AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
89
90
92
91
94
93
95
96
97
98
99
END

88

260 27 7
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨
     ✨ *G.W.F* ✨

CHAPTER 88

Duk yarikice yama rasa abunyi janyuta yayi yasakaya jikin sa ya rungumeta da karfi kaman wanda akace za kwace masa ita,a gefe ɗaya kuma ba abunda zuciyar sa keyi masa sai kai komo,idan har abunda yaji suna magana akai ba gaskiya bane wani shirin sune fa?

Tabbas idan wani abu yasami ta baze yafe musa ba haka zalika baze yafema kansa ba.

Da wannan tunanin yasoma jijjigata yana dan marin kumatun ta a hankali da kiran sunan ta amma ina bata motsa ba ,batama da alaman motsi kaman wanda aka mitsina yamiƙe da sauri yana gyara mata kwanciya ya sauka daga saman gadon yasaka jallabi kitchen ya tafi yaɗauko ruwan gora mai sanyi yazo dashi ɗakin saida ya zauna saman gadon ya shiga yayyafa mata saman fuskanta cike da tsoron saida yazuba mata kusan rabin goran saman fuskan ta tukun ta jawata nannauyan ajiyar zuciya ta soma kiran sunan sa dayi masa magiya duk ta firgita tafita hayyacinta riƙota yakeson yi yasata jikin sa ko zeji sanyi cikin zuciyar sa amma ina sai yin bayake taki yarda ya matso koda kusa da ita duk ta kwuƙwikuye abun rufuwar tana bashi hakuri ganin yanda take a firgice yasan ba zata bari ya taimaka mata tasaka kaya ya kaita asibiti a duba masa ita ba.

Waya ya dauka yakira Dr Hajara bayan sun gaisa nan take tsokanan sa tana cewa"lalle kace yau dole nayi sadaka tunda harka tuna damu har kakira waya Allah de yasa lafiya ba wani lefin mukai ba?tafaɗa cike da zolaya matar Abokin sace Abdullatif tare sukai karatu da shi,hmmm kawai yace jin yanayin da ya sauke ajiyar zuciya be iya yace da ita komai ba,yasata tambaye shi da lafiya kuwa A-B dan haka suke kiransa yawanci tunda Basma ta nace masa take kiran sa da hakan,shiko yana amsa matane ganin A mafarin sunan sane B kuma sunan baban sa"lafiya Haraja amma gaskiya ba lau ba Allah de yasa kina cikin Abuja bakiyi tafiya ba?

Jin muryan sa kaɗai ya isa ta fahinci yana cikin damuwa"ina gari yanzu hakama ina Asibiti dan yau night nake amma lafiya naji kace ba lau ba?Nan yace mata wallahi Madam ɗina ce ba lafiya kuma taƙi bari na taimaka mata balle nakawo ta Asibiti shine nace ko zaki taimaka nazo na dauke kizo ki dubamun ita,ya kare maganan kaman zeyi kuka.

"Subuhanallahi garin yaa?saida ta tambaya ne kuma taji kunyar tambayar tata tayi saurin cewa turamun address ɗin inda kake gani nan zuwa yanzu ba sai kai kazo ba ai bazaka bar mara lafiya ita kadai ba.

Tana kashe wayan nata ta fito dauke da wata ƴa karamar box data zuba kayan aiki tace da Abokiyar aikin ta"dan Allah Joy zan ɗan fita duba Matar wani Abokin mijina koda zazo nemana"Ok koda Oganki ne yazo Joy tafaɗa cikin zolaya tana ƴar dariya dan tasan Hajara a kan Mijin ta bata da sauki.

Ƙaramar dariya ita ma tasaki tana cewa"lalle wato kema Joy yanzu kin zama ƴar sa ido kin yarda da sharrin su Latifa ko?"amma bakiji nace komai ba dan nasanki ina buɗe baki abunda zakice kenan Latifa da yanzu ƙarasowa ta kenan tayi maganan tana kaiwa zauna.

"Kunga nide saina dawo dan nasan inna tsaya na biyewa surutun ki ba tafiya zan ba,tafaɗa tana daukan box din tafita,adawo lafiya sukai mata.

