WAZEER!

By REAL-SMASHER

3.2K 338 50

...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this... More

THRILLER
Mysha!
Divorce
Force play
New decision
Dumb out
Hoor
Interpolated
Decision maker
Guilt-ridden
Camp
Vie
Overlook
Rivalrous
Envious
Power of love
Mission
Mislike
Affinity
Envious 2
Beseech
Inexplicable
Strangerlike
Safwah
Adviceful
Thought pattern
Proposalist
Her wish!
Wedding bell!
Break away!
Chapter 2:Thriller

Wedding march

93 9 0
By REAL-SMASHER

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

        _Follow my account on arewabooks @Realsmasher or https://www.arewabooks.com/u/realsmasher.._


                               11

#Weeding march

                Wani matashin soja da ya ɗan sunkoyo yana kallon Mlm Mu'azu driver bayan ya sauke glass yace "assalamu alaikum" driver ya amsa yana faɗin "Oga barka da aiki" sojan da gaban rigarsa aka rubuta A.Y Jega,yana ɗan leƙa back seat da yaga alamar mutum yace "yawwa! Yallaɓai ina zuwa ne? Gurin wa kuka zo?" Mlm Mu'azu yace "Oga mun kawo yaronmu ne,daga emirate muke.. Muna neman Jega,ance idan mun zo mu nemeshi" Jega yace "ok! Bismillah ku shiga ciki,nine Jega,barka da zuwa" daga inda yake yai magana aka buɗe musu get suka shiga ciki shi kuma ya biyo su a ƙafa,babban guri ne iya ganinka dake ɗauke da ɗakunan kwana,ga Corpers nan da suka zo tun jiya,wasu kuma sun kwana biyu saboda nisan tafiyar da sukai daga jahohinsu zuwa Kano,wasu kuma yau suka iso kamar dai Wazeer,Mlm Mu'azu na yin parking,fadawa suka sauko aka buɗe masa mota,Wazeer da yai nisa a duniyar tunani ya ɗago kansa kafin ya sauko yana kallon yanda mutane ke shigowa da kaya niƙi²,kamar wanda suke shirin barin gari,ya taɓe baki a hankali tare da gyara tsaiwarsa jikin mota,fuskar nan nasa a haɗe babu alamar dake nuna ya san wani abu dariya,Jega ya iso gurin da sallama,Mlm Mu'azu na kallonsa yace "Oga yanzu mene ne abun yi na farko?" Jega na kallon yanda Wazeer yai kicin² yace "za'a kai kayan da akazo da shi Police post.. His luggage would be checked,don tabbatar da bai zo da wani abu da ba'a yarda a shigo da shi camp ba,zai rubuta sunansa a can,za'a ba shi number that is very important during the registration period.." Yana kallon Wazeer yace "take a good care my friend,lokacin da kake shigar da number do not misplace it" Mlm Mu'azu yace "toh! Lallai² sai shi yaron ne zai je,ko kuwa wani zai iya zuwa a madadinsa?" Jega yace "no! Shi zai je,amma kada ku damu i will be there,zan kula da duk abunda zai yi in sha Allah" Mlm Mu'azu yace "toh babu laifi,yanzu za mu jira a nan dai kenan har ku fito ko?" Jega yace "ehh! Ku jira ya kammala registration,bari muje kada mu ɓata lokaci a nan akwai mutane" Jega ya kalli Wazeer dake sanye da mask yace "let's go friend" Mlm Mu'azu ya kalleshi yace "Wazeer ka bishi kuje,zai wuce maka kai komai cikin sauƙi" for the first time Wazeer ya ɗaga kyawawan idanunsa ya kalli Jega,ba wani babba bane ya yi nisan duniya shekarunsa su kai 30,babu laifi yana da ɗan haske amma baza ka kirashi fari ba,cike da izza ya ɗan motsa ƙafafuwansa,kafin suka jera suna tafiya Jega na yi masa magana yana sanar da shi abubuwa masu muhimmanci da za su taimakesa a zaman da zai cikin Camp na kwanaki 21,cikin maganganunsa ya fahimci 12 tips da ya faɗa masa sosai,kuma ya