WAZEER!

By REAL-SMASHER

3.2K 338 50

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... More

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Wedding march
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Inexplicable
Strangerlike
Safwah
Adviceful
Thought pattern
Proposalist
Her wish!
Wedding bell!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Mission

90 18 5
By REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      _Join our group domin samun update https://chat.whatsapp.com/LMWOmafckAGJoQ4ebkvdcG.. Follow the REAL-SMASHER SQUARE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Va5voqA4tRrtP6Mvss2q.. Follow my channel dearest domin samun update na book ɗin *WAZEER* da sauran wanda za su zo,har ma da tsofaffi.. Duk wanda nake da contact ɗinsa yayi following ɗina za su nuna min,idan kuna so nayi saving contact ɗinku chat me up @+234 803 511 6372/@+2348165726609. Thanks so much as u do so._


                               17

#Mission

*SAFWA*

          Monday tushen aiki ko Bature na tsoronki,haka dai Bahaushe yake mata kirari,kasancewar ranar aiki duk ma'aikatan gwamnati sun wuce gurin aiki,ƴan kasuwa zuwa wanda suke sauran sana'o'i kowa ya nufi gurin nemansa,hatta ɗalibai suma tun sassafe sun tafi makaranta,idan kabi streets za kaji ko'ina yayi tsit. Kwance Safwa da bata fita school ba take a saman kujera a parlour tana chat,babu yanda Umma bata yi da ita akan ta shirya ta tafi school ba,tace ita sai ta ƙara hutawa jikinta duka ciwo yake mata,Umma ta gyaɗa kai ta tashi tai wucewarta kitchen,tana shirin ɗora sanwar rana take ci gaba da mita tace "idan Babanku yai magana wallahi dama kada ki sake kice na san wani abunda ya hanaki zuwa makaranta yau,zan ce bansan komai ba tunda dai ya baki transport kuma kin amshe kin ƙi zuwa" Safwa tai dariya tace "kai Umma don Allah" Umma tace "toh shi kenan ki ci gaba da cewa kai Umma,sai ya dawo ya tambaya zan sanar masa komai,ni baza ki janyo min faɗan da ya fi ƙarfina ba wallahi ina zaman²a" Safwa tace "ai kema kin san bazai dawo ba fa yanzu" Umma tace "a'ahhaa! Tsautsayi kuma ai yana iya sawa ya juyo" Safwa tace "a'a in sha Allah ma bazai dawo yanzu ba" Umma tace "uhumn! Allah dai ya kiyaye" Safwa tace "ameen" tayi shiru ta ci gaba da chat ɗinta,number Aley take kallo da bai buɗe morning text da tai masa ba yau,a fili tace "ko dai jikin ne wai har yanzu?" Tayi shiru kamar tana tunani sai kuma ta sake cewa "let me call him naji dai" da sauri ta fita daga whatsapp ta shiga phone call ɗinta,number ɗinsa tayi dialing underneath tana addu'ah Allah yasa kada ace mata a kashe yake,cikin sa'a dai² lokacin wayar tasa yana buɗe,kiranta na tafiya tayi ajiyar zuciya tace "alhmdllh!" Kafin ta sake magana ya ɗauka da sallama,Safwa ta amsa tana faɗin "Friend! How are u? Ya jikin?" Daga can gefensa ya amsa,Safwa tace "Allah ya ƙara lafiya,dama na kira ne saboda na ji ka shiru,though muna ta hidimar biki ban samu kaina ba sai yau" Umma dake kitchen ce ta fito ta zauna ta shiga gyara kayan miya,Safwa dake waya bayan sun ɗan yi magana tace "ga Mom ɗina za ta gaisheka da jiki" bai ce komai ba Safwa tasa kiran a speaker sannan ta miƙawa Umma wayar,Umma na mata alamar waye tace "zan faɗa miki idan kun gama magana" Umma ta gyaɗa mata kai tare da karɓar wayar ta kai kunnenta tace "salamu alaikum" Wazeer dake zaune parlour ɗin gidansu yayi baya tare da jinginar da bayansa jikin kujeran da yake kai yace "wa'alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh! Barka da safiya Mom" Umma tai saurin ɗaga wayar daga kunnenta jin maganar da ƙarfi,Safwa tace "Umma a handsfree nasa" Umma ta gyaɗa mata kai tana sakin fuskarta ta sake faɗaɗa ta da fara'a tace "barka dai.. Mun tashi lafiya? Ya jiki kuma?" A hankali yace "jiki alhmdllh" Umma tace "Allah ya ƙara afuwa yasa kaffara ne" yace "ameen².. Thank u Mom,Allah ya saka da alkhairi" Umma tace "babu komai,Allah ya ƙara lafiya" ya amsa tare da sake yi mata godiya,tace "sai an jima,ga Safwar" tana miƙa mata wayar Safwa ta cire daga handsfree ɗin da tasa ta kai wayar kunnenta tace "hello dear!" Daga can gefen Wazeer yai mata godiya tare da sallama ya katse kiran,murmushi me sauti Safwa tayi da yasa Umma ɗaga kai ta kalleta,Safwa da ta rungume wayarta a ƙirji ta shiga tunani fuskarta cike da murmushi,Umma dake ta kallonta ba tare da ta sani ba tace "ke kuma lafiyarki lau kike ta dariya? Ko kin sami taɓi ne a ƙwaƙwalwa?" Maganar Umma yasa Safwa dawowa cikin hayyacinta,Umma ta sake cewa "waye wannan