WAZEER!

By REAL-SMASHER

3.2K 338 50

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... More

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Wedding march
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mission
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Strangerlike
Safwah
Adviceful
Thought pattern
Proposalist
Her wish!
Wedding bell!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Inexplicable

88 10 0
By REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               22

#Inexplicable

           Rasa me za tace masa tayi saboda yanda maganar yazo mata ba-zata,yana aiko mata sanyayyan murmushi yace "idan baki shirya ba kada kiji komai,just tell me,zan iya jiranki har zuwa lokacin da kika ji kin amince" a hankali ta girgiza kanta tana sauke idanunta ƙasa tace "ni bance haka ba" yace "ok! Me Matar Abuu Turab tace?" Da sauri ta kautar da kanta gefe tana dariya me cike da kunya,yace "Baby are u ready? Ko kina ganin mu jira zuwa wani lokacin?" Tace "Mmm!" Yace "Mmm.. What?" A ɗan kunyace tace "i'm damn ready?" Ya buɗe ido sosai yace "u are damn ready,kike kallon wani waje daban?" Kamar za tayi kuka tace "to da sai nayi yaya?" Yace "sai ki kalleni ki sanar min mana" ta juyo a hankali idanunta sun yi rau² tace "ni bazan iya kallonka ba" yana mata murmushi yace "ok! Yanzu dai kin amince na yi magana da Daddy?" A hankali kamar ba ta so ta gyaɗa masa kai,yace "wow! Thanks Sweet.. In sha Allah zan yi magana da Daddy kafin na zo Kano,and duk yanda muka yi zan sanar miki sai ki sanar da su Abba zuwan mutanena ko?" Ta ɗan ɓata fuska kaɗan sai kuma tayi murmushi tace "ok! Allah ya kaimu" yace "ameen" basu jima ba sukai sallama,ya katse wayar da alƙawarin sake kiranta not too long,wani irin riƙe wayarta tayi,lokaci ɗaya fuskarta ta cika da wani irin yanayin da ba ya buƙatar fassara,kana kallonta za ka iya hango tsantsar farin ciki kwance cikin idanunta da ilahirin kyakkyawar fuskarta,dai² tana sakin ƙayataccen murmushi Baniynah ta shigo tana faɗin "wai matar nan zaman me kike yau a ɗaki? Ki sauko muyi breakfast kin ƙi kin zauna nan ni kin barni sai jiranki nake,cikina tun ɗazu sai kuka yake wallahi kamar babu ƴaƴan hanji fa" murmushin da taga Muniba na yi ya ɗauki hankalinta,tana binta with a suspicious look tace "a'ahh! Wannan smile² ɗin fa Sweetheart?" Muniba ta ɗago tana kallonta,murmushin ta sake yi mata tare da miƙa mata hannayenta duka tace "come Sweet ki ji" da sauri Baniynah ta kama hannunta ta zauna kusa da ita,tana buɗe manyan idanunta tace "what's up?" Muniba tace "albishirinki?" Baniynah tace "goro fari tass" Muniba tace "ok! I have 2 gist for u,wanne kike son ji?" Baniynah tace "duka.. Allah yasa masu daɗi ne" Muniba tayi ɗan jim kafin ta taɓe baki tare da gyaɗa kanta tace "Mmm.. Maybe" cikin ƙaguwa da son jin me za ta faɗa Baniynah tace "don Allah faɗa min,am eager naji ko mene ne yasa ki farin ciki da safen nan" Muniba ta gyaɗa kanta tana ƙunshe dariya tace "Yayanki akaiwa ƙarin girma,kin san ya yi promotional exam,so ya yi passing ya hau rank ɗin Colonel,yanzun nan ya kira ya sanar min" Baniynah tace "awwnnn! Ina taya murna Sweetheart,Allah ya tabbatar da alkhairi.. In sha Allah zan kira na masa Allah ya sanya alkhairi.." Muniba tace "ameee yah Allah" Baniynah tacce "na ji na farko saura na biyun" Muniba tace "kin san me yace min kuma?" Baniynah tace "wait! Shi ne ɗayan labarin?" Muniba ta gyaɗa mata kai,Baniynah tace "a'a! Me yace?" Muniba ta sauke ajiyar zuciya,a hankali ta ɗan sha mur kamar abunda za ta faɗa mara daɗi ne,a sanyaye tace "cewa yayi zai yi magana da Daddy za su zo ayi maganar auren.. Muuu" wani irin ihun murna Baniynah ta fasa da ƙarfi ta rungume Muniba tana faɗin "Alhamdulillah! I'm so so so happy Sweetheart,Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" Muniba tayi murmushi tana rungumeta back tace "ameen.. Amma kin san mene ne?" Baniynah tace "a'a" Muniba tace "wai cewa yayi idan ya kira Daddy duk yanda suka yi,zai sanar min sai na faɗawa su Abba,amma ai kinga bazan iya samun Abba na faɗa masa ba ko?" Baniynah tace "ohh! Noo.. Kada ki damu zan sanar da Mami,idan kun yi maganar sai ki sanar min sanda suka yanke za su zo" Muniba ta saki murmushi tace "ok! Thanks" Baniynah tace "yanzu dai matar Colonel tashi mu tafi muyi breakfast,kin san idan ciki ya ɗauka to komai zai zo da sauƙi,ba'a haɗa jin yunwa da komai" Muniba tace "toh Matar Dr Khalifa Mijinyawa mai rumbun zani,tashi mu tafi kafin kisa yazo yaga laifina" Baniynah tayi fari da ido tace "ya son ranki?" Muniba dake dariya tace "ahh! Ai kin fi kowa sani" Baniynah tai dariya ta kama hannunta tace "let's go ni dai yunwa nake mugun ji" suka miƙe suka fito Muniba na tsokanarta.

