HAWA DA GANGARA

By KhamisSulaiman

718 38 0

Labarin wasu larabawa ne marayu wadanda suka shigo duniya da kafa daya kafin su sako dayar. More

1
2
3
4
5
6
8
9
10
11
12
13
14
15 END

7

32 3 0
By KhamisSulaiman

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                        *page 7*

       Zayyad yace "A cikin rabon ban ji ka saka kamfani a cikin rabon ba"

       Nace "Eh shi ba'a kai ga raba shi ba"

       Zayyad yace "To shima muna bukatar a raba shi kowa yasan matsayin sa!"

        Nace "Shikenan an gama ai hakkinku ne. Kai kuma meye taka tambayar." na fada ina kallon Dayyab.

         Dayyab yace "A cikin rabon banji ka sa kanka ba kuma banji kasa Yasira ba, ko me yasa?"

        Shukrah tace "Nima abinda nake so in tambaya kenan amma don ganin Ummi tayi shiru shi yasa nima nayi shiru, amma don Allah yaya muna son sanin dalili ba wai don muna jayayya da kai ba, mun yarda da kai mun san ba zaka taba yin wani abu mara hujja ba"

       Nace "Tabbas ni da Yasira babu mu a cikin wannan rabon!"

       Dayyab cikin sauri yace "To saboda me?"

       Na kalli Badrah naga tana hawaye tana girgiza min kai alamun kada na fada, na kallesu daya bayan daya naga kowanne alamun tuhuma a fuskarsa.

      Na mai da kallo ga Badrah nace "Ummi kiyi hakuri ki yafe min amma yau zan bayyana gaskiya a garesu don kauda zargi saboda ranar wanka ba'a boyon cibi"

      Na kalli Yasira naga ta kura min ido dauke da alamun tambayoyi barkatai, sai nace "Gaskiya ne cewa ni Yasir da Yasira kanwata bamu da gado a cikin duk abinda Abba ya bari shi yasa ku kaga ba'a raba damu ba dalili kuwa shine saboda mu ba Abba da Ummi bane suka haifemu......!"

      Kaf dinsu babu wanda bai girgiza ba da jin wannan labari.

       Shukrah ce ta taso gabana ta zube a kasa tare da rike hannuna tana kuka tace "Don Allah yaya kace min wannan labari ba gaskiya bane, ko kuma kace min mafarki ne nake yi....!" bata karasa maganar ba kuka yaci karfinta.

       Badrah da Zayyan da Rayyan suma kukan suke yi mai tsuma zuciya, ita kuma Yasira fuskarta ba yabo ba fallasa ita ba mai bakin ciki ba ita ba mai farin ciki ba, kawai sai muka ji shewa da dariyar Zayyad da Dayyab har da tafawa.

        Zayyad ya kalleni yace "Amma gaskiya mutumin nan kason wuce gona da iri, ashe kai da ba dan gidan nan bane babu abinda ya hadamu kai bare ne, amma shine ka dinga azabtar damu kana hanamu jin dadin rayuwa ka zame mana karfen kafa a rayuwa!"

     Dayyab yace "Kuma yasan bashi da gadon Abbanmu amma haka ya kankane ya rike a wajensa, da bamu ce a bamu namu ba da ban san ko ma cinyewa zai ba!"

       Shukrah cikin bacin rai tace "Kai yaya Zayyad da yaya Dayyab wannan wacce irin mummunar dabi'a ce sai kace......!"

       Zayyad ya katseta da hantara yace "Ke dahalla yi mana shiru ko kuma ranki ya baci yanzu"

       Badrah ta tashi a fusace taje ta mari Zayyad ta mari ta mari Dayyab, tace "Koma dai meye shi dan'uwanku ne babu abinda bai yi ba akanku, kuma har abada shi din danmu ne ni da Abbanku!"

       Dayyab yace "A'a Ummi, wannan maganar taki ma babu ita a cikin abinda yake na gaskiya don haka ki danna zero domin goge ta......!"

      Na tashi nayi kan Dayyab ina cewa "Kai Ummi kake karyatawa.......?"

     Zayyad yasha gabana yace "To kai meye naka a ciki? ai mahaifiyarmu ce ba taka ba......!"