da kika bani mukai magana ne?" Safwa tayi murmushi kafin tace "Friend ɗina ne" Umma ta ɗago ta kalleta tace "shima a Bayero University ɗin yake?" Safwa tace "a'a" Umma tace "toh! Allah ya kyauta" Safwa tayi murmushi tace "Umma kin gansa kuwa?" Umma dake ta aikinta tace "ta ina zan ganshi ni Murjanatu bayan ba haɗuwa da shi muka yi ba" Safwa ta kwashe da dariya tace "wallahi Umma ya haɗu,first class ne gurin kyau gashi classy,ko mace albarka wallahi,duk yanda nake jin kaina nake kallon babu wanda ya fini,amma wallahi na yarda shi ya wuce ni" Umma tace "toh! Duk ba wannan ba,mene ne tsakaninku shi nake son ji,kin san dai Babanku bai san komai ba,kuma ba zai so wannan yawan kule²n samarin ba" Safwa ta buɗe ido tace "a'a Umma ce miki fa nayi abokina ne shi" Umma tace "anya Safwa? Kinga nima ban cika son tara samarin da kike marasa amfani ba,gara idan kika samu tsayayye wanda za'a nunawa sa'a sai mu tunkari Engr da maganar duk da bai son maganar aurenki yanzu,amma Allah na tuba ai ba dafaki za muyi mu ci ba,dole wata rana kiyi aure" Safwa ta gyara zama tare da ajiye wayarta gefe tace "wallahi Umma ai nima na fi son nayi auren,ƙawayenmu fa na secondary da wanda muke karatu yanzu sai auren suke yi.. Wallahi gidan Yaa Khalidah ma da muka je sai naji inama gidana ne,sai abunda naga damar yi" Umma tayi murmushi tace "ke dai Allah ya kaimu lokacin,kika samu miji kamar Dr Mohan ai mun yi sa'a" Safwa ta washe baki tace "wallahi kuwa Umma ai sai ma da zamu taho ɗin nan,ji nayi inama ace ni aka kai gidan nan" Umma tace "lokacinki zai zo" Safwa tace "Allah ya kawosa a kusa" Umma tace "ameen.. Yawwa! Wai ni kuwa nace ko ɗan saurayin ma kin yi a bikin nan?" Safwa ta taɓe baki tace "a'a!" Umma ta kalleta da mamaki tace "duk wannan kwalliyar da kayan da kika sa masu tsada,yanzu babu wanda yace yana sonki cikin abokan Mohan ɗin?" Safwa tace "uhumn! Ina dai gani suna kula su Muneerah ana exchanging digits" Umma ta buɗe baki don mamakin da ya cika ta tace "toh amma Muniba fa na ji ance ta yi saurayi? Ko ba a gurin bikin suka fara haɗuwa da wanda naji Baniynah tana magana bane?" Safwa ta kalli Umma tace "waye?" Umma tace "wani babban soja fa da naji ana ta cewa shi ne aminin mijin Khalidah tun yarinta,ni mene ne ma kuwa naji sunansa?" Safwa tai shiru tana kallon Umma,can kamar an mata dole tace "wai wannan Lieutenant ɗin?" Umma tace "shi fa,wallahi sunansa ne ya kwanta min" Safwa ta taɓe baki tace "taɓɓɓ ɗin wannan uban jin kan,meye abun damuwa a saninsa?" Umma tace "toh ki tuna min sunansa mana idan kin gane shi" can ciki² Safwa tace "Abuu Turab" Umma tace "tabbas! Shi ne wallahi,ai har na fara jiyo ƙishin² ɗin iyayensu mata ma sun san maganar,yanzu abunda yai saura dama a gama bikin" Safwa tace "kaiiii! Umma ke duk a ina kika jiyo wannan maganar? Munibar ma da ba wani sakewa take da shi ba,kamar fa ba ta sonsa ma ni nake ga" Umma tace "anya kuwa Safwa?" Safwa tace "wallahi ko magana ba ta masa fa,shi dai yake ta neman guri da siblings ɗinsa" Umma tace "toh! Amma har a gidan bikin naji ana ta cewa saura bikinsu ita da Baniynah nan ba da jimawa ba?" Safwa tace "taɓɓɓ ɗin! Toh sai dai in kuwa auren dole za suyi mata,ko fa a gurin bikinma ba ta um bare um'um" Umma ta kama haɓa tace "amma meye laifin wannan? Ai na gansa dai matashi ne me jini a jiki ko?" Safwa tace "uhumn!" Sai bata sake cewa komai ba,Umma tayi ƙwafa tana jinjina kai,lokaci ɗaya ta ajiye wuƙar hannunta tace "toh amma bari muyi wata ƴar gulma mana" Safwa data ci gaba da chat tace "na me?" Umma tace "kuma ai naga yana da kuɗi kamar ma zai fi Mohan ɗin ko?" Safwa tace "maybe" Umma tace "toh ba ni hankalinki nan muyi magana" Safwa tace "ina ji" Umma tace "ajiye wayar tukuna ki bani hankalinki nace" Safwa ta ajiye wayar ta zubowa Umma idanu,Umma tace "kika ce ba ta sonsa?" Safwa tace "ni dai haka na gani" Umma tace "in ba ta sonsa ai wannan matsalarta ne,za ta iya samun wanda ya fisa tunda ubanta wani ne a garin,kuma yana harka da ƴan siyasa,ko ɗan shugaban ƙasa zai iya samo mata ko ba haka ba?" Safwa tace "haka ne" Umma ta gyaɗa kai tace "yanzu dai ba wannan ba,ke ya yi miki?" Safwa ta tsaya kallon Umma ta kasa cewa komai,Umma tace "tambayarki fa nake dan walaƙanci kikai min shiru" Safwa tace "Umma ban gane tambayar taki ba" Umma tace "ya yi miki as irin mijin da kike son aure?" Safwa ta buɗe ido da kyau tace "Umma!" Umma ta ɗaga mata hannu tace "ba ni amsa tukuna kafin kice komai" Safwa tace "gaskiya Umma in dan kuɗinsa ne ya yi,amma ni ba na son