WAZEER!

REAL-SMASHER

3.2K 338 50

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... Еще

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Wedding march
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mission
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Inexplicable
Strangerlike
Safwah
Adviceful
Thought pattern
Her wish!
Wedding bell!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Proposalist

161 10 4
REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               27

#Proposalist

          Tace "yanzu Mamman ka fi so ka auri wata matar daban akan ka dawo da uwar ƴaƴanka? Shin mene ne laifin Hooriyah ne? Me Hooriyah ta rasa? Shi kenan kai baza'a maka ba dai² ba ka haƙura? Naga Ubangiji ma da ya haliccemu haƙuri yake da mu,duk laifin da muka masa da zaran mun roƙe shi yake yafe mana.. Kai ne baza ka iya yafewa wani ba? To ta ina Allah zai yafe laifukanka kai? Shin baka karanta bane? Baka sani bane? Ko kuwa ina ka kai iliminka da duk ka manta da wannan? Wallahi yau na sake tabbatar da kalar mugun halinka,ace shekaru ɗai² har 20,amma kana riƙe da baiwar Allah a rai,shin ma wai ita ta kashe Sa'adatu ne? Ka faɗa min.. Nace wuƙa ko igiya tasa ta zarge wuyanta ta kasheta?" Hamood ya ɗan kalli Daada,kafin yace komai Daada tace "ina sake faɗa maka wallahi² muddin baka dawo da matarka ba,kayi saken da wani ya aureta,ina tabbatar maka sai ka zo nan gaba kana da ka sani.. Ina cewa ranar da incident ɗin ya faru yarinyar nan ba ta gidan nan,kai fa na kira muka yi magana da kai ka tabbatar min mahaifiyarta aka kira aka sanar mata ba ta da lafiya,unconscious aka kaita asibiti kuma duk cikin gidan nan babu wanda yayi karar ya bi bayanta a ranar,in fact ko bayan nan bamu je mun mata sannu da jiki ba,to ta ina za mu iya zuwa ka yi wannan aika²r.. Shi kenan saboda baka yarda da ƙaddarar data sameka ba,sai ka ɗorawa baiwar Allah laifin mutuwar ƴarta? Kalar na ka adalcin kenan Mamman? In taƙamarka kai uba ne,ita kuma ai naga uwa ce,ta fika sanin raɗaɗi da zafin ciwon data sha,tun daga sanda ta samu cikinta har zuwa haihuwarta da raino.. Saboda son kanka da zuciyarka baka barta da zafin rasa ƴarta da tayi ba,ka rabata da ɗanta again,ka ɗauke shi without sanin kowa har mu iyayenka kai tafiyarka uwa duniya da shi,kamar wani mara mafaɗi kai zamanka can saboda babu wanda yai maka magana ko yace don me.. Shi kenan ka kyauta ka ji Mamman,kayi duk yanda zucuyarka ta raya maka,Allah ya taimaka,mu namu dama ido ne tunda bamu isa mu faɗa kaji ba,Allah ya bada sa'a,aure kuma Allah ya sanya alkhairi,ga kanan ai ga wacce za ka auro,Allah ya baku zaman lafiya.." Fuskarsa ɗaure tamau kamar wanda aka cewa ga mutuwa nan a gabansa ko kuma dai Hooriyah ɗin da bai son gani ko jin zancenta,ƙasa² yace "Daada! Ni fa ba wai yafe mata ne ban yi ba,kawai ni ba na son zancenta,ba na so ana min maganarta da duk abunda ya shafe ta,abunda ya haɗa mu ya raba,don Allah ki daina cewa wai na dawo da ita,ni da ita ko a lahira muka haɗu baza mu taɓa mutunci ba,taje tayi rayuwarta yanda take so nima nayi nawa,Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi.." Daada dake masa wani kallo tace "auu! To ai shi kenan tunda haka kace,Allah ya haɗa ta da wanda zai so ta ya mutunta ta fiye da kai.. Ba don kada nai maka baki ba Mamman,a matsayina na uwa na san muni da illar yin haka,da sai nace duk macen da za ka auro wallahi baza ta taɓa kaiwa Hooriyah ba,mace me haƙuri da son naka,iyayenka da kowa naka mutunta shi take,amma baka duba haka ba.. Babu laifi,Allah ya taimaka" sakin baki Hamood yayi yana kallon Daada with suspicion kafin yayi ƙwafa tare da miƙewa tsaye,rai ɓace yana duban Daada yace "tunda ita kika haifa ba ni ba ai shi kenan.. Sai da safe" wata irin harara ta wurga masa,har ya juya zai tafi kuma sai taga yai turus a gurin yana kallon ƙofa,kallon gurin ta juya kanta tayi don ganin abunda ya tsayar da shi,Wazeer dake tsaye gurin yana kallonsu kawai hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗinsa ya shigo da sallama a ciki²,ransa sosai yake ɓace don babu abunda bai ji ba a maganarsu,amma dake ɗan duniya ne fuskewa yayi yai kamar bai ji komai ba,yanda yayi ɗin nan duk ƙwaƙwar mutum bai isa yace ga wani yanayi da ya shimfiɗa a fuskarsa ba bayan wanda ya saba ajiyewa yau da kullum. Daada ta fara sauke ajiyar zuciya tana barin maganar da tayi niyyar yi tace "Zainul-abideen! Yaushe ka shigo?" Yana zama saman armchair yace "yanzu.. Barka da dare" Daada tace "barka dai.. Ka dawo lafiya? Ya aikin?" Yace "alhmdllh!" Lokaci ɗaya kuma ya miƙe kamar wanda aka tsikara yana faɗin "sai da safe" bai jira Daada tace wani abu ba,haka nan bai kalli inda Dad ɗinsa yake ba ya wuce yayi ficewarsa. Daada dake ta kallon Hamood da ya kasa tafiya,ya yi tsaye kamar wanda aka sassaƙa,tace "ka fasa tafiya ne ko akwai wani abu da ka mance baka faɗa min ba?" Saurin juyawa Hamood yayi yana kallon Daada,yana ɓata fuska yace "Daada please.." Ƙwafa Daada tayi kawai ta ɗauke kai,jin bata ce komai ba Hamood ya wuce yana faɗin "sai da safe?" Ko ci kanka Daada bata ce masa ba har ya fita. Daga nan ɓangaren mahaifiyarsa ko da ya fita zaure ya wuce inda Abba yake,sam bai son maganar ya jima,ya fi son ayı komai wuta² a gama,shi bai ƙi ma ace idan an tashi yanke bikin asa 2 weeks ba,ya yi nisa dai kawai dai duka akai maganar 1 month,sallama yayi tare da ƙarasawa gaban Abba ya zauna,dattijon mahaifin nasa ya ɗan kalleshi tare da faɗin "Muhammad.. Lafiya dai ko?" Hamood da kansa ke ƙasa yace "Abba dama wata magana ce ta kawo ni" Abba na gyaɗa kansa yace "toh! Ba ka bari har na shigo cikin gidan? Yanzu a nan za muyi magana?" Hamood yace "ayi haƙuri Abba" Abba yace "ai ba cewa nayi ka yi laifi ba.." Yana kallon mutanen da suke tare yace "ku ɗan bamu guri za muyi magana" cikin girmamawa duka suka fita,sanda zauren ya rage su biyu kawai Abba yace ",wace magana ce Muhammad?" Kan Hamood har sannan a ƙasa yace "Abba dama ina neman aure ne,to mahaifin yarinyar ya buƙaci na tura magabata na" Abba yana masa wani kallo yace "tou a ina take? Ƴar waye kuma?" Hamood ya shiga bawa Abba bayanin Safwa da iyayenta,duk Abba yana saurarensa bai katse shi ba,sanda ya kai aya kafin yace "yanzu Muhammad ba ka yi haƙuri ka mayar da tsohuwar matarka ba mahaifiyar yaranka? Ka fi so ka je ka auro wacce baka san halayenta ba,itama bata san naka ba?" Ɓata rai Hamood yayi ya ƙi cewa komai,Abba duk yana kula da shi kawai ya gyaɗa kansa yace "shi kenan.. Tunda haka ka zaɓawa kanka,mu a matsayin iyaye namu addu'ah ne,Allah ya sanya alkhairi.. Yanzu sai ka jira na sanar da Yaya,ka san dole zai sa ayi binciken gidan su yarinyar da iyayenta,duk abunda ya faru daga nan kuma zan sanar maka.. Tashi ka tafi" Hamood ya gyaɗa kansa yace "toh Abba.. Allah ya ƙara girma,a tashi lafiya" da kallon tausayi Abba ya bi shi,har ransa yake son zaman ɗan nasa da Hooriyah,amma tunda haka ya zaɓarwa kansa ya ɗauki rayuwa da ɗabi'un turawa,zai barshi yayi yanda yake so,don idan sun takura basu san me zai faru ba,kuma baza suyi shisshigi a lamarin Ubangiji ba,la'alla zaman nasu ne ya ƙare,in kuma da saura za suyi addu'ah Allah ya kawo dalilin da za ta dawo,addu'ah kam dama kullum yana yiwa yaransa duka,hatta su Isma'il da duk matansu suke rashin mutuncinsu bai ware ko mutum ɗaya ba,su gidan sarauta ne komai suka yi idanun mutane kusan duka yana kansu,banda haka a zafin rai irin na Yaa Abdulkarim ma da tuni ya sallami matarsa,su suka tsawatar masa,amma har gobe tayi masa wani abun yana faɗa mata haƙuri yake kuma ta ci darajar su Abba ne,idan ta kai shi bango wallahi sai ta tafi gidansu.

