AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.5K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
92
91
94
93
95
96
98
99
END

97

270 17 4
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITE'S FORUM* ✨

       ✨ *G.W.F* ✨
______________________
GORGEOUS WRITER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_______________________

CHAPTER 97

"Meya fusata Ishaq?naga yanayinka ya canza lokaci ɗaya kake kuma  neman daukar fansa a kansu?"hmmm Badamasi tabon da Sunusi yamun yafi naka,Sunusi yamun tabon da bazan taɓa mancewa da shi ba.

Yasa nakoma tamkar jemage cikin tsuntsaye ban iya nafita ko nan da can da rana ba,saide ko da dadare,ya maisheni matacce a idon duniya dama ahalina baki ɗaya,ya rabani da kowa nawa ya rabani da dangina da kowa nawa yasaka iyalina shiga duniya ba tare da wani nawa yasan inda suke rayuwa ba.

Ya mai dani tamkar wani dabba cikin keji harna tsawon shekar takwas kafin nasamu wasu bayin Allah suka kuɓutar dani,Badamasi nasan Sunusi beyi maka koda kwatan abunda yamun ba,daga taimakon sa ya zama Yarona wanda nafi aminta dashi nabashi dukkan yardata yaci amanata ya wulakanta mun rayuwata taya zan manta dashi mutumin daya saka rayuwata cikin garari wani irin hukunci kake tunin idan yashiga hannuna zan masa hmmm yasauke ajiyar zuciya,zuciyar sa tana masa ƙuna tamkar wuta naci a cikin sa,idanun sa sun canza launi a yanda suke sun koma jaajir dasu a take yanayin sa ya canza zuwa na zallah ɓacin rai tamkar wani ɓakin ƙumurci haka yake huci,dukan su dasuke zaune a falon sun tsorata da yanda yanayin sa ya canza lokaci ɗaya ya cigaba da magana cikon wata murya mai amoo yace ba kashe shi zanyi farat ɗaya ba,idan na kashe shi farat ɗaya ko na damƙashi ga hukuma wannan baze saka na huce taƙaicina ba,zanfi so da kauna kafin ya mutun sai nayi wasa kura da rayuwar sa sai ya rasa komai daya tara sai duniya ta juya masa baya sannan ne hankalina ze kwanta bayan nasa ankaishi gidan ɗan kande dan ya girbi abunda ya shuka.

"Ina bayanka zan kuma tsaya dakai harsai wannan burin naka yacika sai munga bayan su,Ahmad ya faɗa shima Faisal miƙewa tsayen yayi yana cewa"ina bayanku harsai munga bayan waƴan nan azzaluman.

"Sai mun ruguza wannan azzalumar ƙungiyar da yarda Allah ina tare daku ɗari bisa ɗari inji Baristar Anwar dake zaune,murmushi Janar ɗan Musa yayi irin tasu ta manya yana mai cewa"nima ɗin baxa'a barni a baya ba ina tare daku harsai munga karshen su,gyaran murya Alhaji badamasi yayi hankulan su suka maida kansa musƙutawa yayi ya gyara zaman sa ya fuskance su yana cewa"kafin ku tunkari waƴan nan mutanen kuna bukatan runduna.

"Ba runduna muke bukata ba"basira da iya taku Ahmad ɗin ya bama Mahaifin nashi amsa"kamar ya fa?Alhaji badama yasake tambayar ɗan nashi dan neman karin bayani.

Gyara tsayuwa Ahmad ɗin yayi ya fuskanci Mahaifin nashi da kyau yace"Plan shiri muke da bukatan yi ba yaƙin fito na fito zamuyi dasu ba,zamu tsara yanda zamu lalata musu komai nasu ba tare da sunsan mu ne ba,koda kuwa zasu san mune sai mungama dasu komai ya ƙare musu sannan zamu bayyana kanmu da kanmu gare su,kafin sannan kai kana bukatan kaje ka huta.

"Wani irin hutu kuma zanyi Ahmad bayan kana ganin abunda yake shirin tunƙarata,karfa ka ɗauka dan anyi zaman kotun farko ka dauka komai ya wuce a wajen su,idan baka manta ba ai yanzu ɗan jarida yagama fada maka shirin su a kaina shin kana tsammanin zasuyi baccine su manta dani bayan burinsu be cika a kaina ba.