namiji me jin kai irinsa" Umma ta buɗe baki tace "wannan ai ba matsala bane,in dai ya miki kuma kina sonsa ni na san yanda zanyi hankalinsa ya dawo kanki" Safwa tace "Umma gaskiya ni dai a bar maganarsa,da dai wani ne daban ko akan wannan Aliyun da na baki waya kuka gaisa,amma matsalarsa shi har yanzu ban gama saninsa ba tunda bamu jima da haɗuwa ba" Umma ta gyaɗa kai tace "shi kike so?" Safwa tace "wallahi Umma dan baki ganshi bane,ai ko Yaa Mohan da su Yaa Khalifa wallahi albarka" Umma tayi murmushi tace "yanzu shi kike so dai kenan?" Safwa tace "ehh Umma gaskiya,tun ganin farko da nai masa na tafi da shi" Umma tayi dariya tace "toh babu damuwa,zan dai san yanda akayi" Safwa tace "yawwa Ummata Allah yasa min ke a aljannar duniya da lahira" Umma ta washe baki tace "ameen Safwata kin yi addu'ah me kyau,amma ni dan dai kin dage ne,ai da na karɓo miki ɗan taimako akan wancan sojan saboda yayi min a matsayin suruki" Safwa tace "taimakon me Umma?" Umma tace "ƴan addu'o'i mana da maganin farin jini,ai nima ragon azanci nayi na barki haka nan,da tun kafin ayi bikin nan nai hakan da yanzu kin samo min suruki,war haka ma da yanzu Sojan nan ya zama rabonmu,kawai sai na saki jiki kamar kabewa,na ɗauka a yanda kike da kyaun nan gaki fara tas²,kuma mazan wannan zamanin na san yanda suke son farar mace,duk zatona baza ki rasa farin jinin da samari masu shi ɗin za su biyoki ba,amma yanzuma bai ɓaci ba ai tunda ba wani nisa akai ba na gano bakin zaren.. Toh amma ya kike gani yanzu,in sa a karɓo miki dai za kiyi amfani da shi? Kada sai na amso kisa nayi asarar kuɗina a banza? Dan yanzu zamani ya canja,ƴan mata ma wasu su suke kai kansu su nemo sa'a,ai an daina zama kowa mafita yake nema" Safwa ta ƙyalƙyale da dariya tace "wallahi zanyi Umma ki amso,ƙawayenmu fa ina jin suna labarin a makaranta,suna cewa ba a banza samarin suke musu abunda suke so ba,amma kuma idan ka tambayesu me suke yi sai suce falalar salati ne" Umma ta gyaɗa mata kai tace "toh shi kenan sha kuruminki zan kira Hilda muyi maganar,a yanzu dai banga lokacin zuwa Minna ba gaskiya,da ɗaukanki zanyi mu tafi ayi komai a gaban idonki,to amma na san in nai maganar da itama ɗaya ne,za tayi min komai kamar ina nan,in yaso sai ta aiko min kamar yanda aka saba.." Safwa tace "yanda aka saba kuma?" Umma tace "ehh mana aiken da ake yo mana daga can gidan na kayan gona idan akai noma" Safwa tace "aihoo! Ehh wallahi ta aiko" Umma tace "toh shi kenan ai tunda kin amsa na san bazan yi aikin banza ba" Safwa ta gyaɗa kai kafin tace "ni wallahi har mamaki nake wani lokaci idan naga yanda friends ɗinmu suke yin samari manyan masu kuɗi" Umma tace "a'ahhaa! Kema in dai wannan ne za ki gansa a kanki,nan ba da ɓata lokaci ba za ki ɗorar da abunda ke faruwa" Safwa tai dariya tace "wayyo ni Safwa,ai kuwa Umma wallahi nayi saurayi me kuɗi ko,sai kin san ƴarki ta samo miki irin mijin da kike buri" Umma tace "Allah Safwata?" Safwa tace "wallahi kuwa Umma sai wani ma ya san na je inda zaki huta,duk aikin gidan nan sai dai masu aiki suyi miki,ke kuma kina gefe kina hutawa da bada umarni" Umma tai shewa tayi guɗa tace "Allah yasa,ina daga zaune ai min komai" Safwa tace "har Saudiyya zan kaiki,daga can kiga likita akan matsalar ƙafarki" Umma tace "toh Allah ya bamu sa'a" Safwa tace "ameen².. Wallahi har na fara imagination" Umma tayi dariya tace "toh! Ai har kin fini ɗauki da zumuɗi ma" Safwa tace "Allah Umma ni yanzuma ji nake inama ina da kuɗi,ai da tafiya Minna zanyi gurin Aunty Hilda kawai" Umma tace "ahh! Lallai ashe dai da gaske kike" Safwa tace "wallahi i'm damn serious Umma,ƙawaye nawa muna tare da su suna munafurka,ai gara nima na tashi tsaye su san cewa ba su kaɗai suka san kan gari ba" Umma tace "kai amma na ji daɗi da Allah yasa kike da fahimta,yanzu da wata ce sai tace min ba haka ba,ta kama faɗa min ƙauli da ba'adi" Safwa tace "a'a wallahi ni dai ina so" Umma tace "ai kuwa tunda har kika nuna min ina da muhimmanci,yau ɗin nan zan kira Hilda nai mata maganar,dama tana tai min zancen ya kamata nai miki shiri ba tun yau ba,ni ce dai na tsaya ina nuƙu² ina cewa ai ƴata me kyau ce ba sai na wahalar da kaina akan wannan ba" Safwa ta buɗe baki tace "taɓɓɓ ɗin! Toh wallahi Umma har wanda suka fini ma suna yi,ni dai ki mata magana ta aiko min na fara fantamawa nima" Umma tace "toh bari na gama girkin nan dai sai na tsara abunda zan ce mata ayi koh?" Safwa tace "ehh! Ki gama" Umma ta tashi ta kwashi kayanta tai kitchen tana cewa "bari dai nayi sauri na kammala.."

