AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
92
91
94
93
96
97
98
99
END

95

217 14 0
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨GORGEOUR WRITEF✨
        ✨G.W.F✨

ƳAN UWANA INA MAI NEMAN AFUWAR KU NA JINA SHIRU DA KUKAYI,TSAWON WANNAN LOKACI IN SHA ALLAH HAKAN BAZE SAKE FARUWA BA.

CHAPTER 95

Kallon sa yake cike da mamakin ya'akai yasan Abokan nasa kusan ruɗewa yasoyi amma saboda bayason yabada kansa gaban yaran sai yayi kokarin daidaita kansa yana kallon su kaman yanda suma shiɗin suka zubawa ido danson ƙarin bayani kan abunda wannan baƙon yake cewa ganin yaƙi cewa komai yasa Ammi cewa da su Fadwa su tashi sushiga ciki.

Bayan barin yaran wajen Ammi ta kalle sa tace"Alhaji ka bude baki kiyi magana ko za sami bakin zaren nasani kasani Alhaji sunusi shine ummul haba isin komai dake faruwa shi kama alkawarin bazaka bude bakinka ka ambaci sunan ko ɗaya daga cikin su ba"Ma'arufa yakira sunanta da karfi cikin ɓacin rai yakuma daura da cewa zaki rufamun bakin ki yanzu anan ko sai na ɓata miki rai.

"Ai raina yadade da ɓaci Alhaji me kake gudu me kake tsoron faruwa wanda be faru  ba,inaso kasan wani abu guda wallahi koda farshen ɗaya daga cikin ƴaƴana ne ya karye ta sanadin ka bazan yafe maka ba,sai ta fashe da matsanancin  kuka.

Rarrafawa Ahmad yayi ya rungumi Ammin nasa yana rarrashin ta"Ahmad nayi shiru tsawon shekaru naxama makauniya akan abunda nake ganin yana faruwa nazama kurma narufe bakina tsawun shekaru ba tare da na furta komai ga kowa ba,ina tsoron kar wani abu yasami ɗaya daga cikin ku,amma duk da haka Mahaifinka be gani ba,dubeshi so yake ya salwantar da rayuwarsa alhalin yasan su waƴanda yarufe bakinsa dan su ba barin mu zasuyi ba.

"Rayuwace muke yinta cike da makanta zuciya sonkai  cin amana yaudara,kowa kansa kawai da iyalinsa yasani ba ruwan kowa da rayuwar ɗan uwansa ya mutu ko yayi rai,rayuwa cike take da ƙalubale kaddara wata abace da Allah ya kaddara faruwan sa tun ran gini tun ran zane wasu kaddaran kuwa muke rubutawa kanmu da hannuwan mu.

"Ma'arufa yakira sunan ta da karfi"ka gafarceni Alhaji Ammina tana da gaskiya koni kaina sai yanzu wasu abubuwa suke zuwamun wanda daa can ban kawowa kaina ba,nasan zakayi mamaki idan nace na taba ganin cocaine a cikin motan ka cikin maxubin capsule harma na dauki guda ɗaya na ajiye saboda rana irin wannan.

Magana nagaba da zan iya faɗa maka a nan shine Alhaji nasan ba sonmu kake ba,kawai de mun fito duniya ka haifemu ne badan kanaso ba kuma ba yanda zakayi da mu"shut up Ahmad Mahaifin kane fa kake faɗawa irin wannan magana inji Faisal da tun shigowan sa Falon beyi magana ba sai yanzu.

"Dont shut me up Broo shima Ahmad ɗin ya juya yana maidawa da Faisal din martani cike da ɓacin rai a muryar sa,karya nayi masane daya na son mu ba ze zaɓi farin cikin wasu da namu ba,lokacin da mu muke kukan rashin sa su kuma suna zaune cikin iyalan su suna dariya.

Lokacin da muke cikin ɓakin cikin abunda yafaru damu mun haɗa kai muna masu jajantama junan mu suko suna can cikin walwala tare da iyalansu.

