AUREN WUCIN GADI

By zahraaliabdullahi5

19.6K 1.7K 78

labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
68
67
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
92
91
94
93
95
96
97
98
99
END

80

179 25 2
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

STORY ND WRITTEN
    ZAHRA ALI ABDULLAHI

____________________
✨ *GORGEOUS WRITTERS FORUM* ✨

    ✨G.W.F✨

*GORGEOUS,INTELLIGENT,AND EXPERT WRITERS,WE THE BEST AMONG THE REST.*
__________________

CHAPTER 80

  A corridor ya cimmata tare da mummyn ta hajia mariya da ita ma kaman wacce aka mitsina tafito tana kallon mummyn nata ta faɗa jikin ta ta fashe mata da kuka mai ban tausayi cikin kukan take cewa"mummy kema kin yarda da narasa Ahmad kenan ki faɗawa daddy shine wanda ya ƙwaitamun da auren sa tun bansan shi ba shine wanda ya koyamun yanda zan so shi yakuma alkawarta mun da samun sa matsayin mijin aure,amma ya kasa cikamun alƙawarin,bayan ni ba abunda yanemi nayi masa wanda banyi masa ba da karfina da harda jikina dan kawai nacika masa burin sa nason mallakan abun da zuciyar sa ta ƙwaɗaitu dashi to ni mai yasa ba ze cikan wannan alƙawarin ba.

Bayan ni ba abun da yataɓa sani wanda ban aikata masa ba,daddy ka rubuta ka ajiye idan nasa kowa ze rasa.

"A'a Basma karki sake cewa kin rasa ni nine nan wanda ze nema maki abunda ranki keso koda a ƙarƙashin ƙasa yake,sai kuma ya sassauta murya yace koda zan rasa tawa rayuwar dake ki rayuwa yana kaiwa karshe ya fita waje cikin sauri shi kaɗai yasan abunda yakeji a ransa.

"Yau naga ikon Allah ni Tani ta Malam Tanko Gwaggo da take tsaye tun fitowar Hajia Mariya tana sauraron duka abunda suke magana ta cigaba da tafa hannu tace wai Mariya me kike ɓoye manane ni?

Eh ko kina da wasu waƴan da suka fimu ne?
Ina Usmanu?tunda muka zo nake ta baza ido in ganshi amma bashi ba labarin sa,sake tsuke fuska tayi irin ba wasan nan da Gwaggo Tani irin Matan nan ne masu zafi da masifar tsiya da kuma yawan mita idan kayi lefi sai ta kusan yini tana maimata magana dan haka kowa shakkarta yake.

Yayace gun Mahaifin su koda Iyayen nasu suka amsa kiran Allah dukkan su dan gini ne ya rushe da su cikin damuna ana tsaƙa da ruwa ita ta karɓi rikon su basu taɓa kukan maraicin Iyayen nasu ba,ta tsaya musu tsayin daka basu taɓa neman wani abu sun rasa ba.

Haka suka rayu cikin rufin asiri basu taba neman wani abu wanda takasa yi musu shi ba,ta aurad da Hajjo ga wani attajirin mai kuɗin sannan kuma ta aurad da ita Mariya wa Alh Sunusi tun lokacin yana ɗan buga bugan sa daga baya kuma ya haɗu da wani uban gida ɗan jarida yana masa driver sannan suka zo suka fara harkar kasuwanci da uban gidan kafin shima ya amsa kiran Ubangiji Allah.rasa me zata cewa Gwaggo Tani sai kawai ita ma ta fashe da kuka saboda susa mata inda yake mata ƙaiƙayi da Gwaggon tayi wato Usman dan tunda yasaka kafa yabar gidan da sunan fita waje karatu bata sake jin muryan ko mai kama dashi ba.

*****
Aisha na shiga falon ta ga file ɗin a inda yace mata ya ajiye ta dauka har zata fita ta tuna da koran ta da Hajia da ƴarta sukai sai kawai ta koma ta dauki hajibi da tayi salla dashi tasaka tafito yana nan tsaye a inda ta barshi saide yanzu Hajiyar nan da taji ya kira da suna Mami tsaye take sun saka shi gaba da ɗiyar nan tata suna magana duk bata ji mai suke faɗa masa ba,haka kawai taji ta tsane su batason sake zama kusa dasu duk da be fito ya faɗa mata wace alaqa ne ke tsakanin sa da sudin ba.

Tun kafin ta ƙasara isowa   inda suke ya kafeta da ido yana kallon yanayin takunta cikin tsari kaman da gaiya take takawan,zagawa yayi ta bayan su ya isa gareta yana kai hannu ya karɓi file ɗin tare da saƙale hannun ta a nasa hannun ba tare daya kalli fuskar ta ba yashiga ta kowa a hankali dole ta bisa tunda itama din tanason barin gidan dan batasan idan tabari ya tafi dame za su zo mata ba,gashi ba sanin gari tayi ba balle tace zata gudu ta komawar ta inda tafito.