*MUNIBA*

      Shigowarsu gida kenan bayan ta yi parking suka buɗe motar a tare suka sauka,yanda ko'ina yake shiru da kuma parking spot da babu wasu motocin ya tabbatar musu su ne suka fara dawowa,sanda kowa ta ɗauki belongings ɗinta kafin suka nufi cikin gida a mugun gajiye,suna shiga parlour Baniynah ta ajiye komai dake hannunta ta wuce kitchen,Muniba ta bita da kallo tace "hey! Where are u going?" Baniynah bata tsaya ba tace "i'm coming" Muniba tace "okay!" Daga haka ta ajiye handbag ɗinta da car keys,tana ƙoƙarin sauke hijab ɗinta ta ɗan zauna wayarta ya fara beeping,saurin cire hijab dake jikinta tayi tare da buɗe jakarta ta fito da wayar,sunan Abrar da ta gani yasa ta ɗan buɗe ido kafin tai saurin answering,tana kai wayar kunnenta tai sallama,daga can gefen Abrar ta amsa tana faɗin "wa'alaikis salaam.. Good afternoon Aunty" Muniba ta ɗan rufe ido shyly tace "afternoon dear,ina yini? Ya school da su Mom?" Abrar tai dariya tace "kowa lafiya lau Aunty,tun rannan nake son kiranki amma sai nake ganin kamar zan dameki kuna cikin hidimar biki" Muniba tace "ohh! Ai kuma tun ranar Saturday aka gama bikin,kawai dai ba'a kai amarya ba sai Sunday" Abrar tace "ehh haka ne,ya gajiyarku? Ya su Aunty Baniynah?" Muniba tai murmushi tace "yanzun nan ta wuce kitchen,mun shigo gida daga school" Abrar tace "laa! Bari to na bari ki huta,sai an jima Aunty" Muniba tace "Allah ya kaimu,thank u so much dear.. Ki gaisar da kowa please" Abrar tace "kaii mutanen gidanmu fa suna da yawa" Muniba ta sake yin murmushi tace "alright! Ki gaida Mom" Abrar tace "one.. And Then?" Muniba tace "Yaa Hammad ko?" Abrar tace "two.. Ohh! Wait please Aunty,are u really calling him Yaa Hammad ko dai nice naji ba dai² ba?" Muniba tace "no! Haka nace,then Sis Husniyah" Abrar tana dariya tace "alright! Three and?" Muniba tace "and then Sis Abrar" Abrar ta ƙyalƙyale da dariya tace "four.. Then?" Muniba ta buɗe ido da kyau kafin tace "that's waɗanda na sani" Abrar tace "a'a ba shi kenan ba,saura mutum 1 fa baki faɗa ba" Muniba tace "mutum ɗaya? Who's this?" Abrar na dariya tace "a'a nima dai na ji kin ce mutum 4 kuma saura 1" Muniba tayi shiru tana tunani,Abrar dake dariya tace "kaii Aunty kin manta wai?" Har zuciyarta bata kawo kowa ba,kuma bata fahimci me Abrar ke nufi ba,tace "yeah! I think na manta gaskiya" da ƙarfi Abrar tai whispering a kunnenta tace "Yaa Abuu Turab fa" da sauri Muniba ta zaro ido waje,Abrar ta ƙyalƙyale da dariya sosai kafin tace "alright! Yanzu wai har kin manta da shi?" Muniba ta rasa me za tace saboda kunyar da ya cikata,Abrar tace "yawwa! Aunty don Allah ki turo min pics ɗinmu na ranar dinner,na manta ban yi miki magnar ba,and shi ne dalilin da yasa na kira ki" Muniba ta daure da ƙyar tace "alright! In sha Allah" Abrar tace "thanks so so so much Aunty,sai an jima idan mun haɗu online" Muniba tace "Allah ya kaimu,na gode sosai² dear,a gaida Mom please" Abrar ta amsa kafin suka ajiye wayar. Ɗaga kanta tayi