ALMAJIRA ✔

By DielaIbrahim

1.1K 70 5

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She find... More

Prologue
1
02
03
04
05
06
07
09
10
11
12
13
14
15
16
17
AL'ADARMU
18
19
20
SOFIA

08

39 1 0
By DielaIbrahim

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
08

______________________________________

Ranar da ba zan ta ɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwa ta, garin da Abiy ya ajiye mu, ƴan boko haram suka samu damar shigowa garin suka tarwatsa rayuwar al'umma abin babu kyan gani yayi muni da yawa.

Ummu kwanan ta biyu dama bata lafiya ko hannun ta bata iya ɗagawa rashin lafiya ya kwantar da ita, ba wani abincin kirki sai amai duk abin da taci amai take yi.

Hayaniyar da yayi yawa, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un abin da kowa yake faɗi kenan, hargitsi, tashin hankali da tarzoma ya fara zuwa ta in da muke, Harbe harben bindiga da hayakin bomabomai shi ya turnuke ko ina, jama'an gari kowa yana neman ta kan sa, kana gudu kana neman maɓuya sai dai kaji harbin bindiga a jikin ka....Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan tashin hankalin dame yayi kama ni Hadiza.

Muna cikin rumfar mu, mun dukun kule juna a wani kusurwa cikin rumfar tamu Ummu na babu abin da take sai kuka tana bamu hakuri, cewa, "Hadiza kinyi girman da zaki mallaki hankalin ki Hadiza ki kula da kanki kuma ki kula da kanwar ki, Don Allah kar ku bari ruɗin duniya ya rufe muku idanu, ku kasance masu tsare mutuncin ku a duk in da kuke, ke yarinya ce da Allah yai miki baiwar sura da kyau Hadiza don Allah ki zama mai ɓoye surarki da kyan ki ko da kuwa bara za kiyi  shine zaki ci ribar rayuwa" ta tsagaita saboda aman jini da ta keyi, hankali na ya kuma tashi kuka sosai na keyi, Ummu na cewa "Ku gudu kar suyi muku wani abu.

Har na goya Sofia na ɗauki kullin kayan mu sai naji hawaye na bin kumatu na, ina takaicin wai ni na bar Ummu cikin wannan halin naji ba zan iya tafiya na bar Ummu na halin ba.

Muna zaune kuwa sai gasu sun iso, ganin kyayun da Allah yayi mana yasa suka tarkata mu ni da Sofia suka sanya mu a mota, har mun yi nisa sai na ji harbin bindiga a ta rumfar Ummu na, Ina tunanin sun kashe min Mahaifiya ta tun a wannan lokacin.

Kuka ne ya kwace min na tsagaita ina kuka mai tsuma zuciya sosai Anna take rarrashi na, sosai Baffah yake rarrashi na, shima tausayina ya mamaye mishi zuciya.

Na tashi na debo ruwan sama cikin randa na dawo na zauna sai da nasha na kwalkwala sannan na sauke nannauyen ajiyan zuciya kafin na cigaba da cewa,

"Karfin hali da jajircewa irin nawa na sauka daga motar da gudu naje ina duba rumfar danna tabbatar da abin da kunnuwa na suka jiye min.

Labari ya sha banban domin kuwa babu Ummu na babu alamar ta a rumfar ko ɗigon jini ban gani ba, sama da kasa, lungu da sako babu ita na duba gabas da yamma babu wata mai kama da Ummu na....da karfi naji an jani aka sake wurga ni bayan motar toyota tsohuwa wanda bayan ta abuɗe yake, idanuwa na suna kan rumfar tamu ina mamakin ina Ummu na? har mu kayi rumfar ta ɓace wa gani na.

Tafiya mai tsayi mu ka yi, ayi a huta har muka kawo wani gari wai shi sakkwato/Sokoto daga nan aka yada zango a wani daji wanda ko hayaniyar mutane ba kaji sai kukan tsuntsaye.

Ranar dai kaddara ta faɗamin domin kuwa, a cikin ƴan mata sama da goma da suka sace, sun yi ma shidda fyaɗe ciki ma har da Ni.

