ALMAJIRA ✔

By DielaIbrahim

1.1K 70 5

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She find... More

Prologue
1
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
AL'ADARMU
18
19
20
SOFIA

17

44 4 0
By DielaIbrahim

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

LAST PAGE OF FREE PAGES

PAGE 17

______________________________________

Waye kuma *SAGEER*?

Ahmad ya bukaci tambaya jin cewa wai yana kama da Sageer, don yaji maganar ta na karshe daya fito daga bakin ta tace,

"Kai haba it's a lie wallahi ya a kayi kuma naga suna kama da Ɗana *SAGEER*

Kwata kwata bata san cewa maganar ta fito fili ba, ita kawai ta faɗa kogin tunani shin waye wannan da yake tare da Anna kuma mai Kama
da Mujaheed da Sageer kamar su ma ta bace da sageer kaman ƴan biyu, ko dai Mujaheed ɗin ne ma, ta cigaba da tunani a cikin zuciyar ta.

Da Ahmady zai ɗauki Anna ya canja  mata asibiti amma sai ya gwammaci gwara ya nuna musu rashin tsoro, ya kuma gwada masu shi waye, kuma 44 ɗin za ayi mata treatment, waya kawai ya ɗauka ya kira Daddy, jim kaɗan sai ga wasu jerin sojoji na gaban su babban likita ne sanye da kakin soja amma ya sanya labcoat a sama, suka iso inda su Ahmad suke tsaye.

Kafin na girga uku, ya faɗa yana takawa zuwa inda motar sa yake, yana pito irin asalin ɗan tashan nan, duk da sauran sojojin basu san ko shiwaye ba amma suna tsoron gwamnati taji abin da suka yi idan matar nan ta sheka to wallahi zasu fuskanci kalubale babba duk da Madam ɗin su tana kokarin biyan su kuma tana kare su akan dukkan wani matsalar da zata same su.

Matar nan ta jima tsaye tana kallon shi ta kasa aiwatar da komai, Ahmad ya ja tsaki kafin ya kalli jami'an dake wajan ya ce,"Dukkan ku idan na so yanzun nan za a kama ku a kulle ku a dark room, wallahi babu ruwa na da wai ku sojoji ne dukan tsiya zan muku matukar baku ɗauki matar nan kun kai ta ɗakin taimakon gaggawa ba"

A daidai lokacin Anna ta farka don dama ta fara bacci tun muna barau dikko, tiryan tiryan haka na zayyana mata abin da ya faru sai naji Anna na cewa "kayya kayya me yasa kuka kawo ni asibiti da kun bar ni a gida, Ɗan nan baka ji ba ina magana na ce "Ku mai da ni gida don Allah"

Amma ko kaɗan Ahmad baya sauraran Anna sai da ya gama sille su da faɗa tas ya razana su kafin ya fara
kirga ɗaya, ya kirga biyu....Bai ankara ba kawai sai ganin su yayi sun kawo gado sun ɗaiki Anna cak su ka kai ta A &E anan aka bata taimakon gaggawa, Ni dai ina biye da su Ahmad yana rike da Sofia ta ɗayan hannun sa kuma ya tamke mun hannu na muna zaune a gefe ɗaya na wani gado muna kallon Anna.

Ita ma Anna tunanin mu ta keyi ta hakika yau ita rana ta farko da wani ya kwatan mata ƴancin ta a wajan muguwar matar nan, tun bayan rasuwar mahaifin ta, ta girgiza kai tana tausayin Ahmad tabbas yau ya kira ma kan sa ruwa tun da ya tsokano ta yanzu tana cen tana wani sake saken mugun ta, amma bata son wani abu ya samu ɗan mutane shiyasa tun farko taso ya saurare ta, da ya maida ita gida amma ya ki ji...tana wannan tunanin ne aka tsira mata allurar bacci har baccin ya ɗauke ta.