*WAZEER*

      Ko da ya baro gidan Daada yana shiga bedroom ɗinsa ya wuce,tunani da yawa da tarin tambayoyi suna yawo a kansa game da maganar da yaji yanzun nan,shin me yasa Dad zai yi haka? Me yasa bazai ji maganar Daada ba? Me yasa bazai mayar da Mimi ba? Kenan all this while shi ne yaƙi mayar da ita? Kuma dai maganar akan zancen mutuwar Mysha ne babu wani abu bayan nan? Duk tsayin lokacin nan da abubuwan da suka faru da wanda Dad yake sanar masa akan Mimi duk ba haka suke ba? Me yasa Dad zai yi haka? Me yake nema a kan Mimi? Shin hukunci ne hakan ko kuma fansa ce? Allah sarki Mimi yana kallon kamar tana da laifi a wasu abubuwa,ashe duk ba haka bane babu ruwanta bata ma san wasu abubuwan da suka faru ba she's pure,kawai laifinta ɗaya sakaci da bata tabbatar da inda Mysha take ba a ranan ta tafi gurin mahaifiyarta,shima kuma a nasa ɓangaren saboda abunda ya faru wancan ranar sanda yaso jin maganar a bakinta,da taƙi ce masa komai wannan dalilin yasa ya ɗauke ƙafa ya bar zuwa gidan sosai. Shiru yayi lokaci ɗaya tunanin magnarsa da Dad na jiya yana dawo masa,sanda gabansa ya wani irin faɗi tunawar da yayi da Safwa,da sauri ya wuce ya fita bedroom ɗin ransa yana ɓaci,a irin yanayin da ya fito na ko a mutu ko ayi rai ne,yana fitowa kuma dai² lokacin Dad na shigowa,tsaiwa yayi cikin corridor yana kallonsa,Dad ya kalleshi yana sakin murmushi yace "hey! Son" da wani kallo me cike da jin haushin attitude ɗin mahaifin nasa Wazeer ya bi Dad,karo na farko tunda ya mallaki hankalin kansa,ba tare da ya ce masa ƙala ba ya juya tare da shigewa bedroom ya rufo ƙofarsa,da kallo Hamood da ya manta wani abu ya faru tsakaninsu jiya har ya yi masa alƙawari ya bishi, kafin ya tako ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga da faɗin "what's up Son? Me ke faruwa ka kasa amsa min magana? Mmmm?" Fuskarsa a tamke saboda haushin Dad ɗin nasa da yake mugun ji,yace "nothing.. I just don't feel good at all" Hamood ya buɗe ido sosai yace "and what are u doing? Have u call ur doctor? Why are u wearing ur glasses da daren nan? U are not a baby,ain't u know how to take care of urself? Wait! Kana kallon haske da unnecessary abubuwa da dare,right? Shi yayi causing matsalar har ya taɓa maka idanu this much?" Da yake bai saba yin ƙarya ba yana matsa forehead ɗinsa da yake jin yana sarawa yace "yeah! But actually Dad.." Sai kuma yayi shiru kamar yana tunanin abunda zai ce,Dad yana kallonsa yace "uhmn! Just go on,i'm all ears" Wazeer da fuskarsa ke ɗaure tamau yace "u didn't say anything about maganar da muka yi" Dad yana kallonsa yace "which matter?" Kallonsa Wazeer ya tsaya yi for some seconds kafin ya buɗe baki yace "maganar Girlfriend ɗina da Babanta yace na sanar da parents ɗina" tsuke fuska Hamood yayi yana masa wani kallo yace "and what did i say?" Wazeer yayi still yana kallon mahaifin nasa,Hamood yana sauke numfashi yace "i said kada ka sake zuwa gidansu,baka isa yin aure yanzu ba,ban faɗa ba?" Cikin ɓacin rai Wazeer ya buɗe baki zai yi magana,Dad ya tare shi da cewa "don't say anything.. I'm not asking hukuncina kenan,na ce ka rabu da yarinyar mutane,kada ka sake zuwa gidansu,ka barta da wanda suke sonta kuma suke shirye da yin aure" Wazeer yace "but Dad!" Hamood yace "um'um! Chapter closed.. And let me make it clear to u,do not think kayi wani abu stupidity,kada na sake kuma naji maganar nan a bakin kowa,i'm aware and looking for duk abunda kake tunanin yi,if not zan saɓa maka and u will see the other side of me.." Daga haka Hamood yayi wucewarsa ya barshi tsaye kamar statue. Mamakin Dad yake da yanda ya dage akan maganar,tuna maganar da Dad ya faɗa kafin ya bar gurin yasa shi sauke ajiyar zuciya,bai taɓa tunanin haka maganar zai zama ba,a duniya kuma ya san bai isa yin anything without sanin Dad ba,wata zuciyar tace "be patient Wazeer.. Sannu a hankali everything will be fine in sha Allah" haka kawai ya ƙudurce a ransa bazai maganar da kowa ba,even Mimi ba zai sanar mata ba,zai jira har sai lokacin da Dad ya amince,juyawa yayi ya nufi bathroom zuciyarsa na masa ƙuna,har ya fito yayi shirin bacci ya gama ya kwanta maganganun Dad basu bar yi masa yawo a kai ba.