Tsakar dare kowa ya rintsa, na daure na tashi na goya Sofia wacce take gefena tana ta baccin wahala, karamar yarinya wacce bata san komai ba a rayuwa tana ta fuskantar tashin hankalin da bata taba gani ba, wallahi a gaban idanuwan ta su kayi mana kacha kacha, ina jin sautin kukan Sofia tsoro na Allah tsoro na kar suyi mata wani abu.... shiyasa na goya ta, saɗab saɗab na bar wajan duk da ina jin ciwo a kafa na, amma haka na ɗaure ina ta falfala gudu a cikin jeji wanda bana ganin komai sai duhu.

Wallahi bata tsoro nake ba, ban ma san miye tsoro ba a wannan lokacin ni dai buri na nayi nesa da azzaluman mutane...ina tafiya ina tsine musu albarka.

Wayewar gari tangarau a idanuwan *HADIZA* Daga lokacin na fara fuskantar matsalolin rayuwa, Wani kauye na samu kai na a ciki, na zauna na huta na awa ɗaya daga bisani na kara ɗaukar hanya sai da na isa babban gari wato garin Bakura anan rayuwar mu ta cigaba.

Bayan faruwar wannan al'amarin da wata ɗaya sai na fara rashin lafiya, amai da kasala da yawan bacci...ban san abin da ke damu na kenan ba ni dai kawai naga bana da kuzarin ɗaukar Sofia ko na goya ta....Kimanin watanni biyar ina fama da laulayi ashe ciki nake da shi, kammani na ya fara canjawa ciki ya fara girma....ranar da aka sanar dani ina da ciki wata biyar kaman zanyi hauka haka naji....amma daga baya sai na rungumi kaddara kuma muka cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka fara.....Muna zaune lafiya a garin shine watarana suka kawo ma garin ziyara sanadin barin garin kenan nazo nan Kaduna ko zan samu mafaka....na ɗan tsagai ta ina share guntun hawaye na.

Anna kunji labarin mu, Anna ma hawaye ta share ta ja gutun majina tana cewa sannu Hadiza lallai kinyi kokari kin fuskanci ukuba ta wahalar rayuwa, ki cigaba da addu'a wata rana Allah da kanshi zai shafe miki komai kiji kamar babu abin da ya faru dake.

Nayi murmushin karfin hali ina cewa ,"Allah ya sa" Na ɗauki Sofia wacce ta jima da yin bacci ina cewa "Anna ku shigo mu kwanta dare yayi sosai karfe Shabiyu fa"

"Anna ta ce,"To Hadiza , "lallai mun cinye lokaci wajan labari bari mu shigo" ta faɗa tana takawa a hankali Na zo na taimaka musu suka shigo suka nufi uwa ɗakan su, suna min sai da safe., na kara sa kulle kofar falon na sanya sakata da kwaɗo saboda kofar waje a buɗe take kuma rayuwar yanzu komai na iya faruwa, da su Anna a buɗe suke kwana zuwan mu gidan na siyo kwaɗo kullin sai na makala idan zamu kwanta haka ma idan zamu fita sai na makala.

"Na kwanta ina jin ɗan ciki na na motsi da sauri sauri abin har yabi jikina, na saba da motsin nasa, fata na dai Allah ya sauke ni lafiya"

Washe gari

Yau tun da asubahi na gama mana komai na aikin gida, nayi abinci na ci sannan na shirya na zumbula dogon hijabi, ba tare da na musu sallama ba na kama hanya kai tsaye kofar makarantar nan mai mashin ɗin daya ɗauko ni ya tsaya sai dai a rashin sani mun tsaya daidai kan hanya bayan wata mota ce wadda ta tura mu muka faɗa cikin kwata na buga ciki na da karfi na kuma buga goshi na yayin da tuni jini ya fara biyo kafafuwa na, kai na kuma yana sara min.

Babban mutum ne da iyalan sa su suka yi sanadiyar hatsarin sune naga sun fito hankali tashe sun tsorata da ganin halin da nake ciki......cikin kankanin lokaci aka fito dani ana kokarin sanya ni a mota saboda sun lura na buga ciki na ga kuma jini, amma ina tuni na suma.

4hours after

Na farka da kyar nake iya lumshe idanu ina buɗewa a hankali har na buɗe tangaran lokacin dana shafa cikin jiki na sai naji wayam, kamar ma ba a taɓa halittan wani ciki a wajan ba, tsabagen ya shamule ba komai amma kuma kasan mara na kaman an ɗaure da wani abu.

Kai na naji yana ɗan sara min, take likitoci suka shigo suna min sannu, bayan yamin wasu ƴan tambayoyi.

"Ya ce, "Ke matar aure ce?

