ALMAJIRA ✔

By DielaIbrahim

1.1K 70 5

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She find... More

Prologue
1
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
17
AL'ADARMU
18
20
SOFIA

19

27 2 0
By DielaIbrahim

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


ALMAJIRA
PAGE 19

______________________________________

Ahmad karar wayar sa ya sashi yin shiru ran shi na daɗa dagule wa, ya duba wayar yaga still Mummy ce, ita in ta fara kiran waya shikenan ta dunga kenan, ita ce dama take ta kiran sa akan lafiya taga yayi kwana biyi bai dawo ba, sannan ta faɗa masa cewa idan har bai dawo yau ba to zai gansu a kaduna gobe, ko a ina suke zasu nemo sa, Dole ta sa yau zai kama hanyar Abuja da daddaren nan.

Ya ce,"Baffah Iyaye na suna son gani na, yan zun nan zan kama hanya, amma bayan kwana biyu zan dawo ko da kuwa an sallame ku zan same ku a gida...ya tsagaita. ya ɗaga kai yana min wani irin kallo alamar bai son tafiya amma babu yan da zai yi.

Bugun zuciya ta sai ya tsananta kasancewar jin Ahmad zai tafi ban san dalili ba amma sai na tsinci kai na da kunci, yana ta magana da Baffah kamar ɗa da uba sai kwantar musu da hankali yake yi, suma kuma naga suna jimamin tafiyar na sa.

Ya tashi tsaye ya kura min idanuwan sa duk da fara'ar fuskar shi amma sai da kunci ya bayyana, da kyar ya iya motsa bakin sa ya furta kalmomi kaɗan.

"Khadija ga Baffah da Anna ki kula da su kamar yadda kika saba tun kafin na shigo rayuwar ku"

Har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya min murmushi sannan ya ce,"Kimin alkawarin zaki kula min da kanki har na dawo"

Wallahi kunya ta hanani kallon sa wannan karan sai na ɓuya a bayan Anna ya gama kallon da yake min sannan ya wuce, ko amsa ban bashi ba.

Ranar kamar ɗaukewar ruwan sama ɗiɓ haka muka kwana shiru babu mai cewa kowa kala har muka wayi gari da safe.
Satin mu biyu a asibiti, muna ta walwala, Anna taji sauki ta murmure tayi haske, to kullin sai na haɗa mata shayi a kalla sau uku a rana, sa'annan ga breadi, kifin gwangwani, biscuit, cake da su chocolate, kayan shayi kam ba a magana saboda idan kuka gansu sai kun razana, ga maltina katan uku ya siya, da waɗan sh abubuwan da bamu san su ba, hatta kayan abinci dangin su shinkafa taliya, indomie, macaroni, da cous cous, manja, man gyaɗa da maggi duk ya siya da kan sa ya kai mana gida, zuwa nayi kawai naga kayan abinci a cikin ɗaki.

Baffah da Anna albarka kawai suke sanya mishi, Anna alhamdulillah ta samu lafiya kullin ni ke kwana da ita, Baffah na komawa gida shi da Sofia domin kuwa ita ce ganin sa, Sofia yarinya ce mara surutu da magana, amma tana yi da Baffah sosai take nuna masa hanya da zaran ya ɗaura ta saman kansa haka zasu hau napep su sauka suyi ta tafiya suna hira har suje gida.

Mun tashi da safe muna ta haramar haɗa kayyayakin mu domin an sallame mu, Anna ta ji sauki garau, sumul, muna zaune muna karya wa Anna na shan shayi ni kuma na gama ina ɗauraye kofuna a ban ɗakin cikin ward ɗin, ji nayi kawai an turo kofar shigowa da karfi, nayi sauri na fita ina cewa Anna lafiya karar miye naji haka?

Tsayawa nayi cak ganin mutane sanye cikin bakaken kaya sai matar nan ta ranar wacce tai min kama da Anna, gefen ta wani kyakkyawan saurayi ne matashi fari, siriri kuma dogo da alama ba wani shekaru yake da shi ba, ba zai wuce 26 27 ba, ya juya bayan sa hannayen sa sanye cikin aljihun wandon sa.

Matar ta tako har in da Anna take ta kama hannun Anna tana shu'umin murmushi.

Anna ji tayi an kama mata hannu a raza ne ta ke amma sai ta dake, sarai ta gane ko wacece amma sai tayi shiru dama tana gudun faruwar hakan shi yasa tun jiya ta so su koma gida gashi har ta kara ritsa su a asibitin.

Matar ta ce,"*SISTER ANNA* ta cigaba da cewa na san kin gane ni, to na zo gaishe ki ne"

Anna ta girgiza kai sannan ta ce,"Never, That's not what brought you here*LAILA* you think am a fool like you, no am not," I told you time without number that you are selfish *LAILA* I will not stop telling you, don't forget that Allah na tare da ni, kuma zaki ga sakayya" ta ɗaga hannun ta ta nuna Laila da yatsar ta tana cewa, "Maza ki faɗi abin da ya kawo ki, ki bar nan" Anna ta karashe maganar tana huci.

Tun da na haɗu da Anna ko ita ko Baffah ban taɓa ganin su cikin bacin rai haka ba, ban san ma tana da fushi ba, ban san cewa ta iya turanci sosai haka ba, turancin ma na ƴan america, tamkar ma daga kasar american ta fito, domin wasu maganar ma ba gane wa nake yi ba kawai iya waɗannan na ji kuma na fahim ta.

