HAWA DA GANGARA

De KhamisSulaiman

718 38 0

Labarin wasu larabawa ne marayu wadanda suka shigo duniya da kafa daya kafin su sako dayar. Mais

1
2
3
4
5
6
7
8
9
11
12
13
14
15 END

10

29 2 0
De KhamisSulaiman

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                        

                          *page 10*

         Yasir ya sunkuyar da kai kasa yana hawaye ya ka sa ce mata komai.

         Yusrah tana masa wani irin kallo tace "Wannan ya tabbatar min da cewa Ummi ta rasu, shikenan na zama marainiya gaba daya ba uwa ba uba! amma ai ina da kai ko?" ta fada tana kallon Yasir idonta fal da hawaye.

         Yasir ya gyada mata kai idonsa na zubar da hawaye ya kasa furta uffan, gaba daya tausayinta yake yana hango yadda rayuwarta zata kasance, a ransa yace 'Insha Allahu ba zan kiyi rayuwar maraici irin wadda muka yi ba'

       Yasira ta zauna a kusa da ita a daya barin ta dafata, Yusrah ta kalli Yasira sannan ta Yasir, tace "Wannan ita ce Yasira?"

       Yasir ya gyada mata kai a karo na biyu ba tare da yace komai ba.

       Sai Yusrah ta rungume Yasira, tana cewa "Yanzu ke kadai ce 'yar'uwata ta jini domin kuwa tare aka fara shayar damu kafin kaddara ta rabamu"

        Mas'ud da Dr. Ra'is da Dr. Karim da wadannan nurses din kawai kallonsu suke zuciya cike da tausayawa.

          Yusrah ta saki Yasira ta kalli Yasir, tace "Yaya ka kaini naga Ummina nayi mata sallama kafin a kaita a binne"

          Nan fa aka fara kallon kallo a tsakanin mutanen da suke cikin dakin.

         Yusrah ta kula da duk yadda mutanen dake dakin suka yi don haka sai ta sake kallon Yasir, tace "Yaya an kuma samun akasi kenan ko?"

        Yasir yana kallonta cikin yanayin tausayawa yace "Idan baza ki manta ba bayan mun kawo umma asibiti an turamu mu siyo magani a lokacin da zamu tsallaka titi mota ta kadeki, tun daga wancan lokacin ba ki san inda kanki yake ba sai yau da kika farka, daga ranar zuwa yau kimanin wata shida kenan, umma kuma lokacin da aka shigar dake emergency ita kuma a lokacin aka fito da ita ta rigamu gidan gaskiya"

        Sai Yusrah ta sake fashewa da kuka, Yasira ta rungumeta tana rarrashinta.

         Yasir yace "Sai dai idan kina bukatar ziyartar kabarinta sai in kaiki makabarta da zarar an sallamemu"

         Nan Dr. Ra'is ya bukaci dukkansu su fita don ya duba lafiyarta ya gani ko da wata matsalar, an aunata sosai anyi mata gwaje gwaje duk sakamako ya nuna ba wata matsala, nan take ya rubuta musu sallama aka sallamesu suka tafi basu je gida ba sai da suka fara zuwa makabartar da aka binne Bushrah suka yi mata addu'a ita da sauran mamatan musulmai na duk fadin duniya, sannan suka wuce gida. Yusrah tayi matukar farin ciki da yadda Yasir da Yasira suke yi mata, suna matukar kaunarta itama tana kaunarsu babu wanda zai ba uwa daya uba daya suke ba sai wanda ya sani, sun rakata gidansu ta da suke haya ta debo kayan ta wanda take so, wanda bata so kuma ta hada da na Bushrah ta rabawa mabukata, sannan suka dawo suka yi zamansu cikin aminci da yarda.

       A yanzu Yasira da Yusrah tare suke tafiya makaranta, don Yasir ya maidasu makaranta daya suna karatu tare tunda dama duk likitanci suke karanta, rayuwa tana musu dadi duk abinda suke so shi Yasir yake musu yana nuna musu matukar kauna.

