HAWA DA GANGARA

By KhamisSulaiman

927 40 0

Labarin wasu larabawa ne marayu wadanda suka shigo duniya da kafa daya kafin su sako dayar. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
15 END

14

45 2 0
By KhamisSulaiman

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                           *page 14*

      Da daddare Yasir da Yasira da Yusrah da Shukrah da Badrah  suna cikin cin abinci sai Yasir yace " Gobe Zayyan da Rayyan zasu dawo sun gama karatun degree dinsu na daya, zasu hawo jirgin safe ne don haka da wuri zanje na dauko su a airport"

      Yasira tace "Yaya zan rakaka mu dauko su"

      Yasir yace "To shikenan Allah ya kaimu safiyar da rai da lafiya"

      Yusrah tayi farat tace "Ai kwa nima sai naje"

      Shukrah tace "Nima fa zan je yaya"

      Yasir yace "To iyayen gasa! in dai ku ka ji anyi maganar fita waje, jikinku har rawa yake ku lallai a fita da ku kamar wasu yara, idan kun hakura ai zaku gansu tunda cikinku zasu dawo da zama, ba wai baki bane, ba kuma rakasu zamuyi suyi tafiya ba, dawowa suka yi daga tafiya in ku kayi hakuri kuna zaune zasu dawo su sameku"

       Yusrah tace "A'a mu dai gara muje mu tarosu kaga ma a ce suna 'yan'uwa  masu son su"

       Yasir yace "To da wa yace basu da yan'uwa masu sonsu?"

       Badrah ta kalli Yasir tace "Kaima ka rabu dasu mana da maganar, su basa gajiya da surutu, idan zaka je dasu kaje dasu, idan kuma ba zaka je dasu ba ka gaya musu su hakura"

       Yasir yace "Yauwa Ummi ki sa masu aiki su dafa musu abinci irin wanda suke matukar so a tarbe su dashi"

       Badrah tace "In dai wannan ne ka dauka ma kawai an gama, Allah dai ya kaimu goben lafiya"

      "Amin"

      Da sassafe Badrah tasa masu aiki suka gyara gidan fiye dana kullum, sannan suka kama shirin aiki kayan kwalam na ciye ciye da shaye shaye.

      Da misalin karfe bakwai na safe Yasir ya fito da shirin zuwa ya gaida Badrah, kawai sai yaga Yasira da Yusrah da Shukrah a zaune a falo kowacce tayi kwalliya ta dau wanka, suna ganinsa sai su fara rige rige wajen gaidashi, shi kuma sai ya tsaya kawai yana kallonsu.

      Yasir yace "Lafiya dai na ganku a nan a zaune kun wani kwalliya kamar masu zuwa wajen zaben sarauniyar kyau?"

     Yasira tace "Yaya ka manta ne da dauko su Rayyan a airport jiya fa da wuri kace zamu tafi"

      Yasir yace "Au wai dama saboda zuwa Airport din ne ku kayi wannan kwalliya, don kusa idan mun je a dinga kallonmu, wasu ma suce kalli wani ya kwaso mata yana tallansu, ko tallan kanku kuke?"

       Yusrah tace "Haba Yaya wane tallan kai kuma? mu ai mun siyar tunda muka same ka, ban san ko Yasira ba itace a kasuwa"

       Yasira tayi farat tace "To nima din na siyar, sai dai ki sami wata ki gaya mata haka!"

       Yusrah cikin yanayin tsokana tace "Au kema kin siyar? to wa kika siyarwa? waye shi da bamu sanshi ba?"

       Yasira tace "Ai ba lallai bane sai kin sanshi, tunda dai ni na sanshi kuma yayi min ai hakan ma ya wadatar!"

       Yusrah tace "To! waye wannan kuwa? ko dai wannan Mas'ud din ne abokin yaya, mayen kallonki kullum idonsa yana kanki"

      Yasira tace "Idonsa yana kaina ke kuma idonki yana kansa ko, don in ba haka ba ta ya kika san yana kallona?"