Hahhhhhhhhh Laila ta sheke da dariya sannan ta ce,"What's that? kika ce in faɗi abin da ya kawo ni, Hahhhhh daɗi na dake fa duk da na mai da ke nakasasshiya dake da makahon mijin ki, na lalata muku rayuwar ku, na mai da ku mabarata amma har yanzu ilimin ki na nan a tattare dake, kuma naga har yanzu ma da kuzarin ki tun da har kina da kwarin gwiwar mayar min da amsa, Uhmmmm never mind, tun da kince na faɗi abin da ke tafe dani to ya zanyi"

Laila ta ce,"Sageer wannan ita ce Anna, ka tambaye ni sunan waye a companies namu, to sunan ta ne kaf companies ɗin, kana yawan tambaya na wai bani da kowa ko?

Laila ta sake wani shu'umin murmushi sannan ta za ga ta gefen gadon Anna ta ɗan hau saman gadon ta sanya hannun ta ɗaya ta rungume Anna sannan ta ɗaga kai ta kalli saurayin ta ce,"Sageer juyo ka gan ta mana *She is my blood sister*"

Juyowa yayi da sauri yana cewa,"What !!!!!

"Ya ilahi!!!! abin da na furta kenan saboda ganin fuskar Ahmad sak sosai na ke mamakin shin me ya keyi da wannan matar kuma, sannan me yasa ta canja masa suna Sageer, duk ina ta tunani a zuciya na na kafe shi da idanu ban san lokacin da nace "Yaya Ahmad, Ka dawo ne"

Saurayin ya galla min harara kafin ya tsirtar da yawu yana cewa,"Mom let's get out of here please, this ward was boring, and i don't care to see your sister Mom, The only thing i know is, seriouly am gonna change that name that's it"

Ya karasa maganar ya na min harara wanda yasa hanjin ciki na kugi kiris ya rage na fara zawo tsabar tsoro irin nawa.

Anna ta ce,"Ohhh Allah ka shiryar damu zuwa ga hanya madaidai ciya, zuciyar uwar tamkar na ɗan, Laila kiji tsoran Allah wallahi akwai lahira"

"Dallah rufe ma mutane baki, ke kika san da wannan as far as ina da rai, Allah ya mallaka min komai a hannu na me zanyi da wata nasihar ki"

Ta shi tayi daga gefen Anna ta zauna saman wani fancy chair dake ajiye gaban gadon Anna, ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya, sannan ta cire bakin gilashin dake manne a fuskar ta kafin ta ce,"Anna duk wani moves ɗin ku a cikin garin kafuna na san da shi, na faɗa miki tun ba yau ba cewa duk abin da kuke yi a tamkar kuna gaba nane kuke aikata shi, don komai naku na sani,kun samo yara mata guda biyu suna zaune da ku, kuma baku iya kulawa da kanku ba ina ga kuma yara mata guda biyu, bullshits"
Ta faɗa tana kallo na haɗe da galla min harara sai naji hanjin cikin ya kuma kaɗawa jikina na kakkarwa tsoron ta ya bayyana a fili don har fitsari na kusan sakewa a wajan da gudu na koma ban ɗakin ina mai da numfashi, naji Anna na mayar mata da martani.

Anna ta ce,"Don't you dare disrespect my children they are my flesh" na wuce duk yadda kike tunani Laila, ki bar ganin kin raba ni da ɗa na ɗaya tilo, Allah ubangijin da ya halicce mu ya san da mu kuma ya san da abin da kike aikata wa"

Ina bayan gida karar zawo kawai kake ji phaaaatatttttaaaaaaphaaatatttaaattaa sai naji an ce , "Bull shit men, Mom what's that?"

Yana tambaya jin karar zawon, yasa ya toshe hanci ya fita a guje ba kakkautawa.

Ni dai na kasa fitowa ina ta faman aikin zawo ina jin su suna ta zage zage suna buga kofa naki buɗewa saboda na sa key, Kuka shaɓe shaɓe haka na rinka rusa wa ina tausayin kar su kashe Anna na bar ta ita kaɗai ga shi Baffah baya nan, hakanan na cigaba da rusa kukan, zazzakar muryar shi ita ta dawo dani daga zurfin tunanin da nake yi haka nan kuma na dakata da zawon da nake yi na tsabtace jiki na lokaci ɗaya na wanke fuska ta, na gyara jiki na sannan na buɗe kofar don na tabbatar ko shi ne da gaske.

Idanuwa na su kai min tozali da kyakkyawan halitta sanye cikin suit ash color ya matukar kara haske fuskar shi na ɗauke da gilashi ya murtuke fuska masifa rashin mutunci kawai yake musu iya san ran shi....zuciya ta fal farin ciki Yaya Ahmad ya dawo.

Da sauri na nufi wajan Anna na rungume ta ina cewa,"Anna yaya Ahmad ne ya shigo yan zunnan" sai naji Anna ta rankwashe ni tana cewa "Ja'ira masoraciya kawai, kin gama zawayin?

Murmushi nayi na ɗaga kai ina kallon Yaya Ahmad yana ta musu masifa akan su fita waje baya bukatar ganin ko ɗaya daga cikin su.

Na kai duba na ga dogon saurayin da suka shigo da Laila sai naga wani irin kama da suke yi da Ahmad, su kan su kallon kallo suke yi, shin ta yaya akayi suka yi kama da juna haka?

______________________________________

Thanks for reading my novel, Love you fan's

Continue Reading

You'll Also Like

2.7K 86 19
Wani numfashi yasaki mai ƙarfi agigice yajawota tafaɗo kanshi cikin karaji yace nashiga uku indo sa hannu kija zai fita idan kikayi haka . Kamo hannu...
286K 20.9K 25
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
Ice Cold By m

General Fiction

2.3M 86K 50
[boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feelings for so...
1.6M 141K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...