naƙalcesu a ransa duk da bai fito ya nuna ya gane kalma ɗaya cikin abunda yake cewa ba,har suka isa Police post,ya rubuta sunansa tare da karɓar number ɗinsa,Jega yai musu bayanin daga inda yake,jin daga masarauta ya fito yasa ba'a ma nemi kayanshi ba sai dai an tura wanda za su yi checking,yana gamawa da nan suka je accomodation,nan yaga yanda corpers ke bin layi mata da maza babu bambanci,basu tsaya ba Jega ya wuce da shi ciki,bayan ya rubuta suna tare da nuna temporary number da aka bashi a Police post,akai directing ɗinsa ɗakin da zai karɓi katifa,Jega na kallonsa da murmushi a fuskarsa yace "u shouldn't expect comfort a nan kamar dai kana gida,za kaga abubuwa da yawa da baka saba da su ba" Wazeer ya ɗan karkata kansa ya kalleshi,bai dai ce komai ba amma underneath yana tunani da tambayar kansa "me yasa haka?" Sanda suka shiga ɗakin da katifun suke Jega yace "bismillah" kallon mattress ɗin ya dunga yi,a fili ya furta "what's this?" Jega ya fashe da wata dariya yace "don't worry My G,i'm sure they are up to 20 yrs old..They are just an inch thick" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa,Jega ya wuce ya ɗan bincika ya samo masa wata da tafi sauran kumari,shi dai yana tsaye ya kasa motsi,kallon ikon Allah kawai yake yana tunanin yanda zai iya kwanciya akan wannan abun da marbarsa da kwanciya a ƙasa kaɗan ne,ya ga alama katifun gurin za su iya yin shekarun da Jega ya faɗa,shi ya ɗaukar masa suka fita zuwa ɗakin da zai zauna har zuwa sanda zai gama 3 weeks ɗinsa,daga nan suka je yayii registration,it tooks him half of an hour gaba ɗaya,suka je last phase wato kit collection and platoon registration,ya karɓi kayan NYSC ɗinsa,a nan ma Jega yake sanar masa,idan ya duba sun yi masa yawa ko kaɗan zai iya samun wani suyi canji,if kuma he's lucky zai iya samun komai yai masa,luckily takalmi dai yai masa dai² size ɗinsa ya samu,amma kayan kallo ɗaya yai musu ya san baza su shiga jikinsa ba,bai dai ce komai ba saboda Dad yasa an masa wasu,kayan da suke cikin kit ɗin Khaki ne na NYSC,wando da jaket+belts,farar t-shirts 2,farin guntun wando 2 da safa guda 2,sai rigar NYSC,sai wasu ƙananan littattafai kamar Camp schedule,the NYSC anthem,dokoki da ka'idoji (rules and regulations),etc. Bayan ya gama duk wasu abubuwa masu muhimmanci,da taimakon Jega har kayansa duka ya kai ɗaki,after then su Mlm Mu'azu sukai masa sallama suka juya gida,kasancewar shi ne first person da ya fara shiga ɗakin,yasa basu dawo ba suka dunga zagaye cikin camp yana nuna masa gurare yana kuma yi masa bayani "this camp ground is where the 3 weeks NYSC Orientation Course takes place.. It involves physical drills,lectures and training,and social activities intended to foster interactions among Corpers.." Yana sake nuna masa can wani guri daga nesa da sak bai da maraba da kasuwa yace "there is the large market operated by the locals popularly called Mami Market,a nan all camp needs are sold including food and drinks.." Wazeer ya gyaɗa kanshi,yana ci gaba da sauraron surutun da Jega ke masa,sai da suka gama zagayawa sannan Jega yace "idan kana buƙatar wani abu kuma da bamu da shi a nan sai ka neme ni" Wazeer ya sake gyaɗa masa kai,Jega ya bashi wayarshi yace "can we be friends?" Wazeer ya ɗan gyara tsaiwarsa sai kuma ya buɗe ido ya gyaɗa masa