ALMAJIRA ✔

By DielaIbrahim

1.8K 92 14

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She find... More

Prologue
1
02
03
04
05
06
07
08
09
11
12
13
14
15
16
17
AL'ADARMU
18
19
20
SOFIA

10

67 3 0
By DielaIbrahim

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
10

______________________________________

Murna ta sani kasa cin abin ci, ina ɗoki na zumbula hijab ɗina da ɗan silipas ɗina, na kalli kanwata Sofia wacce take zaune daga gefen bakin kofar ɗaki tana ta min murmushin ta mai kara fito da asalin kyan da Allah yayi mata.

Na tsugunna na kai fuska ta dai dai saitin fuskar ta na sumbace ta a goshin ta saboda murmushin ta ya wadatar kuma ya fahimtar dani cewa Sofia na min murna zani makarantar islamiyyah.

Baffah ya rike min hannu har muka kure layin gidan na mu, muka isa bakin titin muka tsallaka sannan muka shiga wani layi anan naga islamiyyar kai tsaye kofar makarantar islamiyyar muka tsaya yayin da naga ɗalibai suna ta karatu a ciki.

Sallama muka fara musu kafin akai mana iso ofishin headmaster na makarantar, anan su ka bamu bayanai akan komai yadda za muyi register, kuɗin makaranta, littafai, da kuma kayan makaranta.

Dama kuɗin suna wajen Baffah ya ciro su duka ya mika min yana cewa, "Hadiza ki cire kuɗin makarantar da na littafai ki bayar"

Na karɓa na cire na biya komai aka sani a aji ɗaya saboda ban iya haɗa baki ba da komai ma, har hadda sai da na shiga, suka bamu kyallen yadin makarantar, ash color.

Muna fita muka wuce kasuwan rafin guza anan muka yanki yadin muka bada ɗinki, aka min Babban hijab 4yard da wando da farar riga ƴar ciki.

Ranar dai sai misalin karfe biyar muka koma gida.

Anna na tsakar gida tana ta kiciniyar sauke girkin dare wanda ta gama a murhun itace...Sofia na kan baranda tana wasan ta.

Ni nayi ta wajan Anna da murna ina bata labari abin da ya faru yau..
Baffah kuma yayi ta wajan Sofia da leda a hannu yana kiran ta ƴar baba zo ga tsaraban kifin ki na siyo miki, Haka suka zauna yai ta bata kifinnan har ta cinye.

Kallon su kawai nayi naji wasu hawaye sun zubo min wanda ban san ko hawayen dadin ganin su tare suna nuna tsananin kauna na ƴa da uba a tsakanin su....Na samu waje na zauna ni da Anna ina lissafo sunayen littafan da aka bani na aji ɗaya wanda ta ce ma ita zata rinka kara min karatu idan an mana sai ta sake koya min, hmmmm ni dai na kalli Anna na kau da kai na gefe, Ina mamakin yadda mutum wanda baya gani zai yi karin karatu kuma ma ita Anna me ta sani, duk tunani na ya na bani Anna bata yi karatun komai ba.

Washe gari ranar lahadi.

Wannan ranar ta kasance rana mafi soyuwa agare ni domin kuwa ita ce ranar da ta kasance wani sashi daga cikin rayuwa ta ya canja launi kwarai kuwa domin na fara karatu wanda a da cen baya ban yi tunanin haka zata kasance da ni ba, ga shi cikin kankanin lokaci Allah ya shafe min wahalhalun da nasha a baya duk da na san bawai rayuwar tawa ta canja bane amma gwara rayuwa ta ta yanzu saboda ko ba komai muna killace a cikin gida kewaye da uwa da uba duk da cewa makafi ne amma sun fi min komai a rayuwa yanzu saboda idan ba dan su ba da ba zamu samu lilliɓi ba.

Babu abin da zan ce wa Baffah da Anna sai dai godiya da kuma addu'ar Allah ya saka musu da mafificin alkhairi.