Saida takira Mijin nata ta faɗa masa zataje duba Matar Ahmad ɗin kafin ta shiga Motar ta tafita daga Asibitin,inda tabar Abdullatif da mamakin yaushe Ahmad din yayi wani Auren dan yana da Labarin ɗage auren su da akai da Basma.

Address ɗin ta bi tazo kofan gidan ta parka motar ta tafito dama ya faɗama maigadi akwai wacce zatazo ya shigo da ita ta karamin kofa kuma yakiyaye bayaso yayi wani abu da ze bada  wata ƙara da zagane anbude wani yashigo ko yafita"inde wannan ne baka da matsala Ranka yadade daga haka yakoma ciki.

Kai tsaye ɗakin yakoma tana nan kwance inda ya batarta tana kuka jin kukan nata kaman ana watsa masa tafashasshen ruwan zafi a cikin zuciyar sa matsowa yayi gefen ta yanayin ƙasa da kansa cikin tsigan rarrashi yace"Eashow kiyi hakuri ki daure na taimaka miki koda kayane ki saka kafin Likitan da zata dubaki ta ƙaraso.

"Bazan tashin ba tace cikin tsiwa a ɗan zafafe da muryarta da baya fita sosai,kuma wallahi saina rama mugunta da kaimu idan wani abu yasami ƙafata wallahi bazan yarda ba,kuma dolene kamai dani Gida tunda auren wucin gadi kai dani shine ka daukoni kazo dani inda bani da kowa kanemi ɓallani,idan ma kai baka sakeni wallahi nice wacce zan rubuta maka sakin da hannu na takare magana tana mai kifa kanta jikin gadon ta cigaba da kuka,harga Allah shi maganar tata ma dariya ta bashi amma ya gimtse abun sa gudun karyayi ya kirama kansa ruwa.

Knockin ƙofa akai ya barta yafita"Sister barka da zuwa yace da ita sanda yabude mata kofan saida tashigo ciki sannan ta amsa masa tana cewa ina Madam ɗin?tana ciki yabata amsa yana nuna mata ƙofan ɗakin"Ok bara na dubata tace tana nufan ƙofan ɗakin tura ƙofan tayi da sallama a bakin ta amma saboda nisa da tayi cikin kuka dakuma zazzaɓi daya rufeta bata iya jin sallamar ba saide kofa dataji anbuɗe ta tabbata shiɗin ne dan haka cikin ɗan ɗaga murya tace"wai dole sai ka taimakamun to nace banaso kuma wallahi saina rama mugunta da kaimun gashi ka gurguntani wayyo Allah wayyo Anna Anty Hajia zokiga irin mugunta dayamun dama basona yake ba"ƙanwata taji ankirata da haka daga gefen ta,hakan yasa tayi saurin bude idon ta kalli Matar dake xaune saman gadon gefen ta,faɗawa jikinta tayi tasaki kuka tana cewa"dan Allah Anty ki taimakamun wallahi ya ɓallamun ƙafa tunɗazu nakeson tashi amma na gagara.

Kwantar mata da hankali Dr Hajara tayi tayi cikin hikima da dabara tazare jikinta daga nata tamiƙe tashiga toilet ruwan zafi ta haɗa mata daidai wanda zata iya zama a ciki ta fito taje falo ta tasami Ahmad zaune saman kugera amma hankalin sa kaco kan yana kan ƙofar dan haka Dr Hajara na bude ɗakin yamiƙe tsaye yataro ta"Sister lafiya ya take?"she's fine ɗan dubo mun gishiri tace dashi,da sauri yashiga kitchen ɗin dake falon sai gashi yafito hannun sa rike da gishirin karɓa tayi takoma ɗakin dakyar de Aisha ta miƙe tsaye da taimakon Dr Hajara saide kafanta nakaiwa ƙasa tasaki wata marayan kuka takoma ta zauna.

