ta rufe fuskarta ta fashe da kuka, kamar yadda Mama ma take kukan marin da Abbah yayi mata.

“Abun da na ga damar badawa kenan idan kin ga dama ki zubar daman baki taba godewa ba ai baki taba godewa ba idan na yi miki abu, kullum cikin kuka kike kuma a cikinsa zaki kare Hajara...”

Ba a iya fatar baki yake mata fadan ba, sai da ya hada mata da duka yana harbin kafafuwanta har sai da ta fadi. Da gudu na nufi gurin da take ina kuka, sai dai kamin na tabata sai ya fisge ni ya jefar a kasa.

“Abbah dan Allah ka yi hakuri”

Na fada ina kokarin tashi na sake nufa gurin da mahaifiyata take. A madadin yayi hakuri sai ya kara rufeta da dukan kamar ana kara masa karfi, ya saba idan ya fara dukanta sai ya canja mata kamannin sannan yake barinta, dukan mahaifiyarmu a gaban idonmu wani abu ne da Abbah ya saba yi, tun muna kanana har girmanmu, agaban kowa zai iya fada mata magana marar dadi, idan kuma ta yi masa ba daidai ba baya duban mu ko a tsakar gida zai iya rufe ta da duka, mu kuma muka kasa sabawa da halinsa. A kullum idan yana dukanta na kam ji kamar ni yake duka zubar hawayena suka fi nata yawa domin ko bayan abun ya laba na kam kebe na yi kukan abun da Abba yake mata.

“Dan Allah Abbah ka yi hakuri...”

Na sake fada ina kwantawa ta inda yake shurinta domin na tare mata, sai ya hada har da ni yana shurin har sai da yayi mai isarsa sannan ya kyale mu ya fice daga gidan. A nan na samu damar tashi na rika Mama ita ma ta tashi, da taimakon Hana  muka kaita daki, karfi hali irin na Mama muna shiga dakin sai ta yanke kuka da take ta share hawayena ta dubu mu ni da kanwata Hana ta ce.

“Kar na ji wani ya fadawa Yayanku abun da ya faru, musamman ma ke Noor kin fi uban kowa baki”

Ta nuna ni saboda ni suke cewa na fi rawar kai da surutu.

“Wallahi Mama ba zan fada masa ba”

Hana ta fada, ni dai na yi shiru domin Allah ne kadai ya sani ko zan iya rike kaina ban fada ko kuma na fada, ya danganta da yadda abun ya tsikare ni. Waje mu ka fito ni da Hana mu ka cigaba da aikin gidan, ita take wanke wanke ni kuma ina shara sai da muka gyara gidan tsab sannan Hana ta fara shiga ta yi wanka bayan ta fito ni ma na shiga na yi wanka na fito mai kawai na shafa ma zauna a kan katifarmu har sai da ta gama shiryawa ta fita sannan na bude durowarta na dauko doguwar rigarta na saka na dauki bakin dankwali na daura, na san zata yi masifa dan haka na shiryawa komai ma. Ina fitowa waje ta hau da masifa na saka mata gown na je na cire.

“Wallahi ba zan cire ba, tufafina duk sun yi datti haka kike son na zauna sirara a gida ko kuma so kike na saka mai datti ko kuma na Mama zan saka, duk masifar da zaki yi sai dai ki yi amman ba zan cire ba”

“Noor ki cire min tufafi kin ga kullum kin fi son mu yi masifa har ana jin mu makota ko? Mama ta miki magana ki daina taba min kaya ba zaki daina ba ko?”

Na marairaice mata fuska.

“Ki yi hakuri daga wannan ba zan sake ba”

“Kullum ai haka kike cewa daga wannan ba zaki sake ba kuma ba zai hana gobe ki sake din ba”

Ban san lokacin da na watsa mata wani kallon banza ba.