      Yasir ya katsesu da cewa "Ke dahalla ku saurara"

      Shukrah ta kalli tace "Yaya jiya kace da wuri zaka je dauko su, amma har yanzu gashi baka shirya ba"

      Yasir yace "Saboda nace da wuri shi yasa ku ka shirya da wuri ku ka zo ku kaci dako, to ba yanzu zasu zo ba jirginsu sai karfe goma zai sauka"

      Duk sai suyi sakato suna kallonsa, kawai ya wuce su ya nufi dakin Badrah, bayan ya gaishe ta ya fito ya yazo ya wuce su ya koma part dinsa. Su kuwa a nan suka zauna har misalin tara da arba'in sannan Yasir ya fito suka tafi, goma saura minti goma suka isa Airport din, don haka basu wani dade da zuwa ba misalin karfe goma da minti takwas jirgin ya sauka, su Zayyan da Rayyan suka karaso reception suka wadanda suka zo tarbarsu ai sai murna da farin ciki, daga karshe suka rankaya suka fito suka hau doguwar motarsu suka nufi gida,  Yasira da Yusrah suna can baya, Shukrah da Rayyan suna tsakiya, Yasir da Zayyan suna gaba.

      Yasir ya kalli Zayyan yace "Kaga yadda ku kayi kiba kuwa kumatunku sunyi bula bula sai kyalli suke, kamar ba wadanda suka a makaranta ba"

      Zayyan yayi murmushi yace "Ai yaya duk wanda yake da yaya kamar ka to ko a kurkuku yake rayuwa kiba ya gama yinta koda baya so"

      Rayyan yace "Ai wato yaya babu abinda zamu ce maka sai dai Allah ya saka maka da alkairi duniya da lahira"

      Yasir yace "Kai meye haka? ai tsakaninmu babu godiya, bani da wadanda suka fiku, idan banyi muku ba suwa zan yiwa?"

      Nan dai suka yi ta hira a motar suna tafiya har suka kai gida, da suka je gidan ma haka suka zauna suka dora da wata hirar har da Badrah.

       Badrah ta kalli Zayyan da Rayyan, tace "Gaskiya kasar nan da ku kayi karatu ta karbeku, kunga kibar da ku kayi kuwa? ko bakwa duba madubi ne?"

       Yasir yace "Nima abinda nace musu kenan, sunyi kiba sun kyau abin su, kamar ba wadanda suke karatu ba duk 'yar ramar nan ta karatun exam su ba suyi ba"

        Rayyan yace "Ai Ummi Yaya ya shagwaba mu kamar 'ya'yan sarakai muke a can kasar komai yi mana ake karatu kawai muke, an kama mana gida babba na alfarma ga masu aiki su suke mana girki da wanki da gyaran gida da aike idan zamuyi, ga masu gadi da securities ga motoci na kasaita da driver, abinci kala kala kuwa ai abin ba magana don fadama fatawa, kai Ummi ai wani abin ma baya faduwa, sai dai muyi fatan alkhairi ga Yaya da fatan gamawa da duniya lafiya"

      Badrah tace "A lallai kwa yi kiba kuyi kyau abinku, irin wannan kyakkyawan kulawa ko 'ya'yan shugaban kasa ai sai haka"

       Zayyan yace "Ai Ummi don ma ba kiga komai ba labari aka baki, da sai al' ajabinki yafi haka"

       Badrah ta kalli Yasir, tace "Gaskiya Yasir babu abinda zance maka sai godiya da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da lahira"

      Yasir yace "Haba Ummi! karki bani kunya mana, duk abinda nayi muku ai ba sai kunyi min godiya ba, wa nake dashi wanda ya kaiku, ku kadai ne nawa don dole ku zan kyautatawa kafin kowa, na yiwa wasu ma bare ku"

     Badrah tace "Allah dai ya saka maka da gidan aljanna, Allah ya baka zuri'a dayyiba"

     Nan dai suka yi ta hira cikin jin dadi da kwanciyar hankali sai can Badrah tasa suka tashi suka koma dining room suka ci abinci da aka shiryawa masu dawowa, komai cikin farin ciki da walwala suke yin shi a haka suka wuni a ranar.

        ***          ***            ***          ***

      Bayan kamar mako biyu rannan  sai Yasira ta shirya zuwa gidansu Mas'ud don ta duba Hajiya Hala, ta samu Yasir ta gaya masa zata je har ya bata kudi yace ta yiwa Hajiya siyayya, sannan taje ta gayawa Badrah, bayan ta shirya ta fito falo sai ta samu Shukrah da Yusrah a zauna.

      Yusrah ta kalli Yasira, tace "Sister unguwa za ki haka babu ko neman dan rakiya?"