kai,za ka rantse ba ya magana,ko kuma dai ya fito cikin halittun reptile ne,musamman ƙadangare saboda ƙaunarsa da son gyaɗa kai,ba komai yasa ya amince zai yi abota da Jega ba sai saboda kirkin da yayi masa,da kuma amfanin da zai masa nan gaba a zaman da zai yi,sukai exchanging digits sannan suka rabu Wazeer ya wuce ɗakinsu,yana shiga babu jimawa wani sabon corper ya shigo,a hankali ya kalleshi yai masa sallama,ganin ya samu abokin zama kasancewar da shi kaɗai ne a ɗakin,guy ɗin duka bazai wuce sa'an sa ba ko shi ya ɗan girmeshi,fuskarsa ma'abociyar fara'a a sake yai masa murmushi yace "i'm Abdul-Waheed Ja'afar,from Kaduna State" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa yace "Aliyu.. Nice meeting u Waheed" Waheed yai murmushi yana buɗe idonsa yace "ohh! Kamar ka san sunan da ake kirana a gida?" Wazeer ya gyaɗa kansa,ba tare da ya sake cewa komai ba ya zauna gefen bunk ɗinsa yana ɗauko ledar gurin Mimi na jiya,kallo ɗaya Waheed ya yiwa Wazeer ya fahimci bai da yawan magana kuma bai son a cikashi da surutu,a hankali yace "friend bari na gama shigo da kayana" ba tare da Wazeer ya ɗago ba yace "ok" daga haka Waheed ya fita ɗakin yai remaining shi kaɗai,here ya fito da all abubuwan dake cikin ledar,bedsheets ne masu kyau har guda biyu masu kyau da tsada,kowanne haɗe yake da duvet sai fine net,ya dunga kallon kayan yana jin zuciyarsa na shiga farin ciki,no one told him ya tafi da wani abu bedsheet da duvet,Dad kuma bai tambayeshi yaji ko yaje ya yi siyayyar da yace masa ba,kawai ya tura masa kuɗi shi kenan,ya ɗauki ɗaya daga ciki ya ajiye gefensa sannan ya mayar da other one cikin ledar,tashi yayi ya shimfiɗa bedsheet ɗin ya saka net,idan ba wai bai ji da kyau ba,a bayanin da Jega yayi masa ya sanar masa akwai sauro a garin,shi kuma bai shiryawa yaita fama da kansa ba,yana ƙoƙarin gyara duvet ɗin wani envelope ya faɗo daga ciki,sunkuyawa yayi ya ɗauka ya zauna a nutse ya shiga buɗewa,kuɗi ne ciki masu dama sababbi a miƙe cikin wrapper ɗinsu ƴan 1K,sai short note da Mimi ta haɗa a ciki,ya dunga juya kuɗin a hannunsa yana tunanin me yasa Mimi tasa masa kuɗi,bayan ta san bazai buƙacesu ba? Note ɗin data rubuta yabi da idanunsa _"i know everything about rayuwar camp Son,ba lallai ne Dad ya tsaya yai maka shirin da uwa mace za tai maka ba,na san za kace babu abunda za kayi da kuɗi,saboda mahaifinka ya wadata rayuwarka da komai,amma za ka buƙaci cash wani lokacin,shi yasa nai deciding saka maka ɗan abunda bai fi ƙarfina ba.. Take a good care of urself for me Son,sannan ka tsare kanka da bin al'adun da suka saɓawa addinin Musulunci.. I love u.."_ Wani sanyi yaji har ransa,yanzu ya fahimci dalilin Mimii na yi masa all abubuwan da tai masa,underneath ya furta "thank uuu Mom,i will always love and proud of u" daga haka ya ajiye kuɗin ya gama gyara kayansa,sannan ya ɗan kwanta saboda ya huta kafin lokacin sallah. Yana kwance yana kallon empty bunks,Waheed ya shigo da sallama ya amsa masa,tas yai parking kayansa kusa da na Wazeer,shi dai bai sake ce masa komai ba,har ya ɗora mattress ɗinsa up bunk ya gama gyarawa babu me cewa wani komai,suna nan su biyu kowa na kwance gadonsa mutane suka fara shigowa da kayansu yare daban²,kafin wani lokaci ɗakin ya cika da hayaniyar sababbin corpers,a hankali Wazeer ya kulle