ta kalli wall clock dake maƙale can yana nuna ƙarfe 2:30pm,a hankali tayi shiru tana tunanin wayar da suka yi da Lieut ɗin da safe kafinsu tafi school,da yake sanar mata ya yi tafiya zuwa FCT a safiyar,tayi ɗan ajiyar zuciya da tazo kan lokacin da yake sanar mata idan ya dawo zai zo ya gaisar da Abba,da ƙarfi gabanta ya wani irin faɗi,tunanin mene ne zai sa shi zuwa gurin Abba da abunda zai ce,har ma da maganganun da za su yi kawai suka tsaya mata a rai,Baniynah ta fito kitchen tana cewa "Sweetheart ni fa wata irin yunwa nake ji yau" Muniba ta ɗago kanta ta kalleta,ganin tray a hannunta,sama plate ne ta ɗebo abinci ga drink da ruwa a gefe,sai spoons biyu ta ɗan waro idonta waje tace "to ai gashi nan za kiyi magnaninta" Baniynah tace "ai har da ke na ɗebo,sa minjaye Ma'am" Muniba tace "a'a ni ba na jin yunwa,na ci chops ai a canteen" Baniynah tace "wannan ɗan small chops ɗin ne har kika ƙoshi?" Muniba tace "yap! I'm ok.. Bari nayi wanka na dawo" Baniynah tace "ok!" Tana ajiye abincin ta ɗauki remote tai powering Cinema ta canza channel kafin ta ɗauki spoon ta fara cin abinci tana kallo,wayar Muniba dake ajiye saman couch ne ya fara beeping,a hankali Baniynah ta juya kafin ta ajiye spoon ɗin ta tashi tana ƴar mita,ta san idan bata ɗauka ta ce ba ta kusa ba,idan wani mara haƙurin ne sai yaci gaba da kira,sanda ta kalli me kira taga number anyi sabin da *L.A* ta dunga kallo tana tunanin what abbreviation ɗin yake nufi? Amma kuma ta kasa guessing,sai da kiran yaje daf zai katse sannan tai answering tasa wayar a speaker da faɗin "hello!" Lieut Abuu Turab da bai zaton za'a ɗauka ba,jin kalmar hello da muryar ya tabbatar masa ba Muniba bace,Baniynah ta sake cewa "hello! If u are hearing me please me wayar ba ta kusa" siririn ajiyar zuciya yayi kafin yace "assalamu alaikum" Baniynah ta buɗe ido da kyau tace "wa'alaikas salaam warahmatullah.. Good afternoon" ya amsa ta cikin sanyin halinsa yace "Ƙanwata! Ya gida da su Mami?" Baniynah ta sake buɗe manyan idanunta fuskarta na faɗaɗa da murmushi me cike da kunya tace "lafiya lau.. Ba ta kusa,idan ta dawo i'll tell her ka kira" yace "alright! Thanks" tayi ɗan murmushi,yace "a gaida mutanen gida" tace "za su ji in sha Allah,sai an jima.." Suna ajiye wayar ta dunga kallon sunan tana dariya,a fili tace "L.A sai kace ba sunan mutum ba,lallai ma Sweetheart haka ake saving sunan wanda ke sonka?" Ta shiga tai editing sannan ta ajiye wayar ta ci gaba da cin abincinta. Muniba na saukowa downstairs sanye da riga da wando ta kwanta saman kujera tana kallon Baniynah da bata gama cin abinci ba har lokacin tace "wai baki gama ba har yanzu?" Baniynah tace "yeah! An kiraki fa" Muniba tace "waye?" Baniynah tace "wai L.A" Muniba ta ɗan buɗe almond eyes ɗinta sai kuma tai shiru tare da lumshe idanunta,Baniynah ta juyo ta kalleta tace "hey! Bacci kuma za kiyi?" Muniba ta buɗe ido tace "a'a ba na so nayi bacci yanzu lokacin sallah ya riskeni a kwance" Baniynah tace "ok!"

