ALMAJIRA ✔

By DielaIbrahim

1.2K 70 5

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She find... More

Prologue
02
03
04
05
06
07
08
09
10
11
12
13
14
15
16
17
AL'ADARMU
18
19
20
SOFIA

1

114 8 0
By DielaIbrahim

SABUWAR SHEKARA SABON SALO
WACCE KUKA FI SANI DA FADILA IBRAHIM TA ZO MUKU DA SABON LABARI MAI SABON SALO

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

In the name of Allah, The beneficient, The merciful

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai

_GODIYA_Ina godiya ga Allah maɗaukakin sarki, Mai kowa da komai, Sarkin da babu kaman sa duk faɗin duniyar nan, Ina kara godewa Allah da ya ara min lokaci kuma ya bani ikon rubuta wannan littafi don faɗakar da al'umma baki ɗaya.

Allah ya bani ikon isar da sakon da yake cikin sa, Allah kuma ya baku ikon karantawa.

ALMAJIRA Sabon Salo
Free page

LABARI DA RUBUTAWA FADILA IBRAHIM

01

______________________________________

SHINFIƊA

Kauyen Bakura, wani kauye ne ko ince wata "ƙaramar Alkarya"da yake tsakanin Zamfara da Sokoto wanda kauyen Bakura yana karkashin jihar Zamfara state.

Mutanen Garin mafi a kasarin su Hausawa ne sai Fulani kalilan, Babbar sana'ar mutanen garin shine Noman rani duk dama karamin gari ne ba kasafai suka cika yin kasuwanci ba.

Bakura local government suna da makarantun allo ta almajirai, wanda mafiya a kasarin yaran garin, samari da ƴan mata, yara yara duk shi suka fi zuwa. Tsiraru ne ke zuwa makarantar bokoko wanda sukai mishi lakabi da "karatun nasara"

************************************
BAKURA LOCAL GOVERNMENT
ZAMFARA STATE
14 AUGUST __________________________
10:00am

A bamu na Allah "babiya Allah"
A bamu na Allah "babiya Allah"
Muna bara a bamu don Allah
"babiya Allah"
A bamu don Ma'aikin Allah
"babiya Allah"
A bamu don Mahaliccin mu
"babiya Allah"


Babban titin dake garin Bakura ta hanyar da zai sadaka da babban masallacin juma'a wanda yake kwalli ɗaya tak a cikin garin.

Cike yake da Mabarata wa'inda babu ruwan su, sudai bara kawai su keyi daga wannan kusurwa zuwa wancen kusurwa.

Mabaratan a kalla ba'a kasari ba sun kai mutane ashirin ko fiye da haka ma kowa da irin lalurar da yake ɗauke da ita, wasu lalurar gaskiya wasu kuma lalurar karya,
Shiyasa suke bara don samun kuɗi da kuma abin da zasu ɗan ci su da iyalensu, duk dama da muryoyi ɗaya ko ince a tare suke jero wakar barar sai dai wata zazzakar murya wacce ta fi kowacce murya daɗin sauraro, kana iya jiyo muryar amma yawan al'ummar dake zazzaune wasu suna tsaye ba lallai ka gane wacece mai muryar ba.

Gefe ɗaya kuma ko in ce tsallaken titi masu talla ne, tallan abinci kala da iri, masu soya kosai da kunu, masu awara da dai sauran su wanda mafiya akasarin mabaratan suke musu chiniki daga safe har dare.

Wata babban mota ce kirar toyota baka wuluk ta kunno kai a daidai layin mabaratan, Nan da nan wasu daga cikin mabaratan suka nufi inda motar take, kasancewar ko da yaushe idan ya zo wuce wa yana ra ba musu ƴan hamsin hamsin sabbi dal.

Hakan yayi daidai da tasowar wata matashiyar yarinya wacce kallo ɗaya nayi mata na furta Ma Sha Allah tabarakallah, Hakika duk da munin kayan da ta sanya amma sai da kyau mai sunan kyau ya bayyana a fuskar yarinyar, Baka ce ba wai baka wuluk ba, za'a iya sanya ta a matakin chocolate color kirar fulani gare ta, sai dai bamu san fulanin ina ne ba.

Saman kanta kaɗai idan ka kalla zaka gane yawan gashin dake kunshe cikin kallabi duk dama suman gaban kan ta ya kwanta lub lub yayi mata saje don kuwa shi ya kara fito da ainahin kyan nata. Ta kanannaɗe suman kanta sannan ta sanya wani yagulallen mayafi ta rufe kan, tana sanye cikin shiga irin ta mabarata. Kaya ne zaka gansu yagaggu kuma zumbula zumbula irin sun masu yawa ɗinnan, kafafuwan ta na sanye cikin wasu shamulallun silipas wanda suka tsufa suka shamule har kana iya hango hujewar su ta tsakiya idan ana tafiya, yayin da saman silipas ɗin ya tsinke yafi so a kirga ana ta ɗaure shi da leda.