Yau ita ce rana mafi wanzuwa a cikin ranakun rayuwa ta, na fara zuwa makarantar islamiyya sannan ranar da zan fara haɗuwa da mutane daban daban, yare daban daban kuma hali kowa da nasa, na kudiri aniya In Sha Allah abin da ya kai ni makaranta shi zan yi.

Misalin karfe bakwai dai dai na gama shiri na shirya cikin sabbin kayan makaranta na, har da safa da nikab babba wanda dama sun saka cewa doka ce sanya nikabi idan za a zo makaranta.
Ni dai har da safan hannu nace wa Baffah ina so, shine ya siya safar kafa, da na hannu bibbiyu nikab ma biyu.... na rataya jakan makaranta na, na fito tsakar gida na tsaya cak yayin da su Baffah da Anna da Sofia suna karin safe koko da kosai wanda Baffah ne yaje ya siyo a bayan layin mu, yau kam zasu fita bara.

Na samu waje na zauna ina gaishe su duka cike da murna na ce "Anna ba zan ci komai ba nikam na tafi makaranta"

"Hadiza kar ki kuskura ki fita baki ci wani abu ba, maza dawo nan ki karya"

"Na ɗan ya mutsa fuska duk da ma na san ba gani na su keyi ba nayi niyan sanfe wa amma sai na zauna na natsu na sha kunu da kosai guda bakwai sannan na tashi da sauri ina cewa "Anna zan makara na gama"

"Kin tabbatar kin gama?

"Eh"na amsa har da kaguwa ina ma Sofia bye bye da hannu.

"Allah ya tsare Hadiza " cewan baffah

"Allah ya kiyaye, idan kin dawo da wuri ki same mu a gada kinji" Cewar Anna.

"To Anna In Sha Allahu sai na dawo"

Na tafi ina murna tun da na fito daga gida ake ta faman kallo na, samari da ƴan mata bina suke tayi da kallo, ni dai na san na rufe fuska ta na rufe jikina ruf babu in da mutum zai gani na sunkuyar da kai na kasa na cigaba da tafiya har na isa makarantar.

Headmaster da wasu mazan aji shidda kawai na gani a bakin kofar makarantar nayi musu sallama, kai na  tsaye ajin da aka kai ni jiya nan na shiga sai naga wayam babu kowa duk basu zo ba kasancewar bakwai da rabi ma ba tayi ba kuma aka ida dokar makaranta karfe takwas daidai ake fara karatu.

Ina zaune sai na hangi wata ɗaliba tana share aji uku, sai na kalli ajin namu shi ma dai yayi datti sosai hakan yasa na tashi na karɓo tsintsiya bayan ta gama nima na zo na share ajin mu daidai lokacin ɗaliban sun fara zuwa ɗaya bayan ɗaya suna tsaye bakin kofa suna jira na gama.

Malamar mu ta shigo bayan na gama sharan, kowa ya zazzauna, ina benchin gaba duk da cewa na fi ɗaliban ajin shekaru amma ba lallai a gane ba saboda bana da tsayi sosai...Alqur'ani shine darasin mu na farko.

Na buɗe nawa alkur'anin sai naji  suna karantawa gwanin ban sha'awa amma bana gane komai kasancewar ban iya ba...haka nai ta kokarin bi ina daɗa nanatawa karin da akayi mana sai da muka fita break nai ta maimaitawa matsalar ita ce ban iya haɗa baki ba.

A takaice dai karfe biyu muka tashi kowa ya tafi gida, mota ƴar kumbula na hau naira talatin a ka kai ni gadar kawo na samu su Anna suna ta shan rana suna bara nima na zauna suna min sannu da karatu.

Kanwa ta Sofia ta rungume ni, nima na rungume ta na zaunar da ita ina koya mata alifun, ba'un kamar yadda aka koya mana har karshe sosai ita ma abin ya burge ta sai tafi ta keyi tana murna.