*HAMOOD WAZIRI*

       In the morning around 7am Hamood ya shiga ɓangaren Daada,suna gaisawa Abba ya fito ɓangarensa,Hamood ya ɗan sauke kansa yana faɗin "barka da safiya Abba" Abba Waziri na zaunawa saman armchair yace "mun tashi lafiya?" Hamood ya amsa,Abba yana kallon Daada yace "Sa'adatu ki yiwa yaron nan Muhammad nasiha" Daada da ta fahimci akan abunda Abba yake magana,tana sakin ƙwafa mai ciwo tace "me zan faɗa masa ranka ya daɗe? Duk wani abu da zan faɗa na sanar masa,amma tunda haka ya zaɓarma kansa Allah ya bada sa'a.." Abba yana gyaɗa kansa ya kalli Hamood yace "well! Mun yi magana da Yaya,ya sa a bincika gidan da kake neman aure,kayi addu'ah kada a samu matsala,don ka san ko yaya muka samu wani abu da bai mana ba ko ya saɓa da al'ada da ɗabi'armu to ina mai tabbatar maka sai dai kayi haƙuri" Hamood ya gyaɗa kansa,Abba yace "za muyi magana idan ƴan aiken Mai martaba sun dawo" Hamood yace "toh Abba" Daada dai na jinsu bata ce komai ba,har Hamood yayi musu sallama ya fita. 2 days tsakani Abba ya kira Hamood yace "Muhammad kana ina?" Cikin girmamawa Hamood yace "ina Company" Abba Waziri yace "alright! Ka sameni yanzun nan ina jiranka,zan fita gidan Sarki kada ka ɓata min lokaci" Hamood yace "toh Abba.." Not too long Hamood dake cikin shigar suite kamar ko wane lokaci ya shigo parlon Daada da sallama,Abba dake zaune yana jiran zuwansa ya amsa yana ɗaga kai ya kalleshi,Hamood ya ƙaraso ya zauna tare da gaida iyayen nasa,Abba ya amsa yana kallonsa yace "ka san dalilin da yasa na kiraka?" Hamood ya girgiza kansa yace "a'a Abba" Abba Waziri yace "toh! A kan maganar da kazo min da shi ne,duk wani binciken da ya dace ayi kan yarinyar da iyayenta mun yi,kuma alhamdulillah za mu iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu.. Yanzu haka abunda Yaya yayi min magana akansa shi ne,za'a tura wanda za suje neman auren daga can fada,so sai ka kira iyayen yarinyar ka sanar da su zuwan mutanenmu yau idan Allah ya amince da yamma" Hamood ya buɗe ido da kyau fuskarsa na bayyanar da yanayin mamaki da kuma farin ciki yace "amma Abba da wuri haka? Na yi zaton magana za'a fara yi kafin kai kuɗin auren?" Abba yayi masa wani kallo yace "haka kaga muna yi a zuri'armu? Ko kuwa kai yaro ne? Ina cewa kayi kada asa bikin ya wuce 1 month?" Hamood ya gyaɗa kansa yace "ehh" Abba yace "shirme kenan.. Ka san da haka za ka kawowa mutane maganar banza?" Hamood yace "Allah ya huci zuciyarka.." Abba ya ɗauke kansa yana faɗin "zan tafi gidan Sarki,Yaya yana nemana.. Daga nan zuwa asr sai ka yanke abunda za ka bayar na kuɗin aure ka sanar mana,i think yau za'ayi komai a tsayar da ranar yanda kace,koh?" Hamood ya gyaɗa kansa yace "toh Abba" Abba ya miƙe riƙe da sandarsa yana faɗin "Sa'adatu sai na dawo" Daada da kamar ba ta cikin parlon ta gyaɗa kai,jikinta a sanyaye tace "toh ranka ya daɗe,a dawo lafiya.. Allah ya tsare hanya" Abba ya amsa ya fita. Juyawa Hamood yayi yana kallon Daada fuskarsa ƙunshe da murmushi yace "Daada!" Daada dake cike da takaici ta watsa masa wani kallo ba tare da ta ce masa komai ba,cikin basarwa Hamood yace "Daada baki ce komai ba" kamar da faɗa Daada tace "me zan ce da kai Mamman? Me nake da shi wanda zan faɗa da za ka ji ni? A matsayina na uwa na baka shawarar da zai amfaneka,amma baka gani ba to me yayi saura kuma? Aure ne dai ko za kayi? Allah ya bada sa'a ya sanya alkhairi.." Zai sake magana ta ɗaga masa hannu da faɗin "ka ga Mamman ka raba kanka da saka ni cikin maganar aurenka.. Muddin ba Hooriyah ka dawo da ita ba,to kada ka kuskura ka sake min zancen aurenka,babu ruwana da matarka.. Addu'ah ce na yi maka nace Allah ya baku zaman lafiya,ba shi kenan ba kuma?" Shiru Hamood dake hango ɓacin rai a idanun Daada yayi,cikin sanyin jiki muryarsa a ƙasa yace "Daada fushi kike da ni akan maganar nan? Don Allah kiyi haƙuri.." Murmushi mai ciwo Daada tayi tana girgiza kanta tace "akan me zan yi fushi da kai? Ka san hausawa na cewa duk abunda babba ya hango,yaro ko ya hau rimi/dala ba zai taɓa ganosa ba.. Ina jiye maka tsoron ranar da Allah zai kamaka da hakkin Hooriyah,kaji tsoron Allah Mamman,ka je ka nemi yafiyarta da na ɗanta da ka tauye ka hana jin daɗin mahaifiyarsa,ba na so kazo kana dana sani a lokacin da bazai maka amfani ba.. Kana da dama a hannunka har yanzu,kuma lokaci bai ƙure maka ba,kaje ku sasanta da matarka ka mayar da ita" ɓata rai Hamood yayi yace "Daada please!" Daada ta kalleshi kawai ta gyaɗa kai tace "ai shi kenan.. Ni dai zan ta yi maka addu'ah,idan rabon dake tsakaninku bai ƙare ba Allah ya dai²ta lamarin.." Saurin miƙewa tsaye Hamood yayi yace "Daada zan koma Company" Daada dake kallonsa ta gyaɗa masa kai tace "saboda ba ka son maganar da nake maka kou?" Hamood na ɓata rai yace "a'a ina da meeting ne yanzu" Daada ta sake gyaɗa kai tace "shi kenan Allah ya taimaka" ya amsa tare da yi mata sallama ya fice,underneath his breath ya furta "why always Hooriyah?" A hankali ya saki siririn tsaki. A hanyarsa ta komawa Company ya kira layin Engr. Ridwan mahaifin Safwa,after sun gaisa cikin mutunci da barkwanci Dad yake cewa "Alh na kira na sanar maka zuwan baƙi daga fada yau in the evening.. Hope za su sameka a gida?" Baba dake saurarensa yace "in sha Allah i'm there" Hamood yace "alright! Na gode sosai,sai mun yi magana later" daga haka sukai sallama.