*SAFWA*

       Kwance take saman gadonta,fuskarta ɗauke da annuri wanda za'a iya kira da cikakken murmushi,a hankali tunaninta ya fara barin jikinta yana nausawa duniyar tunanin yanda al'amura suka tafiyar mata cikin kwanakin da suka gabata,yanda komai yazo cikin sauƙi sam bata taɓa zato ba bare tsammanin abu makamancin haka zai faru nan kusa,tuna a yanda suka je gidan Hjy Gaaji ita da Umma yasa ta sake gyara kwanciyarta tai wani kamewa,nutsuwa ya saukar mata tamkar wacce ke gaban wani babban shugaban da ake tsananin girmamawa. Da farko sanda suka je gidan,though ta ga yanda mutane suke zuwa suna karɓar magani,ita dai haka nan kwata² jikinta bai bata za ta samu abunda take muradi ba,sai dai ta zauna ne ba tare da tace uffan ba,amma underneath gani take babu abunda zai faru har sanda aka zo kansu,after sun shiga suka gaisa da Hjy Gaaji warce Umma ta nutsu ta shiga yiwa bayanin matsalar data kawo su ta ɓangaren Safwa,bayan ta gama saurarensu ta ɗebo kaya ta harhaɗa mata magunguna tare da yi musu bayanin yanda za'ayi,Safwa dai kawai ta yi shiru ne ta karɓi tarin magungunan da Hjy Gaaji ta bata,har da wani zanen hatimi da aka yi a plain papers wanda aka zagaye da rubutun larabci tare da sunan Aley a jiki da nata,su ne wanda Malamar tace ta dunga dafa ɗaiɗaya safe da dare da ruwa kaɗan tana tacewa ta sha,takardar kuma ta tara ta busar da ita sai ta ƙona,banda rubutu kuma da za ta sawa zuma tsayin kwana 7 tana sha da sauran su turare. Kamar wasa ta karɓo suna zuwa gida Umma tasa ta fara yi,wani lokaci ma Ummar da kanta take dafa mata saboda ta fahimci ta fara saka shiririta da wasa,kullum da kalar nasihar da Umma ke yi mata akan banzatar da maganin da take shirin yi,abun kamar wasa ko ace almara,sanda ta gama tasa ta kira Hjy Gaaji kamar yanda tace mata idan ta gama ta kirata ta sanar mata abunda taji,Hjy Gaaji tace "shi kenan ƴata,kinga yanda kikasa takardun nan a ruwa suka lanƙwame?" Safwa tace "ehh Aunty Gaaji" Hjy Gaaji tace "kamar haka zuciyarsa za ta sassauto sai yanda kika so ayi,amma idan kina so zan iya yi miki haɗin baƙar mallaka,wanda ko waye zai ce masa kaza a kanki zai iya jayayya,ko da kuwa ace uwarsa ce mahaifiya" Safwa tace "ina so Aunty,amma sai dai har yanzu ba ya kirana,ko a chat ma bai cika min magana ba" Hjy Gaaji tace "kada ki damu da duk wannan,kina da lokaci yau?" Safwa tace "ina da shi" Hjy Gaaji tace "to idan za ki iya kizo anjima gurin la'asar.. Kin san inda za ki samo nono kindirmo? Pure one nake nufi ba madara ba" Safwa tace "ehh baza'a rasa ma a gida ba,Baba na kawowa saboda yana son fura" Hjy Gaaji tace "maa sha Allah,ki taho da nonon,sai ɗanyen ƙwai guda 3" Safwa tace "toh! Aunty" Suka yi sallama,suna gama waya Safwa ta tashi tabi Umma kitchen tai mata bayanin yanda suka yi,Umma tayi murmushi tace "sai ki haɗa kayan tun yanzu ko,kada ki manta ki tafi haka" Safwa tace "to Umma.." Daf da la'asar ta gama shiri,ta fito ta ɗauki ledar data ajiye na kayan da za ta tafi da su,ta yiwa Umma sallama,Umma na mata fatan sauka lafiya da saƙon gaisuwarta ga Hjy Gaaji,daga GRA zuwa unguwar Ɗorayi Fanshekara da tafiya,me napep na sauketa ta sallemesa ta shiga lungunan da ƙafa,tana tafiya tana addu'ar Allah yasa babu mutane sosai,ko data iso gidan shiru ta tarar babu hayaniyar mutane ƴan zuwa karɓar magani,tayi sallama tsakar gida me aikin Hjy Gaaji ta amsa tare da gaisar da Safwa ta amsa tace "Aunty na nan?" Yarinyar ta gyaɗa kai tace "ehh tana ciki,ki shiga"Safwa tace "ok!" Bakin ƙofar shiga parlon da Hjy Gaaji ke zama ta gana da mutane ta ƙarasa ta sake yin sallama,daga ciki ta amsa tun bata ga fuskarta ba tare "bismillah! Shigo Safwa.. Ni kaɗai ce yau kin yi sa'a babu mutane ko?" Safwa ta shiga tana sakin murmushi tace "wallahi kuwa Aunty.. Tunda