Ahmad dake zaune falo saman kugera dake kusa da bakin kofan saurin faɗawa ɗakin yayi yana tambaya"Sister lafiya?dafe goshin Dr hajara tayi tana"bazade ka jira daga falon ba kenan,juyawa yayi yana kallon Aisha dake kuka ba tare da ya amsa Dr Hajara ba,saide kawai gani tayi ya sunkuce Aisha yayi toilet da ita be direta ko ina ba sai cikin ƙwarmin wanka dake cike da ruwan ɗumi.

Ƙanƙame shi tayi tana mai sake rushewa da wani kukan neman tashi takeyi ya danneta jin ƙasanta take kaman wace aka zubama barkono saboda azaba,tayi tayi ta turesa ta kwaci kanta daga ruƙun da yamata ta kasa kukan da take ma bajinsa ake ba saboda dashewan da muryarta tayi bata fita sosai,sai jujjuya kanta take Dr Hajara ce tashigo toilet din ta korashi waje.

Lallashin ta Dr Hajara tayi tayi harde tasamu ta canza mata wani ruwan saida ta canza mata ruwan sau biyu sannan ta barta tace tayi wankan tsarki,wani kunyar tane yakamata tama rasa yanda zatayi dole de tana jin kunyar kanta da kanta wai yau itace ake cewa tayi wankan tsarki,tana gamawa ta fito taɗanji sauƙi jikinta saide abunda barasa ba,jikin ta ba karfi da kyar take tako ƙafanta  ta fito daga toilet ɗin ɗaure take da wata ƙatuwar towel ba kowa a ɗakin saide an canza zanin gadon zuwa wata harma da abun rufuwa zama tayi dakyar tana cizon lips ɗin cikin a ranta kuwa tana ƙudurta abunda zata masa tarama abunda yamata duk abunda ta ayyana a ranta zata masa idan ta auna da mizani ta kwatanta da abunda ya aikata mata sai taga bata rama ba.

Shigowar Dr Hajara ne ya katseta daga tunani da take murmushi ɗauke saman fuskarta tace"yauwa ƙanwata ashe harkin fito?"eh nafito Anty ta amsa tana sunkuyar da kanta cike da jin kunya,ita ko yi tayi kaman bata gani ba.

"Ƙanwata yanzu de bara  na kawo miki koda tea ne idan kinsha namiki allura sannan idan bazaki damu ba ko zaki ɗan kwanta naga waje?

Zaro ido Aisha tayi jin abunda Anty Hajara tace ba ƙaramin sock taji ba,wannan wacce iriyar tonan silili ce,sai kace da sona akai bayan nima din fin karfi a kaimun shine kuma saboda rainawa mutane hankali harda kirama mutum Likita,wallahi idan na warke naji karfin jikina saina kaishi human right.

"Me kike cewa ne haka mara daɗin ji?eh ƙanwata?saida Dr Hajara ta wurga mata da wannan tambayan tagane ashe ba a zuci tayi maganan nata ba wato zance zuci yafito fili kenan,zama tayi kusa da ita ta cigaba da cewa burin ko wace ƴa mace takai budurcin ta ɗakin Mijinta wannan shine darajar ko wace ɗiya mace sannan inaso faɗa miki wani abu keɗin mai sa'ace da kika mallaki Ahmad matsayin Miji dan shifa tamkar Goal ne sannan inason faɗa miki Ahmad yana sonki kawai faɗa mikine beyi ba,amma dazaran lokaci yayi ze faɗa miki da kansa.

"Nide Anty a'a kawai ki bari basai kin dubani ba,tafaɗa idon ta na cikowa da hawaye"ƙanwata daurewa zakiyi in dubaki saboda gugewa matsala nan gaba bazan kuma gane hakan ba har sai idan kin daure kin cije kin bari na dubaki saboda gugewa abunda gaba zata haifar idan baki samu kulawa da kyau ba wannan matsala dakike ganin ta ƙanƙanuwa tana iya zamema mace babba idan ba ayi sa'a ba takan shafi ƙwaƙwalwa ma.