     Yasira tayi murmushi tace "Ba fa wani guri na daban zani ba, zuwa zanyi na duba jikin Hajiyar Yaya Mas'ud kin san tunda na dawo banje na sake gano jikin nata ba"

      Yusrah tace " Gaskiya dai, to me zai hana nima na shirya mu tafi tare mu dubata, kinga nima na samu ladan"

      Yasira tace "To ai hakan ma yafi kinga dama tafiya bibiyu tafi dadi nima nafi jin dadin tafiya"

      Shukrah tayi farat tace "Ai kuwa ba za'a barni a baya ba nima wajen zuwa, domin Annabi {SAW} yace "Mai zuwa gaida mara lafiya yana kan hanyar aljanna" kinga bana bari ayi babu ni ba"

      Yasira tace "Gaskiya kuwa, to ai sai  ku tashi ku shirya mu tafi kada mu  bata lokaci"

    Sai su tashi su shiga ciki kowacce ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta caba kwalliya sannan ta sanya kaya masu matukar kyau, su fito a kusan tare sannan suje su yiwa Badrah sai sun dawo sannan su fita driver ya daukesu su tafe.

      ***           ***           ***            ***

       Hajiya Hala tana zaune a falo tana yanke farce sai Yasira da Yusrah da Shukrah su shiga gidan da sallamarsu.

     Hajiya Hala tana murna ta tashi ta taro su ta rumgume Yasira tana cewa "Sannunku da zuwa! Sannunku da zuwa!! yau ina da manyan baki, yau 'ya'yana ne suka zo wajena"

      Bayan sun zazzauna sun gaisa, sai Yasira tace "Mama yankan farce kike yi?"

      Hajiya Hala tace "Yankan farce nake yi da kyar da kyar kin san tunda kika tafi nake yi da kaina, Mas'ud baya samun zama a gida bare ya yanke min"

      Yasira tace "To ai yanzu tunda nazo sai nayi aikina" sai ta karbi abin yankan ta fara yanke mata tana yi suna hira har ta gama.

      Yasira tace da Hajiya Hala "Mama saura kitso? ko bai tsufa ba?"

      Hajiya Hala tace "Ban dai sani ba sai dai ki duba" sai ta bude mata kan ta nuna mata.

      Yasira tace "Gaskiya wannan kan yana bukatar sabon kitso"

      Hajiya Hala tace "Yadda kika ce 'yata"

       Sai Yasira taje ta dauko kayan kitso tazo ta fara tsefe mata kan sannan ta kama yin kitson, bayan ta gama Hajiya Hala tayi tasa mata albarka tana yi mata addu'a, sai taje cikin kitchen ta dauko kilishi da snacks da juice ta kawo musu, ta zauna suna hira.

       Sai Hajiya Hala ta tashi tace "Bari naje na girka muku abinci kada lokaci ya kure"

       Yasira tace "A haba Mama! ai in dai ina nan to babu ke babu wani aiki, ki bari ji zanje na dafa, me kike so a dafa?"

       Hajiya Hala tace "Ni kuma ai in dai kina nan bani da wani zabi, duk abinda kika dafa to ina sonsa, na baki wuka da nama kije ki dafa duk kike so"

       Sai Yasira tace "To shikenan mama an gama"

      Sai Yasira ta tashi ta shiga kitchen ta dora girki, Yusrah da Shukrah su shiga su tayata, nan da nan kuwa suka gaure kafatalin gidan da kamshi, a lokaci kankani suka gama, sun dafa chicken al'kabsa rice da mutabbaq da basbousa suka jere su akan dining table suka kira  Hajiya Hala tazo suka zauna suka bada himma.

       A haka suka wuni a cikin farin ciki da annushuwa har yamma, sannan suka yi haramar komawa gida
har sun mimmike da niyyar tafiya.

    Sai Hajiya Hala tace da Yasira "Ni kuwa 'yata ina son yin wata magana dake a kebe kafin ku tafi"

     Yasira tayi murmushi tace "To Mama"

      Sai Hajiya Hala ta wuce ta tafi daki.

      Yasira ta kalli Yusrah da Shukrah, tace "Don Allah kuyi min hakuri ina zuwa"

      Suka ce mata ba komai ba tare da nuna damuwa ba, don haka sai Yasira tabi bayan Hajiya Hala taje ta sameta a daki a zaune a gefen gado, tana shiga Hajiya Hala tayi mata izini data zauna itama a gefen gadon kusa da ita, Yasira ta zauna ba tare da kawo wani abu a ranta ba.

      "Kin san abinda yasa na kiraki?"