*SAFWA*

       Da yamma Umma na zaune parlour ita da Safwa ta ɗaga kai tace "Safwa bani wayata na kira Hilda" duk yanda Safwa ba ta so a tasheta idan tana riƙe da wayarta,amma kıran sunan Aunty'n nata yasa tai saurin tashi tana washe baki,cikin zumuɗi ta tafi ta ɗauko ta kai mata,Umma ta amshi wayar tana faɗin "toh! Allah ma yasa ina da katin da zai isa muyi magana dai" Safwa ta zauna kusa da Umma tace "to Umma na baki nawa ki kira da shi,ni ina da kati sosai a ciki" Umma tace "a'a bari dai naga me nake da shi a balance" tana dubawa taga babu kuɗi sosai a ciki,tace "ai kuwa babu kuɗi a wayar" Safwa ta ɗauki wayarta da sauri tace "bari na kira miki ita a nan" ta shiga ta duba lambar Aunty'n nata da tai saving da Aunt Hilda,tana danna mata kirata ta sa wayar a speaker,bai jima yana ring ba aka ɗauka,daga can gefen akace "hello! Daughter" Safwa tai murmushi tace "Auntynah ina yini?" Hilda tace "lafiya lau Safwa,ya mutanen gida da school?" Safwa tace "lafiya lau Aunty,ya su Meenah?" Hilda tace "suna nan lafiya,ya Sister?" Safwa dake kallon Umma tace "tana nan lafiya,ita take son tai maki magana,shi ne na kiraki" Hilda tace "ok! Tana ina? Wayarta ya samu matsala ne?" Safwa tace "a'a ba ta da credit ne" Hilda tace "ok! Bata wayar" Safwa ta kalli Umma ta miƙa mata,Umma na karɓa tace "hello! Hilda" Hilda tace "Allah ya taimaki uwar gida kuma amaryar Engr Ridwan,daga kanki babu ƙari an rufe ƙofa" Umma tayi dariya tace "toh! Za ki fara ko?" Hilda tayi dariya tace "a'a ba farawa zan yi ba,abunda dai yake akwai na faɗa.. Ina yini?" Umma ta amsa tana faɗin "ya gida da yaran?" Hilda tace "duk suna lafiya,ya su Awwal da Engr?" Umma tace "duk suna school basu dawo ba,gidan daga ni sai Safwa yau,itama dan ta yi ƙwange ne ta ƙi zuwa" Hilda tace "alright! Allah dawo da su lafiya" Umma tace "ameen.. Yawwa! Hilda kina jina?" Hilda tace "Ina ji Sister" Umma tai ƙasa² da murya kamar wani zai jiyo su tace "dama kan maganar nan da kikai min ne na Safwa nasa ta kiramin ke" Hilda tayi dariya son ranta kafin tace "ok! Me kike so ayi?" Umma tace "a'a duk abunda ya kamata mana,ai kema kin san komai ba sai na fito nai miki bayani ba,tunda dama ke kika fara min maganar ko?" Hilda ta sake yin dariya me sauti tai shewa tace "yanzu kuma kin dawo kina so a nemo taimakon? Ke fa kike cewa Safwa na da kyau,kuma she's white kamar yanda mazan Kano suke so" Umma tace "ehh! Ai da ɗin ma tunani ne ban yi ba,yanzunma kuma saboda mun yi magana da itane ɗazu ta nuna min ta amince shi yasa nace zan kiraki,to sai naga har ta ma fini ɗoki akai shi yasa na bawa maganar muhimmanci" Hilda tace "uhumn! Ai dama na faɗa miki yanzu ba'a zama haka,ƴan mata da kansu ma zuwa suke suna nemowa kansu mafita" Umma tace "haka ta sanar min ƙawayensu na school duk suna yi da nai mata magana" Hilda tace "ahaf! Ai na faɗa miki tun farko,ko gurin da na karɓowa Meenah kar kiga ƴan mata a gurin,amma dai bari na samu lokaci zanje ko zuwa gobe,da na karɓo zan aiko miki su,sauran bayanin kuma ma yi ta waya" Umma tace "don Allah dai ki ƙoƙarta ayi komai da wuri" Hilda tace "ba ki da matsala Aunty" Umma tace "yawwa! Sai ki sanar min ɗan abunda za'a bayar idan kin je" da sauri Hilda tace "a'a haba Aunty,sai kace Safwa ba ƴata bace,ai kada ki samu damuwa in dai wannan ne,ina amsowa zan doko miki waya" Umma tace "toh shi kenan,sai na jiki?" Hilda tace "ehh Aunty" suna yin sallama Umma ta katse wayar tare da kallon Safwa tana dariya me cike da farin ciki tace "toh ai kin ji yanda muka yi ko?" Safwa ta gyaɗa mata kai tace "Allah yasa ta aiko da wuri" Umma ta buɗe baki tana kallon Safwa sai kuma ta girgiza kanta kawai.