Lokacin da mu muke ganin duniya ta juya mana,su kuma a lokacinne suke ganin duniyarsu ta dawo musu sabuwa saboda suna ganin burukan su yacika,a lokacin da muka kasa shiga mutane muna masu jin kunya da ƙasƙan da kawunan mu,suko alokacin zasu fito suna masu ɗaga ƙawunan su sama suna masu alfari da kawunsu,lokacin da ƴan ƙannena suka kasa zuwa makaranta suyi karatu su a lokacinne ƴaƴan su kan ƙetare hazo zuwa wasu ƙasar dan yin karatu,gidan mu yakoma tamkar gidan mutuwa zama ake a cikinta tamkar zaman maƙoƙi,an samu gawa a ma'aikarsa cikin Office ɗinsa kasani yasani bashi da masaniya akan abunda ake zarginsa a kai amma ya tsuke bakin sa yayi shiru yaki cewa komai a Kotu saboda wasu can yakeson saka rayuwarmu a garari kaxo kana shuttin ɗin Up a kan me?

Bayan kana ganin yana neman saka rayuwarmu a duhu yakake sone nayi?

Baya ganin halin da matarsa Ammina tashiga ciki a ƴan kwanakin nan,kalleta kalli fa yanda Ammina ta dawo tamkar wacce mijinta ya mutu yabarta da tarin basussuka,ta koma tamkar wata mai takaba da bata da masu kula da ita,baya tunanin ya rayuwarmu zata kasance bayan bashi tare damu.

Nufo inda Janar ɗan Musa yake zaune yayi yaba riko hannun sa yace Abba dan Allah kokai zaka tambaye shi dalilin da yasa yayi shiru kode mu ba ƴaƴan da akasama ta sunnah bane idan ko ya cigaba da yin shiru Wallahi wallahi wallahi saina cinnama gidan wuta mu mutu kowama ya huta,yana karasa faɗan haka ya miƙe yanufi kofa a fusace sanin halin sa na zuciya da tsayuwa kan magana ɗaya yasa Alhaji badamasi ɗagowa da mugun sauri a matukar kiɗime,dama duk kan mutanen da suke zaune cikin falon har yakai bakin ƙofan fita daga falon cikin rarrabuwar murya Alhaji badamasi dakyar ya iya bude bakin sa wajen cewa"dakata cak Ahmad ɗin yaja ya tsaya batare da kara koda taku ɗaya ba daga tafiya da yake ba hakan kuma besa ya juyo ba,shima Faisal ƙamewa yayi daga tsaye a gun dama ya tashine dan nufin marama Ahmad ɗin baya saboda dakatar dashi daga abunda ya faɗa ɗin.

"Yaudarata sukai da farko na haɗa hannu dasu sai daga baya nazo nagane tafiyan tasu da ƙura danayi magana shine suka shiga yimun barazana ganin naƙi rissina musu yasa watarana suka ɗauke Fadwa daga Makaranta suka haɗata da Yara dasuke Safaran su xuwa ƙasashen ƙetare dakyar na samu suka bani ɗiyata nikuma tsoron abunda ze sameku yasa na zaɓi yin shiru da bakina kawai dan na ƙuɓutar daku dama ƴan uwana baki ɗaya.

"Ƴan uwanka kuma?
A tare da Janar da Faisal sukayi tambaya da mamaki,kansa kawai ya iya jinjina musu"how came?Barrista Anwar ya faɗa dan tunda ya zauna a falon ko ƙwakkwaran motsi beyi ba.

"Yanzu haka jirane suke in tona musu asiri su kaddamarma ƴan uwansa dasuke ƙauye musamman ma Mallam mai babban riga yanzu haka gidan nasu kewaye yake da ƴan daba da ƴan sara suka.

Tsit falon yayi bakajin ƙaran komai saita Ac dake falo sai ajiyar zuciya da Alhaji badamasi ke saukewa akai akai.

*********

Aisha da tunda Ahmad yatafi da safe a cewar sa ze dawo zebi jirgin yamma kasa nitsuwa tayi dan tayi kukan tayi magiyan ya tafi da ita amma duka a banza tunda yace mata da yamma ko zuwa dare ze dawo be kara ko kallon ta ba,haka yatafi.

Yinin ranan haka tayi shi sukuku kwance a ɗaki ko abinci ranan bata ci ba,la'asar sakaliya sai ga sallamar Anty Sajida ƙuƙutawa tayi ta fito falo tana kakaro murmushi ta amsa mata sallama tana nuna mata wajen zama.

Zama sukai kusan a tare Sajida tana kallon ta da murmushi tace"bade kewar Yah Ahmad ne ya sakika koma kamar wata mara lafiya ba?hmmm kawai tace tana shafa fuskarta sai kuma tace"ko daya wallahi Anty kawai yau dinne na tashi banajin dadin jikina wallahi.