Suka gama mata komai Ahmad ya biya hospital bill ɗin sannan muka jira muga ya saukin nata zai kasance saboda an mata allurar bacci tana ta shan bacci abin ta.

Bayan sallan la'asar sai Ahmad ya ce min naje in da Baffah yake na taho da shi, ya bamu kiɗin Napep.

Zan tafi ya rike min hannu ya kura min idanu yana min wani irin kallo ya kunshi ma'anoni da yawa, ya sassauta murya a hankali wan da bakin shi kaɗai ne yake motsi amma baka isa kace kaji abin da ya furta ba,

"Khadija please take care of your self for me" ya faɗa cike da tsananin shauki sai naji yar a zuciya ta kunya ta kama ni duk dama ban je boko ba, amma Anna na koya min a ƴan kwanakin da muka yi da ita, na sunkuyar da kai na kunya ta kama ni duk dama na sani bai fito ya furta min wata kalmar so ba, kuma nima ba wannan bane a gaba na yanzu, kawau dai na ji kunya ne saboda yana min wasu abubuwa wanda zuciya ta da gangar jiki na bata saba ɗaukar hakan ba.

Ban amsa mishi ba illa nai masa murmushin gefen kumatu wanda na saba da hakan kuma ni ban ma sanu ba ko idan nayi yana min kyau ni dai ina yi kawai...sai naga Ahmad ya wai ga ya kalli mutanen dake ɗakin majinyatan, ya ajiye Sofia saman gado ya mike tsaye ya sanya hannayen sa cikin aljihu ya ɗaure fuska kafin ya ce,"Biyo ni waje" ya faɗa kuma yayi gaba abin sa.

Bin shi nayi da kallo abin ya bani mamaki daga yin murmushi to ko baya son murmushin ne? ina ta tunani ina bin sa a baya har ya tsaya a wani waje mai ɗauke da kujerun na zama da bishiyoyi mutane kaɗan ne suke ta kai komo a wajan, garin tunani ina tafiya ashe ya tsaya ban sani ba kawai ya juyo kenan sai muka ci karo wanda ya sa har na kusan faɗuwa ta gefe yayi saurin sanya hannun sa ya tallabo ni kawai sai na faɗa faffaɗan kirjin sa nayi matashi da kirjin nasa ina jin saukar bugun zuciyar sa.

Tsahon wasu dakiku sai na ja da baya ina mai sunkuyar da kai na, alamar jin kunya gaba nayi da sauri don bana son ma nai masa masa saboda abin da ya faru.

"Khadija" cak na tsaya jin ya kira suna na amma na runtse idanuwa na bana son ko ido huɗu muyi da shi"

Ya ce,"Ki kula fa"

Sai naji sanyi a rai na wanda har na sauke ajiyar zuciya ina murmushi na cigaba da tafiya har nayi nisa yana wajan dana waiga sai naga yana wajan har na bace ma ganin sa.

______________________________________

"Hello!Hello!! Hello Sageer can you hear me?

"Yeah! Yeah Mom i can hear you well, how are you doing? aka amsa a cikin wayar.

Ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin tayi karfin halin cewa,"Kana London ɗinne?

"Yes but yanzu haka ina airport zan zo Nigeria, bana faɗa miki ba Mom" Sageer ya faɗa yana ɗan shagwaba kasancewar shi Mama's boy

Ta sake sauke wata ajiyar zuciyar kafin tace,"What about the company hope komai na tafiya da kyau"

"Yes Mom as i told you, trust your boy kamar yadda kika san kaf Nigeria babu sanannan Campanin furnitures da Campanin sai da turaruka signatures sama da *MISS ANNA CHERIE FURNITURES AND MORE* To haka zalika a nan London kaf *Kasar wales* babu Furnitures da perfume industry ɗin da ake siya in ba na Miss Anna ba,, Mom we are billionaires as you always know tun kafin ki haife ni and kin sani as usual muna da ma'aikata da suke kula da kowani ɓangare yadda ya kamata, And yes Mom zanzo ma akwai tambayar da nake son miki, da kuma wata shawara da nake son mu tattauna akai bari dai na karaso"

Mom tayi wani shu'umin murmushi mai kama da yawwa dama abin da nale son ji kenan, Sageer kenan yaro ɗaya tamkar dubu,

Ta ce,"Son Allah ya kawo mun kai lafiya kaji, ka kula mun da kan ka fa sosai"

"No problem Mom Allah ya amsa addu'ar ki, Thank you bye!!!!