Murmushi Faisal yayi yana cewa"eh to nima de haka nagani amma idan munkai ka Asibiti ka kwanta a can zaka huta,zamu aje jami'an tsaro na fararen kaya,waƴan da zasu baka tsaro dakuma saka ido akan duk wasu masu shige da fice,ka kwanta a can ka huta kasha vitamin C,koda sun zo gunka idan abu yasoma kwaɓe musu kanuna haryanzu kana tare da su,ka kuma cigaba da nuna tsoron nan da kake da shi akan abunda ya shafe su.

"Lalle Yarana sun girma sunyi hankali sun kuma san takan tsiyar maganin xomon zamani sai karen zamani Allah yadafa muku yashige muku gaba yamuku jagora"Amin Ammin mu suka amsa baki ɗayan su sannan ta kalli Ishaq tace"inason maka albishir"fuska a sake ya amsa mata da"ina sauraronki Hajia Ma'arufa Abdul-jabbar da mamaki duka suke kallon sa barin ma su Ahmad ya 'akai wannan mutumin yasan complete sunan Ammin sa haka shiko Faisal beyi mamakin jin sunan Ammin abakin sa ba,dan Anty hajia ta taɓa ce masa kakannin su ƴaƴan maxa suke duk da bata faɗaɗa masa ba.

Ɗiyarka Aisha ai surkuwata ce Matar ɗanka Ahmad,ba Daddy Ishaq ba hatta da Alhaji badamasi saida yashiga shock da maganan nata,Janar ɗan Musa baki a buɗe yake kallon Ammi shiko gogon naku ƙasa yayi da kansa cike da jin nauyin mutumin shikan sa Daddy Ishaq yayi mamakin jin wai Aisha tana da Auren wani akanta,ko sanda su Alhaji Sunusi suka saka ayi kidnaping ɗinta duk da tabashi labarta masa yanda suka rayu bayan bashi da barin gida da sukai dama garin baki ɗaya irin yanda Anna tasha wahala akansu da yanda sukayi rabu da Anna hatta da zaman ta A gidan Anty hajja da aiki da take a companyn Ahmad ɗin bata ɓoye masa komai ba,sai na auren ta da Ahmad ɗin.

Gwauron numfashi yasauke yana cewa"ikon Allah yanzu dama wannan shine surikin nawa?amma Mamana bata faɗamun tana da Auren ba ko sanda na haɗu da ita"to ko a sa'in ba a daura musu Auren bane cewar Ammi,sai kuma tace dama kahaɗu da itane kafin sannan?kuma ta gane ka?amma mesaya bata faɗa mana ta ganka ba?"Ma'arufa baki canza ba ko kaɗan a yanda nasanki yawan tambaya to yanzu wanne zan amsa miki daga ciki kin cikani da tambayoyi kamar wata ƴar jarida.

Dariya suka saka"duka zaka amsa"to ni nace karta faɗawa kowa ta ganni ciki kowa harda khadija saboda tana cewa ta ganni dole yaran su bukaci ganina,ni kuma banaso mutane su sani saboda farautar rayuwarta da akeyi,dan a sa'in ruwa ajallo Sunusi da Yaransa suke nemana ya bazasu ko ina,kuma banason saka rayuwarsu cikin hatsari sunyi rayuwa batare da sanin ina raye ba,banaso wani abu yasame su ta dalilina yanzu kinji amma nayi mamaki da bata faɗamin tana da aure ba.

"Inaga kunyar faɗa maka takeyi Daddy Faisal ya amsa masa da cewa haka,shiko Barista Anwar cewa yayi"kunya kamar wata ƴar 80c dariya baki daya akayi banda Alhaji badamasi da kunyar duk ta da baibaye shi wai ɗiyar Ishaq ɗansa Ahmad ke aure kaji ikon Allah aure daya dinga ikirari na wucin gadi ne sai gashi Allah yayi ikon sa akai ashema ƴar ɗan uwane a gareshi Allah ƙadiran alaman yasha yarinƙa kira a ransa.

**********

Tun barin Fauza wajen  koda tashiga ɗaki zama tayi daga bakin gado tana mai tariyo fuskar matar da tagani saide duk yanda taso ta wassafa wannan fuskar bata Annan ta bane ba,nutsuwa tayi tana mai tariyo hoton matar da tagani dakuma tariyo yanayin muryar,tabbas ba Annata bace ko shekara dubu tayi ba taganta bata tsammanin zata iya mantawa da ita balle ƴan wasu watannine ko Mubaraq dayake ƙaramin cikin besa yamance kamannin ta ba balle ita data mallaki hankalin kanta,to ita ko wannan ɗin wacece?
Meyasa zuciyar ta taƙi amince mata da Anna ta gani,wai ma yama'akai mutumin nan yasan da ɓatan Anna,ko bana tare da Mahaifiyata ba wanda yasan inda take kuma ina bukatar ta atare dani?ya'akai ma yasan ta harya iya samo vedion ta yakemun nuni da bata cikin nutsuwar tana bukatar taimakona.