na taho nake addu'ar Allah yasa babu layi" Hjy Gaaji tayi murmushi tace "ai nima ganin babu jama'ar yasa nace kizo yau" Safwa ta zauna saman carpet tana faɗin "ina yini Aunty?" Hjy Gaaji tace "lafiya lau,ya Hjy Murja da ƴan uwan naki?" Safwa tace "duk suna nan lafiya,Umma ta ce a gaisheki" Hjy Gaaji tace "ina amsawa,duk kowa lafiya a gidan naku?" Safwa tace "ehh alhmdllh" Hjy Gaaji tace "toh! Yanzu ya muke ciki?" Safwa tayi ɗan murmushi kawai ba tare da tace komai ba,Hjy Gaaji tayi murmushin itama tace "kin yi shiru Safwa" Safwa ta ɗan yada kai tace "ai Aunty ban san me zance bane" Hjy Gaaji tace "toh ina abubuwan da nace ki zo da su?" Safwa tace "ga su" ta buɗe jakarta ta ɗauko tare da miƙawa Hjy Gaaji,ta karɓa ta fito da komai ta ajiye gabanta tana kallo,kafin tace "ban ce miki ki nemi hanta ba ko?" Safwa ta gyaɗa kai tace "ehh" Hjy Gaaji ta gyaɗa kai tace "to idan kin koma gida lallai² ki nemi hanta zan baki rubutun da za ki dafa da shi yanzu" Safwa tace "toh Aunty" plate Hjy Gaaji taja dake kusa da ita ta tashi ta fita ta wanke,sanda ta dawo ta ɗauki nonon ta juye a ciki sannan ta ɗauki alƙalami da tawada ta shiga rubutu a saman nonon,Safwa duk tana zaune tana kallo da mamakin abunda take rubutawa,tana gamawa ta miƙo mata tace "karɓi wannan,ki kira sunansa sau 3 a ranki,sai ki yi bismillah ki shanye" Safwa ta karɓar tayi yanda tace mata,tana shanyewa ta ajiye plate ɗin,ƙwan da Hjy Gaaji ta fito da su daga leda ta ɗauka tayi rubutu a duka ta ajiye,sai da suka bushe sannan ta kalli Safwa tace "kin ga wannan ƙwan?" Safwa tace "ehh" Hjy Gaaji tace "za ki dafa su idan kin koma gida,ki ɓare ki cinye lokaci ɗaya,baza ki zubar da ɓawon ba saboda rubutun dake jikinsa,ko da kin dafa za kiga bai fita ba,za ki busar da shi a inda ya dace,sai kiyi wanka.. Sai maganar mahaɗin hanta,shima ga shi nan,ki dafa ki cinye ke ɗaya.. Sauran bayanin sai daga baya,amma idan kin yi duk abunda na faɗa miki babu kuskure,ina tabbatar miki za ki sha mamaki,a yau ɗin nan ba sai gobe ba Aliyu zai kiraki" Safwa ta buɗe baki da mamaki,farin cikin da maganar Hjy Gaaji yasa ta har fuskarta sai da ta nuna,tace "Allah yasa Aunty" Hjy Gaaji tayi murmushi tace "shi kenan Safwa,za ki iya tafiya kada kiyi dare a hanya ko?" Safwa tace "toh Aunty,na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma" Hjy Gaaji tace "ameen².. Ki gaida gida da Umman takı" Safwa ta amsa da "za ta ji" sannan ta fito gidan. A hanya ita kaɗai take ta saƙe² a zuciyarta,dai² tana shiga line gidansu kafin ta sauka tricycle kira ya shigo wayarta dake jaka,Safwa ta nuna masa get ɗinsu tace "in ka samu guri sauke ni nan" me tricycle yace "toh!" Jakarta ta buɗe ta ɗauko wayarta,sunan data gani screen ɗin wayar yasa ta ƙarasa sauka,da sauri ta ciro kuɗinsa ta bashi tare da ɗaukan kiran ta juya ta nufi get ɗinsu tace "hello!" Wazeer da ya kirata yace "how are u doing?" Safwa tace "i'm good" a hankali yace "where are u now?" Tace "ga ni na dawo daga unguwa" yace "u are not home yet?" Tace "a'a na dawo gida zan shiga" yace "ok! Idan kin huta za muyi magana anjima?" Tace "Allah ya kaimu" yace "ameen.. Thanks,a gaida Mom" tace "za ta ji" yana katse kiran Safwa data shigo compound ɗinsu ta buga wani tsalle da faɗin "yesss!