ZAMANIN MU A YAU

By NEIRNAHDISO

2.7K 116 12

wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta d... More

ZAMANIN MU AYAU 2
ZAMANIN MU AYAU 3
ZAMANIN MU AYAU 4
ZAMANIN MU AYAU 5
ZAMANIN MU AYAU 06
ZAMANIN MU AYAU 7
08
09
10
11
12
13
14
15
16

ZAMANIN MU A YAU 1

577 25 5
By NEIRNAHDISO

*🫧ZAMANIN MU A YAU🫧*

   NA

JEEDDAH ALIYU
          &
NANA DISO

_____

*001*

  Tsaye yake gaban madubi, agogon dake hannunsa yaƙe cirewa. Alamun buɗewar ƙofa ce tasa shi ƙara gyara tsayuwar sa, idan bai manta ba tsawan minti 30 kenan da ya ƙiranta a waya amma sai yanzu  tazo, wani zazzafan numfashi yaja kana ya fesar, tura ƙofar kai tsaye tayi batare da sallama ko wata magana ba, ƙarar rufewar ƙofar ce tasa shi jiyowa gaba ɗayansa ya zuba mata idanuwanshi, cikakkiyar macce ce wacce ba zata gaza shekara 40 ba fara ce sol amma kuma gajeriya ce, manyan idanuwa ta zuba masa a hankali tace  "Yallabai lafiya naji ƙiranka?" Cikin muryarsa mai amo yace "Banida darajar da zan dawo daga aiki naga matata tana jirana ne? Kokuma banida ƴancin ƙiranki aloƙacin da nakeso?" Taɓe baki tayi gami da galla masa harara ƙasa ƙasa batare da tace komai ba ta samu guri ta zauna cike da gadara take faɗin "yallabai when zaka waye? Yaushe ne? Please free world muke banson taƙura kai ba kada aiki sai tattaɓa mace gaskiya ni ba zan iya ba na gaji, idan kuma yunwa ka ke ji ga abincinka can ƴan aiki suna jera maka aƙan dinning idan wanka za kayi kuma sai na kira ɗaya daga cikin masu aikin ta hada maka ruwa dan ni dai ba baiwar kowa bace ba.
Tafada muryarta na rawa. Manyan idanuwanshi ya zuba mata, tare da wata muguwar harara da ya sakar mata, tsigar jikinsa tana mimmiƙewa, baice mata ƙomai ba ya juya tare da bismillah yana cire shaddar dake jikinsa, jiyo da idanuwanta tayi dan aduniya babu abunda takeso sama da wannan mazantaƙar halittar tasa miƙewa tayi tafara nufarsa, bai ankara yaji ta rungumeshi ta baya.Tsigar jikinsa ce taƙara mimmikewa a hankali ya ambaci sunan ALLAH sannan yace " Maryama inason haihuwa inason naga yarana suna..." " Please stop yallabai nace maka na gama haihuwa yarona shekarar sa 20 yanzu aduniya ya isheni, ko so ka ke yi na zama kaza kamar Babarka? banson..." wata irin zabura yayi ya jiyo, ya ɗaga hannunsa yayi ya sauke a fuskarta. Cikin mamaki ta ɗago idanuwanta da suka cika da hawaye tace "Dan na faɗi gaskiya shine zaka mareni? Bazan kara haihuwa ba na gama haihuwa.