Kode yana bibiyarki ne wata zuciyar ta amsa mata eh bibiyarki yake dan son  sanin komai naki dan cimma wata manufa nashi ta daban,idan ko hakanne lalle akwai aiki a gabana kode nafaɗama Ahmad ne ko shi ze iya ya taimaka mini,to shi Ahmad din kinsan kowaye Alhajin a wajen sa tunda ya daukoki ya ajeki cikin gidan sa ai baki isa yin komai ba saide kawai ki masa biyayya kawai ko baki samu komai ba wajen sanin ko shidin wayene zaki tsira da takardun kadarorin Mahaifinki idan kika samu kika dauka zaki iya guduwa a gidan dan tsiratar da rayuwarki.

Ajiyar zuciyar ta sauke da ta gamsu ɗari bisa ɗari da shawarar da zuciyarta ta bata,saide kuma waze taimakamun dan ganin burin nan nawa yacika waye waye wayeee?

Tawani jaa ye ɗin da karfi "nine wanda ze taimakeki dan ganin kin cika burinki yafaɗa daga bakin ƙofa tsaye yake ya rungumi hannunsa a saman ƙirjinsa ya zuba mata idanun sa masu ƙwarjini,batasan adadin wani lokaci ya ɗauka tsaye a wajen ba,muryan shin kaɗai da taji ya sakata neman ruɗewa.

"Karki ji shakkar faɗamuni damuwarki Eashow baki da kowa a nan sai Ni nimaɗin kusan bani da kowa saike karkiyi la'akari da yanda mukai aure ko abunda auren namu ya ƙunsa,kafin wa'adin sa yacika ina tare dake da daɗi babu daɗi waye shi?yayi tambayan da yakusan sakata ruɗewa.

Me yafaɗa miki?

kode barazana yamiki?

Batada wani zaɓi da wuce tafaɗa masa gaskiyarta koda ze cucetane bata sani,batasan sanda tafashe masa da kuka ba,tana rufe da fuskarta da tafin hannun ta.

"Yi kukan ki ba mai hanaki inde yinsa shi ze saka kiji sanyi a zuciyarki,saide inaso kisani ni Ahmad bazan taɓa barin wani abu yasameki ba,a shirye nake dan ganin na cika miki burin ki dan ganin nasadaki da Mahaifiyarki matukar tana a doron duniya, sannan inaso na faɗa miki na haɗu da Abbanki yau saurin ɗagowa tayi ta kalle shi da hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta,jinjina mata kansa yashiga yi ta yarda da abunda yace mata ɗin tunda saninta dashi shi mutum ne mai tsayawa akan gaskiya baya kuma magana biyu yakan tsayane kan magana ɗaya tak idan har yafurta to kuwa ba ze taɓa canzawa ba kuma duk duniya ba wanda ya'isa sakashi canzawa sai ko Amminsa ko Alhaji badamasi wato mahaifinsa duk da babu wata shaƙuwa sosai a tsakanin sa dashi amma yana bashi girmansa da darajashi matsayin sa na Uba mahaifi gareshi, cigaba yayi da cewa ,yafaɗamun komai gami da barin sa gida da irin zalunci da cin amana da akai masa,nakuma yi masa alkawarin tsayuwa abayan sa harsai duk wanda yake da hannu cikin wannan zalunci da akai masa ya amshi hukuncin sa daidai da abunda ya aikata,yanzu ke faɗamun waye shi wanda yake miki baraza da....sai kuma yayi shiru.

Poitin tayi masa da can ɓangaren masu gidan"Mami ce ko Alhaji?

Jinjina masa kanta tayi"Alhajinne da kansa yashigo harnan inda kike yamiki bazaranan ko saida kika je can ɓangaren nasu yasumu zarran yimiki magana.

Shiru tamasa sai ajiyar zuciyar datake saukewa tama kasa bude bakin ta balle tayi masa magana haka kawai taji  bakin nata kaman an saka mata super glue an liƙe.

Sai kokari take dan ganin tamasa maganan take amma kuma ta kasa faɗa yanda sukai da Mami harma da shi kansa Alhajin amma takasa bude baki,sai kawai ta ɓige da cemasa"dama yunwa nakeji tun ɗazu banci komai ba.