       Wata rana da hantsi Yasir da Yasira da Yusrah suna zaune a falo suna hira cikin annushuwa da kwanciyar hankali, kawai sai suka ji ana kwankwasa kofa, Yasir yana daga zaune yayi izini da a shigo, ana turo kofar wa zasu gani? Shukrah ce da Rayyan kana ganinsu kasan suna cikin tashin hankali da damuwa sun rame sunyi baki, suna shiga Shukrah ta fada jikin Yasira tana kuka mai tsuma zuciyar mai jinsa, shima Rayyan kukan yake, Yasir da kyar ya rarrashesu suka yi shiru sannan ya sasu suka yi wanka suka ci abinci suka huta sannan suka zauna gaba dayansu Yasir, Yasira, Yusrah, Shukrah da Rayyan.

        Yasir yana kallon su Shukrah, yace "My sister me ya faru daku ne haka?"

       Shukrah cikin yanayin damuwa tace "Tun lokacin daka sa kafa kabar gida ko bakin gate baku kai ba Ummi ta fadi take ta jiyya har zuwa yau bata warke ba, kuma kullum bata da wani aiki sai na cewa a nemo mata sauran ya'yanta wato Yasir da Yasira, kullum cikin sunanku take, yanzu haka ma ta kai wata uku a asibiti, shine likitanta ya umarcemu damu nemo ku a duk inda kuke ko za'a samu saukin ciwon nata, mun kai wata biyu kullum sai mun fita nemanka amma ko wanda yaga wanda yasan inda kuke bamu gani ba, sai jiya muna kallon labarai a asibitin naji an ambaci sunanka a matsayin mataimakin shugaban wani kamfani shine mukaje kamfanin, to da yake yau ba aiki sai mai gadin kamfani ya kwatanto mana nan don mu zo muga ko kaine"

         Yasir cikin yanayin tausayawa yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! yanzu Ummi tana kwance a asibiti tsawon wata uku? me yasa baku fita da ita kasar waje ba? Ina Zayyad da Dayyab suke?"

       Shukrah tace "Ita ta hana a fitar da ita ko ina tace idan har ta bar kasar nan to ta sake yin nesa daku, kullum sa ran ganinku take, su kuma su Zayyad da Dayyab tun lokacin da suka siyar da kamfani aka zauna aka sake rabon kudin aka bawa kowa nasa, to tun a ranar bamu sake ganinsu ba har zuwa yau"

        Yasir cikin jimami yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! to waye a wajen ita Ummin daku ka taho ku ka barta a asibiti"

       Shukrah tace "Zayyan ne a wajenta, mu kuma kullum ni da Rayyan sai mu fito nemanku"

        Yasir yace "To ku tashi mu muje wajenta"

        Sai suka tashi gaba dayansu su shirya su fita su hau motar Yasir su tafi, Yasira da Yusrah da Shukrah suna zaune a baya, Yasir da Rayyan kuma suna zaune a gaba yayin da Yasir yake tukawa. Sun isa babban asibitin dake kasar, Shukrah da Rayyan suka yi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Badrah, suna shiga sai suka tarar da Zayyan yana rike da ita tana daga kwance tana fadin "Ku nemo min 'ya'yana Yasir da Yasira, ku nemo min su ban san a wane hali suke ciki ba!"

         Zayyan yana rarrashinta yana cewa "Ummi don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki yaya Shukrah da Rayyan sun fita nemo su kamar kullum......."

        Sai su karasa wajen da sauri, Yasir ya zauna a kujera Zayyan ya tashi ya bashi, yace "Ummi gamu, ga 'ya'yanki sun dawo gareki"

       Badrah ta bude ido ta kalli Yasir, tace "Yasir!"

       Yasir yace "Na'am"

       Badrah tace "Ina Yasira?"

       Yasira ta karasa kusa da ita tace "Gani  Ummi!"

       Kawai sai Badrah ta tashi zaune ta rungumesu tana kuka tana cewa "kada ku sake tafiya ku barni komai rintsi,"

       Shukrah da Rayyan da Zayyan sunyi matukar mamakin ganin mikewar Badrah a lokaci guda, domin ta dade a kwance bata iya komai sai anyi mata, magana da kallo da ido kawai ta iya. Da likita yazo ma yayi matukar mamakin ganinta a haka ta samu sauki cikin kankanin lokaci, haka ma da ya aunata sai yaga jininta da ya hau ya sauka don haka sai aka sake mata wasu magunguna, ba tare da bata lokaci ba aka sallamesu daga asibitin.

