WAZEER!

By REAL-SMASHER

3.2K 338 50

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... More

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Wedding march
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mission
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Inexplicable
Strangerlike
Adviceful
Thought pattern
Proposalist
Her wish!
Wedding bell!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Safwah

102 12 4
By REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               24

#Safwah

          Kyakkyawan mutumin dake tsaye yana mata murmushi ta ɗan bi da kallon ƙurilla,ba yaro bane daga ganinsa,but akwai jin daɗi tattare da shi wanda kana kallonsa babu buƙatar sai wani ya sanar maka,a hankali take tunani da tambayar kanta "a ina na san me wannan fuskar?" Sai dai ta kasa tunawa,can kamar wanda akaiwa alluran tunawa ta gano mutumin da ta taɓa gani a mota da jimawa sosai² yana ta kallonta,sake ɗan kallonsa tayi har sannan bata yi magana ba,tsadadden suite ne jikinsa brown color,kana kallon skin ɗinsa da yayi luf² da wani gargasa wanda hutu ya gama jiƙawa za ka san akwai masu gidan rana,sai dai duk ƙwaƙwarka baka isa kace ga shekarunsa ba,saboda gayu da jin daɗi sun gama ɓoye hakan a tattare da shi,ganin Safwa ta tsaya though bata yi magana ba,yasa ya ɗan yi taking steps gurin da take tsaye yace "assalamu alaikum" Safwa dake ƙifi² da ido ta amsa,kwarjinin da yayi mata yasa tace "ina kwana?" Ya amsa yana ɗan dai²ta tsaiwarsa fuskarsa a sake yace "if babu damuwa za mu iya yin magana?" Safwa ta gyaɗa masa kai tace "babu!" Yace "alright! I'm Muhammad Hamood Aliyu Waziri.. Na san kin san gidan Wazirin Kano,right?" Ta gyaɗa masa kai da sauri,tun farko data ɗora idanunta akansa komai ya canja mata,lissafinta ya fara neman sauyawa,bugun zuciyarta ya ƙaru,a duk lokacin data shaƙi daddaɗan ƙamahinsa ji take kamar ba'a duniya take ba,yanzu ko da taji sautin muryarsa sai taji wani yanayi ya saukar mata,duk da bata tantance mene ne shi ba ko me hakan yake nufi,yace "na ganki ne some minutes ago,so babu yanda za'ayi na iya yi miki magana saboda bama kusa,and idan kin tafi kuma ban san where zan samo ki ba,like wancan lokacin" Safwa ta sake gyara tsaiwarta tana buɗe ido da kyau cike da mamakin yanda aka yi ya ganeta,tace "Allah sarki.." Underneath tana faɗin "wayyoo Allah ni Safwa ɗan gidan Waziri ne fa,ai daga gani ma ba sai ya yi bayani ba suna da kuɗi" yace "it seems like u are in a hurry?" Tace "yeah ina da test ne" yace "ok! Bari na barki kiyi test,but zan iya jira har ki fito muyi magana?" Safwa ta waro idanunta waje tace "a kan me?" Yace "saboda ban sanar miki abunda ya kawo ni ba" Safwa tace "a'a gaskiya kayi tafiyarka" yace "u don't want me to stay?" Tace "ina da lectures ne gaskiya,kuma ni ban san me za kace min ba,in fact banma sanka ba yau na taɓa ganinka,Babana kuma a nan yake aiki idan ya ganni ko ya samu labarin na tsaya da wani zai min faɗa" yace "ko dai kina tsoron kula strangers ne?" Ta gyaɗa kanta da sauri underneath tace "ni duk ba wannan ba,ka amshi digit ɗina kawai" a fili kuma sai tace "ehh" yace "ok! Ki bani digits ɗinki sai nazo gidanku na ganki muyi magana,i think u will be safe and comfortable with me a nan ko?" Har zuciyarta sai da taji kamar ta buga tsalle tare da yin ihun murna,while a fuskarta kuma ta nuna kamar ba ta son bada number ɗinta,yace "please My dear,ba zan cutar da ke ba,ban kuma zo miki da wasa ba" Safwa ta gyaɗa kanta kaɗan tace "ok!" Tsadadden wayarsa da ko a labari bata taɓa ganin irinsa ba ya miƙo mata,hannunta har rawa yake ta karɓa tasa masa number ɗinta,underneath sai zancen zuci take tana faɗin "wallahi me kuɗi ne" tana miƙa masa wayar ya amsa yace "what name zan yi saving?" Tace "Safwah!" Yayi ɗan murmushi yace "nice meeting u dear.. Allah ya bada sa'an test" tace "ameen.. Thank u" yace "ok! Bari mu wuce sai mun yi waya ko?" Ta gyaɗa kanta tace "Allah ya tsare hanya" ya amsa tare da yi mata sallama ya wuce. Tana juyawa ta wani ƙwalo ido waje daɗi duk ya gama rufeta,ji take kamar za ta tashi sama,sai kuma ta fara ji kamar tai tsuntsuwa taje ta sanar da Umma,ba komai ya ɗauki hankalinta kamar kuɗinsa ba,musamman da taga ba shi yake driving da kansa ba,ai kuwa yanzuma baza tayi ƙasa a gwuiwa ba za ta