AUREN WUCIN GADI

Av zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. Mer

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
90
92
91
94
93
95
96
97
98
99
END

89

203 17 2
Av zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 89

Watsi yashiga yi da pillows ɗin cikin fitan hayyaci a zabure yamike ya nufi toilet dayake jin ƙaran ruwa yana fatan ace ita dince saide yana tura ƙofan yaga wayam bakowa wajen sai famfo da aka bari a kunne,zuciyar sa yabashi ƙila taga shigowan ka nan dinne ta boye.

Cike da gwarin gwiwa yashiga dubata cikin part ɗin nasu saide ba tanan dama kuma ba wasu ɗakuna bane masu yawa ɗaki ɗayane sai kitchen da store sai toilet ɗaya dake cikin falon,buguzum buguzum haka yafita daga falon cikin fitan hayyaci harya manta da matsayin shi yakuma manta ta yanayin da yake cikin a hakan nashi yanufi bakin get wajen maigadi yama mance da dare ne ba rana bane,yashiga kwalawa masa kiran"Mati Mati da gudu Malam Mato maigadi ya rugo da ƙatuwar Sandar goransa riƙe a hannu yana muzurai jiki na ɓari ganin halin da Uban Gidan nasa yake.

"Bade ɓarayi bane wallahi banga shigan su ba saide idan ta baya suka ɗirƙa ta katanga.duk yaruɗe dan har cikin ransa ya ɗauka ɓarayine suka birkita Alhajin haka.

"Dalla rufawa mutane baki ina masu Gidan nan suke?tsaɓan ya fita a hayyacin sa yama mance da shine maigidan.

"Ƴallaɓai kaine ai Maigidan yabashi amsa.

Zazzago masa idanun sa yayi kaman zasu fito su faɗi ƙasa launinsu ya canza zuwa launin shuɗin idan ba karya idanuna suka gane mun ba kaman hayaƙi nagani yake fitowa ta bakin sa.

Tsoro iya tsoro Malam Mati yashiga dan haka cikin gudu gudu yayi cikin gidan direct part ɗin Sajid yanufa yana xuwa be tsaya sanyin jiki ba,yashiga buga musu ƙofa dakiran Sajid fito yau gida ba lafiya Alhaji yamance kansa,a gigice Sajid suka fito shida Sajida jin abunda Malam Mati yake cewa kuma saiya sake ruɗasu ai kuwa a tare suka isa inda yake a ɗuƙe tsaɓanin ɗazu dayake tsaye,dan yanayin da yatsinci kansa ciki yaba buƙatar yamike iyalan nasa sugan shi,a haka.

Kusan a tare suka isa inda yaken harda Mami da itama ta tashi zatayi fitsari taji bugun ƙofa da Malam Mati yakema Sajid tafito dan tagani shine idonta yasauka kan Alhajin dake ɗuke ƙasa kaman mai naƙuda tayi kansa da mugun sauri tana cewa"yau me zan gani haka Alhaji lafiya?

"Wallahi Hajia dan ma bakiga yanda yazo mun bane yana tambaya wai ina maiGidan?"maigidan kuma Malam Mati kode gamo Alhaji yayine?Mami ta tambaya kaman zatayi kuka"wani irin gamo kuma Mami cewar Sajid fuskan sa da damuwa.
"Yanzu de kamamun shi mushiga ciki ko hayaƙine amasa.

"Haba Mami yazamu shiga da mara lafiya ciki mu ajiye gwara de mutafi dashi Asibiti,suna cikin magana saiga Ahmad shima yafito daga part ɗin su yana isowa yafara tambayan su lafiya?wallahi cewa Malam Mati yashiga labarta masa yanda sukai da Alhajin da yanda yazo yasame shi harma da karin gishiri saida yayi nan Ahmad da Sajid suka kamashi suka saka a mota sai Asibiti.

KANO

CID Office Faisal ne xaune a gaban Ogan sa cikin Office ɗin sa yana duba file din dake gabansa ya dauki a kalla minti goma kafin ya ɗago  yana kallon sa dakiran sunan sa"Faisal yanzu ina kuka tsaya da binceken naku?na karanta report din idan na fahince ka ba Alhaji Badamasi yayi wannan kissan ba,sannan kuma mun kame wasu Mutum biyu da kume kyautata zaton suna da saka hannun wajen aikata muggan lefuka kuma sune manya manyan diloli suna saida miyagun ƙwayoyi suna kuma safaran su daga ƙasar nan zuwa wasu ƙasashen da sunanan magani suna amfani da maxuban maganin capsule dakuma tambari.