       Badrah ta sake marin Zayyad tana cewa "mutanen banza mutanen wofi!"

       Zayyad cikin fushi da fusata yace "To wallahi Ummi ki sani Yasir da Yasira sai bar gidan nan, tunda ba ciki daya muka fito ba!"

       Badrah tace "Ai gidan nan gadona ne ba naku ba don haka baku isa ku koresu ba"

       Dayyab yace "Tabbas gadonki ne amma mu kadai ne 'ya'yanki muke da gadonki ba wani ba muke da ikon aiwatarwa ko hanawa ga dukiyarki tunda ke kin tsufa."

       RABUWARMU DA GIDAN ABDUSSATTAR

       Nan dai rigima ta kaure a tsakaninsu Badrah da Shukrah suna cewa ba zamu tafi ba, yayin da Zayyad da Dayyab suke cewa sai mun tafi ganin abin yana shirin zama babba, na yanke shawarar shiga na debo kayana don tafiya.

      Dayyab yace "Ai babu abinda zaka dauko yadda ka shigo gidan haka zaka fita daga kai sai kayan jikinka!"

      Haka kuwa aka yi muka fito daga gidan daga mu sai kayan jikinmu, ina rike da hannun Yasira wadda na rasa abinda ke cikin zuciyarta, don tunda aka fara wannan abu bata tofa ko uffan ba kuma babu alamun bacin rai a fuskarta ba haka kuma ba farm's, a haka muka bar gidan.

      Bayan mun fito daga gidan sai muka rasa inda zamu don haka sai muka samu wani guri muka zauna a bakin titi, sai a wannan lokaci Yasira ta fashe da kuka nayi ta rarrashinta amma ta kasa yin shiru kawai sai na kyaleta don abin ya kai na ayi kuma nima idan na fiya rarrashinta zan iya yin kukan.

       Tunani kawai nake yi abin yi domin kaina ya kulle na rasa ma meye mafita ni dai tunda nake aikin nan ban siyi wani abin na ajiye ba ko don wataran, kawai na shagala ma sakankance yau kuma sai ga wani ibtila'i bagatatan wanda ko a mafarki ban kawo zai riskeni ba. Kawai sai naji wayata tayi ringing gaba daya ma na manta cewa wayar tana jikina ban zaci tana tare dani ba, garin ciro wayar sai wallet dita ma ta fado sai na yiwa Allah godiya domin a cikin wallet din ina da kudi kuma Atm dina shima yana ciki da sauran katina na masu muhimmanci, na duba wayar sai naga Mas'ud ne yake kira sai na daga.

   "Salamu alaikum"
 
   "wa alaikas salam, kana ina naje office dinka ance baka zo ba, ina dai fatan lafiya?"

   "Eh lafiya, yanzu kana ina?"

   "Ina kamfanin naku ban kai ga fita ba ko in tsaya yanzu zaka zo?"

   "A'a, tambayarka zanyi a cikin gidajenku na haya akwai wanda yake empty?"

   "Akwai wani karami wanda babu kowa a ciki"

   "Ina so zan kamashi ka cike min komai sannan ka gaya min nawa ne kudin zan turo maka yanzu, saboda ina sonsa ne cikin sauri a yau yau dinnan kuma yanzu yanzu!"

    "Lafiya kuwa?"

    "Lafiya kalau, kai dai kawai kayi abinda na bukata cikin sauri!"

    "To shikenan ba matsala ka bani two hours zanje na cike komai, kuma bama sai ka bada kudin ba zan biya"

     Kawai sai ya kashe wayar. Na tashi na kalli Yasira na mika mata hannu nace "Taso mu tafi my lovely sister"

      Haka ta kama hannuna jikinta a sanyaye muka tafi muka tsayar da taxi muka hau bamu zame ko ina ba sai supermarket na siya mana kayan sawa kala biyar biyar da kuma ciye ciye da 'yan kayan amfanin yau da kullum wanda ba zamu samu ba a gidan hayar, bayan mun gama zabar komai mu kaje wajen cashier muka biya sannan aka zuba mana a taxi din da muka zo ta wuce damu gidan hayar da zamu koma.

