09

99 2 0
                                    

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

*009*

A fili Hajiya Nafisa ta tausaya wa Maryama dan har da kuka ta tayata amma a can ƙasan zuciyarta wani shegen daɗi take ji marar misaltuwa da son samu ne ta tashi ta taka rawa tai juyi sai dai babu halin yin hakan a gaban Maryama duk zumuɗi ta dole jira har Maryama ta tafi.
"Ba zan ɓoye miki ba Hajja Nafisa wallahi banaso talauci ko sunansa aka ambata sai gabana ya faɗi, tsakanina da talauci kiyayya ce mai dogon zango.
Maryama ta faɗa tana sharar hawaye da gefen mayafin abaya da ke jikinta.
"Haba ke kuwa Maryama duk duniya wa keso talauci? Ai shi ɗin mugun ciwo ne ko Annabi ya ce mu nemi tsari da talauci, ke fa yanzu rayuwarki tamkar tana cikin kwalele ne ba bu matuki ALLAH ne kaɗai yasan kalolin masifun da suke tunƙaro ki. Dan wallahi ko a cikin ƙawaye mu sai kin sami wacce za ta goranta miki Ido da ido musamman yadda ki ke nuna musu ɗagawa da taƙama ga ki da azababben girman kai sai kace shaiɗan..
"A'ah! Dakata Nafisa kada ki sake haɗa ni da shaiɗan daga na zo miki da matsalata dan ina tunani za ki magance min ita ta hanyar bani shawarwari managarta sai ki buge da yada min magana. Shiyasa a duk lokaci da na shiga matsala ina neman shawara tagari nake tsalla ke ki na je ga Hajja Halima. Da ki ka kira ni da shaiɗan ke wa ya kai ki shaiɗanci ke da har tsafi kina yi gaba ɗaya kin mallake mijinki kin mayar da kishiyarki wata gaula-gaula ita ba mahaukaciya ita ba mai hankali ba...
"Ke! Maryama dawo hayyaci ki banaso fallasa tun kafin tafiya tai nisa kariyar arziki nan ta fara taɓa ki, haka kawai ana zaune ƙalau za ki dinga ɗauko manya-manyan sirrika na kina fallasa wa to ahir! Ɗinki ba zan ɗauki wannan haukar ba. Ki natsuwa na lallabo miki mafita ko ki ɗauki jakkarki ki tafi gidan Hajja Halima ko ba komai za ta buɗe miki tafsir a katafaren falonta. Ta saka ki gaba tana ce miki ALLAH yace Annabi ya ce daga nan ta cika zuciyarki da imani ta hana ki nema wa kanki 'yanci.
"Hmmm! Haka ne kuma zance ki gaskiya ne Hajiya Halima ba abinda ta fi kwarewa dashi irin wa'azi saboda haka kawo taki shawara naji idan batai min ba. Na ƙara ba dan a hali da nake ciki bana buƙatar gurguwar shawara.
Taɓe baki Hajiya Nafisa tayi tana hararar Maryama ƙasa-ƙasa. Kafin ta musguna manyan ɗuwawunka ta gami da yi ƙasa da murya ta ce "Hajiyata shiryawa za ki yi mu tafi Nijar na kai ki guri wani mashahurin malami aikinsa sha yanzu magani yanzu ne. A yi miki aiki da zai sa Abah ya fasa miƙawa 'yan uwansa ragamar dukiyar dattijo, kin ga shikenan za ki ci-gaba da fantamawa abinki.
"Subhanalillah! Tsafi nima ki ke so na fara irin naki Nafisa?" To gaskiya ba zan ɓoye miki ba wannan gurguwar shawarar taki sai dai ki adana abarki idan ALLAH ya kawo wata ɓatatciya irinki sai ki bata amma ni kam la-la-la! Ba da ni ba. Haka kawai na ɗauki kuɗina na kai wa wani gardin banza.
Ta ƙarashe magana tana girgiza kai sosai kalamanta suka baƙantawa Hajiya Nafisa rai cikin fushi ta ce "kada ALLAH yasa ki bayar dama ta za ki iya bayarwa bayan ke ɗin azababben maƙo ne dake.
"Na dai ji duk abinda za ki faɗa ba zan damu ba domin na fahimci abokin zuwa jahannama kike nema.
"Ai ni dake Maryama babu bambanci domin kwaryar sama ce take dukan ta ƙasa, duk mace da bata kyautatawa mijinta bata masa biyayya ita ma masauki ta yana jiranta a jahannama.
"Na ji na ɗauka kuɗina dai ba za su je gidan mushriki ba ai ni Nafisa da na ba wa matsafi kuɗi na gara na siye supplement na gyara jikina.