"Very good Faisal na yaba da ƙoƙarin ka wallahi bakaji yanda nakeji ba gami da wannan case ɗin tunda aka kawo wannan case din hannun na wallahi banji abunda ya faran ta mun rai kaman wannan ba,saide inaso kamun wani abu"ta mefa Sir?Faisal ya tambaya yana gyara zaman sa.

"Inaso wannan abun yaxama tsaƙanin mu,wani irin kallo Faisal yabishi dashi miƙewa tsaye Ogan nasa yayi yana zagayowa inda Faisal din yake zaune saida ya kai zaune saman ƙatuwae desk ɗin dake Office din sannan yace kadena bina da wannan idon naka,sauke idon nasa yayi daga barin kallon sa yace"sorry Sir yafaɗa cikin sanyin murya.

Dafa kafaɗan sa Oga Mus'ab yayi yana cewa"kayi cooling down Faisal karka kariyi dama so nake wannan File din ya zauna a hannun ka,kaima kuma karyi kuskuren barinsa anan ka kaisa gida ka adana shi a waje mai kyau sannan Mutanen da kace kakame ka kaisu ka aɓoye su cikin sirri kuma bance ka ajiye wannan binciken ba ka cigaba dayi duk wanda ze nemi information agunka kanuna kaima kana kan nemane koya kake da mutum.

"In shaa Allah
Amma Sir saboda me kakeso na dayin hakan?

Murmushi yayi yana tashi ya koma saman kugeran sa yana cewa"saboda haka nakeson ayi zaka san dalili na nasan yin hakan  idan lokacin kasanin yayi,miƙewa tsaye Faisal yayi yana ƙamewa haɗe da sarawa ya miƙa masa hannu sukai musabaha yafita daga Office din zuciyar sa fal tunanin me Ogan nasa yake nufi da bayason kowa yasan da wannan batun.

****
Aisha suna isa Gidan Dr Hajara ɗakin ta ta kaita ta sauke ta tace"ƙanwata zauna saman gado bara nasamo miki koda tea ne kisha kafin ki kwanta ko?"girgiza kanta tashiga yi"menene kode harkin fara kewan Mijinki ne tun yanzu?tafaɗa cike da zolaya dan ita akwaita da zolaya dason barkwanci.

da sauri tashiga cewa"a'a wallahi Anty ni banyi kewarsa ba kumama baxanyi bane ko nan gaba takare faɗa tana ciko hawaye a idon ta.

"to ƙanwata karfa azo na riƙeki naƙi maidaki rana tsaka in nemeki in rasa kinyi gun Mijinki"nide dan Allah Anty kima dena haɗani da wannan Mutumin idan na warke sai munyi Shari'a dashi kona rama abunda yamun.

Itade Dr Hajara har dariya Aisha take bata idan tace zata raman nan tace"nice   wacce zan tsaya miki harsai naga kin rama kin kuma gamsu da ramawar da kikayi sannan ne,gyaɗa mata kai tayi cike da jindaɗin cemata zata tsaya matan da tayi har fuskanta saida yanuna hakan.

Fita Dr Hajara tayi tana mata dariya a ranta ta wuce zuwa kitchen dan ɗumama mata ferfesu ta zuba mata cikin wani bowl ta haɗa mata tea mai kauri ta daura saman tray ta kawo mata  tace"oya sauka kicinye wannan tas tea ɗinma kishanye idan ko kinƙi yanzun nan sai na janye maganan tsayamiki kirama muguntan da akai miki,tana jin haka ta sauko daga saman gadon ta zauna ƙasan carpet ta amshi tray ta hauci ita kuma Dr Hajara tuɓe kayan ta tayi tashiga wanka ko kafin ta fito har Aisha ta gama cinye wannan ferfesun tana shan tea din koda Dr Hajara tafito daga toilet din murmushi tayi tana cewa"lalle ƙanwata tanaso mura ai dolene mu taru muyi Shari'a daga nan har kotun koli dariya Aisha tayi saboda ganin yanda Dr Hajara tayi maganan tana gama sha tace shiga kiyi wanka da Alwala kizo ki kwanta dan ni fita zanyi.