"Na ce "Aa"

"To ina iyayen ki?

"Nace suna rafin guza" okay zamu iya kiran su yanzu ki bamu lambar wayar su?

"Nace "Ba su da waya, likita ina cikin dake jikina wai? Na tambaya da sauri"

"Ya share zufan daya keto masa duk da sanyin AC da yake ratsa ɗakin  majinyaci, sannan ya ɗaga kai yana yi ma wata magana Ya ce,"Nurse please"

Nurse ce tazo ɗauke da baby a hannu ta mikawa doc.

Shi kuma ya miko min yana cewa "Baiwar Allah kiyi hakuri, an kawo ki asibiti mu likitoci halin da kike ciki dole mu taimaka miki, jini ya balle miki, ba kya cikin hayyacin ki bugu da kari kuma cikin dake jikin ki scanning ya nuna yana cikin wahala idan bamuyi sauri mun ceci rayuwar sa ba.

To Allah cikin ikon sa waɗan da suka kawo ki su suka sanya hannu akai miki C.s, sannan suka siyo kayan sanyin jariri suka bayar kyauta, Lafiya lau muka ceto ran jaririn ki, yayi kuka kuma yayi walwala har nurses suka shirya sa, amma awa ɗaya daya wuce kafin ki farfaɗo numfashin jaririn ya fara yin sama sama, mun yi iyakar kokarin ceto ran jiririn hakan bai nufa ba Allah ya amshi abin sa.

Inna lillahi wa inna illaihir raji'un

Duk da ban san waye uban ɗan da na haifa ba, duk da kuma ba ɗan sunna bane, Wallahi ban san lokacin da zuciya ta ta buga ba, ina jin wani raɗaɗi mara daɗin misaltuwa, ina tuna watannin baya da tun bani son cikin, tun bana cin abinci saboda takaicin cikin har nazo na fara son sa har cikin rai na kuma nakeyin dukkan abin da zai sa na haifo shi lafiya saboda Allah daya kaddara min samun cikin shi ya fini sanin dalilin halittar bawan sa ko baiwar sa.

Na zubar da kwalla sannan na ce "Allah ka bani kyauta kuma ka karɓi abin ka, Allah kaji kan bawan ka, ka sa me ceto ne"

"Ameen" Likitan ya amsa yana mikamin jaririn, na rungume shi ina tausayin shi cikin rai na, nice sanadin zuwan sa duniya, da yamma na ce ni su sallame ni gida zani, hakanan da suka ga na dame su sai suka sallame ni na nufi gida.

Anna na ta kokarin dakan gero zatayi abinci da shi, Sofia na gefen ta tana wasa da kasa, suka ji sallama ta.

Anna ta amsa tace,"Hadiza kin dawo, mu kam yau muna gida bamuje ki ina ba"

Na ɗan matso kusa da su, ina kallon Sofia wacce take min kallon mamaki ganin Ɗa a hannu na, tana son yin magana amma karancin shekarun ta ya sa tayi shiru, Anna ta ce,"Ina ta magana kinyi shiru kuma"

Na ce,"Anna na haihu.......sai kuma na sarke da shakuwa na duka ina kuka mai tsuma zuciya.

Ai babu batun daka kuma taɓaryar ta a jiye salin alin jin sabon labari ta nufo in da takejin sautin kukana ta lalubo ni ta amshi jaririn tana cewa,"Yaushe kuma Hadiza ashe nayi jikanya, shine baki dawo gida ba, Faɗa min me ya faru?

Da kyar na iya bata labari tiryan tiryan har dawowa ta gida, ta tausaya min don naji saukar hawayen ta a hannu na, daga bisani ta share min idanu tana cewa ,"Dukkan abin da ya samu bawa to daga Allah ne, lokacin da kaddara ta same ki, kin ɗauki dangana, sannan kuma lokacin da kika fuskanci cewa akwai ciki a jikin ki shima kin dauki dangana tun da gashi ya girma har kin haife shi, To ki sani cewa kamar yadda kika ɗau hakuri tsahon wata tara kina ɗauke da ciki a jikin ki to ki share hawayen ki Allah shi ya san daidai kiyi ta masa addu'a kuma Allah yasa me ceto ne"

"Ameen" cewar Baffah wanda shigowar sa kenan da itace  a hannu ya ajiye ya amshi yaron yana cewa bara na sanar da makota na a kai shi makwancin sa.

