AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
84
85
86
87
88
89
90
92
91
94
93
95
96
97
98
99
END

83

197 18 2
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITTERD FORUM* ✨

    ✨G.W.F✨

CHAPTER 83

  Zaro idon tayi kaman zasu faɗo ƙasa tangal rangal tayi kaman zata faɗi tayi baya tafita daga falon ba tare da sun ganta ba,tana fita yasake ta yana komawa inda ya tashi ya zauna cike da bada umurni yace"oya tashi ki wuce kici abincin nan kona miki ɗure.

  Tasan ba wasa yake da ita ba ze iya mata ɗuren kaman yanda yace ɗin dan haka salim alim gwara tazo ci ɗin kaman yanda yace taci,miƙewa tsaye tayi saida ta ɗauki ledan kayan furuit da drink daya shigo dasu takai kitchen ta sakasu a freeze sannan ta dawo ta dauki ledar take away din tabude a hankali jalof ɗin macaroni ce daya sha kayan lambu hade da hanta da aka yanka gutsul gutsul sai ƙunshin nama a fege  tun kan tabude ledar taga abunda yake ciki ƴawun bakin ta yatsinke amma saboda karta bada kanta a gunsa cike da yanga ta bude tana yatsine fuska saida taje ta wanko hannunta kafin tazo ta zauna zaman cin abinci bata wani ci dayawa ba,amma taci naman da ɗan dama dan tamata daɗi sosai taci ta daura da freesh milk mai ɗan sanyi sannan ta mike ta tattare gun ta shiga tayi brush sannan tayi alwala ta fito tayi sallan ta anan cikin falo tana nan zaune tana addu'anta kaman yanda ta saba har ta gama ta gade kaman bashi da niyar dashi yashiga ɗaki ya kwanta.

Dan koo jiyan ma a bisa lalura ta kwana dashi ɗaki ɗaya amma bawai dan ranta yaso mata hakan bane,gyaran murya tayi ya ɗago da dubansa kanta ba tare da yabar abunda yake yi ba.

"Kwanciya nake son yi"and so?
Tura ɗan mitsitsin bakin ta tayi cike da shagwaɓan da itama batasan tayi ba tace"waje zaka bani kuma banason kwanciya cikin haske ta ƙarasa faɗin hakan tana murguɗa baki ganin ya ɗauke kansa daga kallon ta abunda bata saniba shine duk wani motsin ta akan idon sa take dan yana kallon ta a fakaice.

"Kina iya shiga ɗaki ki kwanta"ni fa bazan kwana da kai ɗaki ɗaya ba,tasake ce masa"saide yau kiyi kwanan zaune dan bazan bar aikina saboda ke ba.

"Ai wannan muguntane mutum kawai yazo ya zauna daki ɗaya da mutum bayan yasan rashin halascin yin hakan wannan ai shiga hakkin mutum ne ni gaskiya bazan kwana a wannan ɗakin ba saide kawai ka koma can ni kuma na kwanta a nan din,ta dage sai masifa take amma da zaran ta ga kaman ze ɗago kansa saita fuske.

Ta ishe shi da surutu dan har takai baya iyayin aikin da yake saboda yanda surutun nata ke hawa masa kai miƙewa yayi tsaye ya ajiye systerm ɗin gefe ya nufota ai kuwa da gudu tayi hanyan ɗakin ba shiri tana shiga ta kullo ƙufan girgiza kansa yayi yana komawa da zaman sa inda ya tashi yace"da alama yare ɗaya kawai take fahinta ita sake girgiza kansa yayi yana gajeran murmushi yana tuno moment ɗin su na ɗazo.

Mami tana komawa site ɗinta a falon ta taja ta tsaya tana tuna irin wahala data sha dakuma kuɗi data kashe akafin tasamu Ahmad din yasake waiwayar inda suke amma saide gani take kaman wankin hula yana neman kaita ga yin dare.

anƴa idan ta tsaya kallo burukan dukkan su ze cika kuwa?"kai ina yanzu duk wahala dana sha dan ganin auren sa da wancan Basman beyi ba sai ga wata ita kuma wai Aisha duk da har yanzu bata gama sanin wace alaqa ne ke tsakanin sa da ita ba amma da alama akwai kamshin gaskiya a maganar da Sajid yafaɗa mata ɗazu da safe dan tasan Ahmad ciki da bai inde ba canza halinsa yayi daga baya ba,da dekan tasan harkar ƴan matan basu a gaban sa belle sukai ga sun burgeshi duk yanda yan matan ke bibiyarsa amma shi baya kulasu.