Cike da zolaya Sajida tace"kode babyn mune yake wahal mana dake,wani irin zabura Aisha tayi cike da tsoro da abunda Sajidan tace karfa cikinne da ita da gaske,idan ko hakane takade har buzunta daga auren wucin gadi sai kuma daukan ciki.

Yanda tayi harsai da tabama Sajida dariya,kasa rikewa tayi saida ta dara tace"kinga wasa nake miki irin wannan tsoro haka kode baki son baby ne?

"Koma inaso ba yanzu ba,ta faɗa a sanyaye kaman zatayi kuka ganin duk tayi la'asar yasa Sajidan ce mata"nifa da wasa nake miki kawai inasone kisaki jikinki amma sai naga kaman kin tsorata,wai ma yau kinci abinci kuwa?

Sai a sannan Aisha ta tuna bata ci komai ba,ɗan yatsune fuskanta tayi tace"wallahi Anty ni saima yanzu nake tunawa ashe banci komai ba.

"Kina wasa da rayuwanki Aisha wayace miki mutane irinki suna zama da yunwa kinga bara nasamo miki ɗan abun taɓawa mai ɗan ruwa ruwa da zakiji dadin ci tafada tana mikewa tsaye dan zuwa samoma da Aisha wani abu,daidai kuma Hajia Mami tasako kai taji maganan Sajida na karshe idan kunneta beyi mata karya ba,kaman Sajida nama yarinyan nuni tana da ciki.

"Wai me kuke cewa ne?
Da ɗan tsoro a fuskokin su,suke kallon ta Aisha ce tayi karfin halin cewa"barka da yamma Mami tafaɗa tana zamewa daga saman kugera da take zaune,sai sannan Sajida tayi karfin halin cewa"yauwa Mami gwara da Allah yasa kikazo kin ganta nan ulcer ce da ita ko shekaran jiya daya tashi mata sai asibiti ta kwana shine yanzu ta zauna taƙi cin komai tunda garin Allah ya waye.

Ta dire maganan tana kallon Mamin sake tamke fuska tayi tana"idan ba munafinci ba waya hanata abinci a gidan,nifa tun ganina da ita na farko na gane zatayi munafirci in banda tasaka munafirci a ranta har nan gidan za'ace mutum beci komai ba saboda baƙin hali dason ɓatama mutane suna.

"Mami harfa yanzu"dallah rufamun baki Mamin ta katseta da cewa kinga Sajida fita idona na rufe naga kaman ke kike zugata ko?hannu Sajida ta ɗaga sama alaman ko ɗaya,to idan bake ke zugata ba me ya hanata zuwa cikin gida karɓan abinci ta zauna eh?Aisha da kanta ke duƙe tun shigowar Mami ta ɗago cikin sanyin nan tata tace"kiyi hakuri Mami amma ba ruwan Anty Sajida itama shigowarta kenan ta taddani kwance bani da lafiya amma nasha magani yanzu dama ciwon cikine da dan jiri kuma naji sauki yanzu.

Taɓe baki tayi tana sake wurgama da Aishan kallo mai cike da tsana dan ita gani take itace tashiga tsakanin Fauza da cikan burin ta badan ita ɗin ba da yanzu kila Ahmad din yace yana son a aura masa da Fauxan amma duk inda ta tafi dan neman taimako maganan ɗayace,akwai yarinyar da take rayuwarsa idan ba itace tafita daga rayuwar tasa ba zeyi wuya ya kalli wata ɗiya mace yace yanaso,tun daga sannan ta tsani koma wacece da take rayuwarsa kuma ta dauki alawashin koma wacece sai ta fiddata daga rayuwar tasa wannan dalilin yasa tashiga tafita ta fidda Basma daga rayuwarsa tana ta murna saide abunda ita bata sani ba,kaman taimakama Ahmad din tayi na cire Basma daga rayuwarsa ba karamin dadi yaji ba daya gujema auren nata kuma ba wanda yanemi yaji komai,abunda shima kansa Ahmad din besani shine Mami tayi aiki mai zafi kan wannan da wuya a sami wani daga Familyn nasu duka biyu yasake bude bakin sa yayi magana kan fasawar auren.

"Wannan itace matsalata kenan tafaɗa a fili batare da sun gane me Mamin take nufi ba,Sajida tayi saurin amsawa tana cewa"wallahi Mami Ulcer itace matsalan ta harfa alluran jijiya da ake sama masu ita na hannun nan saida aka mata.