“Wai ke Hannatu baki gajiya da masifa ne kamar tsohuwa kullum cikin bala'i”

“Allah ya raba ni da bala'i ai ke kika ja, kullum sai kin yi abun da za ayi magana”

A raina na yi tsaki na nufi karkashin inuwar mangoro na zauna ina ta hararata, bata dai kula ni ta cigaba da karatun, ni kuwa sai aikin gyara rigar dake zubo min nake daman jikin ba daya ba kayanta sun min yawa ta fini kiba da tsayi idan muka jera wani sa'in ma sai ace ita ce  yaya ni ce kanwa, daman kuma tsakanina da ita wata goma sha uku ne.

“Mtscheeeeeeee bakar masifa tufafi ya mata yawa amman sai ta saka, ko kunya bata ji a ganta da kayan kanwarta”

Daga inda nake zaune nake jiyo ihunta duk da ba ni take kallo ba na san da ni take.

“Ai bala'in neman zuwanki duniya ne ya hana ni kiba, gashi nan Mama tana fadar yadda na sha wahala kamar ba zan rayu ba saboda ke, ko gama shan no-no ban yi ba kika karbe azzaluma”

Kyalkyalewa ta yi da dariya ta kalleni domin ta fahimci a bakin gaskiyata nake maganar.

“Mahaukaciya, daman can ba jikin kibar ne dake ba, ke da aka haifa da wata bakwai ma Allah ne ya so ki Wallahi da yanzu baki duniyar ma”

“Yen yen yen yen... Fuska kamar agwaluma sai baki kamar zunubi”

Na fada ina yamutsa mata fuska, a madadin ta ji haushi sai ta sake kyalkyalwa da dariya tana girgiza kai. A karo na biyu na sake watsa mata harara na dauke kai ina kallo kofa domin na san lokacin dawowar Yaya Nabil ya kusa ko ma nace yayi. Ashe kuwa na canka daidai kamar jiran ake na maida ido a gurin sai gashi ya shigo rike da yar ledarsa kamar na tashi da sauri na tarbo shi, ni ce mai binsa kuma ni ce mai karba duk abin da zai shigo da shi gidan a kullum saboda na san kayan dadi yake kawowa daga restaurant din da yake aiki.

“Sannu da zuwa Yaya Nabil...”

“Yauwa ina Mama?”

Ya nufo gurin da na tashi ya zauna sai na zauna kusa da shi ina fadin.

“Tana daki tana bachi”

“Bachi lafiya?”

“Tun dazun ma take bachin fadan da suka yi da Abbah ne sai ta yi bachi”

Hana ta bude yana kallona.

“Ahhh ke kam kin ji haushin rayuwa Noor kin ji haushi kin shiga uku”

“Toh ai dai ba fada masa na yi nace ya doketa ba, ko kin ji na yi maganar dukan da yayi mata ne? Munafuka me zuwa lahira da kokon dambu”

Ta ja tsaki ta tashi ta nufi dakin Mama, yaya kuma ya jefar da hular ya mike tsaye zuciyarsa na cika.

“Wai Abba yaushe zai daina wannan halin ne? Wai yaushe zai fahimci Mama ta kai matsayin da ya kamata ya daina dukanta, ba zan iya jurar wannan abun ba, gaskiya na gaji, Wallahi ba dan yana ubana ba ba zai saka hannu da doki Mama na bar shi da rai ba, wannan wane irin rayuwa ne...”

Fada yake sosai kana kallonsa zaka san ransa ya bace, daman haka yake hawa idan ya ji abun da ya faru, idan kuma yana gidan tarewa yake baya taba yarda hannun Abba ya kai hannun Mama. Yana cira kafa ya nufi dakin Mama ta fito Hana na bayanta kana gani kasan ta kitsa mata munafurcin abun da na yi, ni kuma ba wai na yi ne dan bana jin maganar Mama kawai dai na fada masa ne saboda mu taru mu yi bakincikin a tare, ai shi ma yana daga cikin iyalan gidan ya kamata komai ya faru ya sani.

“Noor wai ke wane irin kunne ne da ke, me ke motsi a kanki?”