*SAFWA*

       Kwanakin da suka gabata duka sukuku take,amma yau bata san me ya faru ba haka kawai ta wayi gari da ƙarfinta kuma cikin nishaɗin da bata san mafarinsa ba,sanda take saukowa ƙasa ta tarar da Umma tana waya da Aunty Hilda,zaunawa tayi da wayarta a hannunta,haka kawai tayi sha'awar kiran Aley,even though ta yi alwashin baza ta sake kiransa ba tunda ya yaudareta ya kashe wayarsa,kullum babu ranar banza da baza ta kirashi ba ba ta samunsa,amma yau she is feeling ta kirashi ta gaggaya masa maganar da zai hanashi sukuni kamar yanda ya hana mata nutsuwa na kwanaki,wayarta ta kalla tare da shiga phone call ta ciro number ɗinsa,luckily tana kiransa taji wayar yana buɗe,sai dai abun takaicin har kiran ya katse bai amsa ba,ta sake kira nan ma no response,idan ranta ya kai dubu at that time to duk ya ɓaci,cikin wani irin fushi da ɓacin rai ta shiga gefen messages,dai² number ɗinsa ta shiga rubutu babu ji ranta na tafarfasa,ko tantance me take rubutawa bata tsaya ba,dai² lokacin Umma ta gama wayar da take da sister ɗinta ta kalleta tana faɗin "Aunty'nki na gaisheku,tana kuma yi miki Allah ya sanya alkhairi kafin ta kiraki" Safwa dai ko jin Umma ma bata yi ba,don yanda ranta yake a jagule,kallon nutsuwa Umma ta bita da shi,kafin tace "Safwa lafiyarki lau kuwa?" Saurin ɗago kanta Safwa tayi ta kalli Umma tana cewa "me ya faru Umma?" Umma tace "a'a gani dai nayi ina miki magana kamar baki san ina yi ba" Safwa tayi ƙwafa kawai a hankali tace "i'm sorry.. Wani saƙo nake rubutawa ne shi ya ɗauke min hankali,amma me kika ce?" Umma tace "Aunty'nku ce tace a gaisheki" Safwa da hankalinta bai kan Umma kwata² tace "ina amsawa" magana Umma ta ci gaba da yi mata ba ta wani ganewa saboda hankalinta kaf bai gurin,sai da ta kammala abunda take sannan ta ajiye wayar tana sauke numfashi,underneath tana jin gara da Allah yasa haka ta faru,da ace yanzu ta wulaƙanta Hamood Waziri saboda shi yau da ina ta kama kenan? Sake sauke numfashi tayi tana jinjina al'amarin a ranta,she took all abunda ya faru as a blessings. Da yamma gabannin Asr Baba ya dawo,lokacin suna idar da sallah ya fito masjid ya shigo gida,bai wani jima sosai² ba kiran Hamood ya shigo masa,bayan ya ɗauka sun gaisa Hamood yake sanar masa mutanensa sun kamo hanya,Baba yace "toh babu damuwa,Allah ya kawo su lafiya" Hamood ya amsa,suna ajiye wayar Baba ya fara neman line Dr Sulaiman Mijinyawa,ba'a ɗauki lokaci ba ya amsa suka gaisa,then Baba ya sanar da shi dalilin kiran nasa,if he's at home ko yana kusa² yazo don Allah,yayi masa bayani sama²,ganin yanda Baba ya girmama shi yasa Abba ya amsa tare da baro abunda yake ya kamo hanyar dawowa. Duka da isowarsa da zuwan mutanen da suka zo wakilcin Hamood bai fi minti 5 ba,sai kuma ga Alh Nafi'u Baban Radhiya shima da Baba ya kira,ganin mutanen da rawani tare da fadawa yasa Dr Sulaiman Mijinyawa ya fahimci duk inda suka fito ba ya rasa nasaba da gidan sarauta,here yasa aka shigar da su parlon baƙinsa,hakimai ne kuma wasu daga cikin manyan ƴan majalisar sarki zaɓaɓɓu da Mai martaba Abduljalal Yusuf ya turo wakilci,after an gama gaisawa cikin mutunci da mutunta kai,Talba ya shiga zayyano dalilin zuwansu,kafin ya fito da kuɗin aure ya ajiye gaban su Baba,kallon² akai tsakanin Dr Sulaiman Mijinyawa,Alh Nafi'u da Baba,sam babu wanda yayi zaton cewa kuɗin aure za azo kawowa,kuma ko Hamood ma bai sanarwa Baba haka za ta faru ba,Alh Nafi'u yace "toh Alh Lirwanu dama kuɗin auren za mu karɓa ne?" Baba ya girgiza kansa cikin ɗaurewar kai yace "nima dai ban yi zaton haka ba,na nemi iyayensa suzo ayi magana ne before maganar aure ya ƙullu tsakaninsu" Dr Sulaiman yayi murmushi kawai sanin wasu al'adu kaɗan na masarauta da yayi,yasa shi cewa "i think wannan bazai zama damuwa ba,tunda suka zo bai kamata mu tsaya jinkiri ba,a amshi abunda suka zo da shi muyi addu'ah,Allah yasa hakan ya zama alkhairi" Baba yace "amma bamu san haka za ta faru ba Dr" Dr Sulaiman yana girgiza kansa yace "duk mu ture batun rashin sani yanzu,mu fuskanci abunda ke gabanmu" Baba ya ɗan gyaɗa kansa kaɗan cike da damuwa yace "shi kenan Dr.. Allah ya tabbatar da alkhairinsa" Alh Nafi'u yace "ameen" jikin