sanar mata ta waya,tana tafiya a hankali ta waigo sai taga motarshi ya juya though bata sani ba shi yake driving ko kuma driving ɗinsa ake kamar wancan lokacin,a hankali ta sake yin murmushi kafin ta tura hannu cikin jakarta ta fito da wayarta,number Umma ta shiga kira,Umma na ɗauka tace "hello Safwa! Ya ya akayi? Kin isa makarantar?" Safwa cikin ɗoki tace "Ummana albishirinki?" Umma tace "me yake faruwa?" Safwa tace "ke dai Umma ki amsa min" a saɓule Umma ta amsa "goro.." Safwa tace "wani mutumi ne ya biyo ni yanzun nan har school,Umma kin ga motar da yake ciki? Kin gansa kuwa? Wallahi me kuɗi ne,kuma ma ɗan gidan Waziri ne shi" Umma dake saurarenta tace "alhmdllhi! Irinsu nake ta miki fatan ki samu ai,ince dai kun yi musayar lambar waya ko? Bai tafi haka nan ba?" Safwa tace "ya karɓa" Umma tace "toh shi kenan mun gode Allah,sai kin dawo ma yi maganar.. Kun yi test ɗin ne?" Safwa tace "a'a yanzun nan ai muka rabu da shi,ban ma shiga class ba ina hanya ne" Umma tace "to babu laifi sai kin dawo" Safwa tace "to Ummana.. Yawwa Umma yau Aliyu ya ce min zai zo" Umma tace "toh shi kenan sai kin dawo dai" Safwa ta amsa ta katse wayar. Around 2pm ta fito lectures,tare da wasu cikin student abokan karatunta suka fito suna tafiya suna hira har suka kai get,nan kowa ya nemi tricycle da zai yi hanyarsa ya shiga,tunda ta kamo hanyar gida take tunani da sakin murmushi,gaba ɗaya yinin yau da tayi a school ba ta da aiki banda na tunanin Hamood Waziri,lokaci² kuma tana duba wayarta,she's expecting his call amma ko new number ɗaya bai kirata ba,dai² street ɗinsu ta sauka bama ta bari yau har sai da suka shiga ciki ba,ta bashi kuɗinsa yaja machine ɗinsa ya tafi,itama ta wuce gida cikin wani irin yanayi,tana yin sallama Umma ta amsa da fara'a tana faɗin "an dawo?" Safwa tace "ehh! A gajiye nake wallahi" Umma tace "to ai sai aje a huta" Safwa tace "yanzu zanje na kwanta na samu bacci" Umma tace "sai kin tashi za ki bani labarin mutumin?" Safwa ta ɗan ɓata rai tace "Ummaaaaa!" Umma tace "ah'ah! Yo ai baki sanar min yanda kuka yi ba naga" Safwa tace "Umma ba fa yaro bane,kawai dai yana da kuɗi,ni abunda yasa ma na tsaya kenan har mukai exchanging digits,wallahi kuɗinsa ne suka tafi da ni,don baki ga motar da yake ciki ba" Umma tace "ban fahimceki ba Safwa? Kina nufin bai miki bane ko kuwa yaya?" Safwa tace "don yi gaskiya bai da makusa,kawai dai ni na fi son na auri matashi,wannan fa Allah yana da mata,ni bana yiwa kaina fatan auren mijin kowa gaskiya,na fi son na auri nawa.. Kuma ga Aley ma me zan yi da babba?" Umma ta saki baki tana kallonta tace "ke dai kam amma an yi wawuya wani lokacin,ke fa da bakinki kika ce Aliyun har yau bai san kina yi ba,tunda haka ne yanzu kin samu wani ai sai ki bashi dama kiga me zai faru,kuma Allah na tuba yaron da kike magana,ai da shi gara ki samu ubansa,shi babba advantage ɗinsa shi ne da kuɗinsa,duk abunda za ki ganshi da shi nasa ne,mallakinsa ne guminsa da wahalarsa ne,amma shi kuwa yaro nema yake" baki Safwa ta turo tace "ni dai duk da haka ina sonsa a haka,kuma wallahi ban ƙi nayi komai akansa ba" Umma ta buɗe baki tace "to shi kuma wannan fa ki kaisa ina?" Safwa tace "ni kuɗinsa kawai nabi,zan ci rabona na sallamesa" Umma tace "amma wannan ƴa kina da abun mamaki" Safwa tace "me nayi to kuma?" Umma tace "don ubanki ba haka ake yi ba,in dai ya fi Aliyu kuɗi ni dai ban damu da tsufarsa ba,ki kawoshi gida suyi magana da Babanku,cikin ƴan kwanaki ba kawai sai dai kowa yaji ana ayyiriri ba,nima zan aurar dake ki tafi gidanki,sai kuma muji da ƴan uwanki kafin su girma lokacinsu yayi suma" Safwa tace "kaiiii! Gaskiya ni dai Umma a'a kada ma ki fara wannan maganar" Umma da haushi ya ciyo tace "don ubanki ba ke kika kawo min zancensa ba? Ni da ina nan gida ban san kun haɗu ba,don na baki shawarar yanda za kiyi sai kice min ba haka ba? To ai shi kenan sai kiyi yanda kika ga ya yi miki" Safwa ta tashi tana kumbure² tace "bari na hau sama" Umma tace "ki shiga ƙarƙashin ƙasa ma daga can in kin so" Safwa ta kalli Umma ganin yanda ta haɗe rai tace "to Umma ai ba cewa nayi fa bazan kulashi ba" Umma tace "ke kika sani kuma,ni ba ni guri kada kisa raina ya ɓaci" Safwa tace "Allah ya huci zuciyarki" Umma dai bata kulata ba ta ɗauke kai ta ci gaba da abunda ke gabanta.