Babu abin da ke damunta sai tsagwaran talaucin dake manne a jikin ta, abin mamaki anan shine yarinyar dai ba zata wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwai ba amma ɗauke take da cikin haihuwa wanda ya kai wata biyar zuwa shidda....Sa'annan tana goye da wata karamar yarinya wacce dai ba zata wuce shekara uku ba a duniya.

Ta mika siririn hanun ta, aka sanya mata naira hamsin ita ma yayin da ta dunkule tana ni yar barin wajen sai taji wata ƴar uwar ta mabaraciya na cewa,"*HADIZA* ana kara miki kuɗin, ai da sauri ta juya ta kalli mai rabon kuɗin sai yake cewa "Anshi wannan na ƴar ki ne"

Ta sanya hannu ta sake karɓa ta buɗe baki tayi godiya sosai anan na sake yarda ita ce mai ɗauke da wannan zazzakar muryar, kuma kenan yarinyar da ta goya ma ƴar ta ce?

Ta ɗan share zufan fuskar ta da dattin tsummokaran kayan ta, Ta zauna tana huci tsabagen gajiya da goyon yarinyar, a haka ta taka tsallaken titi ta mikawa wata mai kosai tace "Ban na hamsin ladiyo"

Ladiyo ta buɗe robar ta samo leda fara ta sanya mata kosan hamsin tana cewa"kin ga na sa miki gyara"
"Hadiza tace"To godiya nike, kar ki sanya yaji" bayan ta kar ɓa sai ta koma in da take ta kunce goyon da tayi tana cewa,"Sannu Sofia, anshi kosai ki ci"

Sofia ta karɓa da sauri sakamakon yunwar da ta addabi cikin ta don rabon ta da abinci tun jiya da yamma, Sofia na ta cin kosai taga Hadiza ta yi tagumi tana kallon ta, sai ta ɗauko guda ɗaya ta sanya wa Hadiza a baki amma Hadiza sai taki karɓa tana share wasu kwalla da suka cika mata kwarmin idanuwan ta.

Ta ce,"Kanwata Sofia kin fi ni bukata ki ci bai da yawa"

A hankali yarinyar ta furta Yaya ke ma ki ci mana, me yasa ki kuka Yaya?

Hadiza ta zuba wa Sofia idanu ta na tuna irin wahalar rayuwar da suke ciki rayuwar bara, kuma basu san yaushe zasu dena wannan rayuwar ba tun da abincin da zasu ci ma gagararsu yake, tufafin kirki ma basu da shi, babu iyaye basu da kowa sai Allah basu da wajan kwana sai rakuɓe rakuɓe yau su kwana anan gobe su kwana acen, ta sake goge wani hawayen daya zubo a kumatun ta, wannan karan kanwar ke share mata duk da karancin shekarun kanwar amma hakan bai hana ta fahimtar halin da suke ciki ba.

Ta shi tayi ta na cewa "Ya kamata muje muyi bara Sofia, Ta duka da kyar ta na cewa hau baya na goya ki ba zan iya ɗaukar ki ba" kasancewar Sofia tun da aka haife ta, data fara girma sai bata tafiya ko miye dalili ohooo.

Sofia ta tausaya wa yayar tata,duk da karamar yarinya ce amma ta san cewa Yayar na ta na wahala sosai, ta mika hannu ta goya ta, suka shiga cikin mabaratan suma suna ta bara a haka har Allah yasa ta samu naira dubu biyu.

Yamma likis suna zaune a bakin titi, babu sallah babu salati sai bara kawai, sai alokacin ta samu ta sayi ruwan pure water leda biyu, da shi tayi amfani tayi alwala ta kwance kallabin ta bayan ta sauke Sofia ita kuma ta fuskanci alkibla ta jero salloli biyun da ba tayi ba, tana zaune a wajan aka kira magriba, ta tashi ta gabatar da sallar magriba......Tana kallon wasu mabaratan na tafiya masaukin su, yayin da wa su kuma suna zazzaune saboda babu wajan kwana.

Dafa gefen cikin ta tayi sakamakon rashin cin abin ci tun safe sai ya ɗaure yana mata ciwo, da sauri ta saɓa Sofia a baya cikin karfin hali ga ciki a jikin ta, da kyar take iya daga kafa tayi tafiya wanda da taimakon bangon masallacin ta samu kwarin gwiwar dafawa tana jan kafa har ta isa gun wata mai abinci ta durkushe kasancewar cikin ya kulle ba za ta iya mike wa tsaye ba, ta samu ta cire naira ɗari biyar daga cikin kuɗin data samu yau ta mika wa yarinyar tana cewa,"Sa mana taliya da wake na ɗari biyu daban na ɗari daban sai ki sa mana kunun tsamiya na sittin ki bamu ruwa da sauran canjin.