³ Wallahi na yarda da abunda Aunty Gaaji tace,bari ma na kirata na faɗa mata ya kira ni,ai ya kamata ace ita ta fara jin abunda ya faru kafin kowa tunda ita tai silar da haka ta faru" tayi maganar tana duba number da tayi saving da Malama Gaaji,tana kira ta ɗauka da faɗin "ƴata kin isa gida lafiya?" Safwa tace "lafiya kau Aunty.. Kira nayi na sanar miki yanzun nan na sauka napep zan shiga gida ya kirani,ya ce za muyi magana anjima" Hjy Gaaji tace "maa sha Allah.. Lallai ashe bai da jini mai ƙarfi tunda tun ba'a je ko'ina ba har mun fara matsashi" Safwa ta washe baki tace "wallahi kuwa Aunty" Hjy Gaaji tace "shi kenan,ki samu ki kammala sauran ayyukan,in son samu ne ki yi su a daren nan" Safwa tace "in sha Allah Aunty zan yi,na gode sosai Allah ya taimaka ya ƙara girma" Hjy Gaaji tace "ameen.. Sauran bayanin da aiki ma yi magana later" Safwa tace "toh Aunty,sai anjima.." Wani irin ihu ta sake yi tare da buga ɗan tsalle ta shiga rawa saboda farin cikin da yai mata yawa,a haka ta shiga parlour tana kwaɗa sallama,Umma dake kitchen yanda taji yanayin muryarta yasa ta fito,Safwa ta tafi da sauri bakinta ya ƙi rufuwa ta rungumeta tana cewa "Ummana!" Umma tace "na'am! Ya akayi? Murnar me kike haka?" Safwa tace "zo ki zauna Umma kiji" Umma tace "toh!" Suka zauna saman kujera,tas Safwa ta sanar da Umma abunda ya wakana a ɗan tsukin da ta fita,Umma ta saki murmushi da faɗin "alhamdulillahi! Ai haka muke fata,Allah dai ya dai²ta mana lamurran nan.. Sai ki tashi kiyi abunda ya dace,bari na kira Awwal na aikeshi abature ya siyo hantar,yanzu ne dai² lokacin da za'a same shi da arha saboda yamma ya yi kowa na so ya siyar da abunda ya rage masa ya tafi gurin iyali" Safwa tace "Umma kin gama girkin na dafa ƙwan?" Umma tace "ehh yanzu nan na kashe gas shigowarki,sai ki sake kunnawa ai ki ɗora" Safwa ta miƙe ta nufi kitchen da ledarta a hannunta. Guraren maghreeba Awwal ya shigo da leda ya bawa Umma dake zaune parlour,Umma ta ƙwalawa Safwa dake sama kira,ba'a jima ba ta sauko,Umma ta miƙa mata ledar tace "gashi nan an siyo miki" Safwa tayi ƴar dariya tace "Umma ni fa ban san ya zanyi ba" Umma tace "yo ni zan ci miki? Karɓi kije ke kika sani kuma" Safwa ta zauna gefen Umma a shagwaɓe tace "don Allah Umma" Umma tace "a'a bazan dafa miki ba,kije ki dafa da kanki,ni nawa lokacin waye yai min?" Safwa tace "kai Umma" Umma tace "ai gaskiya na faɗa,da kin mayar da hankali kin koyi girkin me zai gagareki yanzu? Tashi ki bani guri ni,hutawa nake na gaji wallahi da kai kawo" Safwa tace "Umma please" Umma tai mata wani kallo kafin tayi ƙwafa tace "tashi muje" Safwa tace "yessss!" Umma tai saurin kallonta tace "ai ba ni zan dafa miki ba,zan dai taimaka miki ne na gaya miki yanda za ki zuba komai" Safwa tace "hakanma it's ok.." Umma na tsaye kanta ta wanke ta ɗora a wuta,aikinta sai dai tace zuba kaza,yi kaza,har ta gama,Umma ta juya ta fice tana cewa "dama idan kin fito ki wuce ɗakinki ki ci,tunda kin san ba'a so kowa yaci,babu wanda ya gani bare kisa azo ana tambayata ina nawa²?" Dariya Safwa tayi ta wuce sama da plate ɗin hanta da dafaffen ƙwanta a gefe guda 3,tas ta cinye ta kora da soɓon data ɗebo a cup.. Abunda ma Safwa batai zaton zai faru ba sanda ta gani da idonta,ta kuma tabbatar lallai Hjy Gaaji maƙura ce a ɓangarenta,tun daga ranan duk abunda ta bata tace tayi ko shakka bata yi take aiwatarwa,sai dai me? Har zuwa yanzu da lokaci ya ɗan tura,tana tare da Aley amma ta kasa sanin waye shi? Ɗan waye? Mene ne sana'arsa? Kimanin watanni biyu kenan da komai ya kankama,amma sau ɗaya bata ji wata kalmar dake nuna soyayyarta ta yi nisa a zuciyarsa ba,ko even ya furta ma baiba,sai dai suna waya sosai,har yazo gidansu ma,yanayin maganarsa kaɗai zai bayyana maka yana son yin magana a wasu lokutan amma sai taji shiru,ta yiwa Aunty Gaaji waya ta sanar mata,ita ke cewa ta zuba masa ido,lokaci ne bai ba,wata rana zai furta yana sonta,ita dai ta ci gaba da shiga jikinsa,cikin hikima da kissa,da sannu za ta samu abunda take so,yau ga shi lokaci na ta tafiya,kwanaki suna juyawa sati,sati na haɗuwa ya koma wata,tun tana lissafin yau ne ko gobe,har yau dai shiru kake ji wai malam ya ci shirwa. A hankali tayi juyi tana sauke ajiyar zuciya,a fili ta furta "when Aliyu za ka ce *KANA SO NA?"*
       