Na sauke kaina kasa domin ban san kalar amsar da zan bawa Mama ba, daman can ko ban yi laifi ba ganin laifina take balle kuma Hana ta kitsa mata munafurci.

“Me na fada miki?”

“Cewa kika yi kar na faada masa”

“To yanzu me kike yi?”

“Fada masa na yi”

“Wane gargadi na yi miki?”

Na dan turo baki gaba na mike tsaye na tsaya bayan Yaya Nabil, domin karamin aikin Mama ne ta riko ni ta fara duka a gurin.

“Cewa kika yi kar na fada, sai kuma na fada”

“Toh ya miki kyau, yau sai kin ci ubanki a gidan nan”

Na yi saurin ba bayan yaya ba tare da na dandana abinci da ya dawo da shi ba, na fito kofar fita gidan na tsaya a nan rai a bace san tun da Mama tace sai na ci ubana sai na ci duka ko wani hukuncin mai tsanani kuwa.

“Ka dawo ya aikin?”

Magana take da Yaya Nabil tana kokarin zauna a gurin da na tashi. Daker ya amsa mata da Alhamdullahi ya nufi dakinsa ni dai ina tsaye a bakin kofar jiran kawai nake na ga ta taso na auna a waje. Ina kallo suka cinye jollof din da Yaya ya zo da ita har da nama Mama bata ba ni ba saboda kawai na fada masa abun daya faru.

“Mama yanzu kuwa cinyewa kuka yi? Ina kallo ku hana min?”

Ina maganar hawaye na silalon min a ido domin abun yayi min bakinciki. A take Mama ta kara min da kalamai masu zafi.

“Ba kin zabi munafurcin, zaki ci ubanki ai kuma karki fasa ki cigaba ko zaman aure sai ya miki wuya Noor saboda wannan halin naki”

Ni dai ban sake cewa komai ba na nufi gurin da Hijab dina yake rataye na dauka na saka talkamina na fice daga gidan. Gida uku na wuce sannan na shiga na hudu da ya kasance gidansu kawata Zee. Sallama na yi aka amsa min na gaishe da Mamanta cikin mutunci sannan na tambayi kawata.

“Umma Zainab na nan?”

“Zainab bata dawo ba, ta tafi gurin bikinsu Salwa na dauka ke ma kina can?”

“Aa ni bana da kudin abun hawa kuma nesa za'ayi event din shi yasa na ce sai dai gobe idan za'ayi kamu sai na tafi”

“Gaskiya ai ya kamata ki tafi kam, Salwa ai kuna mutuncin sosai idan baki je ba ba zata ji dadi ba”

Na zauna a gurin na karbi kayan miyar da take gyara na cigaba da gyara mata ina mata hira. Daman mun saba na kan zauna na yi hira da ita fiye da yadda nake yi da Zainab ma, sai dai duk yawan surutun da suke cewa ina da shi ban taba fada mata labarin gidanmu ba domin na san a inda surutun nawa yake. Sai da gama na nika mata a blender ta sannan na ari wayarta, na shige dakinsu Zee na kira rabin rayuwata Zafeer.

“Hello babyna”

Na yi dariya mai cike da shuki da jindadin yadda ya gane ni dince tun kamin ma na yi magana.

“Ya aka yi ka gane?”

“Da zarar na ga bakuwar number ko an yi min fulashin ko an kira na san Matata ce”

“Toh ka kira kar mu cinye katin wayar Maman Zainab ce”

“Baby Noor me kai ki ga wayar Maman Zainab kuma?”

Na bata fuska kamar yana gaba jin yana kokarin kara min bacin rai bayan wanda aka saka min a gidanmu.

“Zainab bata nan kuma ina son jin muryar ka what do you expect then? Kasan Yaya Nabil ba zai ba ni wayarsa sai idan na sata”

“Calm down Baby is okay bari na kira yanzu”

Na yi murmushi na kashe wayar, haka yake rikicewa idan ya ji raina ya bace ko kadan baya son damuwata. Few seconds da yanke kiran ya kira ni na amsa na kara a kunne na kwanta a kujera ina murmushi.