Irin yanda taga yana riƙe da yarinyar yanzu dole akwai wata alaqa tsakanin su,idan ita din matar sace fa?ta tambayi kanta saurin kawar da wannan tambaya tayi tana kai ina hakan baze yu ba.

Tace tana zagaye falon dan neman mafita,can tatuna da ƙawarta Hajiya Taslima tayi saurin zama tana ɗaukan wayan ta takira ta ringin ɗaya ana biyu ta ɗauka tana cewa"ke ba ajinki ko ganin ki saita ɓaci.

Ajiyar zuciya Mami ta sauke dan ganin tasa meta a waya tace"kede bari Taslima kina ina yanzun?

Taɓe baki tayi kaman tana ganin ta tace"yo ai ke ɗince idan ba dawata matsala ba,ba'ajinki ko ganin ki yanzu de faɗi komade menene dan ina da abun yi.

"Yi hakuri Taslima in sha Allah zan gyara tace da ita cikin marairaice murya"faɗi mana kintsaya kina janjanin magana idan baki da abun cewan kinga ajiye waya ni inada abunyi.

Tafaɗa cike da ƙosawa"hmm dama de ina wannan yaron da kikai ni wajen malamin nan ya mana aiki akan sa"eh naji"to shine ya dawo"masha Allah kice abu yayi aiki yayi kyau.

"I na wani aiki yayi Taslima da sauran rina a kaba zance aiki beyi kyau ba,tunda ana saura kwana uku bikin sa yabar komi yazo nan,amma fa tsugunne bata kare ba.

Bade kinason cemun ba da shirin auren Fauza ya dawo ba?

hmm"kusan hakane ƙawata dan tun jiya daya zo kallon arziki be haɗata da shi ba.

"To ina wannan magani da ranan Malam yabamu yace duk sanda yaxo a samu a zuba masa cikin wani abun ta tambaya tana yin shiru dan sonjin amsa da zata bata.

"Kede bari wallahi ƙawar amana wallahi abinci mai rai da lafiya muka shiryama wannan Yaron amma kaman wanda yasan da wata a ƙasa washe gari cike da zaƙuwa nace taje ta dauko kwanukan mugani ko yaci in gaya miki kaman yanda ta kai haka ta dauko data tambaya sai cewa ma dayayi wai dama yace akawo masa ne ko wannan ƴar iskar da yazo da ita zata bukata kuma ita din ma bata bukaci komai ba.

"Ke yanzu tsayawa zakiyi ki zuba ido kina kallon sa da wata ba take ƴar ba?

"yana daga cikin abunda yasa nakira na fada miki yanzu sannan na faɗa miki gobe idan Allah yakaimu Baban su ze dawo shine nace ko zamu je wajen malamin?
Kinga ni goben inada aiki sosai.

"Indan wannan ne ba matsala bace nide kawai naji dumus a hannuna yanzun nan zaki ga aiki da cikawa,tafaɗa tana ƴar dariya itama Mami dariyar tayi tace"baki da matsala yanzu zakiji alart kafin nan da gobe inason jin kyakkyawar sakamako"angama ran Uwar gida kuma amarya a gidanta yadaɗe cike da farin ciki Mami ta katse wayan tana nufan ɗakin Fauza dan ganin a wani hali take ciki.

WASHE GARI

Koda sukai sallar Asuba a tare dan shi yajasu sukai kasancewa sunyi makaran tashi daga bacci tanan zaune tana azkar dinta na safe ya tashi yashiga wanka yafito ɗaure da towel a  ƙugunsa miƙewa tayi tsab ta barmasa ɗakin dan ba karamin aikin sa bane yanxu sai yasunce towel a gaban ta ba kunya.

Harta kai ƙofan zata fita ta tsinkayi muryar sa yana kiranta"ƴar Amana ƴar amana cak ta tsaya daga barin buɗe ƙofa da zatayi ba tare da amsa masa kiran ta dayayi ba,sannan bata juya ta kalle sa ba,be damu da rashin amsa wartata yaba ya cigaba da shirin sa da yake yana cewa da ita zan ɗanyi tafiya ko zaki bini muje tare.