*MUNIBA*

       Suna saukowa downstairs suka samu Mami zaune tana aiki,Baniynah ta zauna tana dariya tace "Mami!" Ba tare da Mami ta ɗago ba tace "ya akayi my dear? Akwai wani abu da kuke buƙata ne?" Baniynah tayi ƙasa² da murya tace "noo! I just come to tell u something" Mami tace "uhumn! I'm all ears dear,what's it?" Baniynah tace "dama zan sanar miki ne an yima surukinku ƙarin girma" Mami ta ɗago kaɗan tana kallonta ta cikin anti blue glasses ɗin idonta fuskarta ɗauke da mamakin maganar da tayi mata,underneath kuma tana tambayar kanta wane surikin nasu? Don ita tunaninta ma bai kawo kan Lieut ba,tace "wane surukin namu?" Baniynah tace "Lieut" Mami ta ɗan saki fuska ta ƙara faɗaɗa fara'ar fuskarta da faɗin "maa sha Allah.. Allah ya sanya alkhairi" Baniynah tace "ameen².." Mami tace "yaushe kika samu labarin nan?" Baniynah tace "yanzun nan" Mami tace "Allah ya tabbatar da alkhairi.. A bani numbersa,zan kira na masa murna in sha Allah da kaina" Baniynah tace "bari nasa miki" ta ɗauki wayar Mami ta shigar mata da digits ɗin then tayi saving da yanda Mami za ta gane sannan tace "Mami bari naje muyi breakfast na dawo" Mami tace "ok my dear!" Baniynah na ɗagowa ta kalli inda Muniba ke tsaye kamar statue,suna haɗa ido tayi mata dariya ita kuma ta harareta kafin ta juya ta bar parlon zuwa dining room,Baniynah ta fara dariya tace "mene ne za ki wani harareni? Dan na faɗa? To ba abun alkhairi ne ya faru ba?" Muniba dai bata kulata ba tai wucewarta,Mami ma murmushi kawai tayi ba tare da ta ce musu komai ba ko even kallonsu,idan da sabo wannan halin nasu ya ci ace ta saba don tun ƙuruciyarsu suke yi yar yanzu kuma basu fasa ba,sai dai in ba'a zo irin gaɓar da za suyi ba. Suna zaunawa dining Baniynah ta shiga kiran number Lieut da tai saving da *Lieut In-law*,wayar na shiga ya katse ya kirata,tayi murmushi a fili tace "ka ga manya,i really like harkar girma" then tayi answering call ɗin tare da sa wayar a speaker yanda ta san Muniba za ta jisu tayi sallama,cikin kamilalliyar voice ɗinsa ya amsa cike da barkwanci suka gaisa,Baniynah tace "Yayana mun ji abun alkhairi,muna taya murna,Allah ya sanya albarka yasa afi haka.. Congratulations once again" yace "ameen thank u dear,i really appreciate,Allah ya bar zumunci" tace "ameen.. Mami ta ce ayi maka Allah ya sanya alkhairi before ta kira" yace "ameen².. Ace ina godiya sosai,and ki tura min digits ɗin Mami please" tana dariya tace "awwnnn! Kada ta kira ka kasa ganewa,right?" Yayi murnushi tare da cewa "sure" tace "zan tura in sha Allah" yace "ok! I'm waiting,thanks again" tace "babu komai ai an zama ɗaya" yace "sure" sun ɗan yi hira,kafin tayi masa sallama,sanda ta sauke wayar ta kalli Muniba dake zaune,doing nothing but sipping her tea kamar bata san me take yi ba,zaro manyan idanunta Baniynah tayi saboda mamaki tace "hey! Wai baki ji ina magana da LOVE-LOCK ɗinki ba?" Muniba ta ajiye cup ɗin hannunta tace "and