Baba dai duk a sanyaye,Talba da ya fahimci kamar basu so haka ba,ya ɗan kalli sauran mutum 3 da suka zo tare kafin ya ɗan fara magana cikin yanayin maganarsu na masu mulki,sanda ya ɗan kwantar musu da hankali kafin yayi musu bayanin yanda su suke zuwa neman aure daga Fada,Baba dai ya amsa kawai tare da wakilta Dr Sulaiman ya karɓi kuɗin auren Safwa,after then akai addu'o'i sannan su Talba suka tashi tafiya,har bakin mota inda fadawa suke su Baba suka rakosu,Talba na sanar musu idan sun yi shawara zuwa ƴan kwanaki sun amince da haɗin auren sai su tura ɗan aike fada ya sanar an basu yarinyar,daga nan sai a tsayar da ranar aure,Dr Sulaiman ya amsa musu sannan sukai sallama,suna tafiya Baba ya sauke ajiyar zuciya da faɗin "danƙariii!" Alh Nafi'u yayi ɗan murmushi yace "alhmdllh! Alh Lirwanu ai in da ace haka ake zuwa neman aure da abubuwa sun tafi dai²,hakan kuma zai rage yaɗuwar fasadi da ɓarna sosai" Dr Sulaiman yayi ɗan murmushi kawai yace "toh! Duk dai wannan ya riga ya faru,addu'ar dai ita ce mafitarmu.. Allah ya sanya albarka a cikin wannan auren" su Baba suka amsa kafin Dr Sulaiman ya damƙawa Baba kuɗin da ya wakilta shi ya karɓa,Baba yace "Dr ai da ka barsu gurinka,ni yanzu na karɓi kuɗin nayi yaya da su?" Dr Sulaiman yana girgiza kai fuskarsa da murmushi yace "a'a Engr. Ba za'a yi haka ba,kai ne mahaifinta,kai yafi dacewa ka ajiye kuɗin a hannunka" Baba zai sake magana Alh Nafi'u yace "a'a Engr. Ka amshi kuɗin,kamar yanda Dr yace ne kai za ka ajiye su a gurinka,bayan haka ai yana da kyau ka nunawa iyalinka ka sanar da su abunda ya faru" Baba dai duk bai san kan wannan lamari ba,haka ya amshi kuɗin tare da yiwa su Alh Nafi'u godiya yana ta musu addu'o'i sannan sukai sallama suka rabu. Gidansa Baba ya wuce kai tsaye,ya shigo parlour da sallama,Umma da Safwa da suke zaune suka amsa tare da yi masa barka da shigowa,Umma na yi masa kallon tsanaki tace "Engr ba dai har baƙin naku sun tafi ba?" Baba ya gyaɗa mata kai jiki a sanyaye yana zaunawa ya ajiye mata kuɗin da suke ɗaure cikin leda a gabanta,ba Umma kawai ba hatta Safwa sai da ta kalleshi hoping that Umma za ta tambayeshi mene ne wannan? Kamar Umma ta ji maganar da take a ranta tana kallon Baba tace "ranka ya daɗe wannan fa? Mene ne?" Baba na kallon ɗaurin kuɗin yace "kuɗin auren ƴarki ne,sun kawo 500K" Umma ta waro idanunta waje tace "auu! Dama da shirinsu suka zo?" Baba na gyara zama yace "haka dai suka sanar mana suke zuwa neman aure.." Umma da wani irin farin ciki ya cika bata san sanda ta kama hanci ta rangaɗa guɗa ba,Baba dai kallonta kawai yake,Umma tana murmushi cikin tarin farin ciki tace "alhmdllhi! Allah ya tabbatar da alkhairinsa" sai kuma ta ɗauki waya ta shiga kiran ƴan uwa ta fara sanar musu,Baba dai bai ce mata uffan ba ƙarshema tashi yayi ya wuce ɗakinsa. Kasaƙe Safwa tayi kamar wacce aka girke a gurin,tunda Baba ya faɗi cewar kuɗin aurenta ne take kallon ledar da mamakin adadin da taji ya sanar da Umma,yanda Umma ke murna abun har ya so ba ta mamaki,Umma na gama waya da Aunty Hilda ta kalli Safwa tana dariya tace "kinga yanda Allah yayi da ke ko Safwa? Yanzu da wannan arzikin kike ƙoƙarin ki gujewa? Tunda kike ke a cikin GRA ɗin nan kin taɓa ji ko ganin wacce aka kawo kuɗin aurenta haka? To wallahi ki mayar da hankalinki jikinki,Allah ne yake nufinmu da alkhairi,shi yasa ya kawo mana Hamood Waziri,zancen kowa yanzu ya kau,ki sallami duk taron yu³ ɗin nan da suke zuwa su ɓata maki lokaci,kin samu ƙwaƙƙwara na nunawa sa'a,zancen Aliyu yanzu ya ƙare ke da shi ko a lahira,ki amshi wanda Allah ya musanya miki hannu bibbiyu,arziki ke binki da gudun famfalaƙi yana ƙoƙarin hanaki bin tsiya,fatara da talauci" Safwa da tayi shiru tana haɗa maganganun Umma a ranta,a hankali ta gyaɗa kai then ta saki murmushi tace "Umma da gaske ne wannan kuɗin aurena ne?" Umma tace "ahh! Wannan kuma ai kin san tunda Babanku ya faɗa bazai mana ƙarya ba ko?" Safwa tace "haka ne" Umma tace "ahh Toh! In ba gurin irinsu Hamood Wazirin ba dama a ina ake ganin irin wannan harkar arzikin,ke kin san sadaki kuwa sai ya kai Million ko ma yafi.. Allah na tuba ai wallahi yanzu mun wuce da yawa a wanda suke