idanunsa saboda yanda surutunsu yake hawa masa kai,jijiyoyin kansa banda harbawa babu abunda suke,bai taɓa tsintar kansa a noisy guri irin nan ba,duk shi bai san wannan ƙaddara na bautar ƙasa ba,banda a Nigeria ko africa zai ce nema,shi dai bai san ana yin wani abu service ba,guraren zhuhur ana fara kiran sallah Waheed dake bunk ɗin sama ya leƙo yana kallon kamilalliyar fuskarsa yace "Aliyu!" He thought bacci yake shi yasa ya ɗan kirashi yanda zai ji,Wazeer ya buɗe idonsa da sukai mugun ja saboda masifaffen ciwon kai,Waheed ya sauko yana cewa "za ka fita masallaci ne?" Wazeer ya tashi ba tare da ya ce komai ba,slippers kawai yasa sai wayarsa da ya ɗauka suka jera tare suka fita zuwa masallaci,a can gurin alwala suka haɗu da Jega,bayan sun idar sun yi sallah,suna fitowa Jega yace "za ku iya cin abincin nan ko za'a nemo muku wani abun?" Wazeer ya ɗan kalli Waheed alamar yai magana,murmushi Waheed yayi yace "babu matsala Oga,za mu duba Mami market idan akwai abunda muke buƙata" Jega yace "ok! But don't call me Oga again,za ka iya kirana Jega as u can see it here" ya nuna jikin rigarsa,Waheed yace "ok! Thanks" za su tafi Wazeer ya ɗan tsaya yace "a ina zan samu medication na ciwon kai?" Jega yace "kanka na ciwo ne?" Wazeer da bai son magana yace "gurin nan is too noisy,i don't think zan iya zama har 3 weeks" Jega yai murmushi yace "don't worry My G,idan ka kwana biyu za ka saba,yanzu bari na samo maka maganin" Wazeer ya kalleshi kawai,sai dai bai ce komai ba,ba ya tunanin ko kwana 💯 zai yi zai saba,tunda ya taso tsayin shekarun da yayi a duniya,bai taɓa samun kansa a guri makamancin wannan ba,suna komawa ɗaki Waheed ya ciro musu babban pray mat ya shimfiɗa area ɗinsu sannan ya shiga fito musu da lafiyayyen abincin da ya taho da shi daga gida,kallo ɗaya za kai masa ka san ba daga gidan talakawa yake ba,yana kallon Wazeer dake matsa forehead ɗinsa yace "get down friend,mu ci abinci sai na duba maka drugs,i think na taho da medication saboda uzurin gaggawa" Wazeer ya ɗan buɗe idonsa ya kalleshi,Waheed yai masa murmushi kawai,yanda yake bai da surutu da hayaniya yasa Wazeer yaji zai iya zama da shi,sannan ko babu komai neighbor ɗinsa ne,a addinance ya san hakkin maƙotaka,shi yasa ya kasa ignoring ɗinsa,suna zaune Jega ya shigo da maganin a hannunsa,Wazeer ya karɓa yai masa godiya saboda yanda yake taimakonsa babu gajiyawa,zai tafi Waheed ya tsayar da shi su ci abinci,abunka da wanda ya jima rabonsa da abincin gida,haka ya zauna suka ci tare su 3,Wazeer ya ɗauko musu containers da Mimi tai masa chops da drinks,har da wani dambun naman da tai masa,suna gamawa Jega yace su huta kafin yamma yayi za su fita ground,sannan yai musu sallama ya tafi. Ana asar suka shirya suka fita,bayan an musu lectures da sauran duk abubuwan da Jega ya sanar masa da safe,ba su suka dawo ba sai guraren maghreeba,wanka da alwala kawai suka sake yi suka tafi sukai sallah,daga can basu dawo ba suja tsaya tare da Jega,Waheed da shi kawai suke hirarsu,suka duba abunda za su iya ci Wazeer ya biya,daga can kuma suka tafi sallar ishaa,sai a hanyarsu ta komawa ɗaki sannan ya samu ya kira Mimi da su Abba suka gaisa,ya sanar musu ya isa lafiya,duka sai tambayarsa suke baƙunta da kaɗaici,shi dai bai ce musu komai ba har sukai sallama ya kashe wayarsa.