so?" Baniynah tace "baza ki yi ɗan murmushi ba,ki nuna kinji daɗi ma?" Muniba ta ɗaga ido ta kalleta,lokaci ɗaya ta ɗauke kai ta saki murmushi tace "abunda yafi haka zan yi" Baniynah tace "yayyy! Ai tunda kikai murmushi ya bayyana kin ji daɗin" Muniba ta harareta tace "banza" Baniynah tace "banzaye dai" Muniba ta girgiza kai tace "ke kika sani" daga nan ta ci gaba da breakfast ɗinta,tana gamawa ta ture komai tana shirin barin dining,wani kiran ya shigo wayarta dake ajiye saman table,ta ɗan kalli wayar duk da ta san me kiran,Baniyanh ta ajiye fork ɗin hannunta tana tauna fries dake bakinta tace "wai baza ki ɗauka ba? Kin fa san wa yake kiranki.. Ki bar ja mana class gaskiya" Muniba tace "a'a ke nake so ki sani kafin na ɗauka.. Kin manta school nake ja muku ƙarewa" Baniynah ta fara dariya tace "ai na haddace ringtone ɗin ba tun yanzu ba,please pickup jan ajin ya isa kada ya tsinke,kin san idan aka cika ja mana rai ko mu za mu yafe mu nema a wani wajen" Muniba ta harareta kafin tai answering call ɗin ta kai wayar kunnenta tai sallama,Lieut ya amsa da faɗin "good day! Matar Abuu Turab" Muniba tayi murmushi,shyly kamar tana gabansa tasa hannu ta rufe fuskarta,a hankali tace "ina kwana?" Yace "ai mun gaisa kou?" Tace "Mmm! Da yawan faɗa ai gara yawan gaisuwar,haka naji Hausawa suna cewa" yayi murmushi yace "sure.. So how are u?" Tace "alhmdllh! I'm good,ya weekends?" Yace "babu daɗi" tace "me yasa kace haka?" Yace "in dai ba na Kano ai kin san babu abunda zai min daɗi,we are far away,besides Mom and kowa na family kuna Kano.. And then" sai kuma yayi shiru,tana buɗe almond eyes ɗinta tace "and what?" Yace "sorry! Should i just go ahead of.. Dalilin kiran?" Tace "Mmm" yace "ok! Mun yi waya da Ƙanwata yanzu ta min fatan alkhairi" tana gyaɗa kanta tace "Allah sarki!" Yace "and na ji saƙon Mami,ina godiya sosai Love" tace "godiyar fa na mene ne?" Yace "na komai da Maryam tayi min ne,i do appreciate" ta ɗan sake gyaɗa kai kamar tana gabansa,sai kuma suka yi shiru kafin yace "u know what?" Tace "um'um! Sai idan ka faɗa zan sani" yace "mun yi magana da Daddy yanzun,and he said za suyi magana da Dad ɗin Mohan,daga yau zuwa gobe za su tsayar da lokacin zuwa.. Think za suyi magana da Abba" ta gyaɗa kai tace "Allah ya kaimu" yace "ameen.. What are u doing now?" A hankali ta kalli plate dake gabanta tace "na yi breakfast ne" yace "ok! Have u done?" Tace "Mmm!" Yace "idan baki gama ba na bari ki ƙarasa" tace "a'a na gama,zan tashi ka kira" yace "ok! Ina nawa kika ci ke kaɗai?" Murmushi tayi tace "i will send it to u yanzu" yayi murmushi yace "oh no! Thanks.. Thought za ayi min rowa" tace "ba halina bane" yace "yeah! Nima na shaida,Mata na ba ta da rowa" cikin zolaya tace "waye ya baka da kake ce min matarka?" Yace "Allah!" Tana gyaɗa kai tace "ka gama magana" yace "da gaske?" Tace "absolutely" yana lullumshe idanunsa yace "and a reality ma saura kaɗan na mallake ki" tayi