mana gani²" Safwa dai na jin Umma,underneath magana take da kanta akan da gaske sadakinta zai kai Million? Kawai yawan kuɗin take ji a bakinta,amma bata taɓa ganinsu a zahiri ba,500K da ta gani just now gaba ɗaya suka hautsina mata ƙwaƙwalwa ta fara tunani da tuhumar kanta da me ya shige mata gaba ta kasa tunani da yankema kanta hukuncin da zai dace da ita? Lallai Aunty Gaaji da Ummanta sun yi gaskiya kuma sun hango mata abunda ta kasa tsayawa ta fahimta,yau da ta zaɓi Aley wataƙila da ko 50K ba'a kawo kuɗin aurenta ba. Kiran da akai mata da wayarta data fara beeping ya dawo da ita hayyacinta,sunan Hamood Waziri ta gani saman screen ɗinta,sanda ta ɗan ja aji kafin ta amsa cikin yanga suka gaisa,yana ɗan murmushi yace "gimbiyar mata!" Cikin kissar da ita kanta bata san ta iya ba tace "na'am ur Excellency.." Hamood ya saki wani sabon murmushi kansa yana huruwa yace "have u seen irin takun da nayi yau?" Safwa ta ɗan yi murmushi kawai,yace "i have told u that ban zo da wasa ba,da kin bani dama yanzu haka da kina gidana as a wife" Safwa tace "ai komai is a matter of time" Hamood yace "sure.. Arghm! Na kira naji opinion naki akan lokacin da ya kamata a tsayar da ranar auren.. Wane lokaci kike ganin ya yi miki? I don't want na tauyeki,ban san wane irin shiri za ku yi ba" Safwa ta ɗan sauke numfashi kafin tace "i don't have any plans or choice akan wannan maganar" yace "so anytime muka tsayar it's ok for u?" Safwa tace "ehh" ya ɗan gyaɗa kansa cikin farin ciki yace "wow! I'm glad da naji haka.. And ina tunanin duka lokacin bazai wuce 2-4 weeks ba za'a tsayar" Safwa ta ɗan waro idanunta waje tace "bai yi wuri ba ranka ya daɗe?" Hamood yace "no dear.. Do u know how many years na share babu aure? I think and to me bai yi ba" Safwa ta ɗan gyaɗa kanta tace "alright! Zan yi magana da Umma naji me za tace akai" yace "ok! And regarding the duk wani abu da ake nema na hidima let me know as soon as possible,i mean anything.." Safwa ta gyaɗa kanta tace "ok dear.." A ɗan hanzarce yace "sorry dear i will call u later,zan yi answering call" Safwa tace "ok! Bye.." Kallonta Umma dake jinta tayi tace "mene ne naji kina cewa ya yi wuri?" Safwa na ajiye wayarta tace "wai cewa yayi bai so asa bikin ya wuce 2-4 weeks,saboda ya jima bai yi aure ba" Umma tace "toh! Ahhh.. Lallai a shirye yake,ko da yake dama su masu shi ai ko a lokacin suka so sai su yanke abunsu,mu ɗin dai ne dole sai mun yi tanadi,amma in hakan yake so ai mai sauƙi ne,da zaran ya buɗe bakin account komai zai tafi yadda yake buƙatarsa" Safwa tace "Umma kuma sai asa bikin yanda yace?" Umma tace "ahh! Me za'a jira? Ba gara ayi ai auren ba,Allah na tuba dama lokacin nan da ake sawa ai yana yawa,wani fa kiga har shekara guda.. A'a wallahi tunda ya shirya 1 month ɗin it's ok for us,ai kamar yau ne,sai mu fara shirinmu muma,duk wanda zai ce wani abu kuma ya jima bai faɗa ba,amma ko Babanku zan san yanda zan masa magana a bar bikin a lokacin da duk suka buƙata,bare daga Fada za'a tsayar da lokacin a sanar mana,kinga kuwa ai babu batun a ɗaga tunda masu garin suka yanke lokacinsu" Safwa dai ta gyaɗa kai kawai,Umma ta ci gaba da cewa "kinga Allah ya taimakemu,kema kin samu mijinki a dai² lokacin da ƙawayenki suke shirin yin aure,tsiranku duka ba zai fi ƴan kwanaki ba kema za ki tafi naki gidan,kinga zumuncinku zai fi ƙarfi a haka dukanku kuna da aure,saɓanin ace sun tafi sun barki kina ta zaune gida,ba komai za'a yi dake ko a saka ki ba.. Toh! Kinga kuwa ai alhamdulillahi ko a haka ma mun gode Allah,ba don Allah ya taimakemu wancan maƙaryacin yaron ya barki ba da yanzu kina nan kina fama da dakon sonsa.. Kaiii³! Allah kayi mana tsari da talauci.." A fili Safwa tace "ameen.." Har sun yi shiru Safwa tace "Umma kin sanar da Mama kuwa da su Mami?" Umma tace "laaaa! Ke dai Allah yayi miki albarka.. Har gida Hjy Batoolu ta shigo ta sanar min na su Baniynah da aka karɓa,bari kiga naje na sanar mata,ita kuma Dr Aminat sai na kira na faɗa mata kawai" tayi maganar tana miƙewa ta ɗauki hijabi tace "bari na shiga na fito.. Idan Babanku ya tambaya kice na shiga sanar da Hjy Batoolu" Safwa tace "toh!" Umma ta wuce ta fita.