*WAZEER*

        Da yake ya samu hutun sati ɗaya da zai yi shiri kafin ya tafi gurin da akai posting ɗinsa inda zai kama aikinsa na bautawa ƙasa da yi mata hidima,tun ranar Friday da ya dawo wajen dinner bai sake marmarin zuwa ko'ina ba,ko Mimi rabon da yaje gurinta tun ranar,yana son zuwa amma kuma week ɗin nan ya san tana AKTH,kasancewar ta sanar masa morning duty za tayi,shi kuma bai cika don fita da dare ba,sai dai duk safiya ya kan yi kiranta a waya su gaisa,Dad ma kuma tun jiya da sassafe ba ya nan ya tafi Lagos,underneath yana mamakin yawan tafiye²n da mahaifin nasa yake yi tun bayan dawowarsu Nigeria,amma kuma da yake basu cika zama suyi irin maganar nan da shi ba yasa bai ma damu kansa da son sani ba,ƙarƙari suyi sallama idan zai tafiya,in ya dawo kuma yai masa barka da dawowa,shi kenan kowannensu zai shiga harkokinsa. Zaune yake parlour da dare yana tunanin rayuwar da ake a gidan na babu ruwan iyalin wannan da na wannan,babu me shiga gidan wani sai da wani babban dalili,ƙarƙari dai su mazan gidan ma'ana Uncles ɗinsa sukan haɗu a masjid da asuba tun daga can suke gaisawa da juna,sai idan suka shigo gida za su shiga ɓangaren Daada su gaida ita da Abba har su ɗan yi hira kafin kowanne ya shige ɓangarensa yai shirin fita office,sai kuma da dare da suke shiga yi musu sai da safe,nan kam ba wai sai sun haɗu ba duka,kuma abun sam ba ya damun kowa,kowa daga shi sai iyalinsa,a haka kuma sunan ciki ɗaya suke. Dad da ya dawo daga tafiyar da yayi ne ya buɗe entrance ya shigo jaye da luggage ɗinsa,Wazeer ya ɗan waiga kaɗan yana tunanin waye ya shigo,even though ya san shi kaɗai ne a gidan kuma babu wanda zai shigo cikin Uncles ɗinsa,ganin Dad yasa shi buɗe ido sosai yace "Dad!" Dad da ya shigo ya saki murmushi yace "hello Son!" Wazeer ya tashi daga inda yake yana faɗin "welcome back Dad" ya tafi zai karɓi luggage ɗin Dad,Dad ya ajiye gefe yana faɗin "no barshi zan wuce da shi ɗaki idan zan shiga.. So how are u doing? What's happening here?" Wazeer ya girgiza kansa yace "alhmdllh.. Ya hanya?" Dad yace "hanya alhmdllh.. Let me freshen up ko akwai wani matsala?" Wazeer ya ɗan girgiza kansa,Dad ya tashi yaja luggage ɗinsa yace "ok" har ya wuce zai tafi bedroom ɗinsa ya tsaya tare da juyowa yace "arghm! Wazeer" a hankali Wazeer yace "yes Dad" Dad yace "akwai inda za ka ne da safe?" Wazeer ya girgiza kansa yace "nope!" Dad yayi ɗan murmushi yace "ok! Get set za mu fita da kai da safe" Wazeer ya sake buɗe ido yace "where are we going?" Dad yayi murmushi yace "i'll take u somewhere,don't mind za ka sani idan mun je" Wazeer ya ɗan haɗe fuska yace "is it necessary?" Dad yace "capital YES" Wazeer ya gyaɗa kansa sai kuma yayi shiru bai sake cewa komai ba,Dad ya juya ya wuce ciki. Da safe around 11am suka fito cikin shiri,Dad na sanye da 2 piece suite gray color,ka gansu sanda suka fito baza ka taɓa cewa shi ya haifi Wazeer ba saboda jin daɗi da gayu wanda suka ɓoye shekarunsa,ƙananan kaya ne jikin Wazeer da suka amshesa sai ƙamshi suke na different scents ɗinsu masu daɗi da kwantar da rai,ɓangaren Daada suka fara shiga bayan sun sake gaisawa sannan sukai mata sallama suka fice,cikin motar Dad driver ya jasu zuwa Sharaɗa phase II ta can guraren Industrial Estate,a bakin get masu gadi suka buɗe musu,Dad ya sauke glass suka gaisa ya tambayesu aiki then suka ƙarasa ciki,motar na yin parking Wazeer ya kalli Dad dake cewa "get down My dear" then ya sauka motar da driver ya buɗe masa,Wazeer ya buɗe ɗayan gefen ya sauka yana mamakin ina ne nan Dad ya kawoshi,though ya fahimci arean companies ne kawai a gurin,amma bai taɓa zuwa irin ta nan gurin ba sam,babban Company ne da kana kallon gininsa za ka tabbatar ba'a fara aiki cikinsa ba,Dad yana murnusawa ya juyo yana kallon ɗan nasa dake tahowa gurinsa yace "how do u look this place?" Wazeer ya juya ya kalli ko'ina,kamar bazai yi magana ba kuma sai yace "everything is good here" Dad ya sake faɗaɗa fara'arsa tare da