Tun kafin matar ta gama sanya sauran HADIZA ta dulmiya hannun ta cikin robar yarinyar ta yamusa taliyar tana ci tana bama Sofia, tun suna ci suna korawa da ruwa har dai suka cinye roba ɗaya suka sha kunu sannan ta karɓi ragowar na ɗarin suka tafi da shi da sauran ruwan su.

A hankali Hadiza ta furta bawan Allah sai yanzu kake motsi tun safe, wata kil ma yunwar ce ta dame shi shiyasa bai yi motsi ba tun safe....Hadiza ta ce wai wannan wacce irin rayuwa ce muke cikin ta, Allah ka kawo mana ɗauki" Ta faɗa tana share kwallar dake sauko mata saman kumatu.

Wani ɗan rumfa naga ta nufa ta zagaya ta bayan rumfar falangen ta ɗauko wani kullin tsummokaran su, Shimfiɗa tayi musu a kasa suka zazzauna duk da suna jin sanyi amma ya zasuyi nan ne kaɗai mafakarsu koda kuwa ruwan sama ake yi nan suke zama suyi cirko cirko ruwa na ambaliya a rumfar suna tsaye komin dare har sai ruwan ya tsagai ta, basa baccin kirki idan ana ruwan sama.

To yau ma dai kamar kullun an jera kwanaki uku kenan ana samun ruwan sama kuma duka sai cikin dare ake yi....yau ɗimma kamar hadari ne a garin, dama yau da asuba da ta nemo bloo/block wanda wani bawan Allah ya bata guda hudu kyauta ta zo ta rurrufe hanyar ruwan ta sanya wani zanin ta tayi musu labule ta kunce kullin kayan ta ɗauko aci bal bal, ta kunna musu, Sannan ta gabatar da sallar isha'i tayi addu'o'in da ta saba kafin ta janyo ƴar kanwar ta, ta rungume ta bayan ta lulluɓe su da wani zanin kuma don ana sanyi da daddare ba kaɗan ba.

Abin da yasa suke kwana a wajan saboda rumfar wajan yana kallon kofar babban masallacin garin wanda sauran mabaratan suna gefen masallacin maza da mata annan suke kwana, duk dama an hana amma hakanan aka kyale mu saboda idan bamu kwana wajan ba ina zamuje irin da bamu da iyaye, nima wajan samari masu zaman ban za ne shine na samu nike kwana tun bayan zuwan mu garin kimanin wata shidda kenan.

**********************************
RAFIN GUZA, KAWO

KADUNA STATE

Garin kaduna kamar yadda wasu suka sani gari ne mai yalwan mutane, bariki ana yi masa kirari da garin kazo nazo, Kaduna garin gwamna a turance kuma *Center of learning* Kar kuga laifi na because anan marubuciyar ku tayi wayo....back to business.

Karkashin Gadar kawo kowa yasan akwai mabarata da yawa wanda wasu  daga ciki anan suke matashi su kwanta idan dare yayi...dayawa mafi akasarin mabaratan basu da matsuguni wato dai basu da gidaje na kansu da zasu koma su rintsa, da yawansu sun zo ne daga garuruwa daban daban wasu kuma anan garin kaduna suke, wasu suna da gidajen amma basa komawa saboda suna ganin kamar idan suka bar wajan za a raba kuɗi basanan shiyasa sai su kwana abin har ya zame musu jiki suna yawo da tsummokaran su ba wanka, da yawan su ba alwala bare sallah, kuma babu ilimin addini bare na boko....da wannan rayuwan wasu suke samun ciki kuma su haife shi a wannan wahalar shima ya girma da son kuɗi ya girma yana bara.....wallahi wasu daga cikin su zaku ga babu abin da suka rasa na rayuwa dai dai gwargwardo amma sai kaga sun fito bara, dole dai sai anyi almajiran ci, wasu kuma ba laifin su bane halin rayuwa ne ta jefa su suke yin almajiran ci kamar yadda idan kuka biyo ni zakuji dalilin rubuta ALMAJIRA SABON SALO.

Cikin Kawo akwai wata unguwa mai suna Rafin guza idan ka shiga cen asalin rafin guza akwai tsofin gidaje na ginin laka wanda akalla an jima da gina su a wannan wajen a haka kuma na hango wani matsakaicin gida daga gefe wanda kofar shiga ma babu anyi amfani da kara aka kewaye gidan, tamkar dai muna kauye amma baza a kira wajan da kauye ba tun da suna cikin gari ne, kawai dai gidajen su ne suka tsufa.