*MUNIBA*

        Saukowa take daga upstairs waya ƙare a kunnenta tana magana fuskarta da murmushi,kaga yanda tayi wani masifaffen kyau kamar ka taɓa jikinta jini ya fito,fatarta sai wani irin ɗaukan ido yake kamar na jaririya sai kaji kamar ka saceta ka gudu,yanayin yanda take magana zai sa ka fahimci ba gama garin waya take ba,a hankali ta ƙarasa kusa da Baniynah dake kwance ta zauna,while tana faɗin "ok! When are u coming?" Shagwaɓe fuska tayi muryarta can ƙasa tace "um'um! So kake ka tafi bamu yi sallama ba wai?" Tayi ɗan shiru kafin tana kallon nails ɗinta da suke gyare tatas suna wani ƙyalli tace "ok! Fine.. Thanks.." Tana faɗan haka ta katse wayar tana sakin ƙwafa. Kallonta Baniynah dake chat ta ɗago tana yi,yanda take jera yin ƙwafar kamar me bitar karatu,tana ɗan girgiza kanta tace "what's up? Faɗa kuka yi?" Muniba tai saurin waigowa ta kalleta,ba tare da ta ce mata komai ba ta sake yin ƙwafa ta ɗauke kai,Baniynah dake ta kallonta non stop ta taso da sauri ta zauna,fuskarta cike da damuwa tace "Sweetheart answer me.. Nace faɗa kuka yi?" Muniba bata kalleta ba tace "a'a za muyi dai in har bai zo ba" yanda ta ɓata rai da ta ƙare maganar kamar Lieut Abuu Turab na wajen yasa Baniynah cin serious tana ɗan yatsina fuska tace "i think bai kamata kuyi faɗa ba,ko da bai zo ba ai normal ne,tunda kwana nawa ya rage a kaiki gidansa?" Da sauri Muniba ta kalleta,Baniynah da tayi fuska ta ɗaga kafaɗa tace "yesssss!" Muniba na mata wani kallo cike da faɗan da bata saba ba tace "tafiya fa yace min zai yi,kuma shi ne bazai zo muyi sallama ba? Ok! Fine.. Wallahi Allah in dai ya tafi without yazo na ganshi ko.. Hmmm!" Tana faɗan haka tai saurin tashi ta wuce sama,haka kawai taji ranta duk ya ɓaci,ga wani kukan da bata san na mene ne ba dake shirin zuwar mata,tana saka ƙafarta cikin bedroom kiransa na shigo mata,amma da yake akan tsini take bata iya amsawa ba,iya iyawarta take yaƙi da kankin kanta kada hawayen da suke idonta su sauko,amma she couldn't ta faɗa gado kawai ta fashe da kuka,tana ji yana ta kiranta ta kasa ɗauka. Almost 15 minutes aka buɗe ƙofar aka shigo,da mamaki Baniynah ta tsaya riƙe da waya a kunnenta,kafin kamar wacce akai playing ɗinta ta ƙarasa da ɗan gudunta hankalinta na tashi ta shiga kiran sunanta "Sweetheart! Mene ne haka kuma? Me akai miki don Allah? Ke da waye please?" Bata ɗago ba kuma bata ba ta amsa ba sai kukan da ta ci gaba da yi,but ta rage sautin kukan nata tunda taji shigowarta,Baniynah ta zauna kusa da ita har sannan bata katse wayar da take ba,in fact kamar ma ta manta tana waya ta shigo,cikin damuwa ta kai hannunta bayan Muniba tana faɗin "Sweetheart please let's talk,meke damunki? Me akai miki? Wallahi kin sa hankalina ya tashi,ki tashi muyi magana idan ba so kike na kira Mami tazo ba" saurin ɗago kai Muniba tayi tana share fuskarta,Baniynah tace "mene ne yasa ki kuka?" Rai ɓace tace "nothing" Baniynah data saki baki tana kallonta tace "babu komai kawai sai ki zo ki kama kuka,ki faɗan me akai miki ko kuma wallahi² zan je na kira Mami" Muniba na turo baki ta miƙe za ta bar gurin,da sauri Baniynah ta kamo hannunta ranta ɓace also tace "baza ki faɗa min ba? Ok! Fine.. Bari na kira Mami,ai ita za ki faɗa mata,and baki isa kice mata babu komai ba" ta miƙe za ta wuce tare da sakin hannun Muniba,cikin sauri Muniba ta riƙota tace "to ai na ce miki babu komai,ni kawai zuciyata naji tana min ƙaiƙayi,ban san me zai faru da ni ba,but it's like wani abu zai faru da someone close to me,i don't know ko ni ce ma,ina jin babu daɗi sosai har cikin raina,gabana yana yawan faɗuwa.." Tana maganar wasu hawayen suna sake saukowa idanunta,ita dama haka take wata irin mutum ce dake da rauni da raguwar zuciya,magana kawai idan za tayi yanzu za kaga tana kuka sadidan,rasa me ma Baniynah za tace mata tayi saboda yanda maganar ita kanta ya daketa,cike da soyayya,dauriya gami da lallashi tana gyaɗa kai tace "i think addu'ah ya kamata kiyi ba kuka ba,kuka ba ya maganin komai sai dai yasa miki wani