93

313 14 2
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

     ✨G.W.F✨
________________________
GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITTER'S WE ARE THE BEST AMONG THE REST.
_________________________

CHAPTER 93

"Waye ta sake cewa a hargitse bata kallo mutum amma tanajin yanda hannun mutum ke yawo a sassan jikinta Hasbunallahu ya Allah tasake cewa da karfinta tana kuka da rarrabuwan murya,ihun nata ne ya tashi Ahmad da bacci ya ɗauke shi bada jimawa ba.

Da gudu yayo ɗakin datake haryana tuntuɓe da kujera,swich ɗin ɗakin ya kunna take haske ya gauraye ɗakin zaune take saman gadon duk ta ruɗe ta ɗimauce da sauri ya nufi saman gadon idonta a kulle suke"lafiya?Aisha yace da ita sanda ya'isa bakin gado,zaburowa tayi ta rungumeshi ta ɗaura kanta saman ƙirjinsa wani irin yamm yamm yakeji cikin jikin sa ji yake jinin sa na tsinkewa.

Kaman giftawan mutum ya gani zameta yake ƙoƙarin yi daga jikin nasa dan yaleƙa yagani sake riƙeshi tayi tana cewa dan Allah karka tafi ka barni tsoro nakeji,kaman yanda jikinta ke ɓari haka ma zuciyarta ke bugawa very fast bata cikin nutsuwarta daka ganta kasan a matukar tsorace take dan haka bashi da zaɓi daya wuce sakata  a jikinsa yana tofa mata addu'a har yasamu bugun da zuciyarta yake ya daidaita hakama jikin nata yadena ɓarin da yake sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai har yasamu bacci yayi awon gaba da ita.

Ƙura ma kyakkyawar baby face ɗin ta ido yayi kaman yau yasoma ganin ta,tana da sassanyar kyau amma mutum baze gane tana da kyau daga kallo ɗaya da zemata harsai ka tsaya ka nutsu sannan zaka gane hakan,a fuska idan ka ganta zakace bata da hayaniya amma fa wannan ɗan ƙaramin bakin nata bade tsuwa ba,idan ka cijeta saita rama bata barin ta kwana rashin tsoronta inde muddin akan gaskiyarta ne yana burgeshi dan mutum komai girmansa idan akan gaskiyar bazata yi shayin gaya masa ba.

Ajiyar zuciya ya sauke yakai hannun sa yana gyara mata gashin ta daya barbaxu saman fuskarta saboda tsorata da tayi,maida a kalan tunanin sa yayi kan waya tsoratata?kode har yanzu Alh na Allahn ne be hakura ba duk da abunda yasame shi?idan ko shine lalle za suyi ba daɗi dashi,dan baze bari a taɓa mutumcin ɗiya mace yana gani ba balle kuma ace matar sa ta sunna.

Sosai ya tsunduma cikin tunani kaman wanda aka mitsina yayi zumbur ze mike sai kuma yatuna da ita a jikin sa,fasa tashin yayi yana mai komawa ya kwanta ƙwanyarsa fal tunani sako da aka aiko masa jiya inda yake cewa Abun harin ka yana kusa dakai kusa sosai fa,to waye wannan GAGARA BADAU ɗin nan da har mahaifin shi ya gwammace yin shiru koda ze rasa rayuwar saboda kawai su surayu,waye shi?aina yake da zama?wa yake kusa dashi?suwaye mutanen nan biyu daya gani tare da Alhaji na Allah har ɗayan yake cewa dashi suna da hannu jari amma mai yasa Alhaji na Allah aikoma mutumin da sakon mugun kallo daya sakashi yin shiru dole akwai ayan tambaya a kansu amma kafin nan bari ya tuntuɓi Faisal yaji yanda ake ciki,waye ya tsorata Aisha yanzu?kode har yanzu Alhaji na Allah be hakura ba kenan.

ALHAJI SUNUSI

Ya kalli barrista rai a ɓace yace"wai kai ya ina gabas kana yamma ne"Alhaji ina jin fa kaman baka gane abunda yake cewa bane cewafa nayi da kai Barrista Anwar ɗan fodio ne ke riƙe da case ɗin nan Alhaji be taɓa yin Case ya faɗi ba,kowa fa tsoron karawa dashi yake a Court"to sai me shima Alhaji sunusi ya tare masa numfashi da cewa idan yakawo hujjarsa kai ma saikai ƙoƙarin kawo naka hujjan wanda ze rushe nasa"hmmm Alhaji harfa yanzu ina ga baka gane abunda nake son faɗa maka bane.

Rai a ɓace yasake cewa"kaga barrista idan ba zaka iya ba sai in nemo wani abu na kuɗi kuma ha'an,ritsinar da kai barrista Tafida yayi yana cewa"Alhaji abunfa bakaman yanda ka ɗauka bane shi shari'a tsabanin hankaline kuma dan bakasan waye Barrista Anwar bane tunda yake be taɓa faɗi a a Court ba,har yau basamu wani Barrista wanda yakara da shi yayi winning ba,hhhhh dariya sosai Alh sunusi yayi saida yayi mai isansa sannan ya ɗago ya kalli Barrista Tafida ido cikin ido yace"ka kaddara cewa kaine mutum na farko da zekaishi ƙasa ka kaddara kaine mutum na farko da zakayi breakin record nashi sai mun ɗaukakaka sai munsa kazama abun kwatance"Allah ko Alhaji da ko naji daɗi yafaɗa yana murmushi cike da farin ciki daya kasa ɓoyewa a fuskansa"idan har kayi yanda muka saka mai ze hana Alhaji sunusi yamaida masa da fadin haka.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now