*SAFWA*

      Kwana biyu kenan kusan kullum sai ta duba Damfo a WhatsApp,amma har sannan taga babu alamar ya ga message ɗinta,dole tasa ta yanke hukuncin kiransa,sai dai wayar nasa bai tafiya saboda tsohon number ɗinsa Baniynah ta turo mata,da yake da shi yake chat,a yanzu kam cike take da ɗokin ta san nawa ne kuɗin ɗinkinta ta biya ta huta,sauran kuma tayi uzurin gabanta tunda ta samu enough kuɗi. Kasancewar yau Monday tana school,kuma su Muniba ma ta san suna school ɗin,shi ya hana ta kiran Baniynah,amma duk dare yau idan ta koma gida za taje gidansu Muniba suyi maganar,duka kwanaki biyu na weekends basu haɗu ba,saboda bata dawo gida ba,ta shiga ranar Saturday gurinta,a tunaninta data ce mata za ta dawo ranar ta dawo ɗin,sai ta iske Khalidah kawai a gida,ita ta sanar mata Baniynah bata dawo ba tana can gidansu Muniba,shi yasa yau ta yanke hukuncin za taje gidansu. Daga school ko data gama lectures,sai data koma gida tai wanka ta shirya sannan ta sanar da Umma za taje gidan Commissioner,Umma tace "toh! Akan maganar ɗinkin naku ko?" Safwa tace "ehh! Amma ina ga za muje siyan takalmi da jaka daga can" Umma tace "toh! Shi kenan,nima kya duba min plat ɗan dai² haka,ki siyo min da ƴar jaka da zan yi fitar biki" Safwa dake kallon Umma tace "kai Umma gaskiya ki bari na gama nawa siyayyar,Allah yasa ma kuɗin su isheni nima,kike ba ni sautunki" Umma tace "toh shi kenan.. Ki sissiyo dai komai irin nasu,ko color ban yarda ku bambanta ba idan da hali" Safwa tace "ai dama nima bazan yarda suce ayi haka ba" Umma tace "sai kun dawo,maza ki tafi kada ku ɓata lokaci" Safwa tace "sai na dawo" Umma tace "Allah ya tsare" Safwa ta amsa da ameen. Daga gidansu babu nisa zuwa Commissioner road inda gidansu Muniba take,kasancewar duka cikin GRA ɗaya suke,amma duk da haka bata iya tafiya da ƙafa ba,sai data samu tricycle ta hau,tafiyar 5 minutes ya kawosu line,ta sauka tare da sallamar me napep sannan ta isa get ɗin gidan,ɗaya cikin police get keeper da suke zaune yana kallonta yace "Hjy! Gurin wa kika zo?" Safwa tai masa wani kallon ƙasƙanci tace "so kake kace baka gane ni ba?" Yace "sure" tace "toh gurin masu gidan nazo,daga gidan Eng. Ridwan nake" gyaɗa kansa Police ɗin yayi yace "ok! Ki jira a nan,sai an bada izinin ki shiga" Safwa ta kalleshi daga sama har ƙasa tace "ni ce zan jira a nan? Kamar yau na fara