*HAMOOD WAZIRI*

       Yammaci sosai yana shirin barin company ya tuna yarinyar da suka haɗu,murmushi ya saki yarinyar sosai ta burgeshi,yana son abu me kyau a rayuwarsa,duk da jimawar da yayi ba ya mu'amala da wata ƴa mace,a karon farko Safwa ta ɗauki hankalinsa,yarinya ce sosai kuma yaji kawai yana sonta yana son kasancewa da ita matsayin matarsa,al'amarin da ko a mafarki bai taɓa zaton zai faru da shi ba,ɗan murmushi ya sake yi kafin ya fito office ɗinsa,office ɗin Wazeer dake opp da nasa ya ƙarasa yayi knocking,daga ciki Wazeer dake haɗa belongings ɗinsa shima zai fita yace "yes" Dad ya buɗe entrance ya shiga yana cewa "son yanzu za ka tafi ne?" Wazeer ya ɗago idanunsa yana kallon Dad,a hankali yace "yeah!" Dad yace "ok! Let's go home together" Wazeer yace "no! Ba gida zan yi ba,zan je aski ne yanzu" Dad yace "ok! Sai ka taho,ni bari na wuce" yayi masa sallama ya fita,yana ƙarasawa gaban motarsa da driver ke jiransa a gaban building ɗin Company ya fito da wayarsa,number ɗinta da ya ajiye ya shiga kira,dai² lokacin driver na buɗe masa mota ya shiga,Safwa na ɗauka da muryar bacci tace "hello!" A hankali ya ɗan yi resting bayansa jikin seat yace "hey! How are u? It's Hamood Waziri" saurin waro idanunta tayi yana mutsikasu,Hamood yace "so how was ur lectures today?" Safwa da bata gama wartsakewa ba tace "alhmdllh" Hamood yayi shiru kamar yana tunani sai kuma yace "it seems like kina bacci na tasheki?" Safwa tace "ai na tashi dama before ka kira" yace "ok! Ya mutanen gida,Mom and dad?" Tace "kowa fine" yace "good" yanda take jin turancinsa fluently sai taji kamar Aley,murmushi tayi me ɗan sauti,Hamood yace "ohh! Is this smile for me?" Safwa ta buɗe ido da kyau,tuna kuɗinsa yasa tace "yeah!" Yace "wow! Thank u.. So yaushe za'a bani appointment nazo mu gaisa,and na sanar miki ƙudiri na a kanki?" Safwa tai ɗan shiru tana tunani,Hamood Waziri yace "pleaseeee! A duba a sanar min" a hankali tace "a day after tomorrow" yace "ok! Jibi kenan in ji bahaushe?" Ta gyaɗa kanta tana ƴar dariya tace "ehh" yace "alright! Allah ya kaimu" Safwa ta amsa,yace "and ur address?" A hankali tace "will text to u" tace "ok! Thanks dear.. A gaisar da Mom" Safwa tace "za ta ji" suna yin sallama Hamood ya sauke wayar yana kallon contact ɗinta yana sakin murmushi,underneath kuma yana saƙa abubuwan da za su faru between kamar dai bai fi ace ya ƙifta idonsa ya buɗe ba,har suka kai gida murmushi yake saki,sanda driver yayi parking ya fita ya buɗe masa ya sauko ya wuce cikin gida,direct ɓangaren Daada ya shiga da sallama,Daada dake zaune tana lazumi ta amsa,ya ƙarasa fuskarsa a sake ya zauna saman kujera yana faɗin "barka da yammaci Daada" Daada dake kallonsa tace "barka dai Mamman.. An dawo lafiya? Ya aikin?" Yace "lafiya lau alhmdllh" Daada tace "yau kuma ina Zainul-abideen ɗin na ganka kai kaɗai?" Dad yace "zai je aski ne" Daada tace "to yanzu naji batu" Dad yayi ɗan murmushi kaɗan,Daada ta kalleshi tace "lafiya dai ko kake dariya kai kaɗai?" Dad ya miƙe da sauri yana sake sakin kyakkyawan murmushi yace "lafiya lau Daada" Daada tace "to alhamdulillah.." Dad dake tsaye yace "Daada bari naje nai wanka,lokacin sallah ya kusa" Daada tace "ehh! Gaskiya kam,to abinci fa?" Ya wuce yana cewa "sai na dawo daga masjid" Daada tace "to a dawo lafiya" ya amsa tare da ficewa.