Baffah ya ce "Sofia da kina da kafa kema da an saki amma nan gaba kaɗan zan saka ki In Sha Allah"

Nace "Ameen Allah ya kai mu Baffah"

"Ameen ya rabbi" Anna ta amsa.

Ranar sai bayan magriba muka koma gida, ni na ɗaura mana taliya a murhun gawayi, muna ci muna hira

Muna gamawa Anna tace na ɗauko paper da pencil ta kunna hasken touch light ta karɓa ta fara rubutu....sai data gama ta karanto min Huruf, daga farko har karshe sannan ta fara koya min yadda ake haɗa baki, tana yi tana rubutawa ina fahimta wanda ko malamar tamu ban fahimci nata sosai ba kamar yadda Anna ke koya min.

Sai da ta tabbatar na koya sosai kafin muka kwashe komai karfe tara da rabi sannan muka shiga muka kwanta, dama tun tuni Baffah da Sofia sun jima da yin bacci.

______________________________________
ABUJA

Zaune yake a ɗaya daga cikin fancy chair dake cikin babban conference hall na company ɗin su, suna having presentation wanda shi ne yake presenting contracts da su kayi da ɗaya daga cikin companonin da suke kasuwanci tare.

Clients din shi da employees din shi, sai kujeran Daddy da yake kallon nasa kujeran.

Bayan Clients ɗin sun gama sun tafi, sai su Daddy suka zauna again suna da 2nd meeting.

Daddy ya dubi Ahmad ya ce," I.B WORLDWIDE CONSTRUCTION LTD kamar yadda kuka sani shine company mai tashe har yanzu anan garin Abuja, na fara aiki a company ɗin kafin Allah ya ba ni nawa, Hakan yasa yanzu suka neme ni suna son mu haɗa hannun jari akwai contract ɗin da za muyi a London wanda nake da yikinin idan har mun yi nasara to zamu ci riba sosai.

Daddy ya cigaba da cewa "Na wakil ta Ahmad akan wanda za kuyi magana da shugaban company ɗin"

"Daddy ni kuma why not you?Ahmad ya faɗa da sauri.

"Yes you" You are the CEO of this company and............"

"But Daddy I have so much contract to cover it up" Ahmad ya faɗa bayan ya katse Daddy wanda bai ma karasa abin da yake faɗa ba.

Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya gyaɗa kai yana cewa,"Forget about the rest of the contract, I will handle them myself, just focus on this one and make me proud as you always does"

Ahmad yayi murmushi kaɗan sannan ya ce,"Alright Daddy no problem, I will do as you say"

"Thanks for that"

"You welcome Daddy" Ahmad ya faɗa kafin ya kalli sauran employees ɗin sa yana tambayar su ko suna da shawara akan issue ɗin, suka ce babu duk shawaran da Daddy ya yanke ya wadatar.

Ahmad ya sallami kowa ya rage daga shi sai Daddy, Daddy ya ce,"Meet me at my office now"

Ahmad ya gyaɗa kai yana fatan Allah yasa ba wata magana bace kuma don yana bukatar ya huta ko brain ɗin shi zai samu lokacin tunanin *khadija* sai kawai ya tainci kanshi da yin very cute smile ya kara fitowa handsome yana tafe yana murmushi har ya isa office ɗin Daddy....Ya same sa zaune saman Sofa ɗin sa yana shan hot ginger tea  don Daddy akwai al'amarin son shayi.

Sai da Ahmad ya jima a zaune ya ɗauka ɗayan kofin shayin ya fara sha tun kafin ma Daddy yace ya ɗauka.

Daddy ya ce,"Uhmm naughty boy na baka izini ne?