murmushi. Baniynah data gama breakfast ta tashi tana cewa "lovebird sai an jima" Muniba bata kalleta ba kuma bata kulata ba,Lieut da ya jita kamar da shi take,yace "Sister na takura min mata fa" Muniba dake zaune har sannan tace "na lokaci ne za tayi ta gama,idan tayi aure ai ba kullum za ta dunga gani na ba" yace "idan tayi ko idan muka yi?" Tace "kowanne ma dai² ne" yace "um'um! Hakan dai dana faɗa,i know ko su Abba za su so ace sun aurar da ku lokaci ɗaya,and zan iya cewa hakan suke expecting tunda aka zo yanzu ba'a yi aurensu ba" Muniba data buɗe ido da kyau tace "aurensu da wa?" Yace "ni kike tambaya da wa?" Tace "ehh mana" yace "ok! Idan na zo Kano ki sake maimaitawa" dariya ta fara,yace "what's so funny?" Tace "nothing!" Yace "uhumn! U ask for it.." tace "aahh! Nifa ba wani abu nace ba" yace "nima bance kin ce komai ba,yanzu kije kima Mami aiki,za muyi magana later" tace "Allah ya kaimu" yace "ameen.. sai anjima?" Tace "Mmm! Allah ya kaimu" suna yin sallama ta tashi ta ɗauki plates da cups ta shiga da su kitchen. Da dare sanda Abba ya shigo gidan,bayan sun yi masa barka da dwowa ya amsa tare da zaunawa nan suna ɗan hira,ganinsu a parlon all together suna hira happily Muniba ce kawai babu,itama kuma kiran da Lieut yayi mata ne ya tasheta a gurin,hakan bai hana Abba ya buɗe baki ya sanar da Mami sun yi waya da deputy governor ba,har ya sanar mata batun zuwansu a gobe,Mami tayi murmushi tace "Allah ya kaimu da rai da lafiya" Abba da su Khalifa suka amsa,Muniba data dawo parlon babu wanda ya sanar mata abunda ke faruwa,ko Lieut ma bai sanar mata cewar gobe su Daddy za su zo nemar masa aurenta ba,tunda Daddy ya sanar masa sun yi magana da iyayenta maza,duk yanda Baniynah ke jin ɗokin su keɓe ta ƙyanƙyasa mata zancen though ta san zai wahala bai sanar mata ba,sanda suka taso daga parlour sam ta sha'afa,ko don Muniba ta rigata hawa sama ta barsu a parlour suna magana ita da Khalifa,sanda ta shigo kuma tana waya,so bata samu damar yi mata maganar ba gaba ɗaya har sukai bacci. Da safe sanda Abba zai fita yake cewa Mami "lallai ki tambayi Muniba tana son Abuu Turab? Ko kuwa akwai wanda take so? Kada muyi garaje" Mami tace "in sha Allah" yace "duk yanda kuka yi let me know please da wuri kafin su zo" Mami ta sake cewa "in sha Allah,i will let u know as soon as possible" har compound suka fita Mami ta rakashi gurin mota suna tafiya suna maganar Khalifa da Baniynah da basu ma sako zancen a gabansu ba,so suke ayi komai lokaci ɗaya tunda Allah ya kawo musu sauƙi,Abba na fita gidan Mami tayi hamdala sannan ta juya ta koma ciki. Guraren zhuhur Abba ya kira Mami ya sanar mata sun karɓi kuɗin auren Muniba da Lieut har an tsayar da lokaci,in the next couple months,so sun tsayar da lokacin gaba ɗaya har na su Baniynah,suna gama waya kiran Mama na shigowa Mami,ta amsa suka gaisa cikin farin ciki tare da yiwa juna murna,after then duka suka shiga sanar da ƴan uwa maganar auren.