        Yasir ya kaita gidansa yace ta zauna anan kafin ta warke gaba daya, sai Badrah tace ai ko ta warke ba zata koma ba sai tare dashi, shi kuma sai yaji a ransa kamar ba zai iya komawa gidan ba, sai dai in su zasu zauna tare dashi.

       Da daddare Yasir yana zauna a dakinsa yana aikinsa da ya saba a computer, sai Yusrah ta shiga wajen sa.

       "Yaya sannu da aiki, ashe kaima baka yi barci ba?"

       "Wallahi kuwa, ina nan ina yin wani aiki ne wanda ake bukatarsa zuwa da safe. Amma ke me ya hanaki barci?"

        "Babu komai, kawai dai nakasa yin barcin ne, shine nace bari nazo naga kai kayi barci, idan baka yi ba sai na tayaka hira"

        "Ko dai don kun samu karin mutane a dakin ne shi yasa kika ka sa yin barci? nasan da a gidanku dakinki daban ke kadai"

         "A'a wallahi yaya ba haka bane kawai dai yanayi ne. Amma me yasa baka gabatar dani ga wadannan bakin ba, kuma suma baka gabatar min dasu ba"

         "Ai su ba wasu baki bane, sune wadanda na zauna a wajensu tun Yasira tana jaririya har zuwa girman mu, kinga kuwa ai ba baki bane"

        "To amma duk da haka ai ni ban san su ba kuma suma basu sanni ba"

        "To shikenan kiyi hakuri ai yanzu na gabatar miki dasu, sauran ke da safe zan gabatar dake garesu"

        Da safe kuwa Yasir ya shiga dakin da Badrah take, bayan sun gaisa kafin ma yayi mata maganar Yusrah ita ta fara tambayarsa wacece ita? nan ya kwashe labarinta gaba daya ya sanar da ita, amma ya boye mata cewa suna soyayya, bai fada mata wannan ba. Suka cigaba da zamansu a wannan  gida, an warewa Badrah dakinta daban, shima Yasir dakinsa daban, yayin da Yasira da Yusrah da Shukrah suke daki daya, haka ma Rayyan da Zayyan dakinsu daya, a haka suka cigaba da rayuwa cikin jin dadi da kwaciyar hankali.

        ***          ***          ***         ***

        Yasir yaje ya samu Alhaji Mansur ilyas Walid mai kamfanin Walid artistic constructions development company, shi kuma ya kai Yasir gidansa cikin iyalansa suka ci abinci tare, bayan nan ya jashi wani Garden dake cikin gidansa suka zauna suna tattaunawa.

      Na samu labarin abinda ya faru da kai da kamfaninku gaskiya abin bai yi dadi ba, ni kuma tun daga wannan lokacin nake neman ka domin ka maye min gurbina na maida ka shugaban kamfanina na Walid artistic constructions development company, amma rashin sa'a ta yasa ban sameka ba har sai da ka kama aiki da kamfanin Fahima & Brothers a matsayin mataimakin shugaba, sannan muka hadu."

       "Alhaji ai komai daka gani mukaddari ne daga Allah, sannan yarda da kaddara mai kyau ko Kishiyarta yana daya daga cikin shika shikan Imani nasan ka fini sanin haka"

      "Yasir makasudin gayyatarka da nayi gidana shine ina so na ajiye aiki gaba daya na huta kafin rai yayi halin sa amma ya faskara, saboda 'ya'yana basu da gogewa shekarunsu ma bai kai na mika musu ragama ba, ina ta neman wanda zai rika min ban samu ba, sai kuma na samu labarin abinda ya faru da kai, ina ta neman ka na danka maka ragamar harkokina amma ban same ka ba, sai gashi wasu sun sameka a bagas sun baka mukamin da bai kai wanda nake son baka ba!"

       "Alhaji har yanzu fa banyi ko shekara da fara aiki a kamfanin Fahima & Brothers ba"

       "Kenan dai ba zaka karbi tayi na ba?"