Ta ƙarashe magana tare da samu guri ta zauna tana kuka ahankali.  gaba ɗaya hankalin sa tashi yayi to wai shi wacce iri mace Allah ya basa? Wannan wacce Irin akida ce? Ilimin bokon hauka ne? A hankali ya furta "Ya Allah" manyan idanuwanshi ya sauke akanta sannan yace " Wannan shi ne mugun harafinki na ƙarshe akan mahaifiyata naga wayewar taki tana sakawa kina tunanin mun zama ɗaya? To ki sani har abada gaba nake dake sannan ƙarkashina kike, maganar haihuwa ko kina so ko bakyaso sai kin haihuwa shekaru daya har ashirin ba wasa bane ba na gayamiki, kada ki ɓatamin rai maryama kada kisani cikin wani hali ina ragamiki ne saboda anty da darajarta da nake gani ba wai dan ba zan iya wulaƙantaki ba.
Miƙewa tayi ta kallesa gaba ɗaya illahirin jikinta rawa yake yi yayin da tsigar jikinta ta shiga miƙewa a dalili yadda ta ganshi ta ɗaure towel ga yanayin gashin jikinsa ya mimmike saboda bacin rai, ƙallonsa ta koma yi sannan ta kau da kanta zuciyarta na ayyana mata, she is not that cheap da zata kai kanta gurin namiji. Saukewar ajiyar zuciyarsa yasata yin murmushi tace " Am not going to say it again, Ahmad Shema kasani ni maryama Ado na daɗe da cire mahaifata, nagama haihuwa! Banida ra'ayin haihuwa kamar kaza, idan har.... bata karasa ba ya shige banɗaki yana rufowa da ƙarfi saboda ɓacin ran da yake ciki, sunan Allah ya shiga ambata a cikin ranshi a hankali ya kunna shower ta fara sauka akansa gaba daya ransa ya gama ɓaci, a gaggauce yayi wanka sannan ya fito ya shirya ciķin wani lafiyayyen yadin filtex yunwar da yaji yana ji ne yasa shi fitowa daga ɗakinsa ya nufi palour, mamakin ganin karamar ƙanwarsa Fati yayi tare da ƙaninsa farouk sai matarsa maryama dake waya a gefen kujera da alama da mahaukatan ƙawayenta ne take waya dan yaga yadda taƙe faman babbaka murmushi. "Barka da fitowa Abah". suka faɗa a tare murmushin nan nasa mai sanyayya zuciya yayi musu sannan ya fara taƙawa zuwa dinning  cikin kasalalliyar murya  yace " Maryama zoki zubamin abinci. Ta ɗan  saukar da wayar gefe tace "waya nake yi ka zubawa kanka.
Sannan ta ƙarasa fita daga part din. Wani mugun takaicine ya ziyarci fati, farouk kuwa kasa cewa komai ya yi. Fati da taga alamar yayan nata na ƙoƙarin zubawa tayi saurin miƙewa ta nufi wurin shi tana fad'in "Abah kawo in zuba maka please.  Ƙoƙarin boye damuwarsa yayi kafin ya bata cokalin ta zuba masa, kallon ta yayi yaji sanyi cikin ransa dan shi mutum ne mai son ƴan uwansa, duk da zafi da hali irin na mahaifiyarsu ta basu tarbiyya mai kyau tun daga girmama na gaba dasu da kuma mutuntawa, cikin sanyin murya da sunan da yake kiranta dashi yace "Batoul zuba muku keda farouk" ya faɗa yana fara cin abincin, cikin girmama ta zuba musu har suka gama cin abincin sannan yace  "Meke tafe daku?" Farouk ne yace "Abah zan je makaranta ne dan ALLAH kayi haƙuri in-sha-Allahu zan mai da hankali, na gayawa Alhaji yace tsakaninmu babu ruwansa.  "Batoul ke kuma fa?
"Abu nifa banason aure kuma hajiya ta ɗage sai nayi ni kuma karatu na keso dan ALLAH talk to her.
Murmushi yayi gami da cewa "na ji zaku iya tafiya.