*SAFWA*

        A can gidan su Baniynah Mama ta rufe kanta ta fita zuwa gidansu Safwa sanar da Umma abun alkhairin da ya faru a safiyar,sanda suka gaisa Umma ke cewa "Hjy Batoolu kwana biyu,ya gurinsu Dr da yaran? Ina amarya Khalidah a gidanta?" Mama tace "duk lafiya lau alhmdllh Hjy.. Yanzuma shigowar nan nawa,zuwa nayi na sanar miki an karɓi kuɗin auren ƴaƴanki Muniba da Baniynah yau,har an tsayar da lokacin auren watanni biyu" Umma tace "kaiii³! Maa sha Allahu,Allah ya sanya albarka,yasa muna raye za ayi,wallahi na yi murna da jin wannan labari,Allah ya tabbatar" Mama tace "ameen².. Saura Safwa in sha Allah" Umma tace "toh! Allah ya kawo mijin dai" Mama tace "ameen yaa hayyu yaa ƙayyum,Allah ya kawo na gari" Umma ta amsa,Mama bata daɗe sosai ba ta tafi,fitarta babu jimawa Safwa ta shigo daga gidansu Radhiya ƙawarta,tana yin sallama Umma ta amsa tace "Safwa! Albishirinki?" Safwa da tace "goro" Umma tace "an kawo kuɗin auren ƙawayenki yau har da sa rana" Safwa da tayi sororo tace "su waye?" Umma tace "Muniba da Baniynah,yanzun nan babu jimawa Hjy Batoolu ta shigo faɗa min" a mamakance Safwa tace "an kawo kuɗinsu?" Umma tace "wallahi kuwa,biki nan da 2 months" Safwa ta gyaɗa Kai tace "Allah ya kaimu" Umma tace "ameen.. Allah ya kawo na ƴan baya" Safwa dai ta zauna mamaki ya hana ta yi magana sam,don cikin su biyu babu wanda ta sanar mata maganar za'a karɓi kuɗin,lokaci ɗaya kuma kamar wanda aka tunatar wani muhimmin abu ta ɗauki wayarta.

*WAZEER*

      He can't tell cikin kwanakin da suka gabata,me ya faru da shi ko ya shiga cikin ƙwaƙwalwarsa,haka nan komai yake yi sai tunanin Safwa ya shigo ransa,ko da kuwa bai yi niyyar hakan ba,sometimes ma sai ya kirata sannan zai samu nutsuwar yin abunda ke gabansa,har dai akai ceremony na opening Waziri pharmaceutical company,though yanzu bashi da lokaci sosai,yana zuwa hospital,gurin 12pm kuma yake ficewa ya tafi Company,don yanzu aiki ake a Company komai ya kankama,idan ka ganshi zaune to sai in dare ya yi lokacin ya koma gida,nan yake samun lokaci sosai har yayi chat da kiran waya,ko Mimi yanzu bata cika ganinsa ba in ba a hospital ba ya je gaisheta. Kwance yake a parlour shi kaɗai,bai jima sosai da dawowa daga gidan Sarki ba da yaje ya gaisar da su Mami,a hankali wayarsa dake ajiye saman couch ya fara beeping,kallon wayar ya juya kansa yayi kafin yasa hannu ya ɗauko,sunan Safwa da ya gani sai da yasa gabansa ya wani irin faɗi,hausawa na cewa faɗuwar gaba.. Asarar namiji,amma shi dai tun gabannin 2 months da suka wuce,duk sanda zai kirata ko yaji muryarta sai gabansa ya faɗi,wanda zai iya cewa bai san dalilin faruwar hakan ba,katse wayar yayi ya kirata,tana ɗauka ko sallama batai masa ba tace "dear! U know what?" Yayi shiru for some seconds kafin yace "what's up?" Babu wata² Safwa tace "an kawo kuɗin auren ƙawata yau" wani irin faɗuwa gabansa ya shiga yi,ƙirjinsa ya fara heaving kamar wanda ke da attack na asthma,cikin dauriya da jarumta yace "which one are u talking about?" Safwa dake sakin murmushin kissa da samun nasara tace *"MUNIBAHH!"*

          _#Pray for ur Real-Smasher please,wallahi i don't know what really happens to me sam ba na jin daɗin typing yanzu,da na fara nake jin gajiya na ajiye,ko chat ba na son yi.. And don't forget kusa min Bilal a addu'o'inku ba shi da lafiya,pleaseee!_

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*


#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Continue Reading

You'll Also Like

48K 799 27
Falling in love with my best friends dad isn't something that was meant to happen. Will it last? Is he the person i think he is? *first time writing...
BETRAYAL By Uniy

Mystery / Thriller

6.2K 264 28
Have you ever had someone you loved more than anything betray you? Inseparable, triplets from different mothers, that's what they were. They grew up...
49.9K 1.9K 23
Its from malishka 'imagination but in my story its happen for real.
32.5K 4K 66
#1-mishti on 4-6-2021 #1-kuku on 1-7-2021 #2-mishbir on 20-12-2020 #3-mishbir on 19-12-2020 This is the story of a girl of middle class family and a...