*WAZEER*

     Daga Company bai dawo gida ba ya wuce zoo road plaza ɗin da yake zuwa aski,kasancewar babu mutane yasa yana zuwa akai masa ya fito ya nufo gida,dai² yana yin parking ana kiran maghreeb,bai ma kama hanyar shiga gida ba,ya wuce gaban masallaci gurin taps,a nan yayi alwala sannan ya wuce ya shiga masallaci,ana idar da sallah ya fito ya wuce cikin gida,plat ɗinsu ya nufa yayi wanka ya shirya cikin simple jallabiya fari mara adon nan,yasa hular tashi ka fita naci a kansa,yanda ya fito kamar wani ustaz,kai baza kace ma wani guri zai je ba da ya wuce masjid ko islamiyya dai haka na manya maza,wallet ɗinsa da wani ƙaramar wayar da ya siya ya ɗauka ya fito ya rufe bedroom ɗin,ɓangaren Daada ya wuce ya shiga da sallama,Daada ta ɗaga kai tana amsa masa tace "ka dawo ashe?" Cikin miskilanci yace "Mmm" Daada tace "sannu.. Ya aikin?" Yace "alhmdllh" tace "Allah ya taimaka yayi jagora" yace "ameen" Daada tace "a kawo abincin yanzu?" Girgiza mata kai yayi yace "um'um! Zan je masallaci,na ji an fara kiran sallah yanzu" Daada tace "ehh haka ne,to sai ka dawo kenan?" A taƙaice yace "ehh" ta gyaɗa kanta kawai,juyawa yayi ya fita daga gidan. Sanda ya fito masallaci bai dawo gida ba,bakin titi ya ƙarasa ya tsayar da me tricycle ya sanar da shi inda zai kaisa,ya shiga suka ɗauki hanyar state road. Dai² get ɗin gidansu Safwa ya sauka ya sallamesa,ya ciro wayarsa yana kiranta Safwa ta ɗauka tace "hello dear" yace "i'm outside" tayi dariya tace "ok! I'm coming" ta katse wayar,ko minti biyar bata yi ba ta fito gidan,ganinsa tsaye yasa ta ƙarasa inda yake tana sakin murmushi tace "welcome darling" maganar yai escaping daga bakinta,wayar dake hannunsa ƙarama me keypad ya ɗan sauke yana kallonta yace "how are u?" Ta ɗan rausayar da kai tace "i'm fine.. Ya aiki?" Yace "alhmdllh" juyawa tayi ta kalli get ɗinsu kafin tace "bismillah! Mu shiga ciki,i know u are tired" ya ɗan gyaɗa kansa yace "ok! Thanks" suka jera zuwa cikin compound ɗinsu,kujerun da Baba ya siya mata na zance ta ɗauko ta ajiye musu,ya zauna yana faɗin "thanks.." Basu yi wani hira sosai ba,don dama shi bai cika magana ba ko ya zo,Safwa ta tashi tana cewa "dear i'm coming please" yace "ok" ta wuce ta tafi cikin gida,bata jima sosai ba ta fito da tray ta ajiye gabansa,wayar dai ne a hannunsa yanzuma yana operating,Safwa ta ɗauki glass cup ta zuba masa zoɓo dake ta ƙamshin cocumber da ginger ta miƙa masa da plate na small chops tana cewa "bismillah dear.. And don't say no,ka ga dai tunda kake zuwa ban taɓa kawo maka abu ka ci ba,kuma hakan bai sa na yi zuciya na daina maka ba" kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa yasa hannu ya karɓa da faɗin "thanks" wani irin buɗe ido Safwa tayi tana kallonsa ta saki murmushi sosai tace "this is the first time da ka min abunda naji daɗi" bai ce komai ba,ya ɗauki ɗaya ya kai bakinsa,ya ɗan ci kaɗan ya sha zoɓon,duk da ba wani abu special akasa a lemon ba haka nan dai yaji ya yi masa daɗi,har guraren 9pm saura suna zaune,sanda ya kalli lokaci kafin ya fara shirin tafiya,Safwa ta rakosa har bakin street ɗinsu,suna tsaye gurin suna sake yin sallama tace "arghm! Wai me ya faru na ganka da irin wayar nan yau?" Wazeer ya ɗan kalleta kafin ya girgiza kansa yace "nothing" tace "amma ban taɓa ganinka da shi ba sai yau,ina wancan phone ɗin naka?" Kamar bazai yi magana ba kuma sai yace "ohh! An ɗauke min waya,wannan ma allowance ɗina na this month ne na siya da shi,kada ayi ta kirana ba'a samu ne" Safwa tace "ayyahhh! I feel sorry for u" yace "ohh! Thanks" bata sake cewa komai ba sukai sallama,sai da taga ya wuce ya tafi sannan ta juya tana dariya,farin ciki duk ya gama cika mata zuciya saboda soɓon data bashi ya sha da chops.