       "Alhaji ba wai ina son watsa maka kasa a ido bane ko kuma na kushe abinda kazo min dashi bane, akwai yarjejeniya da alkawari a tsakanina da Hajiya Fahima mai kamfanin, na cewa zanyi shekara uku ne tare dasu bayan nan zan ajiye aiki saboda nima ina son bude nawa kamfanin"

        "A ganina bisa kwazonka ai zaka iya rike ofisoshi guda biyu"

       "Eh tabbas zan iya, amma bazan karbi tayinka ba saboda yarjejeniya da alkawarinmu. Amma ina da wata shawara"

        "Ina sauraronka"

        "Idan har kana son nayi aiki da kamfaninka to sai kaje ka samu Hajiya Fahima har office dinta ka nemar min izinin yin hakan, kuma ka nuna mata hakan ba zai taba aikin kamfaninta ba ko kadan, wannan yayi nan, wancan yayi can"

       "Wannan ai mai sauki ne, ka sani bani da girman kan da zai hanani yin hakan"

      Washe gari ta kama ranar Monday Alhaji Mansur yaje office din Hajiya Fahima kamar yadda Yasir ya bukata, yayi mata bayanai sosai sannan ya roketa cikin siyasa har ta amince. Tun daga wannan rana Yasir ya kama aiki tukuru ba kama hannun yaro, yayi hikima yaja 'ya'yan Alhaji Mansur a jiki suna yin komai tare don su dinga ganin komai kuma su iya komai kafin lokacin da zai bar musu aiki.

      ***           ***              ***           ***

     Zayyad da Dayyab tun lokacin da suka siyar da kamfani aka raba kudin kamar yadda aka raba gadon tun farko, don haka da suka hada kudadensu waje guda basu zame ko ina ba sai kasar waje su da Abokina harkarsu, Zayyad ya tare a gidan karuwai, shi kuma Dayyab ya tare a gidan giya bangaren 'yan shan kwaya. Kullum basu da aiki sai wadaka da bushasha da dukiyarsu ta gado, kowannensu ya zama tamkar sarki a inda ya sauka shike sawa da hanawa saboda tarin dukiya.

       ***            ***          ***           ***

       A tsawon shekara biyar Yasir ya zama hamshakin attajiri, a yanzu ya mallaki kamfani nasa na kansa, ya gina katafaren gida babba, yana zaune a ciki tare da Badrah da kannensa.

     Wata rana da safe Yasir ya shiga dakin Badrah domin ya gaisheta sai ya tarar da ita da Shukrah, bayan sun gaisa sai Badrah ta tsayar dashi.

      "Yasir ina son yin wata muhimmiyar magana da kai, ko fita zakayi?"

      "A'a Ummi, ba inda zani kuma ma koda ina da abinyi sai na barshi tunda kika ce kina son magana dani, ai sawun giwa ya take na rakumi"

     "Yasir a yanzu kusan duk wani abu a dan adam yake bukata Allah yayi maka, abu daya ya rage maka yanzu a duniya, shine kayi aure ka haihu tunda sauran kuruciyarka kafin lokaci ya kure maka"

      "Gaskiya ne wannan Ummi, nima nasan yanzu abinda ya rage min shine aure, dalilin da yasa gina wannan sabon gidan kenan nayi bangarena can daban inda zan tare idan nayi auren"

      "To Alhamdulillahi naji dadin hakan, amma abinda nake so da kai idan ka tashi yin aure ina so ka auri 'yar uwarka Shukrah!"

                !!!              !!!               !!!

                   *Alkhamis KSA*

Continue lendo

Você também vai gostar

1.5K 81 24
Kubi sannu dan sanin inda ma'ana da kuma jigon lbrn ya nufa
1.4K 95 24
Hakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi....... Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska...
37.8K 1.2K 33
Lance is a normal guy, funny, good looking, he's going to night school so he can work and get his degree. Keith however, he's a bad boy, someone even...
7.3K 195 8
"You fucking Catfish!" ▬▬▬▬ Y/n Y/l/n, 21, is undercover as a high school student East Highland when she meets Maddy Perez, 18. What will happen when...