zuwa?" Yace "sure" Safwa ta dunga kallonsa ta kasa cewa komai,lokaci ɗaya ta ciro wayarta ta fara kiran Muniba,ring biyu wayar yayi ta ɗauka,Safwa da ranta ya gama ɓaci tace "hello!" Muniba tace "hey! Ya kike? Ya su Umma?" Safwa tace "ga ni get ɗinku get keeper ya hana ni shigowa" Muniba tace "a'ahh akan me zai hanaki shigowa? Bashi wayar" Safwa ta miƙa masa wayar tana aika masa kallon banza,ya karɓa yana kallonta ya kai wayar kunnensa,Muniba tace "hello! Ka barta ta shigo,she's my friend" yace "ok Hjy" daga haka ya miƙawa Safwa wayarta yace "za ki iya shiga" Safwa taja siririn tsaki ta wuce ta barshi a gurin,tana shiga compound sai ga Muniba ta fito,hango Safwa na shigowa yasa ta tsaya balcony har ta iso gurin,Muniba tace "sorry Babe! Basu taɓa ganin kin shigo a ƙafa bane,shi yasa suka tsayar dake" Safwa da ranta ke ɓace ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta gyaɗa kanta tace "maybe" Muniba tace "zo mu shiga.. Sannu da zuwa" Safwa tabi Muniba a baya zuwa ciki tana cewa "Mami fa?" Muniba tace "Mami bata dawo ba tana BUK,sai mu kawai a gidan" Safwa ta gyaɗa kanta,a parlour suka tarar da Baniynah kwance,ta ɗago ta kalli Safwa tai mata ɗan taƙaitaccen murmushi tace "hey Babe" Safwa tai mata murmushi also tace "how far? Ya skul?" Baniynah tace "fine.. Ya Umma da su Bilal?" Safwa tace "suna lafiya" ruwa da drink Muniba data tafi kitchen ta kawo mata,tana ɗan murmushi tace "sai kika ga mutuniyar shiru bata dawo ba" Safwa tace "wallahi shi yasa ai kika ganni na zo.. Dama akan maganar ɗinki ne da zuwanmu super market nazo naji ya ake ciki,na yiwa Damfo magana na ga he didn't respond" Baniynah tace "halan kin samu masu kauri?" Safwa tai wani murmushi tare da fari da idonta tace "ke dai ki bari kawai,na taka babban dami" Baniynah tace "Allah ƙawata?" Safwa tace "wallahi" Baniynah ta tashi zaune tace "anya bazan shiga jakarki ba kuwa Hjy ta?" Safwa tai dariya tace "shigo mana,ai baki da matsala" Baniynah tace "yeah! I see" Muniba dai na jinsu tana murmusawa,Safwa tace "yaushe za muje super market ɗin yanzu? Ya kamata asa date" Muniba tace "sai dai mu bari weekends,shi ne ranar da Mami take nan,and muma babu abunda muke yi" Safwa tace "alright! Allah ya kaimu" suka amsa da ameen,har Mami ta dawo daga aiki ta sameta,ba ita ta bar gidan ba sai dare,Mami tasa driver ya kaita gida.