“Zafeer ka dawo school?”

“Na dawo ina gurin aiki ma”

“Zafeer na so?”

“Me zaki yi a nan”

“Na gan ka kawai”

“Aa nan gurin aikina ne Babe Noor be kamata kina zuwa ba sai da dalili, anjima ai zan shigo sai mu ga juna ni ma na yi missing dinki”

“Okay”

Na amsa shi sai ya dauko wata hirar ta soyayya mun kusa minti talatin muna wayar sannan ya muka yi sallama yana ta tsokana ta da ce min amaryarsa. Bayan mun gama wayar na fito waje na yi alwala na shiga dakin da na fito na yi sallah ban daga daga kan sallayar ba Umma ta kawo min shimkafa da miya a plate har da spoon da ruwa. Aiko na gyara zama ina godiya da Allah yayi min sakamakon da abincin da Mama da hana min gashi na samu shimkafa da miya my favorite. Rabi na ci na sha ruwa na dauko plate din na fito waje na samu murfi na rufe.

“Gida zaki je da shi?”

Sai na juyo na kalleta a kunyace domin ban yi tsammanin tana daga bakin kofarta zaune ba.

“Zauna ki ci, idan zaki tafi sai na zuba miki a cooler ki kai musu”

“Aa daman rufewa zan yi kar na bar abincin a bude saboda na koshi...”

Ta yi dan murmushi domin tasan karya nake, plate biyu ma zan iya zama na cinye balle plate daya, kibar ce kawai babu amman cin abinci nake sosai kamar yar yunwa.

“Ke Nooriya zauna ki cinye abincin, nan ba gidan bakuncinki ba ne, Idan zaki tafi zan zuba miki wani nace, ni kike kunya ko kuma su Zainab da basa gidan?”

A kunyace na zauna waje na cinye abinci tass sannan na aje plate dinta. Sai ta tashi ta shiga kitchen dinta ta zubo min wani abincin a madaidaiciyar cooler ta rufe ta miko min na karba ina godiya kunya na lullube ni, da ma Zainab dince ba zan ji kunya ba amman mahaifiyarta ai da nauyi.

“Na gode Umma”

“Babu komai, ina wayata kin gama da ita?”

“Eh tana dakin su Zainab a can na aje”

“To zan dauka idan kin je ki gaishe da Mamanki”

“Zata ji”

Na juyo na nufi kofar fita har lokacin kunya nake ji, ina fitowa gidan na lullube abincin da Hijab, ko kofar gidanmu ban kalla ba na wuce na mike hanyar har na fita kwararon gidanmu na kama hanyar titi, daga unguwarmu zuwa unguwar da Zafeer yake aiki babu wani tazara mai yawa, dan haka da kafa na taka har gurin aikinsa yana hango ni ya aje karfen dake hannunsa ya taso ya nufo inda nake da mamakinsa a fuska.

“Baby i thought mu yi magana ba zaki zo ba”

Na dan yi fuskar shagwaba kamar zan yi masa kuka.

“Abinci na kawo maka fa...”

Na bude hijab din sai kular da na boye ta bayyana. Ya saka hannu biyu ya karba da sauri yana kallon fuskata da manyan idanuwansa masu tsananin fari da kyau.

“Ban sani ba I'm sorry... Na kusa tashi ma wacan motar kawai zan yi ma faci sai na tafi, zo ki zauna ina gamawa sai mu tafi gida”

Shi ya fara wucewa gaba ni kuma na bi bayansa har muka isa gurin motar ya bani cooler na rike shi kuma ya shiga yi ma motar faci. Ta gilashin motar da ya kasance baki nake kallon kai na ina gyara girata da ta yamutse, ba zato ba tsammani aka fara zuke gilashin motar har aka saukeshi kasa, ban taba zaton akwai mutun a cikin ba har sai da na yi arba da wata kyakkyawar matar da nake kyautata zatin budurwa ce amman ta girme ni nesa ba kusa ba, irin yan matan nan yayan masu kudi masu ji da kamsu.
Murmushi ta yi tana gyara zaman katon gilashin dake idonta.