*SAFWA*

        Tana shiga gida ta tarar da missed call ɗin Hamood Waziri,waro idanunta tayi tana shirin kashe wayar saboda wani plan ɗin da yazo mata,sai kuma ga wani kiran ya kuma shigowa,kamar baza ta amsa ba taita kallon wayar dake beeping a hannunta,wani tunanin na zuwa kanta daban tai saurin ɗauka tace "hello!" Daga can gefen Dad yace "hey! How are u My dear? Ya darenki?" Squeezing face tayi ta sake cewa "hello! Are u there? Kana ji na?" Dad yace "yeah! I'm hearing u.. What happened? Ba ki jina?" Safwa dake pretend tace "ba na ji fa" sai kuma ta cire wayar daga kunnenta tana cewa "think wayar nan da ya faɗi ya samu matsala.. Ohh! Me yasa ba na ji to? Kuma bai fashe ba fa? Maybe internally ya samu problem" data tabbatar ya jita sai ta katse kiran ta kira,Dad ya ɗauka yana faɗin "hello dear" nan ma dai Safwa taita cewa "hello!² Ba na ji still,kayi haƙuri idan kana jina,muyi magana via text" tana faɗan haka ta katse kiran,sai kuma ta shiga typing message ta aika masa,tana turawa ta shiga kiran number Aley taji idan ya isa gida,suna cikin waya da shi text ɗin Hamood Waziri ya shigo,buɗewa tayi ta karanta tai masa reply,haka sukaita texting juna har sukai sallama da take cewa she's sleepy,tunani taita yi kafin ta tashi ta fita ɗakin ta sauka downstairs. 2 days da dare suna zaune parlour kiransa ya shigo wayar Bilal data karɓa aro tace tana dawowa za ta bashi,Bilal dai bai wani damu ba don shi dama haka halinsa yake,abunsa bai tsokane masa ido ba na kowa ne,cikin ƴan uwansa babu wanda bai taɓa kayansa kuma ya zauna lafiya,don bama zai ɗaga kai ba bare ya tambayeka don me ka ɗaukar masa abunsa without his permission? Wayar Safwa ta kai kunnenta tace "hello!" Hamood yace "i think in dai address da kika turo na yi following ɗinsa dai² to ina cikin street" Safwa tace "ok! Let's see.. Ga ni nan fitowa yanzun" Hamood yace "alright! I'm waiting" tana katse wayar ta wuce upstairs da gudu,turare taje ta sako da na maganinta ta sauko,Umma ta bita da kallo,Safwa ta nufi waje without ta ce komai,tana fita get ɗin gidan ta hango wani babbar mota da yayi parking 2 houses away da gidansu,wayar hannunta ta buɗe za ta kirasa,akai mata horn kafin motar ya taho inda take yayi parking,ɗaga kai tayi tana kallon motar da mamaki,ba wancan Benz ɗin bane na ranar da suka haɗu,wannan wani irin Toks range rover ne 2023 edition,driver ne yazo ya buɗe masa,Hamood ya fito daga back seat yana sakin murmushi idanunsa akan Safwa dake tsaye speechless,Hamood ya ƙarasa gabanta da sallama ta amsa tana faɗin "barka da zuwa ranka ya daɗe" yace "barka! Gimbiyar mata,na sameki lafiya? Ya su Mom?" Safwa tace "lafiyarsu lau" ya ɗan gyaɗa kansa dake sanye da hula,sai kuma yana kallon gidan Dr Sulaiman Mijinyawa yace "wannan kamar gidan Dr Sulaiman Mijinyawa,right?" Safwa ta gyaɗa kanta tace "ehh!" Yace "ai na sanshi sosai,he's my business partner" Safwa tace "Allah sarki.." Sun ɗan yi shiru Hamood yace "hope u won't leave me a tsaye haka,kin san ba na juran tsaiwa sosai" Safwa ta ɗan waro ido waje sai kuma tace "laa! I'm sorry,bismillah bari nasa a kawo maka seat" yace "o! Thanks" Safwa ta ɗaga wayar hannunta ta kira Umma,a hankali tace "Mom don Allah kisa Bilal ya kawo min chairs ɗin nan" daga haka ta katse wayar,ba'a ɗauki lokaci ba Bilal ya fito da chairs ɗin yasa a compound,sai kuma yazo yayi musu sallama,Hamood da Safwa suka amsa,Bilal ya durƙusa yace "ina yini?" Hamood ya amsa yana kallonsa da murmushi a fuskarsa,haka kawai nutsuwar Bilal ya burgeshi,yana miƙa masa hannu yace "come here.. What's ur name my friend?" Bilal yace "Bilal" Hamood tace "Bilal! Will u be my best friend?" Bilal yayi ƴar dariya yana kallon Safwa,Safwa ta ɗauke kai tace "ni bar kallona ba wani abu zance ba" Hamood yana kallonsu yace "dont look at her,za tace a'a ko?" Bilal ya sake yin dariya yana girgiza kansa,Hamood yace "ok! Will u?" Bilal ya gyaɗa masa kai,Hamood yace "wow! Nice meeting u Bilal" Bilal ya kuma kallon Safwa kafin yace "Yaa Safwa na kawo miki" Safwa da kanta ya wani huru saboda yanda Bilal ya nuna she's bigger than him tace "ok! Thanks bro" yace "u're welcome" ya kalli Hamood yace "sai an jima Uncle" Hamood yace "ok! Friend a gaida Mom" Bilal ya amsa ya wuce zai koma cikin gida,Safwa ta sake kiransa "Bro!" Bilal ya tsaya,Safwa tace "ka kawo min ruwa please" ya gyaɗa mata kai yace "toh!" Yana tafiya Safwa tace "bismillah" Hamood yace "thanks!" Suna shiga ciki ya zauna,ba'a jima ba Bilal ya kawo ruwa da cups,Safwa tai masa godiya tare da cewa "ungo wayarka Bilal tafi da shi,in na shigo zan amshi sim ɗina" yace "ok!" Ya amsa sannan ya tafi,Hamood na kallonta yace "aron waya kika yi gurin Bilal?" Safwa tayi murmushi kawai,yana kallonta da kyau ya kauracewa zancen da yake mata na aron waya yace "so! I'm here,wai hausawa suke cewa zuwa da kai,ya fi saƙo.." Nan ya shiga sanar da ita komai da ta shafesa da dalilin zuwansa,Safwa dai ta yi shiru tana saurarensa,bai iya ɓoye mata komai ba har maganar rabuwarsa da matarsa da yaransa,sai to 9pm har da wasu minutes sannan Hamood yace zai tafi,sukai sallama da shi yana kallonta yace "sai yaushe dear?" Safwa tayi murmushi kawai,Hamood yace "ok! I'm going.. Idan mun yi waya za'a sanar min ko?" Ta gyaɗa kanta tace "ehh!" Yace "ok! Ya za'ayi yanzu? Ina son ganin friend ɗina kafin na wuce" Safwa tace "ok! Bari na kirasa" Hamood yace "alright.." Cikin gida Safwa ta shiga,not too long suka fito tare da Bilal,yana zuwa ya ɗan sunkuyar da kansa yace "Uncle ga ni" Hamood ya kama hannunsa yana kallon Safwa yace "za muyi magana ne,u can go" Safwa ta buɗe ido tace "ohh! Kuna korata kenan?" Cikin barkwanci Hamood yace "nope! Sirri za muyi irin na friends" Safwa tace "ok! Sai da safe" daga haka ta tafi ciki,tana tafiya Hamood yaja hannun Bilal suka fita gidan,bakin motarsa suka tsaya,driver ya sauko motar yana faɗin "barka da fitowa ranka ya daɗe" Hamood ya amsa yana faɗin "open the booth ka fito da kayan da suke ciki,sai ka tayashi ku shigar da su cikin compound" jikinsa na rawa ya amsa ya buɗe ya sauko da manyan ledojin da suke ciki,da taimakon driver suka shiga da kayan compound,Hamood na kallon Bilal ya zaro 5K ya bashi yana cewa "next time za mu haɗu friend,kayan na Aunty'nka ne ka kai mata" Bilal yayi masa godiya sosai,suna tafiya Bilal ya wuce cikin gida,manyan ledojin ya ɗauka ya shiga da su,a parlour yana yin sallama Umma da Safwa suka amsa,da kallo suka dunga binsa ya ajiye ledojin gaban Safwa yace "gashi injisa.. Umma kinga ya bani kuɗi" ya fito da kuɗin ya bata,Umma ta lissafa taga 5K sababbi,kai da ganinsu za ka san daga cikin ƴan uwansu aka fito da su,Umma ta washe baki tana faɗin "ahh! Lallai Safwa kin yi kamun babban kifi.. Bari muga meye a cikin nan kuma" ta janyo ledojin ta shiga bubbuɗewa,manyan set ne na kayan kwalliya da turaruka masu tsada,sai ɗaya ledar kayan ciye² ne chocolates masu yawa,sweets,ice cream,cakes,manyan biscuits masu tsadar gaske,da fruits da akayi packaging fresh one,Umma sai murna suke aka shiga bubbuɗe biscuits da komai ta fara rabawa,kayan turarukan kuma tana kallon Safwa tace ta kwashe ta mayar cikin ledan,sai ga wani leda me kyau a ciki ƙarami da basu kula da shi ba,Safwan tasa hannu ta ɗaukoshi tana