10

105 4 0
                                    

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

*10*

Kafin umma habiba ta dawo da likitocin barister har ya sumar da salma! Yana gefe sai faman haƙi yakeyi, gabadaya annurin fuskarsa ya gushe ita ƙanta surayya ba ƙaramin tashin hanƙali tashiga ba ganin yanayin da bata taba gani ba atare da mijin nata. Dr be yayi ƙan salma suķa shiga bata taimakon gaggawa, barister kuwa barin daƙin yayi sannan ya figi motarsa yabar asubutin, aduniya bai taba tsanar abu irin yarinyar nan ba, tabbas dabadan ganin ta dauƙe numfashinta ba to dakuwa sa yayi tsautsayin da zaijawo masa danasani. Tunda surayya taga yanayin mijinta gaba daya zazzabi yarufeta hakan yasata zama tayi shiru,Bayan kusan mintuna talatin dakyar take jan numfashinta maganarta ta farƙo shine " Ko kasheni zakuyi baku isa ku rabani da yazeed talba ba azzalumai nayi danasanin kasancewa cik'in ku, surayya ce tamike duk da irin zazzabin dake damunta tayi kanta umma habiba tarike hannunta suka fito harabar asubutin, " Surayya duƙa ko zagi bashine zai gyaramana salma ba addu'a ce, danAllah ita yakamata muna tayata da'ita banason wannan duƙan yanzu kishige ga driver ya maidake gidanki karki saka wata damuwa aranki kina dai ganin yanayinki ko." Kukan da surayya tarike ne yafara zubowa akan ƙwancinta, batare da tace komai ba tafita domin bin driver yakaita gidanta zuciyarta kamar ana hurawa.

Mahaifiyarsa ce ke zaune baƙin gadonsa da alama wani mugun abun yakeyi dan daga ganinta yayi saurin rufe wayarsa, amma saboda saƙaci irin nata yasa batabi takansa ba saboda ba wannan ne gabanta ba kuma koma dai menene ai free world muke yagirman da zaiyi abunda yaga dama." Cikin dan tsoro yazeed yace " Why kika shigon daki?" " yazeed why are you like that? Why yazeed ? Bazaka rabu da wannan yarinyar ba ga yaran manya nan ka aura?" Murmushin gefen baki yayi yace " That girl is my queen and babu wanda ya'isa yahanamu aure kamar yadda nagayamiki next week daurin aure bazan kara maimaita miki ba idan zakiyi even is all fine but am not going to attend any one ko baby salmata." " Babu komai son abunda kakeso shi nakeso what about lefe and kayan gidanta." "Karki daamu zanyi handling komai." " Okay kawai tace tafita."

Zazzabin da yarufe surayya tunda ta dawo bata bi ta bangarensa ba part dinta tayi taje ta kwanta dan tabbas zata iya zubewa itama, har karfe biyar baiji motsinta ba kuma yaga shigowarta amma baijita ba abunda ya tayar masa hakan yasashi saurin zuwa part dinta bata dik dakunan nata sai wani dak'inta da yasan batafiya kwanaba yana budewa yaganta tana rawar sanyi wani cikin zafin nama yaƙaraso zuciyarsa na masa wata ƙalar tafasa, innalilahi wainna illahirrajiun surayya menene?? Menene? Ke wallahi wallahi kika jawomin asara saboda wannan ƴar iskar yarinyar wallahi sai na baki mamaki, batasan sanda ta kamo hannunsa ba wani zafi yaji hakan yasashi kiran doctor babu shiri, gaba daya yakasa zama zuciyarsa zafi yaa Allah yafada yana mai rungumar surayya addu'a yashiga jira mata.

Bayan wasu awanni Rungume barister yake da'ita wani sabon ƙaunarta ke yawo cikin jinin jikinsa, my love yafaɗa yaana ƙara rungumota tare da sumbatar bak'inta, kallonsa surayya tayi tana murmushi. " ina kaunarka barister na." Kallon cikin idonta yayi tsigar jikinsa tana zubawa." " My surry kinsan Allah kaunar da nake miki bazan iya misiltawa ba kiga yadda kike kuladani kike bani kulawa my love duk wataƙalar soyayya kauna da kulawa kina bani ubangiji yasaukeki lpya yabani ikon farantamiki, danAllah ina neman alfarma agurinki." Dariya tayi duk da zafin jikin datakeji tace " kawuce alfarma sai dai umarni my man." " To danAllah kidaina saka lamarin sha shashar yarinyar nan aranki kinji." " Insha Allahu man zan kiyaye banason kana shiga damuwa." " Allah yayi miki albarka mata tagari a hankali ya sumbaci bakinta.

Duk yadda baba yaso ya manta da lamarin salma amma ina abun yafaskara idan yatuna abunda kunnansa yaji masa sai hankalinsa yakuma tashi, umma ce taturo kofa tashigo daƙin nasa, zama tayi kusa dashi tace " DanAllah ina bukatar taimakonka." Banason yiwa mumyn salma magana yanzu danAllah baban salma kayiwa salma aure kaji? " Dawa zan mata? " " da yazeed talba?" DanAllah kada ki baƙanta mini, bazan mata ba ita ta haifeni?" " haba baban salma haba alhaji na wannan shine masalaha garemu duka yarinyar nan ikrarim guduwa takeyi wallahi danAllah, kabarta ta aure wanda takeso mu bita da adduar alkhairi." " tashi kibani guri naga alamarin naki harda kishi danda diyarki da kika haifa ce wallahi nasan bazaki barta ta auri dan gidan talba ba, amma saboda ɗiyar kishiyarki ce ai gashi kinyi gaba akai." " Murmushi umma habiba tayi sannan tace " Allah yayafemaka baban salma da wannan maganar da kayi wallahi rashin bata yazeedu sai yazame mana matsala baban salma batashi shine mafi alkhairi agaremu baki daya, sannan salma ban taba yimata ƙallon bani na haifeta ba bama itaba duk yaran mumy dan banda wannan muguwar zuciyar wallahi kakuma sani idan diyata ce wacce na haifa salma sai inda ƙarfena yakare gurin ganin an aura mata yazeedu dan shine mafi alkhairi tunda har takaita da jaye jayen magana da iyayenta, shi kuma yaron da bayaji magana maganinsa kakeyi da wuri don ko ba asiri yazeedu yayiwa salma ba to tabbas akwai wahallalen so acikin Al amarin nata wanda bayajin magani ko duka ko wa'azi bayajin fada sai addu'a kaɗai idan kuma har yanzu kallon son ranka kakemin to mujima dayawa nikam nafita sai anjima.

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now