"Daddy ai ka sani nima na ɗauko halin ka bana wuce tayin tea balle ginger tea irin naka, sai dai kawai kayi hakuri" ya faɗa yana dariya

Daddy yayi gyaran murya sannan ya ce, "Bana son yin maganan gida a office amma na lura a ƴan kwana kinnan kamar muna ƴar wasan ɓuya da kai"

Ahmad ya dago kai yana ɗan tsuke baki.....Daddy ya cigaba da cewa ,"Ya maganar da mu kayi kwana ki, kasan na ce na zaɓa maka mata ko, kuma abin farin cikin ma haɗin gida za muyi"

Ran Ahmad in yayi dubu ya baci, ya sani ya san Daddy baya da wata magana face wannan kullun, shi ya rasa yadda zai yi da su Daddy su gane cewa shi fa baya son zancen auran nan for now.

Daddy ya ce,"Na sani dama na san bazaka kula ni ba, anyway na faɗa maka ne saboda ka sani idan kuma ka matsu kasan ko wacece to ja same a gida anytime zan faɗa maka, amma idan baka matsu ba to ka san da sani cewa ina nan ina ta shirye shirye sai dai kawai kaji an ɗaura aure"

"And don't come for any question after your wedding, na baka right time ka zo ka same ni kafin komai ya faru" Na gama zaka iya tafiya.

Kam bala'i, ai tuni Ahmad ya ɗauke wuta zuciyar shi na dukan uku uku, anya Daddy ya san abin da nake going through kuwa da zai yanke min wannan ɗanyen hukuncin, lallai dole na san abin yi, How on earth zasu matsa min a aure na na farko, and yanzu ma suyi ta matsamin" a fili kuma ya ce da karfi, "Shin ni bani da freedom ne Daddy? bani da damar zaɓan abin da zuciya ta take so ne?

Ya hura iskan bakin shi kafin ya cigaba da cewa,"Daddy ku sani fa aure na na farko na dawo daga school na gama degree na iske an ɗaura min aure da marigayiya and haka na hakura nai muku biyayya na zauna da ita for good and to make you both happy" and now sakamakon da zan sake samu kenan daga wajan ku?

Yana kai wa nan ya bar office ɗin ran shi a dagule idanuwan sa suna son zubar da kwalla kai tsaye gida ya wuce part ɗin sa ya tura wani sliding door ya shiga wani babban room an masa white paint, ɗakin nan dai nasa na zane nan ya shiga ya cire suit ɗin sa na saman ya balle boturan hannun shirt ɗin sa, sannan ya jawo wata doguwar kujera ya zauna yana facing wani babban skeche pat board gefen sa kuma dangin su brush ne da colors, manyan pencils na zane.

Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sannan ya hura iskan bakin sa kafin ya fesa wani farin paint a board ɗin kamar spray yake yana gamawa ya hau yin zane.

11am ya dawo gida kuma 1pm ya gama zanawa ya jima yana kallon board ɗin zanen kafin daga bisani ya ajiye komai ya nufi washing hand vase ya kunna tap ya wanke hannun sa da hot water ya wanke face ɗin sa, sannan ya ɗaura da alwala yana gamawa ya fito ya wuce masallacin gidan na su wanda yake cikin gidan su amma an fitar da kofa ta waje na gida dole sai ya fita waje, ya bi jam'i.

Suna idar wa ya fito part ɗin Mummy ya wuce har bedroom ɗin ta bai same ta ba, yana ta kiran ta.

Mummy! Mummy!! Mummy where are you now?

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

Continue Reading

You'll Also Like

22.9K 89 12
Issac is an average thirteen year old. Except for one thing, he likes diapers. And when his mom catches him wearing a pull up. She decides since he l...
503K 36.9K 38
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
148K 15.4K 18
[Sequel of 'MY SUBCONSCIOUS DESIRE'] Once again, a tale of desire and respect Once again, a tale of Rathod and family bond A multi-couple story. F...
407K 42K 23
انا العاصفة الحمراء ألتي تراهن وتربح انا القوة العظيمة الذي سوف تنهك كُل الارواح الجنون والتلاعب بحد ذاته هنا أستطيع ان اتلاعب بعقلك حَد الجنون امر...