Da damuwa kwance saman fuskanta Aisha tace"Anty ina zaki kuma ki barni ni kadai karfa yabiyo ni nan kuma,ta ƙare maganan tanayin narai narai da ido kaman zatayi kuka.

Oh yau ni Hajara ammade ke dagani ƴar farice keko?kai ta gyaɗa alaman eh ba bakin magana dan idan tace zata bude bakin to kukane ze kubce mata.

Riko hannunta Dr Hajara tayi tajata ta zaunar da ita bakin gadon tace"kinga kwantar da hankalin ki Ahmad baze zo nan a irin wannan lokacin ba,ba inda zani zan ɗan leƙa Habibina ne nan ɗakin daga yau dakin kine har zuwa ranan da zamu cika burin mu na rama muguntu ta da akai mana dan ba yarda zamuyi ba,idan ta kama har kotu zamu abi mana hakkinmu,sai kuma tayi shiru ta kalli Aisha tace to idan munje kotun kuma ƙanwata me zamuce an mana?

Tayi shiru tana kallon Aisha da tayi ƙasa da kanta cike da kunya dan itade tasan ko karen haukane ya cijeta baxata iya cewa kowa ga abunda akai mata take neman hakkinta akai ba,ammafa ita saita rama muguntan da yamata.

Har toilet Dr Hajara ta jata ta tahaɗa mata ruwa takuma faɗa mata yanda zatayi kafin ta fito har ta ajiye mata riga dazata saka saida ta shafe jikinta da turaruka masu daɗin ƙamshi tana saka rigar Dr Hajara ta sake shigowa hannunta rike da goran ruwa mai ɗan sanyi da kuma magani pain relief tabata tasha ta kwanta saman gadon taja mata bargo tarufa mata daidai saman ƙirginta tace"ƙanwata kiyi bacci mai daɗi karki saka abunda ze hanaki bacci a rai balle harta kaiki da kasa bacci kinji ko?"in shaa Allah Anty nagode da kulawarki a kaina Allah ubangiji yasaka miki da mafificin alheri"ameen ƙanwata saida safe na bar Habibi na yana jira daga haka tafita taja mata kofa tare da kashe mata wutan ɗakin ta barmata mara haske.

Washe gari da asuba koda ta tashi ruwan dumin tahaɗa kaman yanda taga Anty Hajara tanayi tashiga tajima cikin ruwan kafin tayi wanka tafito bayan ta daura alwala riga tasaka doguwa mara nauyi cikin kayanta data zo dasu jiya tayi salla tana zaune tana azkar Anty Hajara tashigo tana cewa"ashe harkinyi sallah"eh wallahi na tashi Anty ina kwana ta faɗa duka kusan atare.

"Lafiya lau ƙanwata ya kwanan bakunta dakuma karfin jiki?Alhamdullahi anty ko da aiki da zan tayaki muyi.

"No yi kwanciyarki kanwata keda kike fama da kanki inake ina iya yin wani aiki,ai tsakanin ki da mai jego banbancin kaɗanne zauna bara na haɗo miki breakfast nakawo miki yanzu tana fadin haka ta juya tafita a ɗakin ba tare da tabata daman ta furta komai ba.

Itako maganace fal cikin ta ita da maijego to ita mai haɗinta da mai jego kuma?hakade ta rinka tunani har sanda Dr Hajara takawo mata breakfast taci ta ƙoshi tasha maganin ta tana nan zaune saiga Dr Hajara ta saike dawowa cikin kwalliya kaman wacce zataje gasar fidda gwana ita kanta Aisha kwalliyar tata ta dauki hankalin ta sai satan kallon ta take,duk inda kaga Babba babba ne hankalin sa daban dana karami tace"ya kikaga kwalliyata tayi kyau ko?cike da zolaya ta tambayeta dan so take tasaki jiki da ita ta daurata a karatun ma'aureta dan alamu yanuna mata Aisha batasan komai gami da aure ba,tanaso ta daurata can saman network ƙololowar hawa ta yanda Ahmad ze sake haukacewa a kanta.