Jim kaɗan sai ga maza sun shigo suna ta mana ta'aziyya aka sanya shi a likkafani suka mai sallah sannan aka tafi da shi.

______________________________________

Daddy da iyalansa sun yi ma Nurain registration, suka sallame sa misalin karfe biyu suka mishi sallama yana kuka baya son rabuwa dasu, duk da kuwa ya haɗu da abokanan sa, amma nisan da zai yi da iyayan sa daban ne, In fact bai ma taɓa yin nesa dasu ba haka suka tafi suka bar shi yana ta kuka.

Mummy ta umarci Driver da ya bi ta asibiti domin su duba mara lafiyar nan kafin su koma Abuja....da shigar su ɗakin da suke da tabbacin nan aka ajiye ta akan zasuje su dawo, sai suka tarar wayam.

Likita yai musu bayanin abin da ya faru, kuma ta tafi gida abin ta, jikin su yayi sanyi akan abin da ya faru, da son samu ne ko taimakon kuɗi ma da sun bata ta rage wani abin.

Daddy yace "Is okay Mummy tausayi mu koma mota muna da journey fa"

Mummy ta ce,"Daddy wallahi yarinyar ne taban tausayi karama da ita"

"Ba a jin tausayin irin su, sai kiga sun fika sanin abin da duniya ke ciki, beside ya a kayi ta samu cikin dake jikin ta at her young age" and secondly me yasa ta tafi bayan ta farfaɗo at least sai ta tsaya idan har yarinyar kirki ce kuma jaririn da uban sa wallahi tsayawa za tayi babu in da zata har sai family nata sun zo  Faɗar Daddy yana faɗa ran shi bace.

Mummy ta taɓe baki tana cewa,"Things doesn't gonna smell good, May be maganan daka faɗa akwai gaskiya a ciki, But trust me there must be reason behind what that girl does because I feel her pain," Faɗar Mummy tana kokarin shiga mota.

Daddy kallo ya bi Mummy da shi, yana mamakin yadda tausayin rarinyar ya mamaye zuciyar ta lokaci guda, bai sake maganar ba haka kuma sai ya sauya akalar hiran nasu.

Karfe uku da wani abu suka koma gida suna parking Mummy taga motar Ahmad abin ya ɗaure mata kai duk da tasan cewa flight yabi amma ba tayi tunanin zai dawo da wuri haka ba...

Nadiya ta fito tayi ɗakin ta, Yayin da Kamal ma yayi nasa part ɗin yana makale da bluetooth a kunne da alama waya yake yi....Mummy kam Daddy ta kalla wanda yake ta kokarin saka seat bell da alama driver zai fita da shi ne.

Ta duka ta window tana cewa,"Daddy dama Ahmad bai tafi bane, naga da safe bamu haɗu ba, ko dai maganar jiya ce ta bata masa rai kasan Ahmad"

Daddy yace,"I may think so, you check him please, I have to go somewhere now now as you can see"

"Alright you carry on, I'll check him, Make sure you come back soon please"

"In Sha Allah Take care" Ya faɗa yana ɗaga mata hannu.

Karya corner tayi ta shiga part ɗin sa sai ta samu komai a kashe yake amma tana jiyo kamshin turaren sa daga bedroom hakan ya kara tabbatar mata da yana ciki kenan, kai tsaye ta shiga bedroom ɗin anan ta iske shi lulluɓe da bargo ta karasa tana cewa,

"Dear what's wrong with you?

Taji shiru ta san halin Ahmad zazzabi ne kaɗai yake sashi ya lulluɓe da bargo, Ahmad ko sanyi a keyi baya rufuwa tun kuruciyar sa, shiyasa aka samishi room heater a ɗakin sa da falo ko da yaushe kunna wa yake indai sanyi ya shigo, sai dai kawai kaga yana fama da track suit da canvas sai normal jacket mara nauyi.

Ta kai hannu ta dafa goshin sa, "Ya salam" ta faɗa da sauri tana cire hannun jin zafin da jikin sa ya ɗauka sosai ya ɗaga mata hankali.

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

Continue Reading

You'll Also Like

12.2K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...
3.8K 99 4
Just like some other reactions... i wanted to make my own..? i do hope that with this shit story i can learn to better my English and grammar. Got an...
298K 21.7K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
2.6K 225 27
Wannan ne littafi na na farko,Allah sa inyi abin arziki your comments and likes will be appreciated 😅 Life is full of ups and downs,when we think...