"A'a ba sai munje taren ba Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya tasamu bakin ta cewa yaji daɗin addu'ar tata har cikin ransa"da amin ya amsa yana saka rigarsa tana nan tsaye bata tafi ba sannan bata juya ta kalle ba harde yagama shirin da yake ya tako a hankali bataji takun nasa ba saide kawai jin mutum tayi ya riƙo ƙugunta da hannun sa biyu yana matso da ita jikin sa sosai dan zabura tayi tana cewa"subuhanallahi .

Iska ya kumtsa a bakin sa saida ya fesar ya dubeta ganin yanda tayi zuru da ita harta so bashi dariya amma ya gimtse cikin kamewar nan tasa yace"me kike zabura da kiran sunan Allah kaman kinga abun tsoro dan common na riƙeƙi halalina na taɓa kuɗin Ammin na sakina.

A fusace ta kalli cikin idon sa ita tayi saurin zanyewa saboda baxata iya kallon cikin idon nasa ba,kiyi magana mana yarinya yanzu zakiga aiki da cikawa,shiru tayi masa kaman ruwa ya cinyeta bata wajen,ganin bazata magantu ba yasa shi cewa ki kula da kanki sannan kiyi nesan ta kanki da duk wani abu da kikasan ze shiga tsakanin ki da ƴan gidan na ɓacin rai saboda ita ɗin tamkar Ammi take a wajena,sannan Sajid ki dauke shi tamkar Faisal ko Malik idan na gama abunda naje yi zan dawo koman dare ne idan kuma aikin be kare ba zan iya ɗaukana gobe ko jibi duk wanda ya tambaye ni kice masa na fita da safe koda zasu so jin inda naje ɗin.

Zan bawa wani sako ze kawo miki idan kina da bukatar wani abu ki faɗamun ko kuma kiyi list ɗin sa zaki iya girka duk abun da kikeso kici tunda yafara magana tayi shiru tana sauraron sa saida ya gama yana batun sakin da taga riƙon da yamata cikin tausasa murya tace"idan zama nan ɗin akwai taƙura akan aiki da kaxo yi me ze hana kasani a mota ko ta hayace in koma gida inaga idan kayi hakan kaima zakafi samun kwanciyar hankalin ko?

Tallaɓo fuskan ta yayi da hannun sa ya mannawa mata kiss a kumatu yakai bakin sa daidai nata yana batun tsotsa tayi sauri kauda kanta gefe tana tura baki tana kunkuni beji abun da take cewa din ba ya dalle mata bakin da yatsa yace wannan bakin tsiwan naki zanyi magana shin wataran.

Riko hannu ta yayi suka fito tare yana duba agogo dake daure a dantsen hannun sa yakai dubansa gare ta yace"ko zakimun rakiya ne?

Girgiza masa kai tayi duk tayi kalan tausayi.
Duk sai yaji ba daɗi shi kaɗai tasani bata saba da mutanen gidan ba kuma yanzu yace mata zeyi tafiya,shi kansa sai yake ganin kaman be kyauta mata ba, duk sai yaji tausayin ta yana neman tasiri akan sa kaman yafasa tafiyan yake ji saida yayi da gaske sukai sallama da ya tafi ya barta.

Bata taɓa sanin tayi sabo da shi harhaka ba saida yace tafiya zeyi idan be dawo yaudin bafa ta faɗa tana kaiwa zaune saman kugera rabka tagumi hannu bibiyu tana samun kanta tayi da yimasa addu'an Allah yasa yagama yajuyo a yau din idan kwana ya kamashi batasan ya zatayi ba.

Tana nan zaune tana karanta wasikar jaki taji anyi knockin ƙafa tashi tashi tayi tanufi kofan tabude Sajida ta gani tsaye,tana sakin fuska tace"ina kwana Anty Sajida?

"Lafiya lau Aisha ya kwanan bakun ta?

"Alhamdulillahi Anty ki shigo mana ta faɗa tana kaucewa a hanya"basket ɗin da take rike dashi ta miko mata tana cewa"idan kingama kizo kiyi aikin da Mami tace miki zakiyi jiya.