faɗin "mene ne wannan a ciki?" Tana fito da shi taga waya ne apple product iPhone 14 pro max,kan kace me ta fasa wani irin ihun murna tana faɗin "wayyoo Allah! Umma my dream phone" ihun da Safwa tayi yasa Awwal saurin shigowa yana faɗin "lafiya ke kuma?" Bilal yana taya ta murna yace "waya aka kawo mata yanzun nan" Awwal ya zauna yana kallon kayan da suke barbaje a parlon yace "wannan kuma fa?" Umma tace "duka nata ne" Awwal ya zauna yana cewa "aahhh! Bari mu zauna ayi damu,yau banza ta faɗi.. Shi ɗin wane ne ko nace wane me kuɗin banzar ne?" Bilal yace "wani saurayinta ne yazo,nima ya bani 5K" da sauri Awwal yace "haba?" Bilal yace "wallahi suna gurin Umma na bata ta ajiye min" Awwal yace "zo kaji ɗan ƙanina" da sauri Umma ta ɗago taiwa Awwal wani kallo tana tura cake bakinta tace "babu abunda zai ji,yazo kayi masa wayo ko? Saboda bai san daɗin kuɗi ba?" Awwal yace "Umma don Allah kiyi shiru babu ruwanki a cikin maganarmu,wannan tsakaninmu ne" Umma tace "sai kayi kuma,ba dai kuɗin suna hannuna ba?" Ta ci gaba da kasonta tana yi tana sa wani a bakinta,Safwa ta sauko daga sama bayan tasa wayar a charge ta ajiye kayan da Umma tasa ta tafi da su,Awwal ya kalleta yace "ina tsohuwar taki wayar to? Ina riƙonta" Safwa tace "taka kuma fa?" Yace "haɗawa zanyi na siyar sai na canja wata nima" tace "to akwai wanda naiwa alƙawarin zan bawa" Bilal dake zaune yace "kaiii Yaa Safwa ki bashi mana please,abun duniya fa fararre ne kuma ƙararre" Safwa ta wurga masa wani kallo tace "bazan bayar ba ɗin,tunda ka damu ka bashi kuɗin nan sai ya cika ya siya" Bilal yayi shiru yana kallonsu,lokaci ɗaya yace "Umma bani kuɗina" Umma tace "me za kayi da su yanzu da daren nan?" Yace "a'a so nake zan siya banki sai na dunga tarawa" Umma tace "to bazan bayar ba,idan ka siyo ka kawo min bankin zan ajiye maka shi gurina" a hankali ya kalli Awwal sai kuma ya koma ya kwanta jikin Awwal ɗin yai masa raɗa,babu wanda ya jisu tsakanin Umma da Safwa,gara ma ita ta ga abunda ya faru amma Umma hankalinta na kan kason da take,tana gamawa ta ɗago tace "Safwa zo ki ɗauki naki gashi nan" Safwa ta ƙarasa tana kallon kashi²n da Umma tayi har 7,tace "Umma wai dawa² kika raba ne?" Umma tace "dukanmu mana har Babanku" Safwa tace "auuu! Thought kin yi makuwa ne da farko" Umma dai bata ce musu komai ba,Safwa ta ɗauka sannan Umma ya bawa su Awwal nasu,suna ci suna hira Bilal yace "Umma ki ɗan bani 1K please,zan yi amfani da shi na siya wani littafi gobe" jin ya ambaci littafi yasa Umma ta ɗauko ta bashi tana cewa "tunda dai harkar makaranta ne ga shi" yana karɓa yayi murmushi ya bawa Awwal tare da yi masa alamar kada yayi magana,Safwa dake kallonsu ta buɗe baki tace "munafiki.. Wallahi Umma ƙarya yayi miki,Awwal ya bawa ina kallonsu" baki buɗe Umma tace "ni zaku yima wayo? Lallai ma yaran nan,na haifeku kuce za ku maida ni wata sakarai?" Awwal na hararar Safwa yace "banza ƴar ciki baƙi" Safwa ta waro idanunta waje tace "ni kake cema haka?" Yace "an faɗa ɗin" Safwa tace "kanka ka yiwa baƙin ciki wallahi" Bilal yana kallon Umma fuskarsa da murmushi yace "Umma ki yi haƙuri,kema ki ɗauki 2K,sai ki bawa Yaa Safwan 1,1 kuma ki rabawa Asim da Zunnu 500²,ni sai ki ajiye min 1K" Umma ta tsaya tana kallonsa da mamaki,tace "to ai ka rabar mana da kuɗin duka" yayi murmushi yace "abunda ka bayar shi ne rabonka Umma,haka Mu'allima take faɗa mana,ta ce mu dunga yin kyauta da sadaƙa,suna maganin masifa da annoba" Umma ta gyaɗa kanta tace "Allah sarki Bilaluna,da kai ne babba wallahi na san zan ji daɗi sosai.. Allah ya raya min kai,ya maka arziki me amfani" Bilal yace "ameen Ummana.."

