59

178 12 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

CHAPTER 59

   Fizge wayan hajia mariyah tayi daga hannunta tana kallonta cike da fushi tace"amma anyi shashashan yarinya wallahi bakiyi kuka a gidan ubanki ba sai ga gadin miji tunma kafin kishiga wannan idan kuma kin shiga ciki yakenan?

Faɗawa tayi jikin umman nata tace"dan Allah mummy kiyi wani abu wallahi ina sonsa zan iya yin komai saboda shi,bansan abunda yasa yatsani har haka ba wallahi mummy dan Allah koke zaki gwada kiransa a waya ki bashi hakuri yaxo ya fiddani kunya.

Kallon baki da hankali tamata sannan ta juya ga Alh dake hakimce tawatsa masa wani muguwar harara tace"wallahi Alh kabani mamaki har yaushe zaka biyeta ka zubar da ƙimanka ga wannan yaron mara kunya da besan mutuncin na gaba dashi ba,idan kai bega  girmanka ba ai yasan girman uban da ya haifesa kai kuma kana da iko da uban nasa kira ɗaya zaka masa kafin nan nikuma yanzu zani wajen mai charbin ƙwai ba matarsa ba har uwar da ta tsuguna ta haifesa inaga sai yanance sunan ta bare wata mata tashi kishare hawayenki  jeki kici gaba da shirinki zuwane kaman yayi kai kuma sai ka amshi wayan kakira uban nasa dolene ya turasa.

Daga haka tasa kai yafita daga falon tana magana da ƙawarta hajia shema a waya kan su haɗu a hanya dan zuwa gidan mai charbin ƙwai.

****
Aisha ƙudundune take cikin duvet tayi luf tana sauraron yanda kanta ke sara mata ji tayi anyaye mata lulluɓin saurin runtse idonta tayi dan duk a zatonta ta ɗauka anty malika ce da tun ɗazu ta dameta data tashi ta wanke bakinta koda tea ne tasamu tasha saide tsaɓanin tunaninta jin ƙamshin turaren sa"oya tashi yafaɗa mata muryar sa ba wasa ciki miƙewa tayi zaune dafe da kanta dake barazanar rabewa biyu.

Amshi nan miƙa mata kufin hannunsa yayi ɗan kauda kanta gefe tayi zaki karɓane ko sai namiki ɗaure yanzu yafaɗa da kakkausan murya,tura bakinta tayi tana ɗan mutsu mutsun kaman mai magana oh zagina kikeyi ko?

Sake tura bakin tayi batare data amsa masa ba,wayansa ne yayi kara hakan yasashi fita daga ɗakin bayan ya dire mata da kofin tea yana cewa minti goma nabaki ina jiranki kisame ni waje karki kuskura nasake shigowa nasamu baki shirya ba,daga haka yasaka kai yafita yana amsa kiran.

"Assalamu alaikum daddy barka da warhaka yafaɗa kaman yana kallon sa cike da ladabi.

Madadin daddy ya amsa masa sallamar sai cewa yayi"to sannu ishasshe nace sannu ishesshe tun daga nan ya fahinci inda daddyn nasa yadosa dan haka cike da zolaya yace"Alhaji wai lafiya kuwa irin wannan fusatan haka kasanfa ni yau nake ango dan yanzu haka ina shirin kai surukuwarka wajen ƙunshi gashi naga kaman...."dallah rufamun baki wanda besan inda yake masa ciwo ba,yanzu Ahmad saboda Allah ga inda akeson yima gata amma kaɓige da shashanci"wai Alhaji mai akace nayine?

"Yanzu kaman Alh sunusi yakira yana neman alfarman yau kaɗai kaje wajen taron yarinyar nan kona minti goma amma ka iya bude baki kace masa bazaka ba wai....katse mahaifin nasa yayi yana cewa"daddy dama saboda wannan kka fusata nifa na mijin mata biyune Alhaji yakare magana cike da zolaya.

Jin abunda yake fadin yasake tunzura Alhaji badamasi sai faɗa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba karshe yarufe da cewa kashirya anjima karfe bakwai na dare kutafi kodasu khalid ne wannan umurni nake matsayina na mahaifinka idan ko kaki tafiya to wallahi ran uwarkane ze ɓaci dan nasan ita ke zugeka.

saka Amminsa ciki yasa shi yaruntse idonsa cike da ɓacin rai zuciyarsa na masa suya can yace"Alhaji tun tuni munyi da ita bazan halarci ko wani irin taronsu ba,kuma ta amince sannan kuɗina ko kwandala na bazeyi ciwon kai ba"ai idan naka beyi ciwon kai ba ni nawa sunyi dan duka party goma da sukayi nina ɗau nauyin bakwai daga ciki kama daga abunda zaci awajen da abun sha da biyan kudin hall da zasu gudanar da taron kai harma da makaɗa da za gaiyato duka"yanzu Alhaji a wannan marran dakuma halin da kake ciki shine...."dakata mun Ahmad yakatse sa cike da fushi wai kaine ka haifeni ko nine na haifeka?

AUREN WUCIN GADIजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें