AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
92
91
94
93
95
97
98
99
END

96

223 12 1
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

     ✨  *G.W.F*✨
_________________________
Gorgeous writters forum we are the best among the rest.
_________,,_______________

CHAPTER 96

Bakinta na rawa kar kar kar yanda laɓɓanta ke rawa kawai zaka kalla kasan cewa tana cikin halin ruɗewa"Annata tana raye kuma kasan inda take zaka sadani da ita da gaske?

Jinjina mata kansa yashiga yi dan tabbar mata da abunda yake faɗi,riƙe masa ƙafanta tayi tashiga rasgar kuka tana mai cewa"dan Allah ka sadani da ita ko kafaɗamun inda take ni zani da kaina dan....katseta yayi yana cewa"kwantar da hankalin ki zaki cigaba da rayuwa tare da ita idan kinaso,saurin amsa masa tayi da"eh inaso dan Allah tana ina faɗamun inda take.

Kwantar da hankali yarinyar zaki ganta ne matukar zakiyi abunda nace kuma bazaki tsaɓa abunda nace miki ba.

"Zaka sameni dayi maka biyayya akan abunda kace matukar zaka sadani da Annata saide zanyi maka koma meyene matukar be tsaɓama Allah da ma'aikinsa ba,idan ko yatsaɓa faɗin Allah Alhaji saide kadauki hakuri dan bazan aikata saɓo ba"koda zaki rasa Mahaifiyarki datayi sanadin zuwanki duniya takuma sha wahala daku duk da ƙazafin da akemu ku  keda ƙannenki?ya tambaya yana mai tsareta da idanun sa mai kaman na mujiya.

Jinjina masa kai tayi cikin nauyin baki data zuciya tace"ƙwarai kuwa ciki harda rasa tawa rayuwar nasan Allah yana tare damu kuma be manta damu ba,ta amsa masa cike da kwarin gwiwa jifanta yayi da wani shu'umin murmushi sannan yace"kwarin gwiwarki ya birgeni saide kafin ki yankewa kanki hukunci kan rashin amincewa da bukatata kalli wannan videon.

Ipad dayake hannun sa ya shiga shawafa sai yamiƙa mata,da fari ƙin amsa tayi saida yamata alama data karɓa sannan ta karɓa hannun ta yana rawa tashiga kallo ai bata iya kaiwa karshe ba,ta zube saman gwiwarta ta haɗe hannunta gu ɗaya alaman roƙo idonta na tsiyayar da kwallah tashiga bashi hakuri.

"Alhaji dan girman Allah kayi hakuri zanyi duk abunda kace amma dan Allah kace su barmun Annata wallahi zanyi yanda kace rayuwarta tafimun komai a duniya zan iya sadaukar da tawa rayuwar dan ita ta rayu cikin salama,da wani irin dariya yafashe mai ban haushi sai kuma yashiga cewa"zaki rayu cikin farin  farin ciki da salama da yardar mu zakiyi albarka.

Duk da zuciyarta a cunƙushe take dan ganin abun da yanuna mata tana kuma jin zafin halin da taga Mahaifiyarta ciki duk da bata ganin fuskan Matar sosai amma taji a zuciyarta zata iyayin komai dan ta ceto rayuwar ta"saide da yardar Allah de bada taku ba"eh komade me zakice kizama cikin shiri nan da kwana biyu zan nemeki dan jin inda mukatsaya a maganan tamu,ganin yana batun fita daga falon yasata tayi saurin katseshi tace"dan Allah kamun wata alfarma mana?''alfarma ta mecece?ya tambayeta yana tsareta da idonsa masu tsoratata ƙasa tayi da kanta tana maijin tsoron yanda ze ɗauki bukatata cikin sanyin murya tana maisake yin ƙasa da kanta tace"ko zaka bani Annata naji muryarta koda sau ɗayane"ba yanzu ba harsai kin cika sharuɗan mun kafin na sadaki da ita yana kare faɗa mata haka yayi ficewar sa daga falon yana mai jin daɗi a ransa ganin nasara tana tunkaro shi.

Yana barin falon Aisha ta fashe dawani irin kuka mai ban tausayi na kewar Annan ta abunso da kaunanta,idan ta tuna halin da ta ganta yanzu ta cikin wayan saita sake fashewa da sabon kuka"me kikayi musu? suwaye sukayi miki haka?waye wannan da rannan yakira sunanki muka gudu da yayi sanadin rabuwarmu?ya rusa mana ɗan farin ciki da muke da ita,waye waye?ya Allah Ya rahman Ya rahim ya quddus Ya salam kabamu salama acikin rayuwar mu ka kawo mana ɗauki ka agaza mana idan wani lefin iyayena suka maka ya Allah kake hukuntasu da wannan yarabbi ina rokonka ka yafeme su kakawo mana dauki ka agaza mana ja karemu daga sharrin masu yinta,sharrin mutune ko na aljanu ko ta dabbobi,haka ta kasance ta dauki lokaci mai tsawo tana addu'a tana zubda hawaye.

"Na haɗu dasune a wata seminar a garin Abuja mun dauki tsawon sati biyu dasu harde nayi ɗan sabo dasu ranan wata laraba da yamma da bazan mance ba bayan mun tashi daga wajen taron suka biyoni har matsaukina a nan suka zomun da bukatar su ta son haɗa hannun dani wajen sarrafa magani dan suma sunaso jaharmu ta arewa ta amfana da su,da farko naƙi amince musu da bukatar da suka zomun da ita sai sukai ta kawomin misalai iri iri suka kuma bini da roƙo da magiya harde na amince zamu fara harkar nan dasu amma ban amince musu saka hannu jari da suke nemi sakawa ba.

Nade amince musun ne amma nace sai nayi tunani da haka na rabu dasu,ban kuma sake bi takan maganan tamu dasu ba,har tafiya ta kamani zuwa ƙasar China inda na dauki wata shida kafin dawowata kaman dama jiran zuwan nawa suke inda suka sake taso da maganan wannan karon ba Sunusi kaɗai bane harma da Alhaji Na Allah dama Alhaji Surajo kai tsaye naki amincewa da tayin nasu,dakyar de na amince shima din dan ganin Alhaji na Allah tare dasu dayake shi na Allah abokina ne tun na yaranta tare mukai makarantar secondary da shi nasan shi.

Saide abunda ni bansani ba,su bata yanda suka zo mun da magana haka yake a gunsu ba suna ha'intata ba tare dani nasani ba,suna amfani da mazubin maganin mu suna safaran miyagun ƙwayoyi saida muka ɗauki a ƙalla wata biyar a haka bani da masaniya kan abunda sukeyi ranan wata litinin da baxan taɓa mancewa da ita ba a rayuwa ta ina zaune a cikin Office ɗina sai ga Manager na yashigo bayan yanemi izinin shigowa na bashi sai da ya zauna saman kugera yana fuskantata niko ganin yaƙi cewa komai na ɗago daga abunda nake na dubeshi ina cewa dashi"Malam Adamu ina fatan lafiya kashigo bakace komai.

Saida yasauke gauro numfashi sannan ya ajiyemun mazubin Roba da muke amfani dashi wajen zuba capsule na kalli Roban sai kuma na ɗago kai ina kallon sa dan neman karin bayani.

"Ka gafarce Alhaji ka dauki wannan Roban ka duba da kanka shin da sanin ka ake wannan ta'asar a wannan Company ko rufa rufa sukai maka?

Bangane abunda kake magana a kai ba malam Adamu nace dashi turamun Roban yayi zuwa gabana yace dani kaide ka ɗauki wannan abun kagani.

Ba karamin kaɗuwa nayi ba da abunda na gani ɗin,ɗaukan Roban nayi na nufi guest house ɗin Alhaji na Allah inda nayi sa'an samun su su duka a waje da zuwana nawurga musu Roban ina cewa dasu dama abunda kuke aikatawa kenan a Company na bansani dama kunsan irin abunda kuke aikatawa shine kukaimun rufa rufa kuna cin dunduniya ta batare da nasani na ba.

To wallahi ƙaranku zanyi kuma daga yanzu na sauke ƙwantiragin dake tsakanina daku,basu tankamun ba saida nakai  aya sannan suka kalleni cikin halin ko in kula da rashin damuwa a saman fuskokin su suka shiga mun dariya sannan Alhaji na Allah ya kalleni yace"yanzu kai Badamasi saboda wannan ɗan abun katashi hankalinka ai na ɗaukama ranace ta ɓaci mana da rashin damu saman fuskansa yake magana yakara da cewa yanzu de zauna zamuyi magana dakai.

Zama nayi ina huci bayan na ɗauki Roban nasaka aljuhuna saboda kafa hujja in bukatar hakan ya tashi,ruwa mai sanyi Alhaji Surajo yabani cikin glass cup ina shan ruwan bansake sanin inda kaina yake ba saide tashi nayi na ganni kwance a wani ɗaki saman gado ba tufafin komai a jikina,yana kaiwa nan da maganan sai ya fashe da matsanancin kuka kaman wani karamin. yaro da jin yanda yake kukan kai kasan abunda yafaru da shi yaƙuna masaa marai ainun kuma ba abune mai daɗin faɗa ba,,ruwa Janar ɗan musa dake zaune kusa dashi ya mike masa karba yayi ba tare da ya musaba yasha"na gode yace yana sharan hawayen sa"ko zamu ɗage zaman zuwa wani lokaci na ga kaman kana bukatar hutu"cewar Janar"No wannan shine lokaci daya dace ya fada mana komai dan musami bakin zaren inji Ahmad dayake tsaye tun sanda Baban nashi yasoma magana,murmushin karfin hali Alhaji badamasi yayi sannan yace"ai ko baka ce ba nima din bazan saken barin ku cikin duhu ba,nasan Ammin ka tajima tana zargina da aikata ba daidai ba.

*******
Tana nan turƙushe saman gwiwarta kaman mai neman gafara tajima ahaka kafin ta lallaɓa tsunmar rayuwarta tashiga ɗaki koda tashiga ɗakin ma rasa abunyi tayi takasa taɓuƙa komai wa kanta ashe dama kowa yasan Aurwn wucin gadi Ahmad ɗin yayi da ita,ta tabbata bmara hankali tanama mutanen nan kallon Biri suka ashe kallon ayaba suke mata,ashe shiyasa Hajia Mami ta nace sai takoma zama cikin ƴan aikin gidan ashe da dalilin ta nayin haka ashe shiyasa Fauza ke mata wani gani gani ashe da abunda suke kullawa,ina kallon kaina ina da wayo ashe wayon banzan gareni dana bari yarabani da budurcina ƙimata yarabani da masoyina na gaskiya ashe ashe haka tayi ta magana ita kaɗai a ɗaki bayan fitan Alhajin daga ɓangaren su.

Tana nan zaune tsaban yanda takejin zuciyarta na mata suya hatta da hawayenta neman su tayi tarasa burinta yanzu a duniya be wuce ta ceto Annan ta ta dauketa suje can inda ba wanda yasansu su rayu da ƴan ƙannenta cikin farin ciki kaman yanda suka gina rayuwar su daa can cikin soyyar junan su da kaunan junan su.

Tana nan zaune tana ta tukka da warwara aka kira sallan La'asar tashi tayi ta lallaɓa tashiga toilet ɗin da ke cikin ɗakin tayi fitsari tare da ɗauro alwala tafito tayi sallah tana nan zaune tana addu'oin ta taji anyi sallama a falo fitowa tayi tana jan carbi,binta da kallo tayi ganinta tsaye ƙiƙam tana zuba mata ido itama zuba mata nata idon tayi ba tare da tanƙa mata ba,yarinyar da suka shigo tare da alama ita tayi sallamar ta ajjiye mata wata kula da alama abinci Mami ta aikota dashi,tana ajewa ta juya ta fita itade Aisha kallon su kawai take dan alamun yarinyar yanuna kaman a tsorace take da Fauzan da suke tare"ƴar rainin hankali jira kike sai na gaisheki?

Cike da faɗa taje howa da Aisha tambaya,kallon ta tayi ta watsar saida tanemi wajen zama ta zauna dan bazata iya dogon tsayuwa ba saboda juwa dake neman kadata,sannan ta amsa mata da"Rabin naki.

"Ni zaki rainawa hankali ina tambayanki zaki wani ce rabin nawa waye Ubanki a garin nan wallahi idan bakiyi hankali ba sai na saka an sakaki a inda baxa makiga Rana ba balle iska ƴar matsiyata sai wani holoƙu da huhhura hanci kike.

"Idan kin gama zan iya komawa ciki dan ban karasa addu'a da nake ba nafito kinsan zama ba addu'a hatsarine ga ire iren mu masu ƙananun shekaru saboda neman kariya daga sharrin tsoffi data yara,sai ta kanne mata idon ta ɗaya tace ina fatan kin gane.

A matukar fusace tabude baki da nufin tayi magana sai kuma tayi shiru komai ta tuna oho
fuuu ta juya tafita daga ɓangaren ita kaɗai tana tafe tana magana dama sai da nacema Mami baxani ba amma tanace sai naje din garinta nan ai, tana shiga falon tayi cilli da ƴar yalolon gyalen dake kanta tace"dama saida nace miki bazan je ba amma kika matsa sai naje to ai gashi nan yarinya da bata wuce ƴar aikina ba take neman yimun rashin kunya.

"Kai Fauza banson hayaninya fa,yanzu ita Aishan har wuyanta yayi kaurin da zata gaya miki magana acikin gidan nan keda gidan Uban ki,gyaɗa mata kai Fauzan tashiga yi sai kuma tace"Mami wallahi Yarinyar nan ƴar rainin wayoce ko gaisheni fa Mami batayi ba danayi mata magana ma sai cewa tayi wai Rabin nawa"ita Aishan?