*WAZEER*

     Zaune yake ya tisa MacBook gaba yana wani aikin da ya shafi Company su na Waziri pharmaceutical,kiran da ya shigo tsadadden wayarsa yasa ya ɗan tsaya kaɗan tare da kallon wayar dake gefensa,sunan wacce yaga tana kiransa sanda yasa gabansa faɗuwa,yayi shiru kamar bazai ɗauka ba,sai kuma yayi answering tare da saka wayar a speaker,dama halinsa ne idan yasan za ka wuce 1 minute kuna magana,saboda ba zai juri barin wayar a kunnensa ba,ya gwammace ya saka a speaker ka faɗi duk abunda kake so yana saurarenka,a hankali yace "assalam alaikum.." Da sauri Safwa tace "hello dear" yana ɗan tsayar da aikin da yake yace "hey! How are u? Why baki amsa sallamar ba?" Cikin ƙaguwa tace "sorry! But zan iya ganinka gobe?" Yayi shiru kamar zai ce a'a sai kuma yace "what's happening?" Safwa tace "nothing.. I just want to see u" yana ɗan gyaɗa kansa yace "ok! I will sort everything out da wuri,zan zo in sha Allah" tayi murmushi da wani excited murya tace "alright! Sai na ganka,me zan ajiye maka?" Yayi shiru kamar yana tunani,Safwa tace "should i make u soɓo irin na ranar can?" Wazeer ya ɗan lumshe idanunsa,har ransa ba ya buƙata amma kuma ya kasa ce mata a'a,sanda sukai sallama ya ajiye wayar tare da yin shiru yana nazari. Washe gari da ya dawo gurin aiki a gurguje ya shiga gida yayi wanka ya fito ya shirya,yau ma jallabiya ne jikinsa me arha gray color,sai ƴar wayarsa me keypad daya jefa a aljihu,ka ganshi baza ka taɓa cewa ya mallaki wani abu ba na dukiya,ya koma wani irin talaka futuk,sanda ya yi sallar maghreeba da ishaa kafin ya wuce GRA,yana sauka ya ƙarasa get ɗin gidan ya tsaya waje,wayar ya fito da shi ya kirata,Safwa na ɗauka tace "hello Baby,ka ƙaraso ne?" Wazeer yace "yeah! I'm outside" tace "to ka shigo compound gani nan saukowa" yace "ok!" Suna ajiye wayar ta fito daga ɗakinta sai ƙamshi take,ƙasa ta sauko tasa Bilal ya kai mata chairs waje,tana fitowa ta tarar da shi zaune yana lallatsa wayar hannunsa,tayi ɗan ajiyar zuciya tana zaunawa tace "welcome Babe.." Yace "thanks.. How are u? Ya Mom?" Tace "she's fine" yace "maa sha Allah" yanda ya faɗa sak irin yanda ustazai suke yi ne,Safwa bata san sanda ta fashe da dariya ba,Wazeer ya tsaya kallonta da idanunsa masu cike da kwarjini,bai dai ce mata komai ba har ta dakata don kanta,yana kallonta yace "kiran fa?" Safwa ta ɗan buɗe ido kafin tace "ok! Wait a little,bari na dawo" yace "ok!" Bata jima ba ta dawo da tray da kwalin wayarta a kai,tana zuwa ta ajiye tray ɗin ta ɗauke kwalin,lafiyayyen jellop ta buɗe da yaji dry fish da spices sai ƙamshi yake,tasa spoon tare da miƙa masa tace "eat first then sai muyi magana" ya kalleta kaɗan kafin ya sauke idonsa akan abincin,ba girkin kowa yake ci ba,in fact ba ma komai ya iya ci ba shi a abincin Nigeria,tuna yanda suka yi 3 days ago kawai yasa ya amsa,Safwa ta waro idanunta waje tace "awwnnn! What am i seeing? Yau za ka ci abincina?" Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe,sosai zuciyarsa ke bugawa fast²,yana jin kamar bai yarda da abincin ba da ita kanta,ganin ya kasa ci Safwa ta kai hannu ta ɗauki spoon ɗin ta ɗebo kaɗan ta kai bakinta,Wazeer ya buɗe ido yana kallonta irin kallon mene ne haka? Amma kuma bai yi magana ba,ta kalleshi itama idanunta sun yi rau² tace "na ga kamar baka yarda da ni ba har yanzu,na ci ka gani babu komai cikinsa" ɗan buɗe ido yayi yace "what?" Hawaye na ciccikowa idanunta tace "ni ban san me kake tunani ba,amma ina jin kana zargin ina saka maka abu ciki shi yasa ba ka ci ko?" Cikin in'ina yace "um'um!" Tace "wallahi haka kake nufi,idan ba haka ba kuma me yasa ba ka ci?" Yace "last time da na zo ai na ci" tace "ehh ka ci amma ai ba abinci bane" yace "please Safwah.. Ni ba komai nake iya ci bane yanzu,kin san ban jima da dawowa Nigeria ba,na faɗa miki na je karatu,and it takes me long enough a can" Safwa ta tsaya kallonsa kawai,yace "believe me ban yi tunanin komai ba,if it's chops zan ci,abinci me nauyi ba ya shiga cikina da dare" tace "ok! Na ji wannan,amma ai ba cewa nayi sai ka cinye ba,just 3 spoon ma kayi zan ji daɗi" yace "ok²!" Bai jira me za tace ba ya ɗauki spoon ɗin,sanda yayi bismillah kafin yaci 3 spoon,Safwa ta saki ajiyar zuciya tace "thanks.. Hopefully za kana ci idan na kawo maka ko babu yawa?" Ya gyaɗa mata kai yace "in sha Allah.." Cikin jin daɗi ta ɗauko tsohon wayarta Galaxy S3 ta miƙa masa,ya kalli wayar ya kalleta yace "na mene ne?" Safwa na karyar da kai tace "tukuici ne,ka karɓa kayi amfani da shi,ni na samu wani" yana girgiza mata kai yace "um'um! A hankali zan siya wani" tace "idan ba rainawa kayi ba ka amsa please" sake girgiza mata kai yayi kafin yace wani abu ta haɗe rai kamar za tayi kuka tace "ni dai Allah sai ka ansa,idan ba haka ba bazaka sake ganina ba" ajiyar zuciya yayi yana gyaɗa kansa yace "ok! Thanks.." Kafin yace komai ta ɗaga masa hannu tace "stop please.. Ni ba sai ka yi min godiya ba,mene ne don na baka wayar da yama tsufa? Ni naga dama ai na baka ba tambayana kayi ba,komai nayi maka ban faɗi ba because I LOVE U.."

         #🤔🙄 To fa! Da gaske ne wannan maganar please ko dai mafarki ne?

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Continue Reading

You'll Also Like

33.2K 2.7K 34
#Winner of The Awesome Awards 2018 & Stardust Awards 2018(chicklit category) 4 in #friendfiction on 11/07/2018 6 in #husbandandwife on 23/05/2018 The...
2K 77 23
An innocent love story between a village girl and the crown prince. ~~~ Blair Wettin, a village girl, finds her life turned upside down when she is...
Love and Lies By Bitsy

General Fiction

43K 3.2K 31
**SPIN OFF OF MARRIED TO MY BEST FRIEND** LOVE...The feeling that makes you feel complete. And once blessed with it, you do everything to cherish it...
432 54 19
The cycle of sahil-Gautami to Anirudh-Gautami to again Gautami-sahil to let's see who's next sooooo what's next? let's dig into this story with me...