Kinga ni kisaki jikinki dani ki daukeni tamkar Yayarki wacce kuka fito ciki ɗaya kinji ko"da to ta amsa a sanyaye"yauwa ƙanwata tashi kizo ku gaisa da Habibina yana can falo kafin ya fita.

To kawai tace hijabin da tayi salla dashi ta zura tafito zaune yake saman kugera wayarsa rike a hannun sa yana latsata jin sallamar su yasashi ajiye wayan yana kallon ta,har ƙasa ta zauna tana gaishe shi amsa mata yayi fuska a sake da tambayanta ya jiki,kin amsawa tayi ciki da kunya yanzu kenan kowa yasan abunda yasameta kenan,bade ganewa akeyi ba da zaran mutum yakalli fuskar ta?"kai ina samma hakan ba maiyuwa bane ai nima ba dason raina akaimun ba,ita kadai take maganar a zuciyar ta.

"Allah yabaki lafiya kuma yabaku zaman lafiya keda angon naki gaskiya ke mai sa'ace ƴar Uwa"kode abokin nakane mai sa'a dayayi nasaran samun tauraruwar Mata matsayin mata ba,taba Mijin nata amsa cike da raha haka suka cigaba da wasa da dariya itade Aisha na zaune tana wasa da zoben ta.

Haka suka yini da Dr Hajara sai nan nan take da ita motsi kadan idan taga tayi sai ta tambayeta me takeso,haka bayan sunci abincin dare suna zaune suna hira a falo mafi yawanci suke hiran su itade Aisha zaune take duk tabi ta takura kanta ganin yanda Anty tata bata ko kunyar yima Mijinta wani abu kodan ganin idon ta.

"Zanje na kwanta Anty yanda tayi maganan kaɗai saida yasa Abdullatif ɗagowa yana kallon ta yace"are you ok?kai ta jinjina masa kin tabbata hakane koda wani abu dakike da bukata?"murya a sansaye ta amsa bakomai"ok yace a takaice tamike cikin sanyin jiki tanufi ɗaki wanka tashiga bayan ta fito ta shafa jikinta da mayuka da turaruka masu sanyin ƙamshi tabi ta mulƙe jikin ta dauki rigar bacci tasaka tabi lafiya gado ta kwanta tashiga tunanin duniya tana karanta wasikar jaki har bacci ya dauke ta.

Cikin bacci taji ana mata tafiyar tsutsa a ƙafanta dayi mata wasu abubuwa haka dayasa tsigar jikinta tashi tajinta tana shiga wani irin yanayin da baya misaltuwa jin abun take kaman amafarki tasaki jiki sosai tana in joy saida tasaki jikinta sosai jikinta yana amsan sakon lungu da sako duka na jikinta tasaki jiki sosai taji kaman ana saka hannu cikin pant ɗinta tayi saurin matse kafa tana kai hannunta daidai sanda taji kaman zata shiɗe saboda wani abu da taji mai dadi kaman kuma zata saki fitsari tayi sauri buɗe idonta sai a saman kyakkyawan fuskansa duk da ɗakin bawani haske mai yawa zabura tayi zata miƙe tsaye yayi sauri jawota ta faɗa jikin sa yasa duk hannun sa biyun yana mata zobe.

Ihu taso ƙurmawa yayi saurin haɗe bakin sa danata saida yama lips ɗinta tsotsar sweet na kusan minti biyar kafin ya saketa yana maida numfashi.

Cike da jin haushi da tsanar abunda yayi mata take binsa da harara tana goge bakinta cike da jin haushi tana tofar da miyawu tace"wallahi bazan yarda ba sai narama duka mugunta da kaimun kuma ni kadena zubamun wannan ƴawun a bakina takare faɗa tana fashe masa da kuka.

ALLAH YASA MUDACE

Fortsätt läs

Du kommer också att gilla

325K 26K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
192K 15.1K 22
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
629K 33.3K 50
𝐒𝐜𝐞𝐧𝐭 𝐎𝐟 𝐋𝐨𝐯𝐞〢𝐁𝐲 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐡𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 〈𝐛𝐨𝐨𝐤 1〉 𝑶𝒑𝒑𝒐𝒔𝒊𝒕𝒆𝒔 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ☆|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
663K 68.6K 26
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...