Gidan ginin laka ne sosai, Na kutsa kai na shiga ina mai kwaɗa sallama anan na ci karo da ɗakuna guda biyu sai barandar ɗakunan wanda suke kallon yamma, sai ban ɗaki dake gefe an kewaye shi da kara, sannan sai randa na kasa wacce aka binne su manya manya guda uku ko wanne da moɗar ɗiban ruwan...daga gefe kuma ta hanyar ɗakunan anan naga wata karamar bishiyar gwanda wacce kasanta wata randa ce sai tulu, da alama wannan keɓantaccen ruwan shan su ne...tsafta a gidan ba a magana saboda komai kal kal babu alamar yaro a gidan.

Na zuba idanuwa ina son ganin mamallaka gidan, Idanuwa na ne suka min tozali da dattawa guda biyu Mace da Namiji su biyu sun fito reras suna rike da sanda hannu ɗaya Namijin yana musu jagora, ita kuma tana rike da tabarmar kaba a ɗayan hannun nata.

Dattijon mutumin yana sanye cikin shiga ta farin kaya, Dogo ne kuma fari tas kamar balarabe ga wani kwantaccen saje duk da tsufan da yayi , kana iya hango kyau mai sunan kyau a tare da mutumin.
Kayan dake jikin sa sun canja launi daga launin fari zuwa wani kala daban, duk sun tsufa sun sha jiki ga shi sun yayyage...yana rike da wata sanda doguwa wannan sandar ita ce dai ganin sa domin kuwa shi ɗin makaho ne baya gani, ya na ta tafiya yana dogara sandar sa har yazo wajan da langar ruwan su yake hannu yasa yana lalube har ya samu moɗar ɗiban ruwan da karfin sa ya damke ta sannan ya laluba kasa ko zai samu ƴar butan su, da ikon Allah ya ci karo da wata fatattakiyar buta duk ta fashe ta huje a haka ya kama ruwa sannan ya ɗauro alwala ya nufi kofa don zuwa masallaci.
 

Dattijuwar macen ita ma makauniya ce ba ta gani, fara ce sol kamar dai mijin nata sai dai ita tafi shi haske nesa ba kusa ba, tana da ga shi mai laushi wanda ya sauka har gadon baya.
Tana sanye cikin shiga riga daban zani daban sai wani chukurkuɗaɗɗen hijabi wanda ya yamutse ya tsufa sosai, ba laifi ya rufe mata jiki don ya sauka har kafafuwanta, itama dai sallar magriba ta gabatar...ta zauna tana lazimi.


Ko da ya dawo nan ya iske ta ya zauna shi ma,
Ta ce"*Baffah* sannu da dawowa"

"Yawwa sannunki *Anna* Fatan kin mana addu'a? ya tambaya yana ɗan lankwasa kai alamar yana jiran amsar ta.

"Tayi murmushi wanda ya kara fito da asalin kyawun fuskar ta, lallai ita ɗin kyakkyawa ce ajin farko, Muryar ta mai daɗin sauraro tana cewa,"Kullin ai bana manta wa da burin mu kamar yadda kai ma na san kake daurewa kana yi mana addu'a haka zalika nima na jajirce wajan ganin na koka wa Allah bukatar mu, uhmmm ta ɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa,"*Baffah* na san mun ɗau tsahon shekaru a haka kullin muna rokon Allah da ya biya mana bukatar mu, Amma har yanzu shiru, Ina da yakinin wata rana burin mu zai cika,ko rayuwa zata canja mana.

Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce,"Anna kwarin gwiwar ki ita ce take kara kwantar min da hankali, In Sha Allah, Allah bai manta da mu ba kuma muma zamu cigaba da mika masa bukatun mun"

"Allah yayi jagora" Cewar Anna sannan ta buɗe musu samira tuwo ne miyar kuka ta ce,"Muci abinci *Baffah*"

Suka dulmiya hannayen su, bayan sun gabatar da bismillah, suka ɗaura da cin tuwo suna yi suna hira abin su gwanin ban sha'awa dai.

______________________________________

TO WAI SU HAKA SUKE RAYUWAR SU MAKAFI NE FA KUMA SU KAƊAI A GIDA,KU KASANCE TARE DA FADILA IBRAHIM TARE DA DANNA MIN LIKE HAƊE DA RUBUTA COMMENT DON TABBATAR DA CEWA LABARIN YA FARA NISHAƊANTAR DAKU.

200 naira kacal zaku biya  dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

Continue Reading

You'll Also Like

31.7K 889 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...
2.9K 315 67
labari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya m...
1.7K 138 10
labarine da ya kunshe soyayya tausayi kishi
1K 27 8
ADAM da BIE mata da miji ne da suka yi auren soyayya, kamar kowanni aure TOGETHER FOREVER suka yiwa junansu alƙawari, sai dai bayan shekara goma Bie...