Girgiza kansa yashiga yi dan yafahinci ba wannan taso faɗama masa ba,tallaɓota yayi yasaka ajikinsa sosai yasaka babban yatsan hannun sa yana shafa lip ɗin ta dashi yana kuma hura mata iska daga bakin sa yace"ba wannan maganan wannan ɗan ƙaramin bakin sukaso faɗamin ba,amma tunda rowa akemun ba'ason nasan sirri nabari amma fa bawai dan na yarda ba,yanzu de taso muje naciyar da Baby na idan kinci kin ƙoshi sai aramawa kura aniyarya ko?

Bata gane me yake nufi da ramawa kura aniyarta dayace ɗin  ba,itade burinta tasamu taci abincin inde yazo mata fashi da harwani dishi dishi take gani saboda tsaban yunwada takeji,dan haka bata ce dashi komai ba,illa kawai falo data fito ta tadda ashe harma take away yayi musu saida taci abincin ta ƙoshi sannan ta tuna ashe ko sannu da zuwa bata yi masa ba.

Ɗan ƙasa tayi da kanta cike da kunya tabuɗe bakin ta a hankali tace"Oga sannun ka da zuwa ya hanya.

Shi har dariya taso bashi amma ya gumtse yayi kaman ma bejita ba,ya cigaba da latse latsen wayan sa yana tunanin yanda ze ɓullowa lamarin akwai abunda Na Allah bayaso shi Ahmad yasani game shi,to me nasaka yarinyar da batasan komai ba aciki,yarinyar ko kanta bata gama sani ba,yarinyar duka rayuwarta tayitane cikin ƙunci da maraici ta dan samu freedom a yan watan nin kuma yakeson saka rayuwar ta cikin wata ƙangi bazan taɓa barin haka yafaru ba,nima ina da target a kanka kuma sai ya bari yayi murmushi aransa yana cewa zakayi kuka da idanun ka wallahi idan  na setaka.

Ya dade yana latse latsen wayan sai can yaɗago ya kalle ta yace"ke haka kikaga Anty hajia tana tarɓan mijin ta idan yadawo gida?dafe baki tayi tana waro manyan idanun ta masu haske akansa miƙa mata hannu yayi alaman tazo gareshi cikin sanyin tafiyar ta tamiƙe batare da ta kama  hannun daya maki mata ba,ta tako a hankali tazo ta zauna ɗan nesa dashi ta tsunƙuyar da kanta tana wasa da zoben azurfa dayake yatsan ta .

"Matso kiga wannan abun ina bukatar nutsuwarki da hankalin ki baki ɗaya,kaman tace bazata iya bashi hankalin ta ba amma saboda ƙwarjinin dayake dashi a idanun ta yasa ta kasacewa dashi komai saima matsowa da tayi kusa dashi ɗin,wayan da yake riƙe a hannun sa yamiƙa mata yace yashigo nan minti uku da shigowar matar sa tafita ta barshi da ke,barazana kawai yake maki besan inda Mahaifiyarki take ba,soyake yayi amfani dake dan cinma wata manufa tasa ta daban.

Kallon wayan takeyi sosai kuwa suɗin ne,dawani abun mara kyau tayima da yanzu yagani,ina ya'ajiye camera cikin falon nan bata sani ba.

Kaman yasan abunda take tunani yace mata"karki dami kanki da sai kin san inda cameran yake kawai inaso muyi magana dake na tsanake,kai kawai ta iya ji jina masa dan zuwa yanzu lamarin mutumin yadena bata mamaki tsoro yake bata mutum sai kace wani aljani.

So nake daga gobe zaki koma cikin gidan dazama zaki binciko mana wasu takardun kadarorin Mahaifina acikin ɗakin maigidan sannan zan baki camera ki dasa  inda hankalin mutum ba zekai kai ba.

Sauran tsarin zakiji daga baya"Mahaifiyata tafurta a hankali,sakeyin ƙasa tayi da kanta tana tsiyar da ƙwalla tace Uwa fa tafi gaban komai meyasa kowa yatashi kansa kawai yasani me yasa kowa cikan burinsa da muradin sa kawai yasa gaba.

Taya zan yarda dakai alhalin kafaɗa musu cewa Auren wucin gadi mukai kana jiran samun wani abune daga gareni karabu dani,wannan shi yazo yace Mahaifaiyata tana tare dasu yakuma nunamun halin da take ciki na neman agaji daga gareni yanzu kai kuma kazomun da kanason na dauko maka takardun kadarorin mahaifinka,ni tawa Uwar ko oho"Eashow ya kira sunan ta da karfi.