ɗora hannunsa a sholder ɗin ɗan nasa yace "ok! Let's go in and see ciki da komai.. Sabon Pharmaceutical company da nayi planning ginawa ne wannan,soon za mu fara harkar magunguna,so an gama komai yanzu na yima Company registration,muna da license already,abunda sukai saura ɗaukan ma'aikata da fara aiki ne in sha Allah" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa cikin mamaki yace "Allah ya taimaka Dad yayi jagora" Dad yace "ameen.. Muje kaga yanda tsarin gurin yake" suna tafiya heading to cikin Company Dad yake masa bayanin komai,tun daga lab ɗinsu zuwa cikin industry,warehouse har babban office ɗinsa,ya ɗauko wani folder da bayanin komai yake ciki a cikin drawer ya bashi papers ɗin yana faɗin "check this kaga ko akwai abunda baiba.. I know My Son is brilliant,za ka iya yima mahaifinka gyara akan some abubuwa,though ba field ɗinka ne harkar sarrafa magani ba,but muna da alaƙa tunda ka iya karantar medicine without my knowledge" yayi maganar cikin barkwanci,kamar project haka Dad ya tsara komai,tun daga preliminary information yake kallon how Dad yayi designing everything na yanda zai tafiyar da his pharmaceutical company,Drug designation,selection of essential medicines,drug classification,levels of use,quantitative evaluation of needs when launching a programme,layout of a pharmacy,premises,characteristics of a warehouse,interior layout of a warehouse,arrangement of drugs and supplies,management of a pharmacy,organization of activities,stock management,donations of recuperated medicines and medical samples. Da ya gama gani ba ƙaramin jinjinawa mahaifinsa yayi ba,duk yanda Dad yake yabonsa idan magana ya tashi,zai iya cewa shi kansa gadon ƙwaƙwalwa yayi gurin iyayen nasa biyu,da ace ana gadon ilimi ma tabbas da bai shiga aji an koya masa wani abu ba,don ko Miminsa da first class yaga ta fita sanda suke maganar lokacin da tayi karatu har ta ɗauko masa result ɗinta ya gani,haka Dad ɗinsa duka takardunsa duk da ba'a Nigeria yayi karatu ba da first class ya fita,murmushi ya ɗan yi kaɗan ya ɗago suka haɗa ido da Dad,Dad yayi murmushi shima yace "so everything is fine?" Wazeer ya gyaɗa kansa yace "hundred percent sure" Dad yayi murmushi tare da dafa kafaɗar ɗan nasa yace "so! Let's go kaga wani abu" Wazeer yace "again?" Dad yace "yeah! Let's go" ya kama hannunsa tare da miƙar da shi tsaye suka fita,wani office dake opposite da nasa yasa key ya buɗe,lafiyayyen office ne iya ganinka da baida bambanci da na Dad,an zuba komai ciki sai dai chairs da komai a rufe yake da leda kamar na sauran guraren da suka je,suna zuwa gaban table ɗin Dad yace "ka san ina ne nan?" Wazeer yai shiru bai ce komai ba sai dai kamar yana tunani,Dad yace "wannan shi ne office na marketing manager ɗin mu,nan is ur office,kai ne me alhakin tsara yanda za'ayi distribution na medicines ɗinmu a Nigeria zuwa maƙotan ƙasashe.. So congratulations Son,Allah ya bamu sa'a.."

              #Za ku karanta amma ɗan like ɗinma baza ku yi min ba sai na roƙa? Fisabilillahi kuna kyautatawa kuwa? That's why fa har yanzu muke a nan,ko da dai ace ba ni da lafiya,amma hakan zai ƙwarara min guiwa na daure nai muku update akan lokaci..😪


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Continue Reading

You'll Also Like

1.4K 4 19
You are a boy that gets betrayed by your team. Cause You can't use your sacred gear and they try to kill you. But you get reincarnated as a devil. To...
69.6K 11.3K 74
~BOOK 3 IN THE DESIRES SERIES~ STARTED. ON 20-JANUARY-2021 FINISHED. ON 15-OCTOBER-2021 #1 in mothers. On. 7-08-2021 #1 in introvert...
3.1K 77 23
An innocent love story between a village girl and the crown prince. ~~~ Blair Wettin, a village girl, finds her life turned upside down when she is...
BETRAYAL By Uniy

Mystery / Thriller

6.2K 264 28
Have you ever had someone you loved more than anything betray you? Inseparable, triplets from different mothers, that's what they were. They grew up...