   Zaune take a tsakiyar palournta ƴan aiki guda biyu suna gefenta ɗaya tana mata tausa, fati ce ta ƙara kallon hajiya tace " Gaskiya matar Abah ba tayi ba wallahi.
Wani kallon tuhuma mahaifiyarta tayi mata cike da nuna bacin rai tace " maryama sa'arki ce?"
"A'ah amma hajiya ba kiga abunda take masa ba mu ma fa ko amsa sallamarmu bata yi har cewa tayi muna damunta da shige da fice a part ɗin ta mu kiyayye wai ni kan Hajiya akanta akafara boko ne?" yanzu ki duba Hajiya maleek tabarshi yazo cikin danginsa na tahana yanacan England yana rayuwa shi ƙadai wallahi ko kaɗan bata dace da ɗan uwana ba.
Gaba ɗaya hajiya tattara hankalinta ta zuba gurin maganganun autar ta ta, duk da gaskiya take faɗa amma tayi mamakin har yaushe maryama tasamu saken nan? Cikin isa da taƙama ta dago kanta tace "Fati barmin palour. ta faɗa tana sauke kallonta akan Larai, ta ce "ki je ki ce ina son magana da maryama yanzun nan.
"To! larai tace sannan ta wuce zuwa sashin uwar daƙin nata, taje ta sanar da sakon hajiya sannan ta koma." Maryama tana isa tace "Barka da rana hajiya.
    Cikin isa hajiya tace  "Mairo!
Da mamaki maryama ta jiyo, hajiya ta ci-gaba da kallonta a ɗage kafin cikin gadara tace "ko ba sunanki kenan ba Ko ba dashi nasanki ba?"
Shin Mairo na aura miki yarona ne dan ki wahalarmin dashi? To bari na ƙara tunasar dake babu wata halitta da za ta zo cikin iyalina ta jawomin matsala, duk abinda ki ke yi ba ki isa ki juyamin ɗa ba ko kuma ki wulaƙanta mishi, wannan gidan mijinki ne amma kuma iyayensa na tare dashi, idan bokon naki ne yake nuna miki kina da babban freedom why not ki kashe auren sai ki zauna a ƙarƙashin kanki da kanki kinga shikenan kin zama independent woman?" Da sauri maryama ta kalli hajiya "Ba kallona za ki yi ba ki kiyaye don kuwa ina kamar shekarun baya muddin kina so kanki da lafiya karki sake maimaita makamancin abinda ki ka yi a yau ɗinan hakan zai sa mu zauna lafiya! Sannan kuma maleek na bada sati ɗaya ya dawo Nigeria da zama cikin danginsa idan ba haka zan ɗauki babban mataki akanki.
"Hajiya ki yi haƙuri In-Sha-ALLAHU zan gyara maleek kuma ai kafin satin ma yana naija. Mamakine ya
kama hajiya amma sai tayi murmushi tace "Ga hanya ta nuna mata hanyar fita da yatsanta.  Miƙewa tayi zuciyarta tana tafarfasa tana shiga part dinta tacja mugun tsaki "Mtsssss! Wallahi sai na tabbatar miki da ke ba kowa bace a idon ɗanki, sai na mulke gidan nan iya son raina.
Ta ƙarashe magana gami da yin ƙwafa.