Ɗaga masa hannu tayi cike da tsuwar tata data bari a ƴan kwanakin nan ta dauko ta haɗa da arowa kanta jamurumta tace"ba sunana kenan na,hakan na nuni da cewa bakin ku ɗaya idan na daukoma abunda kake nema shima nabashi kaina ina shi kenan ko.

Wai meyasa ku masu ƙuɗin nan bakuda tausayin na ƙasa daku ne?"me kuka ɗauki talaka bayi suyi muku aiki ku biyasu su bauta muku shi kenan basu dawata amfani dayawuce haka a wajen ku.

Mesaya kukeson maidani abun wasanku?

Waye shi?

Wace alaƙace tsakaninka dasu ɗin dan ban yarda da kai bama ni yanzu.

Kuma aina kasan Mahaifina?meyasa kukeson amfani ni da bayanai na wajan son cimma manufa naku?

Wai mesaya kullum sai ni.

Sake fashewa tayi da kuka ta haɗa hannun ta waje ɗaya alaman roƙo tace na haɗaka da girman Allah kamai dani Kano banason zama anan ɗin idan na cigaba da zaman nan ɗin zan iya bashi rayuwata kaman yanda ya bukata ni kuma bazan iya hanawa ba saboda Mahaifiyata,zan iyayin komai saboda ganin na cetota daga halaka.

"Komai fa kikace Eashow are you mad yafaɗa a zafafe,maida masa da amsan tayi itama azafafen"eh komai idan nace komai ina nufin komai harda mutuncina...kafin ta idasa faɗa taji saukan mari a ƙuncinya yana nunata ɗan yatsa idanun nan nasa ya kaɗa yayi ja jir yace"ni kuma zan kashe duk wanda yayi yunƙurin shiga gonata daga haka ya hankaɗata tafaɗin ƙasa yasa kai yafita a falon cikin ƙunan rai.

Ganin yafita itama sai tasake fashewa dawani sabon kuka tana cewa"nide naga ta kaina wai meyasa haka yake faruwa da nine kode ni ɗin ce bani da rabon rayuwar farin ciki kaman ta sauran mutane,me yasa kowa yake neman cika burinsa akaina,wayyo Allah wani wace iriyar rayuwace wannan mai kudi vaya tausayin na ƙasa dashi mesaya mutane kaman waƴan nan suke neman saka rayuwata a halin ha'ula'i menake dashi banda rayuwata danake da menake dashi da suke neman ƙarasata kafin wa'adin Allah yacika akaina.

Wayyo Anna ina kike ina kika shiga ina bukatarki kusani Anna ina kewarki Annata wayyon Allah wayyo mamata wayyo Abbana haka takwanta a wajen tayi ta kukan ta tana sambatu.

"Faisal bazan iya ba bazan juri wani banza mushiriƙi yashiga gonata wallahi wallahi kode yatsan hannun ta yayi gigin taɓawa saina guntule yatsan,idan ko yashiga gonata wallahi sai na yanke mazaƙutansa,yafaɗa cike da ɓacin rai a muryansa,daga ɗaya ɓangaren ko Faisal dinne dayake kan waya yashiga bashi hakuri yana kwantar masa da hankali akan tayi hakuri yabi komai a hankali Aisha ai yarinyace ƙarama shekarunta vazasu iya daukan wannan temp...kit yaji an datse kiran.



ALLAH YASA MUDACE.

Continue Reading

You'll Also Like

192K 38.6K 57
Becca Belfort i Haze Connors, choć przez swoich znajomych zmuszani do spędzania razem czasu całą paczką, od dawna się nie znoszą. Dogryzają sobie prz...
640K 66.9K 26
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...
2.7M 150K 43
"Stop trying to act like my fiancée because I don't give a damn about you!" His words echoed through the room breaking my remaining hopes - Alizeh (...
1.8M 141K 63
"ရှင်သန်ခြင်းနဲ့သေဆုံးခြင်းကြား အလွှာပါးပါးလေးကိုဖြတ်ကျော်ခါနီးမှာမှ ငါမောင့်ကိုစွန့်လွှတ်တတ်ဖို့ သင်ယူနိုင်ခဲ့တယ်၊ လူတွေက သံသရာမှာ ရေစက်ရယ်၊ဝဋ်ကြွေး...