“Wannan kanwarka ce?”

Matar da tambaya kamshin turarenta na fitowa dake cikin motar da kida yake tashi a hankali. Zafeer ya dago ya kalleni yana mikewa tsaye.

“Aa....”

Ni kuwa na yi karaf na tare numfashinsa na ce.

“Eh ni kanwarsa ce”

Zafeer ya kalleni da sauri sai daga masa gira.

“Yaya zan aje abincin a can”

Shi dai mamaki ya hana shi ce min komai har na juya na nufi gurin da yake zama na aje abincin, juyowar da zan yi sai ganinsa na yi a bayana.

“Me yasa kika ce haka Baby Noor”

“To ka sani ko sonka take yi, baka ga mai kudi ba ce”

“Idan tana so, me hakan zai kare ni da shi”

“Sai ta rika baka kudi”

“And...?”

He asked still confuse.

“Sai ka aure ni..”

Murmushi ne abun da ya biyo bayan mamakinsa sai ya girgiza kai ya juya ya koma gurin motar, ni ma na bi bayansa ina murmushi ina tsaye gefensa yayi mata facin ya gama, sai ta cire gilashin idonta ta miko masa 5k. Tana masa wani kallo kamar wata rikakkiyar karuwa.

“Gashi you can keep the change”

A take na ji ana kirkira wani abu mai kamar wuta kamar garwashi a zuciyata.

“Na gode”

Ya furta sannan ya juyo ya kalleni.

“And wannan matar da zan aura ce In Shaa Allah, so ba kanwata ba ce I'm her fiance an mana engage da ita shekara uku da suka wuce”

“Wow Maa shaa Allah Allah ya sa alheri”

Ta fada sannan ta rufe gilashin motarta ta yi mata key ta kama hanya. Na dube shi

“Me yasa ka fada haka? Gashi har ta baka kudi mai yawa ma tun yanzu”

“Ta saba ai duk lokacin da ta zo kudi mai yawa take badawa, and ni bana jiran kudin wani na kusa kare karatu kuma ina wannan aikin waya san me zan zama nan gaba? Ban ga amfanin yin karya ba saboda na ci kudin wani, and be kamata na boyewa kowa a alakarmu ba i love you so much ban ga dalilin da zai saka na boye alakarmu a guron wani ba, you're my life Noor ke tawa ce har abada”

Cikin tsakiyar idanuwana yake kallo yana kitsa min maganar da ta dade da zaunawa a zuciyata. Na yi murmushi wutar sonsa na kara huruwa a zuciyata.

“Mu tafi gida Zafeer”

“Jira ni a nan zan bawa oga kudinsa sai mu tafi, i love you”

Ya kashe min ido daya tare da yi min blow kiss. A gurin ya bar ni sai da ya bawa ogansa kudinsa ya dauko kayan aikinsa da cooler da na kawo masa abinci muka kamo hanyar gida muna tafe muna hira. Har muka shigo unguwar mu dabam tsakanin gidanmu da gidansu gida biyar ne a tsakani sai dai be shiga gidan na su ba duk da Kasancewar ya fi kusa har sai da ya rakani har kofar na mu gidan sai da na shiga sannan ya juya.





#KhadeejaCandy

Continue Reading

You'll Also Like

1.5K 73 13
KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not worry, for it was all destined...at what...
1.1K 70 23
Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She finds her self begging in the middle of the...
22K 1.2K 31
Labarin wata matashiyar budurwa 'yar hamshaƙin attajiri me murɗaɗɗiyar AƘIDA, Tace So imagination ne da ɓata lokaci katsam.......... 😜 find out in A...
53.6K 3.1K 50
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...