Ya kashe wayar, tana zaune ne a falon ta, a babban sashin ta wanda yayi kama da sashin sarauniya tamkar dai gidan sarakai na zamani a cikin katafaren gidan ta dake kan titin Abubakar tafawa balewa way, Marafa estate Kaduna state.

______________________________________

Ina zuwa karkashin gadar kawo na haɗu da Baffah wannan mugun mabaracin wanda yake masa hassada sun kama sa suna ta bugun sa ko me ya musu ohooo kuma mutanen wajen suna gani amma sun rasa yadda za suyi su kwato Baffah.

Da sauri na kutsa kai ina hawaye ina kiran sunan Baffah, abu ɗaya na tuna Anna na cen asibiti mun gama da nata nan kuma ga Baffah garin nemo na sawa a baki yana ta shan duka babu gaira babu dalili, da kyar nai masa rumfa da babban hijabi na suka karasa dukan a kai na har suka fasa min baki jini na zuba amma ni ba wannan ne damuwa ta ba, damuwata su rabu da mu kawai.

Sai da suka yi mai isar su kafin suka sa kai suka kama hanyar su suka gudu, wani matashi ne naga ya kura ma Baffah idanu yazo wuce wa a mota, mu kuma muna ta gaban motar zamu wuce kamar a kunne na naji matashin ya kirawo suna *IBRAHIM*

Na wai ga don naga shin dawa yake ne, amma sai naga yana nuna Baffah, Baffah kam baya cikin hayyacin sa hakan yasa nayi gaba abi na ina tsaida  mai napep kafin mutumin ya karaso in da muke har mai napep ya ja mun tafi.

A kofar asibitin 44 muka sauka na taimaka wa Baffah muka shiga cen na hango wani fanfo a wajan na tsaya na ɗauraye masa fuskar sa da kafafuwan sa ya sha ruwan yana mai da numfashi ina ta mishi sannu, daga bisani ya dawo hayyacin sa amma duk aun ji masa ciwo a fuska.

Baffah ya dago ya kalle ni tamkar yana gani, Ya ce,"Ina ne nan Hadiza?

Na ce,"Asibitin 44 ne" na bashi amsa

"Me yasa kika kawo mu nan" ya bukaci tambaya

"Anna na ciki an kwantar da ita saboda jikin nata yayi tsanani"

Baffah ya dafe kai yana cewa amma ta yaya aka bar ku kuka shiga?

Na dade ina kallon fuskar sa da alama ya san cewa akwai abin da zai faru shiyasa tun farko ya hana mu kai ta asibiti ya ce sai ya dawo zai siyo mata magani.....na bashi labarin abin da ya faru zuwan mu Garkuwa da Barau dikko....ina kallon shi wallahi hawaye ne suka zuba a idanuwan sa.

Na share masa ina cewa,"Baffah bani labarin ku don Allah"

Baffah ya ce,"Ba yanzu ba, ki kai ni wajan Matata please"

Tausayin makafin yasa na tashi da sauri nai masa jagora zuwa ɗakin da aka kwantar da Anna.

Ahmad na ganin mu ya tambaye ni,"Me ya samu Baffah ne Khadija?