Suna gaf da giftasu Mami ta kalle hannun su dake sarƙafe dana juna tana yatsune fuska tace"kaji mun wani sabon tashanci anan yanzu Ahmad ko kunyar ido na ba kayi zaka riƙe hannun ta haka,ai ko mutuwa tana kunyar ido a kan wannan abar kake koƙarin wulakanta ƴar uwarka itadin wacece a wajen ka?

"Matar sace taji an amsa mata ba sai ta wahal da kanta wajen juya ganin mai maganan ba tasan murya Sajid ne da ƙarasowar kenan ya bata amsa,da wani irin speed Fauza ta juya tana kallon Yayan nata idanun ta kaman za su faɗo ƙirjita na tsanan ta bugu,hawaye datake riƙewa tun sanda ya riƙe hannun Aishan suka samu daman gangarowa saman fuskan ta toshe bakin tayi da hannu da ƙwasa da gudu tayi ciki dan batason ta bada kanta gaban wannan ƙanƙanuwar yarinyar ta ta raina ta bazata taɓa give up a kansa ba sai tasame shi matsayin miji koda na wucin gadine saita amsa sunan ta matsayin matar shi.

Mami ma bata ƙara tsayuwa ta saurari tsoki burutsun Sajid ɗin ba ta rufa mata baya,kallon Sajid ɗin yayi yana langwabar da kansa gefe alaman why.

Idonsa ya lumshe yana budewa sake hannun nata yayi yace"ki gaisa da ɗan uwana"ƙasa tayi da kanta cikin sanyin murya tace"ina kwana

"Lafiya lau amaryar mu yafaɗa yana sakin murmushi idan ya tuna yanda Ahmad yatsani kula ƴan mata musamman masu karancin shekaru dan a ganin sa nemawa kai raini ne amma sai gashi ya bige da auren yarinya ƙarama ƴar shilla da bazata wuce sha bakwai zuwa sha takwas ba,idan an ƙiyasta.

"Bafa nason murmushin gulman nan yafaɗa yana kame kans, sake faɗaɗa murmushin sa yayi yana riƙe haɓa yace"ya da tsarguwa haka Malam daga nayi murmushi?ya faɗa yana ƙaramar dariya.

Kwafa Ahmad din yayi yana cewa da Aisha"muje ko.
"Ina kuma zakaje da ita?Sajid ya tambaya da mamaki.

Shiru Ahmad din yamasa yasan kuma ba zece komai ba,kuma koda bece ɗin ba ya zargi wani abu daga yanayin Mamin sa da ƙanwar tashi,ko yanzu fito wanda yayi ya fitone saboda Sajida matar sa tafito da gaida Mamin sa shine taga sun tasa Aisha a gaba suna zagi takoma ta faɗa masa dan batasan da zuwan Aishan ba,haka shima Sajid ɗin dan Ahmad bece masa yana tare da ita ba jiyan.

Shine fa yafito dan ya gani yakuwa ganin dan be taɓa tsammanin hakan ba,ko sanda ɗan jaridan nan yamasa tambaya ranan partyn Basma daya je da ita,amsar Abokiyar sa da yace yatsaya masa a rai harya kasa hakura saida yakira khalid a waya tunda shi kullum suna tare kuma bugu da kari tare  ya gansu a videon party shine ma yake sanar masa da Matar sace amma shi Ahmad be ɗauki abun wani serious ba dan cewa yake Auren sa da ita na wucin gadine da zaran yasami ya shawo kan Ammin sa ze rabu da itane.

Yana gama tunani sai yace"Abokiya ce ko?
To nagade tayi kankanta dayawa balle nace girl fried dinka ce,sannan kuma...koda yake ai kaima cewa ɗan jaridan can kayi ze iya...mtsss tsaki da Ahmad din yayi yasashi yin shiru yana kuma tsuke fuska yace"to ai sai muje ciki ka barta da Sajida tunda aiki zaka ina ganin hakan zefi.

Yaji dadin wannan shawara ta Sajid dan dama tunani yake inda ze barta idan sun fitan,amince masa yayi ba tare da tunanin komai ba dan yasan Sajida bata da matsala tana kuma da kirki bugu da kari bata da rawan kai ko yawan magana.

"To ai saika wuce mutafi Malam yace da shi yana yin gaba rike da hannun Aisha cikin nasa hannun,falone ma daidaice kaman wanda suka sauka banbanci sa nasu kayan cikin da sallama suka shiga tana tsaye a falon da alama tsayuwan jiran zuwan mijin nata take dan taji wacece wacce Fauza tasa gaba tana surfa ruwan masifa haka?