Ai ba'a shiga ɗakin amare a irin wannan lokacin yanzun ma karambani nayi da nazo ta kare magana tana ƴar dariya tare da ɗan waigawa tana duban bayan ta.

"Kai Anty Sajida amma kin iya zolaya wallahi"lalle Aisha haryanzu da sauran ki ai wallahi bari kiji in faɗa miki ba'a wasa da rinsu Ahmad da irin sune burin kowace ɗiya mace tasamu ta mallake sa matsayin miji ki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo yamiki kafa idan ma bakisan yanda ake tattalin miji ba ni nan sa inkoya miki yanda ze mace a kanki ba boka ba malami.

Saida ta gama faɗin abunda takeso fada ɗin kuma saita riƙe baki tana cewa"kinga sai sakin magana nake haka sakaka Allah de yasa be jini ba.

"Anty bari nayi nazo naje kar banje da wuri ba Mami tayi faɗa kuma"ke kinyi magana bara nima naje kinga idan kin gama dawuri ki sameni can kitchen ki tayamu aiki kema kiga yanda ake tarɓa miji idan ya dawo daga wata tafiya ko a office dan wallahi waƴan nan tsofin basa wasa da lamarin miji wallahi"kede kika sani Anty kuma Oga yana nan zaune kikayi ta sakin layi"na shiga uku ni Sajida amma be yasa bakiyi mini alama ta yanda zan gane ba,tace tana jan gyalen ta rufe saman kanta tabar kofa tana fatan kar Ahmad yafito ya ganta awajen.

"Barka da safe Mami?
"Ummm kawai tace tana ɗauke kanta gefe.

Shirune ya ratsa wajen ita Aisha na tunanin ta ina zata fara ita kuma Mami ji ƙimarta ba ze bari tta fara cewa ta tashi tayi ba,gani take tunda jiya ta riga ta faɗa mata ai tagama komai kuma ita haka kawai takejin zafin yarinyar dan ganin ta tare da Ahmad.

Sajida ce tashigo falon ganin yanda Aishs take tsugune rakiɓe gefe tace"bade har kin gama sharan ba?tayi hakan ne da sanin ta dan tasan Mami tunda ta saukar da kai jiya ta faɗa mata to yau da wuya tasake maimaita matan.

"Ina fa zatayi yarinya tun bata gama sanin komu su waye ba take son raina mu"haba Mami ai ko ita bazata raina ki ba inaga rashin sanin kan gidan ne kawai ya zaunar ta nan din tana jiran umurnin ki.

"To sannun uwar baki haka tace miki"yi hakuri Mami tace tana yin ƙasa da kanta sannan tayi gaba tana cewa da Aisha biyoni,miƙewa Aishan tayi cikin sanyin jiki tabi bayan Sajida har kofan ɗakin ta nuna mata sannan itama ta koma kitchen.

Shara tafara yi tayi moppin sannan tashiga goge goge saman mirrow side drower dade sauran su sai da tagama sannan ta kunnu turaren wuta har taja kofan zata rufe ta tuna wani takarda da ta gani tafasa fitan tayi tana komawa inda taga takarda papers ne guda takwas da alama copyin akai ta ɗauki ɗaya daya ja hankalin ta.

Suna da tagani rubuce ji saida yakusa sumarta cikin rawar jiki da murya ta furta"ISHAQ IBRAHIM HAKIMI.

saurin daukan duka papers ɗin tayi tana sauya musu wajen zama tayi tana turawa......

ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

234K 16.2K 19
#2 IN HIS SERIES π•π’π€π«πšπ¦ 𝐒𝐒𝐧𝐠𝐑 π‘πšπ­π‘π¨π«πž The elder son of the Rathore family and the future King of Rajasthan, he was cold, arrogant...
114K 1.7K 26
Rajveer is not in love with Prachi and wants to take revenge from her . He knows she is a virgin and is very peculiar that nobody touches her. Prachi...
617K 32.9K 50
π’πœπžπ§π­ 𝐎𝐟 π‹π¨π―πžγ€’ππ² π₯𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐑𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐒𝐞𝐬 γ€ˆπ›π¨π¨π€ 1〉 π‘Άπ’‘π’‘π’π’”π’Šπ’•π’†π’” 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 β˜†|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
1.7M 101K 40
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...