Na bashi labarin anin da ya faru, sai naga yana ma Baffah sannu, Baffah ya ce,"Ba komai Ahmad kai ni wajan Mata ta don Allah"

Ahmad ya kai shi daf da gadon Anna, ya jawo kujera ya zaunar da shi sannan ya kama hannayen sa ya ɗaura su saman hannun Anna, ya sauke Sofia a gefen Baffah yana cewa, "Sofia ga Baffah ina zuwa ko"

"Sofia ta gyaɗa kai tana masa murmushi"

Ya jawo ni muka fito waje bayan ya tambayi wani da ya bashi First aid box aka mika masa, zaunar da ni yayi a wani kan dakali wajan babu mutane sosai, ya kura mun idanu a hankali ya ce," Bana ce ki kula mun da kan ki ba, khadija ko housefly/kuda bana son yana taɓa ki balle kuma ma har ya kai ga mutum ya taɓa mun ke"

Na ɗan zumbure baki ina cewa,"Nazo taimakon Baffah ne shine suka kai min duka"

Ina kallon shi ya wani runtse ido irin abin ya taɓa sa sai kuma ya buɗe idanun  sa ya buɗe first aid box ɗin yaga komai na ajiye a ma ajiyar sa, kasancewar yana kallon yadda Dr Rasheed yake komai idan an kira sa yazo gida, so shima hakan yayi.

Ya sanya auduga a ruwan spirit kaɗan  ya kalli kyakkyawar fuska ta da kyar ya sanya hannun sa ɗaya ya tallabo haɓar gemu na, ya fara goge mun jinin.

Wani zafi naji da raɗaɗi a daidai sanda naji saukar ruwan spirit ɗin a gefen baki na, ban san lokacin da na runtse idanuwa na ba, na ɗan yi kara kaɗan.

Da sauri ya cire yana min sannu, shima tamkar shi yake jin zafin, Na ce,"Yaya Ahmad da zafi"

"Lord!!!!!!!" sautin da tayi anfani da shi wajan ambatan Yaya Ahmad shi ya rikita shi, sai da yaji abin har cikin zuciyar shi ya kura mata idanu yana mata kallon love.

Ya ce,"Khadija ki ɗaure kinji kaɗan ya rage na goge jinin bari na karasa, ya kara manna audugan yana goge jinin na daure har ya goge sannan ya rufe abin yana min sannu.

Na ce,"Thank you Yaya Ahmad"

Murmushi yayi yana cewa " What did you say?"

"Thank you Yaya Ahmad" na maimaita ina dariya kaɗan hakwarana farare mai ɗauke da wushirya suka bayyana kansu sai naji ya nuna ni da hannu ya ɗan zare idanu irin yaga abin mamaki ya ce,"Lahhhhhh wushirya"

Ban san lokacin da wata dariyar ta suɓuce min ba, saboda yadda yayi abin ya ban dariya, sai naga ya kura min ido ni kawai yake kallo yana murmushi.

Tsayawa da dariyar nayi na natsu waje guda na tsunkuyar da kai na kasa saboda wannan karan na gaza fahimtar in da kallon nasa ya dosa.

Yayi relaxing a kan kujeran dakalin ya zauna very confortable ya mikar da kafafuwan sa, sannan ya nannaɗe hannayen sa akan kirjin sa ya lumshe idanuwan sa yana tunani.

Ina gefe duk ina kallon sa sai naga ya birge ni karo na farko kenan a rayuwa ta da naga wani ɗa namiji ya birge ni, na zuba ma kwantaccen sajen sa ido da lallausan bakin gashin kan sa tamkar na lararabawa tsabar laushi da taushi da kyalli da komai ma, kamannin Anna ne sak a fuskar sa, ban san lokacin da nace," Amma kasan kuna yanayi da Anna ko?

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Continue Reading

You'll Also Like

2.8K 106 4
AmatulMaleek and the grt ASH TALBA
1.6M 141K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
8.1K 152 13
Labari ne akan wani rich,young and handsome dr whose mother is igbo by tribe while his father a Fulani..duk dunia babu qabilan daya tsana kaman Hausa...
749 65 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...