   Misalin ƙarfe goma na dare zaune yake a gefen gadonsa da alama waya yagama yi, yanayin tsigar jikinsa dake miƙewa ne yasaka shi ambaton ALLAH yana ƙara dafe kansa, arayuwarsa bai taba samun gamsuwa cikakkiya tare da maryama ba kowanne lokaci tanada uzuri wani lokaci ma sai ya cika mata jakkarta da kuɗin d ata buƙata, last time tureshi tayi ma ta ce yayi iya na kuɗinsa shi ne dalili da yasa ya yi zuciya har yau, bai ƙara tambayar hakkinsa ba, ALLAH yasani shi mutum ne mabuƙaci duk yadda yayi fushi da matarsa to tabbas sai ya sakko. Yadda yaji yanayin halittun jikinsa na canzawa ya sakashi zura silifas ɗinsa tare da ɗaukan wayarsa ya nufi shashin maryama tund aga bakin ƙofa yake jin wani ɗaddan ƙamshi yana cika masa hanci murmushi ya saki dan yasan matar tasa gwanace a gurin kwalliya da ƙamshi, har ya haye samanta ya bude bedroom ɗinta sannan ya sauke hamdallah dan ba ƙaramar sa'a yaci ba da bata saka key ba, kwance ya tarar da ita da alama bacci ya fara ɗaukarta murmushi ya ƙara saki sannan ya cire kayan jikinsa ya zama daga shi sai gajeran wandon ya bi jikinta da kallo dake daga masa hankali a duk lokaci da idanuwanshi suka yi tozali da ita nan take ya shiga, ambaton ALLAH yayi sannan yashiga cikin bargon yana mai jawota izuwa cikin jikinshi tare da sauke wani gigitaccen ajiyar zuciya, rawar da jikinsa ya shiga yi ne ya saka maryama sauri ture shi tana faɗin "what are you doing? Nace me za ka yi  Why can't sleep in peace? Ahmad ina ji yau 2nd march? Ko ka manta kai da ne mana sai on 20th? Babu damar na kwanta sai ka nemi ka ta kuramin. Cikin wata kasalliyar murya mai cike da buƙatuwa yace " Please my love ina tsanani bukatarki kada ki azabtar dani dan ALLAH, Maryama kin fi kowa sanina ahakama manage na keyi, kuma kinsan bana bin mata ko so ki keyi in fara ne? Ki taimaka min please. Fizge jikinta tayi ta tashi tana faɗin am not ready sai on 20th na gayamaka. Dan ALLAH ki taimaka.
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa tsaye , idanuwanta ta sauke a gajeran wandonsa yadda taga erection ɗinsa yasa hankalinta mugun tashi sannan cikin rawar murya tace "ko magani ka ke sha ne Abah? Idan ma shine kai kasani domin za ka karka kashe kanka ne a wofi saboda ni dai am not ready ta fita tana mai banka kofar ɗakin. Hawaye ne ya fara bin fuskarshi cikin rauni murya yace "Ya Ubangiji ka sanyaya min kayi min afuwa yaa Allah ka yafemin, ka sauƙaƙamin abinda nake ji ka yi min sauyi na alkhairi a rayuwata. Tsawon lokaci ya ɗauka kafin ya fito ya koma part ɗinsa yana zuwa bedroom ya wuce ya sake wanka tare da ɗaura alwala, ya shiga jera nafilfili gami da kai wa Ubangiji sammai bakwai kukansa.