"Ai a haka za ki ƙare ba ma za ki rena kanki ba sai mayyukan ki na bleaching sun ƙare jikinki zai dawo nan fari can baƙi sannan kuma karki manta a hali yanzu ten million ki ke nema da za ki yi hips and boobs surgery na ga uban da zai ba ki su.
Ran Maryama ya yi mugun ɓaci musanman da Hajiya Nafisa ta tuno mata da shimfiɗaɗe ƙudurin da ke ranta, ta kuma tabbata abinda Nafisa ta faɗa gaskiya ne bata da uban da zai ɓata waɗannan makudan kuɗaɗe, dole ta hanya Abah ne kaɗai za su fito ita ga ta ALLAH ya yi ta malalaciya duk abinda za a wahala akansa bata so shiyasa bata taɓa sha'awar kasuwanci ba. Hakazalika aikin gwamnati ma bata da ra'ayi ita duk abinda zai sa jikinta ya wahala bata maraba dashi gaba ɗaya rayuwarta ba abinda take so irin ta huta. Maryama bata damu da saving money ba duk yawan kuɗin da Abah zai bata daga sutura sai kayan gyaran jiki da turaruka take ƙarar dasu, shiyasa idan ka shiga bedroom ɗinta kamar kamfanin turare. Idan Maryama ta zauna a wuri sai tayi one hour da bari guri ƙamshinta bai tafi ba. Mace ce mai masifar so ƙamshi da ado koda yaushe tana cikin kwalliya.
Duk yadda Hajiya Nafisa taso ta amince su je Nijar amma taƙi amincewa daga ma sai suka rabu baram-baram. Dama sun saba da wuya su haɗu ba su yi faɗa ba saboda kowacce su bata da haƙuri kuma ba zai hana anjima kaɗan su shirya. A fusace Maryama ta ja motar ta ta baro gidan Hajiya Nafisa akan hanyar tai tunani bari ta je gidan mahaifiyarta tai mata magana ko za ta yiwa Abah magana ko zai fasa ƙudurin sa saboda tasan yana matuƙar jin maganar Aunty, a falon ta tarar da ita tare da mai aikinta wacce ta kasance 'yar uwarsu ce ta jini amma ko kallon kirki bai haɗa ta da Maryama ba cikin izzarta da taƙama wacce ta zame mata jini jiki, ta zauna akan cushion tana sauke numfashi, Aunty ta ɗauke ganinta akan akwatin talabijin ɗin da take kallo ta mayar kan fuskar Maryama rai ɓace ta ce "Ke kuma daga ina kin wani shigo min falo ba sallama balle na sami arziki gaisuwa ko Lami da ta gaida ki ba ki amsa ba, sai kace ba gaba take da ke ba. Wai Maryama sai yaushe za ki yi hankali kina girma kina cin ƙasa.
Ɓata fuska Maryama tayi gami da faɗin "Ba kinsan irin damuwa da nake ciki ba Aunty shiyasa ki ke min korafi.
"Kowacce irin damuwa ki ke ciki dole ki yi mana sallama kamar yadda addini musulunci ya tanadar dan nan ba gidan arna bane.
"Dan ALLAH Aunty ki ajiye zance sallamar nan a gefe ki saurare abinda na zo dashi fisibilillahi! Na zo da tawa matsala kina ƙoƙari ƙara min wata.
"Wacce matsala ki ke ciki banda reni wayau da kika saba dashi wallahi bara ki ji in gayamiki ba zan ɗauki wannan sakarci ba tsofai-tsofai dake ki shigo min ba sallama.
Duk cikin maganganu Aunty ba kalamar da ta daki Maryama irin kiranta da tsohuwa da tayi kasa magana tayi sai kallon Aunty take yi, kafin a kufule ta figi jakkarta duk kira da Aunty take mata ko waigo wa bata yi ba ballantana tasa ran za ta dawo.
"Shikenan ki fi ruwa gudu sakarya banza da wofi wacce batasan inda yake mata ciwo ba.
Aunty ta faɗa tare da ja guntun tsaki.
_____________
Sai misali ƙarfe 11:30am Barrister Suleiman da Surayya suka baro gidansu Surayya zuwa lokaci Baba ya farfaɗo jikinshi ya yi kyau sosai har Mummy ta dama mishi kunu gyaɗa ya sha. Akan hanyar su ta komawa gida Surayya ta kalli Barrister ta ce "Sweetheart mu biya asibiti naga hali da Salma take ciki.
"Whats? Salma fa ki ka ce Surayya?
"En!
Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba.
"Me za ki je gani ga yarinyar da ta zaɓi ta bijerewa iyayenta akan wani ɗan iska marar mafaɗi.
"Sweetheart duk abinda Salma ta zama 'yar uwata ce jini jikina hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar!
"Wallahi sai dai in hannu bai dame ka da ɗoyi ba domin ba ka sani lokaci da za ka yanke shi. Surayya kin sani ina girmama duk wani ɗan uwanki amma akan Salma bana tunani zan iya miki kara. Domin na tsane ta tsanar da ko sunanta banaso a ambata min. Ni a tunanina ko mutuwa Salma tayi ba za ki yi gaggawa zuwa ga gawarta ba...
Gani yadda ta tsare shi da idanuwanta da suka yi jajir a dalili kukan da tasha ga fuskarta ta bayyanar da rashin daɗi maganganun da yake faɗi sai kawai ya haɗiye raguwar kalamansa, ba tare da ya sake magana ba ya karkata akalar mota zuwa asibiti room 10 shine number ɗakin da Salma take ciki bakunansu ɗauke da sallama suka ƙofar ɗakin, umma Habiba tana zaune akan rubber chair gaban gadon da Salma take kwance, ta rafka tagumi tana kallo ikon ALLAH wanda yafi gaban mamaki tun sanda Salma ta farfaɗo take ta faɗar maganganu marasa daɗi akan Baba da Umma Habiba ta nemi taka mata birki ta wani hayyaƙo mata, shiyasa ta ja bakinta tai gun! Domin ba za ta bari yarinyar da aka haifa a tafin hannunta ta zage ta ba. Umma ce ta amsa musu sallama a sanyayye duk shigowar Barrister Suleiman da Surayya bai sa Salma tai shiru ba sai ma ƙara sauti maganarta "Wallahi idan akan Zeed Talba ne na shirya gagarumin shiri kodai ni na mutu ko kuma wanda ba sa sonshi su mutu akan wane za a hanani aure wanda nake so? Na ga dai ko shi Baba aure soyayya ya yi shi ne ni dan tsabar baƙin ciki zai hanani mallakar abinda nake so.
Tun shigowa su Barrister Suleiman ya gaida umma Habiba ya koma jikin bango Ya jingina gami da yi folding hannuwanshi, bai kalleta amma duk abinda take faɗa yana ji yayin da wata irin tsanarta ke bul-buluwa daga can ƙasan zuciyarshi, idan aka bashi dama zai iya kashe yarinya nan har lahira.
Surayya ce ta tako da sauri ta nufi gadonta tana faɗin
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Salma kanki ɗaya kuwa?"
"Bansani ba sai ki zo ki shafa ki ji aiki banza aiki wofi wallahi ina bari asibiti nan zan haɗa kayana na bar muku matsiyaci gidanku, da babu komai cikinsa sai zalunci.
"Salma!
Surayya ta faɗa gami da fizgota cikin tsanani ɓaci da takaici ta balla mata mari, a kufule Salma ta ɗago dafe da kunce tana Surayya kafin ta ce "ALLAH ya isa muguwa baƙar azzaluma....
Tun kafin Salma ta ƙarasa magana Barrister Suleiman ya yi kukan kura ya damƙi wuyanta ya danne akan pillow ya shiga wanke mata fuska da maruka. Sai kakari mutuwa take yi gashi Umma Habiba da Surayya sun kasa kwatar ta a hannunshi sai cewa yake yi "ku barni na kashe ta ko ba komai nayi jihadi meye amfani bari iri-irinta cikin al'umma?"
Gani haka yasa Umma Habiba ta kwasa da gudu ta fita neman taimako domin da gaske Barrister Suleiman yake yi kashe Salma zai yi sai dai duk abinda zai faru ya faru.

#Jeeddah Aliyu
#Nana Diso
#Abah
#maryama
#Surayya
#Barrister Suleiman
#Salma
#Team Tagwaye Biyar

*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️

GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA
GUDA BIYAR 1500.

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)

ACCOUNT NUMBER

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis

KATIN WAYA

+234 706 528 3730

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now