"To naji Suda mai bakin magana ita bata da bakine saike koke na tambaya eh tafada tana mai daka mata tsawa"yi hakuri Mami tace tana fita daga sashin Aishan ba badan ranta yaso ba.

Bayan fitan Sajida Mami ta kalli Aisha da ɓacin rai a fuskarta tace"me tsakanin ki da Ahmad ɗin da xakuyi rayuwa cikin ɗaki daya alhalin ko ba muharraman juna kuke ba.

Itade Aisha batayi mata magana ba sai sake yin ƙasa da tayi da kanta,a zuciyar tana mamakin wannan matar wani irin ƙiyayya take mata ne.

Tsinkayo muryan Mami tayi tana mai cigaba da mata sababi batajin me tace da farko saboda nutuni daya ɗan ɗauketa saide jinta yanzu da tayi tana cewa,wallahi mutukar ina raye dolen ki kifita daga rayuwar Ahmad dan yafi karfinki idan ma ba jaraba irin ta marasa asali ba,me mutum kaman Ahmad ɗan dangi zeyi dake.

Kin liƙe masa sai kace wata kaska to barima kiji idan mafarki kike ki bude idonki dan Ahmad cemun yayi zaman Auren wucin gadi yakeyi dake da zaran yasami abunda yakeso ze koraki ki koma inda kika fito bar ganin ƙanwar mamarsa tana yinki ki sakankance kisaki jiki dashi kema kinsa babban goro sai magogin karfe ai irin su Ahmad sai Fauza wato ƙwarya tabi ƙwaya.

Tunda Mami tafara mata magana bataji komai aranta ba kaman yanzu da take ce mata Auren wucin gadi Ahmad ɗin yakeyi da ita da zaran yasami abunda yake nama awajen batasan sanda wasu hawaye masu ɗumi suka sauko mata daga gurbin idon ta ba.

Ƙokarin tsaida su take amma sunƙi tsayuwa saboda kukan yataso matane tun daga karƙashin zuciyarta,duk da haka kokari take wajen danne kanta karta fashe da kuka ƙasa tasake yi da kannata hawaye sai fareti suke saman kyakkyawar fuskar ta yana ɗiga saman cinyanta.

"Haba Mamin Yara ba girman ki bane wannan,yafaɗa daga bakin ƙofan shigowa falo sanye yake cikin manyan kaya kanshi sanye yake da hula damanga baƙine gajere,tunda Aisha taji muryan mutumin duk da bata ɗago ta kalli fuskan sa ba,tun randa tafara ganin sa kallon da ya jefeta dashi idan ta tuna sai taji faɗiwar gaba.

Fita waje Mami tayi da fitar ta kamar ta kaman dama jira yake ya ƙarasa shigowa ciki,ta ƙasan ido take binsu da kallo duk da hawayen sunƙi tsayuwa duk da ƙoƙarin ta na hanasu zuba da takeyi.

Kaman jiran ficewar matar tashi yake ya shigo cikin falon sosai yasaka hannuwan sa yana mai dafata ɗan jaa da baya tayi,da wani irin shu'umin murmushi da shi kaɗai yasa ma'anarsa yabita.

"Kibar zubar da tsadadden hawayen ki ƴan mata,yafaɗa yana kafeta da ƙwala ƙwalan idon sa kaman na mujiya,ita ko Aisha duk tsiwarta da rashin barin ta kwanan ta amma wannan mutumin tsoro yake bata koda muryar shine idan taji sai taji zuciyarta ya girgiza uwa uba kuma idanun sa idan ta kalla kaman zuciyarta zata faso ƙirjunta ta faɗo ƙasa haka takeji saboda yanda zuciyarta ke buga mata.

Murmushi ya sakar mata yasake bude wagegen bakin sa yace"minti goma kacal nake so ki bani na kasance dake ni kuma zan saki farin ciki na tsawon shekara goma,nasan ba abunda kikeson gani sama da Mahaifiyarki tana raye,saurin ɗahowa tayi ta zubama fuskan sa ido karon farko tun shigowan sa falon"Anna tana raye..


ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

324K 26K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
190K 15K 22
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
661K 68.4K 26
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...
215K 15.4K 20
"YOU ARE MINE TO KEEP OR TO KILL" ~~~ Kiaan and Izna are like completely two different poles. They both belong to two different RIVAL FAMILIES. It's...