*WAZEER*

        A hankali da daɗi da babu har ya fara sabawa da yanayin wahalar camp,safe da yamma kullum sai sun fita lectures da training,da dare kuma suna da gurin da suke zama shi da Waheed da Jega da ya zama makusancinsu,komai suke buƙata wanda babu shi cikin Mami market,zai fita cikin gari ya nemo musu,hayaniya ne dai har yanzu Wazeer ya kasa sabawa da shi,kullum cikin ciwon kai da rashin magana yake,a yini guda tas za ka ƙirga kalmomin da ya furta,abunka da wanda ya saba rayuwa cikin AC,zafin garin yasa yai wani irin duhu ya rame,duk da babu abunda suke bayan fita training kullum,wankin kayansu asu suke yi ba akwai masu yi musu,abinci ma basa cin na cikin camp,babu ruwansu da shiga sabgar kowa,idan ya wuce sallama ga Musulmi da gaisawa da sauran ƴan ɗakinsu lokacin da aka tashi da safe,basa ƙara zama ɗakin sai dare lokacin bacci,a haka kuma gara Waheed ya ɗan saba da mutane,Wazeer kam ba sawa ba hanawa,maza sex ɗinsa ma bai kulawa bare mata,kullum fuskarsa na cikin mask,in banda Waheed,Jega da ƴan ɗakinsu babu wanda ya isa yace maka ya san ai nahin kamanninsa,a haka sukai 1 week suka shiga second week,ba ƙaramin dauriya yayi ba ya kai zuciyarsa nesa yaƙi kiran kowa a gida ya sanar da halin da take ciki,duk kuwa da cewar ya mugun takura,cikin hukuncin Allah har suka shiga last week ɗinsu,ranar alhamis duk ya matsu ya bar gurin,a ranar ya gama shirinsa tas yai parking kayansa,haka Waheed ma ya kammale komai nasa,bayan sun yi exchanging address da alƙawarin ziyartar juna bayan sun koma gida,tun a daren suka gama clearance,ranar Friday suna tashi lectures dai² lokacin masjid suka fito da komai nasu shi da Waheed,a nan ya bada abunda zai bayar,luuggage ɗinsa kawai yai saura,Mlm Mu'azu na zuwa ɗaukansa akasa kayansu a mota,sukai sallama da Jega yai masa alkhairi,cike da kewar juna suka shiga mota sai Kano,ko da suka shigo gari sai da suka fara sauke Waheed a motor park zai wuce Kaduna a ranar sannan suka wuce Tudun wuzirci,Mlm Mu'azu na yin parking ƙofar gidan Wazirin Kano ya sauko ya wuce cikin gida,ɓangaren Daada ya fara shiga da sallama,Daada ta ɗago tana kallonsa,lokaci ɗaya ta saki murmushi tana faɗin "oyoyo Waziri me jiran gado" ya ɗan saki fuskarsa shi ba dariya ba kuma bai haɗe ta yanda ya saba ba,ya zauna kusa da ƙafarta yana cire mask ɗin fuskarsa yace "Daada barka da rana?" Daada dake ta kallonsa da mamaki tace "barka dai Zainul-aabideen,ya hanya?" Yace "alhmdllh" tace "ince dai ka yi cuta a can garin ko?" Ya kalleta kaɗan kamar bazai magana ba,sai kuma yace "me kika gani?" Tace "na ga ka rame ka yi duhu" yai ɗan ajiyar zuciya lokaci ɗaya ya tashi yana faɗin "Dad ya dawo?" Daada tace "ehh ya dawo tun wancan satin" Wazeer ya kalleta sai kuma yace "ok! Bari naje na watsa ruwa" Daada tace "toh! Amma baka ci komai ba,baza ka bar wankan ka yi daga baya ba?" Ya girgiza kansa yace "um'um!" Daada tace "toh shi kenan,a fito lafiya" ya amsa tare da jan luggage ɗinsa da aka shigo masa da shi ya wuce part ɗinsu.