Zumbura baki tayi tana cewa Mami kaman baki yarda da abunda nace ɗin ba?ai dama saida nace miki ba zanje ba kika nace naje shiyasa naje idan ba haka ba kema kinsa ko kallo wannan Yarinya bata isheni ba balle muyi musayan ƴanwu da ita"na yarda dake mana shalele kawai mamakin karfi halinta nake,bama wannan ba ince wancan munafukar matar yayan naki bata wajen nata ko?

"Bata nan Mami nina rasa wace iriyar mata Yaya ya auro mana mace bata da aiki sai munafinci da iyayi dan ma ɗiyar ƙawarkice ita.

Ran Mami ya ɗan sosu da maganar ɗiyartata ɗan cunƙushe fuska tayi tace"kinga Fauza tashi ki shige ciki muna maganar arziki dake kinzo zaki ɓata mun rai ni narasa mai Alhaji yake nufi da a kai mata abinci har yana wani cewa a tabbar taci kar arinƙa barin ta zama da ƴunwa to me tafaɗa masa bayan barina wajen.

"Mami magana kikene?
Fauza data zauna tasoma latsa latsan waya ta jeho ma Mami da tambaya"ba magana nake ba waƙa nake aikin kenan kullum baki da aiki sai latsa waya shekara hudu kika ɗauka kin kasa saye zuciya mutum ɗaya koda soyayyar wucin gadi ce kuyi kin kasa wannan sai tarin majina a kai ba basira balle dabara sai tarin girman kai idan abun yamiki zafi saide kice Mami kiyi wani abu akai amma kee sai ta yarfa hannu Ahmad ɗaya ƙwallin ƙwal kinkasa jan hankalin sa gareki"Maami ta kira sunan ta da karfi.

Alhaji na Allah

Kallon sa Alhaji Sunusi yayi yace"kana ganin wannan Yarinya bazata kawo mana matsala a wannan tafiya namu ba?

Saida ya kurɓi juice mai sanyi dayake riƙe dashi a  hannun sa sannan ya ɗago da kallonsa garesu yace"ina ai ta tsorata sosai da videon da ta gani na nuna mata,dan ma baka yanda ta zube ƙasa tana kuka da neman alfarma na haɗata da Uwartata ba.

"Kace mun kusa kawo karshen  Al hakk hmm ya sauke numfashi sai kuma ya cigaba da cewa ni Sunusi tamkar mutuwa nake bana ma abu kallo biyu matukar namasa kallon tsanake.

"Hmmm Sunusi kenan bansan abunda yasa kake yarda da kanka dawaba,kaima kasan wannan basiran tawace ba taka ba,cewa Alhaji na Allah daya kure Alhaji Sunusi da ido.

Ma'arufa kiyi hakuri nasan ban kyauta miku ke da yaran mu ba,matsayina na wanda yake da hakki a kanku ba,kuma ban baku soyayya data dace wa  ƴaƴa matsayina na Uba garesu ba,na zama tamkar Raƙumi da akala sai yanda akai dani,na zamo tamkar driver dake riƙe da sitarin Motan sa juyata yake yanda yaso.

Nazama tamkar na'aura sarrafani ake bani da katabus sai abunda suka daurani akai kuyafeni,koda zan rasa komai dana mallaka na dukiya ciki harda rayuwata Janar Ahmad Faisal da Barrista da kai Hantsi ɗan jarida inaso kukawo karshen su Allah sunusi inaso kafin nabar duniya naga faɗiwar su inason ganin tsoro ruɗewa a idon su kumun wannan Alkawarin.

Daddy Ishaq ne yamiki tsaye yana cewa"inde wannan ne karkaji komai Sunusi shiyafara wasan saide mune waƴan da zamu gama,Sunusi sai najaka a ƙasa saman titi sai duniya tasan ainin waye kai sai na ɗauki fansa ta akanka.

ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

9.5M 628K 75
An Arranged Marriage Story. #1 Hot (17-11-23) #1 Happyending (17-11-23) #2 Shy (13-11-23) #3 Cold hearted (27- 10- 23) POWER!!!!! That's what he alwa...
2.7M 150K 43
"Stop trying to act like my fiancรฉe because I don't give a damn about you!" His words echoed through the room breaking my remaining hopes - Alizeh (...
3M 201K 51
" Do not be mistaken little flower, you are mine and mine alone. Any man who looks at you longer than three seconds will be dealt in a manner I find...
473K 44.8K 33
She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful She is innocent He is cunning She is broken He is perfect or is he? . . . . . . . . JI...