Cike da tsoro da bayanin Dr ta kwanta tashiga dubata aji rauni sosai saida tamata dinki sannan ta faɗa mata yanda zatayi amfani da ruwan zafi"kinde ga yanda mukai yanzu ko?kai kawai ta iya ggyaɗawa idan kikayi duk yanda nace din nan cikin kwana biyu zaki jiki zam zam,sannan kiyi ƙoƙarin ganin bakiyi gardama next time ba,dan gardama da kikayi shine yakaiki gajin wannan ciwon da zaki kula...."Anty kiyi hakuri nifa bansan duka abunda kike magana a kai ba gardama naji kaman kike cewa ko?eh jin amsa da Dr Hajara ta bata atakaice yasa kawai tasa mata kuka tariƙe mata hannu tana cewa dan Allah Anty ki tafi dani karki barni anan nasan ke macece kuma Likita zakifi sanin matsalan da yake damuna fiye da duk wanda zan faɗa masa a baki dan Allah ki nisantar dani da gidan nan dan Allah.

Nide ki tafi dani"haba Ƙanwata ki kwantar da hankalinki ba abunda ze faru dake"akwai Anty nide kiwa Allah da ma'aikin sa ki ceci rayuwata inaji ajikina kaman akwai abunda yake shirin faruwa dani kuma mara daɗi,Anty naji ana cewa ciwon ƴa mace na ƴa macece kenan bazaki dubi halin da nake ciki ki ceci rayuwata matsayinki na Likita mai ceton rayuwar Al'umma idan ƙanwarkice ni ko ƴarki ce ni nake wannan halin na neman taimako shin tsallake ni zakiyi ki wuce ko tsayawa zakiyi ki riƙo hannuna ki jani ki rungumoni,ko barina  zakiyi na cutun.

Shiru tayi bakajin komai sai shasshaƙan ta ita kanta Dr Hajara jikin ta duka yayi sanyi da maganganun ta dakuma yanayin da yarinyar ke ciki.

Dr Hajara jan Ahmad dake tsaye yana jin duka abunda suke maganan tayi suka fita falo tace"A-B wai me kakema yarinyan ne naganta duka a ruɗe ne wai?

Ajiyar zuciya ya sauke yace"Sister ba abunda nake mata na mugunta amma zan miki bayani daga baya yanzu de kawai ki ɗauke ta ki tafi da ita gidan naku idan ba wata matsala,kafin nan bara nakira Abdul ɗin nafaɗa masa"habade A-B ai basai kakira sa bama nide izinin ka kawai nake bukata zan tafi da ita yanzu idan ta dawo hayyacin ta ta buƙaci dawowa zan dawo maka da ita"na baki kawai yace.

Bayan tafiyan Dr Hajara da Aisha Ahmad yayi sauri shiga ɗakin baccin su ya jera pillows tsakiyar gadon yarufe da Bargo ya rage hasken wutan ɗakin zuwa mara haske ya seta camera a ɗakin yafita.

Karfe 1:00 am daidai ya miƙe daga kwance dayake cikin sanɗa yafito daga ɗakin baccin su,yaja ƙofan ɗakin a hankali yake tafiya gudun karyayi motsi mai karfi yatashi kowa ta ƙofan baya yafita gudun karya fito ta gaba maigadi ya hangoshi ta hasken fitillon gidan.

Ta ƙofar kitchen yafita yabi ta bayan part ɗin ya yanufa shidinma ta baya yashiga ɗakin da yake kyautata zaton nan ne ɗakin yashiga yana shiga ya hangota kwance saman gado bayan ya murzawa ƙofan key ya shafe jikin sa da magani da aka bashi yanufi saman gadon da saurin sa yana isa be tsaya wata wata ba kawai yayi sufa yafaɗa saman gadon yana kaiwa pillows ɗin wani irin wawan cafka.

ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

1.7M 102K 40
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
195K 38.9K 57
Becca Belfort i Haze Connors, choć przez swoich znajomych zmuszani do spędzania razem czasu całą paczką, od dawna się nie znoszą. Dogryzają sobie prz...
211K 14.8K 19
"YOU ARE MINE TO KEEP OR TO KILL" ~~~ Kiaan and Izna are like completely two different poles. They both belong to two different RIVAL FAMILIES. It's...
3M 196K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...