*MUNIBA*

      Sosai suke cikin hidima,tunda aka shigo satin biki basu da zama,sun yi rabon IV da komai sun gama,ranar Wednesday sukai henna day na iya ƴan mata,da yammacin ranar kuma akai football tsakanin family'n biyu,yau Friday shi ne za'ayi mocktail (non-alcoholic party),Safwa an yi kane² kai baza kace bata da alaƙa da family'n Mijinyawa ba,kayan duk da su Baniynah suke shirin sawa a bikin ɗai² ne wanda bata yi ba,Dinner ma har biyu ake shirin za'ayi,ɗaya Family'n amarya suka shirya shi,ɗayan kuma na ɓangaren ango ne,duka kuma sai after Nikah (ɗaurin aure),card ma duka har yau ba'a kawo shi ba sai zuwa dare. Duk sun yi make-up light saboda event ɗin ranar,kaga Baniynah da Muniba sai ka so ka sake kallonsu,lallen nan jaa baki ya hau farin fatarsu ya ƙawatasa,haka suka je mocktail ɗin nan da aka yisa cikin tsari suka dawo,Safwa anga maza iyayi ya ƙaru,sai guraren 10pm sannan suka dawo gida,har sun shiga za su kwanta bayan sun yi removing make-up sun yi wanka,sai ga me kawo card yazo,Mama ta kira Muniba a waya tace su karɓa su ajiye can baza ta iya da mutane ba idan suka gani,za su tada zancen cewa a basu tun daren,zuwa da safe sai su kawo masu,Muniba tasa hijab ita da Baniynah suka fita,basu daɗe ba suka shigo da babbar leda a hannunsu,Safwa na kallon Baniynah dake cewa "Yaa Khalidah gashi mun amso,ya za'ayi da shi?" Khalidah dake kwance kan gado tace "a'a ku bari zuwa da safe sai ku tambayi su Mama,ni bazan karɓi card ba" ta yi haka ne saboda ba'a gida suke iya su kaɗai ba,sun so iya su ƴan matan suyi zamansu gidansu Muniba har a gama bikin,Umma tai tsagal tace suzo nan gidanta ba sai sun yi nisa da gida ba,kuma can gidan ma akwai mutane family'nsu,da son gwaninta a tafi ana cewa ai tana da kirki,yasa ta bar musu ɗakinta nan suke komai tunda aka fara hidima,kiran da akai wa Safwa a waya yasa ta tashi ta fita amsawa,fuskar Khalidah babu walwala sosai ta kalli Muniba tace "guda nawa ne card ɗin?" Muniba tace "a'a bamu sani ba,gasu dai da yawa" Khalidah tace "toh! Ku cire mana namu da nasu Yaa Khalifa,sai ku kaima su Mama nasu kawai" Muniba tace "to kuma sai mu ɗiba? Baza mu bari har zuwa safiya ba?" Khalidah ta kalli Baniynah ganin Safwa ta dawo,tai mata alamar su cire ɗin Baniynah ta gyaɗa mata kai,bayan sun ajiye suka fara hira,a nan aka fara lissafi kowa na faɗan adadin yanda take so,Safwa kam kusan 20 card tace tana so,Baniynah dai sai mamakin abunda za tayi da cards da yawa haka take,sai dai bata ce komai ba tai shiru,ko ita guda 10 kawai ta tsaya,suma duka friends ɗinsu ne na school,sai na cikin unguwa da akayi islamiyya tare,Safwa tace ai badon² ba da an bani nawa tun yanzu na adana su,Muniba za tayi magana Khalidah ta rigata tace "ai kuwa sai ki jira zuwa safe,idan Mama sun cire nasu abunda ya rage mu kaca²la.." Safwa tace "Allah ya kaimu" underneath ta shiga lissafin mutanen da take son gayyata dinner,lokaci ɗaya tunanin *ALEY* yazo ranta,a duka mutanenta da take ji da,shi kaɗai ta sha'afa batai inviting bikin nan ba,kuma ya san da bikin tun kafin a kawo lefe,kwana biyun nan ta ga kamar yana cikin uzuri shi yasa bata cika yi masa magana ba,musamman kuma da aka shiga week ɗin nan,suma basu cika samun lokacin zama ba sai dare...


         #Me kuke zaton zai faru jama'a? Anya Wazeer dake jin izza,bai son noisy guri zai je gurin bikin nan? Ni dai na ce bazai zo ba,ku fa me kuka ce?


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

Continue Reading

You'll Also Like

431 54 19
The cycle of sahil-Gautami to Anirudh-Gautami to again Gautami-sahil to let's see who's next sooooo what's next? let's dig into this story with me...
43.5K 4.4K 31
So that's my second story 😊 thanks for supporting me 🙂 in my previous story i.e. will hate change into love💕and again I'm telling u plzz logic par...
49.9K 1.9K 23
Its from malishka 'imagination but in my story its happen for real.
216 37 23
BAP members in this story. Hope you enjoy. Story of Magic and Love, Betrayal and Pain.