ciwon,and regarding the faɗuwar gaban da kike in sha Allah khaiir,muyi ta addu'ah koma mene ne zai zo da sauƙi if Allah wills.." Muniba ta gyaɗa mata kai a hankali jikinta duk ya yi sanyi,Baniynah za ta sake magana wayarta ya shiga beeping,saurin kallon wayar da bata ma san yaushe ta ajiye ba tayi tana waro manyan idanunta waje ganin wanda ke kiranta tace "oh My Goodness.. Wallahi na mata In-law ya kirani muna magana na shigo kawo miki wayar,he said that yana kiranki ba kya ɗauka,na duba masa ke if u are fine na baki wayar,Allah yasa bai ji abunda ya faru ba" wani lafiyayyen kallo Muniba ta watsa mata ta miƙe za ta bar gurin,Baniynah tace "ohh! Don't do that.. Ki tsaya ki amsa wayar,idan ma laifi yayi miki just ki sanar masa ku shirya,ni ba na son kuna dogon fushi da juna,biki na tahowa kawai ace amaryarmu da ango ba'a zaman lafiya,though faɗan masoya hutu ne amma dai ki tsaya kiji me zai ce" kallon Baniynah Muniba tayi,Baniynah ta gyaɗa mata kai tace "just karɓi wayar ko ki kirashi da naki,wallahi hankalinsa ya tashi da kika kashe wayar,kuma yana ta kira kin ƙi picking,kada kiji yanda yake min magana,pleasee Sweetheart!" Gyaɗa kanta tayi kaɗan,Baniynah tace "ok! Gashi to call him wannan kiran ya katse" tsume fuska Muniba tayi tace "ni bazan kirashi ba" Baniynah tace "c'mon Sweetheart,kada kiyi haka,call him ku sasanta tsakaninku,ok? Throw up kome yayi miki da bakya so,don't give him any space da zai kai ƙararki gurin kowa,idan kun samu misunderstanding ku sasanta babu wanda ya sani.. Bari na baku guri kuyi magana" Baniynah na faɗan haka ta wuce za ta fita,sanda ta kai entrance tace "ki fa kira pleasee" Muniba ta maka wata harara,Baniynah na dariya daga inda take tsaye tace "yanzu ne,bari ya miki busa a kunne,za kizo kina min addu'ah ne later" Muniba ta girgiza kai kawai murmushi na suɓuce mata,Baniynah ta wuce ta fita abunta itama tana ƴar dariya da sake tsokanarta. Wayarta ta ɗauka za ta kirashi kamar yanda Baniynah tace mata sai ga kiransa ya shigo,a hankali ta dunga kallon wayar kafin tai answering tasa wayar a speaker,kafin ma tayi magana ya rigata da faɗin "pardon me Babyyy.." Shiru ta sake yi ta ƙi cewa komai,yace "ok! Come out yanzu ina jiranki,sai ki yi min kukan zan bada haƙuri" daga haka ya katse kiran,waro idanunta waje tayi da mamakin wai har ya zo,sai kuma ta saki murmushi ta tashi da gudu ta wuce bathroom,fuskarta ta wanke ta fito ta gyara tasa kajol a ido da lip balm sai turaren data fesa sannan ta wuce ta ɗauki veil tayi waje. Tana saukowa downstairs ta tarar da Baniynah da Mami suna hira,Baniynah na ganin saukowarta tace "Sweetheart albishirinki" Muniba da ta gama saukowa tana kallonta tace "what's up? Goro!" Baniynah tace "an kawo kuɗin gaisuwar ƙawarki" Muniba ta ɗan yi shiru tana kallonta kamar tana tunani,then tace "i don't get u.. Wacce?" Baniynah na dariya tace "Safwah!"

          '''#Anjad aasifik'thriir habiibaatiiy! Dole da yanayin rayuwa suke hana ni yin update on time,ina son yin rubutun saboda ku,but ina cikin jarabawar wani irin rashin lafiya.. A kullum kuna raina,da tunaninku nake kwana na tashi,amma al'amarin ya fi ƙarfin sarrafawata,ku taya ni da addu'ah don Allah,Allah ya ƙaramin haƙuri da ikon cinye jarabawarsa gareni..🫥🥹😪'''

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*


#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Продолжить чтение

Вам также понравится

431 54 19
The cycle of sahil-Gautami to Anirudh-Gautami to again Gautami-sahil to let's see who's next sooooo what's next? let's dig into this story with me...
Yaha waha hai tu by Vrushy kairafan01

Любовные романы

36.3K 1.6K 21
In this ff,Kaira love eachother alot....but suddenly due to some reason naira lied to Kartik that she betrayed him.......what will happen now....read...
26.1K 1.7K 14
❤️ This FF starts after Talent hunt 💙
33.2K 2.7K 34
#Winner of The Awesome Awards 2018 & Stardust Awards 2018(chicklit category) 4 in #friendfiction on 11/07/2018 6 in #husbandandwife on 23/05/2018 The...