      "A'a mama sai kin fada"

      "Akan maganar yayanki Mas'ud ne, yace min ya fada miki abinda yake zuciyarsa amma kamar baki karbi tayinsa ba, abinda baki sani ba shine Mas'ud yana matukar kaunarki fiye da tunaninki kuma ya dade da wannan son a zuciyarsa amma bai taba gayawa kowa ba sai ni, yanzu ma ni na tilasta shi akan lallai sai ya sanar dake, a matsayina na mamanki ba a matsayina na maman Mas'ud ba, ina rokonki daki so Mas'ud in har babu wani a zuciyarki, don gaskiya nima ina matukar son hada zuri'a dake"

       Kai Mama! wallahi har kin bani kunya, nima ina son Yaya Mas'ud kamar yadda yake sona kuma babu wanda nake so sai shi, sannan ni a ganina ai mama ba sai kin rokeni akan wani abu ba ko menene kuwa don kinfi karfin komai a wajena"

     "Gaskiya naji dadi mara misaltuwa kuwa, ke kuma Allah ya saka miki da alkhairi 'yata"

      "Amin Mamana"
    
       Nan dai suka fito Hajiya Hala ta rakosu har bakin gate inda motarsu take driver yana jiransu, ta kawo wata jakar leda ta bawa kowaccensu amma ta Yasira tafi girma da alama abinda yake ciki yafi nasu yawa suka yi godiya suka hau mota driver yajasu suka nufi gida.

       Su Yasira basu dade da tafiya ba sai ga Mas'ud ya dawo daga office, da Hajiya Hala ta sanar dashi cewa yanzu su Yasira suka fita sai da yayi kamar ya bisu don doki sai Hajiya Hala ta tsayar dashi

      Hajiya Hala tace "Ai daka bisu gara ka tsaya kaji abinda tace a kanka"

      Mas'ud cikin yanayin doki da zakuwa yace "Mama me tace don Allah ki gaya min da sauri!"

      Hajiya Hala tace "Yasira ta amince da kai ka aureta, tana sonka kamar yadda kake sonta"

       Kawai sai Mas'ud ya fadi kasa yayi sujjada sannan ya dago yace "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!!!"

       Hajiya Hala tace "Nima kaina abin yayi min dadi fiye da tunaninka, abinda kawai zance maka ka rike amana kuma duk rintsi duk wuya ba zaka bata rabuwa da ita ba"

       Mas'ud yace "Nayi miki alkawarin koda Yasira tana saba min to ni ba zan taba bata mata ba"

       ***            ***           ***           ***

           Bayan su Yasira da Yusrah da Shukrah sun koma gida, da daddare suna daki sunyi shirin barci sai kowacce ta dauko jakar ledar da Hajiya Hala ta bashi ta bude don ganin ko menene a ciki, a cikin ledar Yusrah da Shukrah turaruka ne da kayan kwalliya, amma a cikin ledar Yasira bayan turaruka da kayan kwalliya sai ga wata box koda ta bude abinda yake ciki ya kusa sawa numfashinsu ya tsaya don al'ajabi, abinda yake cikin box din sarka ce da 'yan kunne da warwaro da zobe har da agogo duk na diamond jewelry.

      Yusrah tana kara mamaki tace "Gaskiya al'amarin Hajiyar nan akwai alamun tambaya!"

      Yasira ta kalli Yusrah, tace "Game da me fa?"

      Yusrah tace "Da alama tana so ne ki zama surukarta mata a wajen danta"

       Yasira cikin tsananin mamaki tace "Ta yaya akai ke kika sani?"

       Yusrah tace "Gashi nan alamu da yawa sun nuna hakan"

       Yasira tace "Kamar me da me fa?"

        Yusrah tace "Yanayin yadda take miki da yadda take mana da bambanci duk da gaba dayanmu ta kiramu da 'ya'yanta, kuma ki duba yadda take janki a jiki kamar 'yar da ta haifa a cikinta, sannan gafda zamu taho ta ja ki kunyi sirri a dakinta, tayi mana kyauta amma taki kyautar tafi tamu, haba sister ai ko ba'a gaya miki ba kin san da magana, akwai tambaya don ruwa baya tsami banza"

        Shukrah ta jinjina kai tace "Gaskiya dai akwai kamshi gaskiya a cikin maganar Yusrah, domin banza bata taba kai zomo kasuwa, kema idan kika tsaya kika yi tunani za ki gane akwai wata a kasa koda ba'a fada miki ba domin in dai har kaji gangami to da labari"

        Yasira tace "Wannan ai tsohon labari ne kune baku sani ba, Yaya Mas'ud yana sona da aure kuma nima ina sonsa"

         Yusrah tayi dariya tace "Haba koda naji! ai wannan kan nawa yana kawo wuta wallahi, ni din bata wasa bace"

        Shukrah tace da Yusrah "Gaskiya dai sister ke intelligent girl ce"

         Yasira tace "Ni fa tunanin da nake yi anya kuwa mama tana sane ta sako min wadannan  jewellery din?"