Ganin dawowar sa yasa ta sauke ajir zuciya ta nufosa da nufin ta tambaya sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon Aishan dan ta ganeta a videon partyn saboda yanda videon yayi shura a media ake kuma tabka muhawara a kai masamman inda ɗan jaridan nan yayi masa tambaya.

Ai batasan sanda bakin ta yafurta Abokiya ba.

Itade Aisha sai binta da tayi da ido dan batasan abunda suke magana kai ba,dan bata da waya balle taga hiran da yayi ranan wanda Suhail ya bata kuma ta ajiye ta bataso ta kunna yakira ta dan batasan abunda zatace dashi ba na gami da auren da aka lakaɓamata jira take wa'adin sa yacika ta rabu da raƙau.

Sai kuma saurin daidaita kanta ganin idon Ahmad ta fara cewa"lale marhabin da mutane Kano ku shigo mana kun tsaya,

Shigowa sukayi suka zazzauna a falo ta gabatar musu da breakfast black tea kaɗai Ahmad yasha shima din kaɗan yasha yamusu sallama ya ɗankai kallon kan Aisha da itama shiɗin take kallo ta marairaice masa kaman zatayi kuka.

Ko kunya babu ya riko hannun ta cikin yin ƙasa da murya yace ki kula da kanki kada kikoma can ɓangaren harsai na dawo ok,kanta kawai ta jinjina masa ya fita yana ɗaga mata hannu.

Bayan Ahmad ya fita shima Sajid fita yayi a bayan sa saida ya fita sannan Sajida ta haɗo musu breakfast ta kawo musu nan falo tana jan ta da hira tun Aisha na na nokewa harde tasake sukai kari tare suka ƙwashe komai suka gyara wajen tare suka shiga kitche Sajid na wanke wanke ita kuma Aisha na tayata da ƴan goge goge sosai Sajida taji daɗin yanda Aisha ta sake da ita kuma ta yaba da hankalin ta sosai ganin bata da son jiki kaman na wasu ƴan matan mu na yanzu,suna gamawa suka dawo falo da zama nan Sajida ta kawo mata Album ɗin Auren ta suka shiga kallon hotona.

Ahmad koda ya fita a gidan be zarce ko ina ba sai office dinsu inda yasamu tarɓa na musamman wajen tsoffin Abokan aikin su dasukai aiki tare dashi a baya dan sunajin daɗi aiki dashi.

Office ɗin shugaban su ya wuce a nan yake gabatar masa da ƙudurin sa nason komawa aiki amma yanason komai ya zamana cikin sirri harsai ya cimma abunda yake nema.

Ajiyar zuciya shugaban nasu ya sauke bayan ya gama sauraron duka bayanin da yake masa yace"Ahmad banƙi ta taka ba,amma inason kasan cewa waƴan da kake son tunkara mutane su masu hatsarin gaske sannan suna da manya a bayan su.

Dan murmushi Ahmad yasaki yana mai gyara zaman sa ya fuskanci sa da kyau yace"Oga inaso kasan wani abu guda ɗaya barin irin waƴan nan mutanen suna yawo a doron ƙasa musibane cikin al'umma idan ka manta bari natuna sheka sanadin su muka rasa jajirtattun yaran mu shekarun baya,Iyayensu sun rasasu sannan matayen yaransu sun zama marayu haka zalika wasu dayawa suna rasa yaransu ta sanadin su faɗamun,idan bamu tashi mun yaƙesu ba haka zasu ringa bi suna mana dauki ɗaiɗai ayi shiru a barsu suna gurɓata mana matasa ta hanya sayar musa da kwaya suna sha.

Oga yanzu fa shaye shayen nan yazama kaman adone dan hatta mata ba barsu a baya ba,inason kawo karshen koma wani taƙadari cikin ƙasar nan tamu"taya kenan?

"Hmmm Oga kana manta wanene A-B idan yasaka abu a gaba baya juya masa baya harsai yaga karshen sa GAGARA BADAU shine target ɗina yanzu inason a haɗamun term amma cikin sirri banda sayar masa da bayane idan hakan ta faru..sai kuma yayi shiru sorry to say.

Miƙewa yayi ya fita ba tare da yajira amsa gun Ogan nasu ba,shi kansa Ogan ajiyar zuciya ya sauke bayan fitan Ahmad din a fili ya furta"bazaka taɓa canzawa ba.



ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

9.5M 627K 75
An Arranged Marriage Story. #1 Hot (17-11-23) #1 Happyending (17-11-23) #2 Shy (13-11-23) #3 Cold hearted (27- 10- 23) POWER!!!!! That's what he alwa...
252K 1.1K 37
Warning - Extremely erotic and sexual. People below 18 might find it disturbing. Suggestion to my readers - Visualize everything! Description - I am...
184K 14.5K 22
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
195K 38.9K 57
Becca Belfort i Haze Connors, choć przez swoich znajomych zmuszani do spędzania razem czasu całą paczką, od dawna się nie znoszą. Dogryzają sobie prz...