**********

Washegari cikin yanayi na rashin kwari jiki ya tashi dashi tamkar wanda bashi da lafiya, ko kaɗan babu kuzari a tattare dashi. Misali ƙarfe goma ya fito cikin shirin tafiya office jikinsa sanye da tsaddadiyar shadda getzner royal blue in colour, cikin takonsa na ƙasaita yake saukowa downstairs kafin ya ƙarasa cikin parlourn ƙamshin design perfume ɗinsa ya gauraye parlour. Ɗaya daga cikin masu aiki ya hango tana goge tv stand a can kuma dining room ɗayar tana arranging table, cike da girmamawa masu aiki suka gaidashi ya amsa musu a takaice domin fuskar nan tashi a haɗe take babu annuri ko kaɗan ko kallon part ɗin Maryama bai yi ba ya wuce part ɗin Hajiya, a ƙaramin parlourn ta ya tadda da sallama ɗauke da bakinsa ya ƙarasa "Barka da safiya Hajiya!
Ya faɗa sa'ili da ya kai zaune akan kujerar da ke kallon wacce Hajiya take zaune akai. Ba tare da Hajiya ta amsa ba ta shiga ƙara masa kallo shi kanshi sai da ya tsalgu da kallon da take masa gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. A maimakon ta amsa gaisuwar tashi sai kawai ta buge da faɗin
   "Meke damunka?"
   "Na'am Hajiya!
Ya faɗa cike da rashin sani takamammiyar amsar da zai bata.
  "Abah!
Ta kira sunanshi shaye da toka ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa da "Na'am!
  "Zan sake tambayarka a karo na biyu ka tabbata ka bani gamsasshiyar amsa.
  "Tohn Hajiya!
Ya faɗa cikin rawar murya yana mai ƙara sadda kanshi ƙasa tare da murza yatsun hannunshi.
  "Abah meke damunka?"
Shiru ya yi na some seconds kafin ya ɗago amma bai bari suka haɗa idanuwa ba ya amsa da cewa "Hajiya yau na tashi da rashin kwari jiki gashi ina da muhimman ayyuka a gabana ina tunani a yanayi da nake ciki yadda zan yi handle ɗinsu.
   Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke kafin ta ce "Wannan bai isa ya zama hujja da za ka jefa kanka a damuwa ba neman duniya ba hauka bane ka natsu kada ka jawowa kanka wani ciwo na dabam wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zan sake ganinka cikin wannan yanayi.
Ta ƙarashe magana cike da nuna isa da ba da umarni kai tsaye.
   "To Hajiya in-sha-Allah ba za a sake ba.
  "Ka yi breakfast?"
"Eh to na dai sha tea.
Ya faɗa cikin sigar so ta yarda dashi.
   "Maganar banza tea har abinci ne da zai iya riƙe mutum ka jira yanzu fati za ta kawo maka abin kari kumallo mai ɗan nauyi wanda zai iya riƙe maka ciki na ɗan lokaci.
  Ya sake amsa mata cikin girmama wa ta shiga kwallawa Batoul kira sai ga ta ta zo sai da ta fara gaida yayan nata kafin ta juya ga Hajiya umarni ta bata da ta kawo masa abinci da sauri ta juya zuwa kitchen jim kaɗan sai ga ta, ta dawo ɗauke da ƙaton tray da food warmers a sama Batoul tai masa serving kana ta koma ɗakinta sai da ya cika cikinsa kafin ya tattara hankalinsa akanta ya ce "Hajiya jiya yara nan son zo min da buƙatarsu musanman dai Batoul.....
"Ya isa tashi ka tafi office idan ka dawo za mu yi magana.
Hajiya ta katse mishi hanzari ba tare da ya sake furta uffan ba ya miƙe haɗe da yi mata sallama ya fice ta bishi da addu'ar fatan alkhairi.
   Hamshaƙiyar taku Madam Maryama ba ita ta tashi daga bacci ba sai around 12 o'clock, cikin izza da gadara ta sauko parlour ƙasa ta nemi cushion ta kame cikin ɗaga murya ta shiga kiran Hamida ɗaya daga cikin masu aikinta wacce take a bangaren girki da bawa maigida abinci da gudu Hamida ta fito daga kitchen ta zube a gabanta "Barka da tashi Hajiya?"
  "Barka Hamida Yallabai yaci abincinsa kuwa?"
    "A'ah Hajiya asalima da sassafe ya fita.
"Mtsssss! Can ta matse mishi tashi ki zubo min abinci amma banaso mai nauyi.
   "Tohn Hajiya.
Hamida ta faɗa cikin sauri gami da miƙewa ta koma kitchen, kafin Hamida ta dawo ta ɗauki ƙaramar wayarta ta kira abokiyar ci mushinta Hajiya Nafisa ta shiga labarta mata yadda tayi da Hajiya har izuwa wulaƙanci da ta yiwa Abah a daren jiya.

Continue Reading

You'll Also Like

235K 14.9K 47
This novel featuring Amie and her childhood friend, Mahir. It's a delightful tale of friendship, lost connections, and the power of rekindling old fl...
241K 14.4K 64
𝐓𝐨 𝐞𝐯𝐞𝐫𝐲𝐨𝐧𝐞 𝐰𝐡𝐨 𝐭𝐡𝐢𝐧𝐤𝐬 𝐭𝐡𝐞𝐲 𝐚𝐧𝐝 𝐭𝐡𝐞𝐢𝐫 𝐜𝐫𝐮𝐬𝐡 𝐚𝐫𝐞 𝐧𝐨𝐭 𝐦𝐞𝐚𝐧 𝐭𝐨 𝐛𝐞 𝐭𝐨𝐠𝐞𝐭𝐡𝐞𝐫. ...
550K 35.1K 71
"Sshhhhh....." he hushed and pinned us against the wall leaving no space between us. I held onto his biceps with my hand in reflex. He shook his head...
769K 108K 39
Yaduvanshi Series #3 it is a book under yaduvanshi series. But it could be read as standalone too. Nitya Raghavendra is a telugu businesswoman earnin...