        Yusrah ta kalli Yasira tace "Ka ji ki da wani zance! to ita Hajiyar tayi tsufan da zata sako abu ba tare data sani ba?"

        Yasira tace "Ko dai ba haka bane ni dai zan buga mata waya na tambayeta"

         Shukrah tace "Eh hakan ma yayi"

        Nan dai suka yi addu'oinsu sannan suka kwanta suka kama barci amma ita Yasira ta ka sa yin barcin, don hakan sai ta dauko wayarta ta ga karfe goma sha biyu saura kwata, ta kama tunanin ko Hajiya Hala tayi barci ko ba tayi ba, ko ta kirata ko ta bari sai da safe, data ga dai in har bata tabbatar da gaskiyar wannan abu ba ba zata iya rintsawa ba kawai sai ta kira wayar, bugu daya aka daga wayar.

      "Salamu alaikum"

      "Amin wa alaikis salam mamana"
     
      "'Yata kece da daddaren nan ba kiyi barci ba?"

       "Eh nice mama, banyi barci ba"

       "Ince dai ko lafiya?"

       "Lafiya kalau mama, kawai dai na kiraki ne nayi miki godiya akan abin arzikin da aka yi mana dazu"

        "Haba 'yata kada ki bani kunya mana, yanzu ni a matsayina na mamanki don nayi miki kyauta sai kin bugo min waya kin min godiya, ai duk abinda nayi miki a matsayina na uwa hakkinki ne ya ke 'yata"

        "Duk da haka mama, idan har 'ya ta gari ce to ko iyayen nata ne suka yi mata abin arziki ya kamata ta gode musu, don zuciya ma tana son mai kyautata mata, Allah ma yana son masu godiya har karin ni'ima yake musu"

       "Gaskiya ne 'yata ke dai Allah yayi miki albarka"

       "Amin mamana, sannan a cikin ledar tawa naga wasu jewellery na diamond"

        "Naki ne' yata"

        "Duk ni kadai mama"

        "Duk naki ne 'yata, wannan tukuici ne na karbar soyayyar Mas'ud da kika yi, kuma wannan ma somin tabi ne wani abin ma sai kin aureshi, ke dai kawai ki kwantar hankalinki kiyi barci wannan ba wani abu bane"

       "To mama Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara arziki"

          Sai ta kashe wayar ta kwanta cikin matukar farin ciki, koda tayi shirin barci yanzu ma sai abin faskara tayi ta juyi tana karawa, a dazu rudani da kokwanto ne suka hanata barci, yanzu kuma doki da farin ciki ne suka hanata, haka tayi ta juyi tana ta sake sake sai can wajen asuba sannan barci ya saceta.

      ***            ***            ***           ***

      A yanzu manya sun shiga al'amarin soyayyar Mas'ud da Yasira don sun zo anyi magana gemu da gemu, a yanzu haka anyi musu baiko za'ayi bikinsu a lokaci daya dana Yasir da Yusrah da Shukrah. Kusan kullum yanzu Mas'ud yana gidan su Yasir.

     Shirye shiryen bikin Yasir da Yusrah da Shukrah da kuma na Mas'ud da Yasira abu ya kankama don yanzu abin ya zo daf, hidindumu sun fara kankama, Yasir ya dauki duk amaren sun je dubai sun siyo kayayyakin da zasu yin amfani dasu a bikin, kama daga kayan sawa na amare da ango da kayan daki na Yasira tun shi gidan da zai zauna akwai komai na amfani a ciki sunyi siyayya mai tarin yawa don duk wani abu da Amarya zata bukata na bikinta Yasir ya siya musu gaba dayansu, haka suka dauko jirgi ya kawosu su da kayansu.

                *Alkhamis KSA*

Continue Reading

You'll Also Like

7.9K 139 7
LABARIN RUGUNTSUMI: SARKAKIYAR RAYUWA, MAKIRCI DA TSANTSAR HASSADA, SHIN NA FADA MUKU YANA DAUKE DA TSAFTATACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE? LABARI NE NA...
7.8K 124 12
"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa...
12.1K 645 35
MUGUN ZALUNCI Labarin Ruk'ayyatu, tana tsaka da rayuwa da mijinta Lami'do mutuwa ta raba tsakanin su, bayan wani lokaci Ruk'ayyatu ta auri Abubakar...
990K 30.7K 61
Dans un monde où le chaos et la violence étaient maitre, ne laissant place à ne serrait ce qu'un soupçon d'humanité. Plume était l'exception. Elle...