                 MUN SAKE GIDA

    Muna tafe a hanya Mas'ud ya kirani a waya ya shaida min an gama komai sannan ya turo min da bayanan komai, don haka kai tsaye can muka nufa muna zuwa muka tarar dashi a harabar gidan yana jiranmu, bayan mun sallami mai taxi tare da Mas'ud muka shigar da kayanmu ciki. Gida ne kyakkyawa dan madaidaici akwai 2 bedrooms da living room da 2 toilets da kitchen da  dining, bayan mun zuba duk kayan da muka siyo na sawa a wardrobe sauran kayan kuma kowanne a muhallinsa sai muka dawo falo muka zauna.

      Mas'ud cikin yanayin damuwa yace "Wai me yake faruwa ne? ba dai ku zaku zauna a gidan nan ba?"

     "Mu zamu zauna anan gidan ni da Yasira!"

     "To me ya faru?"

     "Mun samu sabani ne a wancan gidan shi yasa!"

   
     "To amma me yayi zafi haka?"

     "Ni Yasir da kanwata Yasira mun kasance ba 'yan gidan bane, mai gidan da matar gidan basu suka haifemu ba, wannan shi yasa!"

        Ban gayawa Mas'ud komai ba shima kuma bai takura akan sai ya sani ba, duk duniya bani da wani aminin aboki sama dashi, ya dai girgiza da jin labarinmu.

       Mas'ud yace "Amma daka gaya min tun farko ai da gidanmu zaku koma ba nan ba, tunda  gidanmu ne zakuji kamar kuna can kaga daga ni sai Ummina ne muke rayuwa a can"

       Nace "Mas'ud bana son takurawa kowa kuma sannan da wannan abu ya faru naji ina bukatar kadaici ne da 'yar'uwata wanda banyi ba a da"

      "To shikenan Allah yasa haka shi yafi alkhairi"

      "Amin summa Amin"

       Daga nan muka cigaba da hira Mas'ud  bai bar gidan nan ba sai bayan magariba da muka fits yin sallah ya wuce gada can ni kuma naje restaurant na siyo mana abinci na dawo na tarar da Yasira tana karatun kur'ani akan dardumar da tayi sallah, don haka sai na ajiye na zauna ina sauraronta har ta gama sannan ta taso tazo ta zauna a kusa dani.

      "Sannu da dawowa yaya"

      "Yauwa sannu da kokari kanwata, ga abinci nan Ki zuba mana muci"

      "To yaya"

      Ta tashi ta dauka taje ta shirya mana shi a dining sannan muka zauna muka fara ci. Muna cin abincin nayi ta yi mata nasihohi akan yarda da kaddara mai kyau ko akasinta dangane da faru da hakuri akan duk wata jarrabawa ta ubangiji, nasihohin sun shigeta don yanzu ji take kamar ma babu abinda ya faru.

     Na kalleta nace "Da fatan dai gidan yayi miki"

    Tace "Gida yayi yaya, sai dai jina nake kamar a wata sabuwar duniya ta daban"

      Nace "Ai dole ne saboda tunda kike babu inda kika taba zuwa kika kwana in dai ba'a gida ba, kuma zakiji fiye da haka ma a lokacin da kika yi aure"

      A haka muka zauna a wannan gida tsawon watanni shida, duk wata Mas'ud shi yake kawo mana kayan abinci da sauran kayan amfani irinsu perfume, toothpaste, detergent, soap, da mayukan shafawa.

      Yasira ta cigaba da karatunta na aikin likitanci da take tun muna gidan Abdussattar.

     Mas'ud ya damu akan lallai sai na nemi aiki a kamfaninsu amma ni kuma naki. Wata rana muna zaune muna kallon labarai a gidan tv sai naga sanarwa cewa ansa kamfanin Abdussattar & sons a kasuwa, nayi matukar bakin ciki sosai amma babu yadda na iya.

      Nasa Mas'ud ya dauko min wani babur dinsa wanda ya daina hawa saboda ya sayi mota sai nake amfani dashi a matsayin abin hawa.

        
           HADUWATA DA YUSRAH

                    *Alkhamis KSA*

Continue Reading

You'll Also Like

5.4K 231 11
Labarine da yake tafe da LOVE, COMEDY AND TRAGIC(Romantic Suspense)
3.7M 291K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
37.8K 1.2K 33
Lance is a normal guy, funny, good looking, he's going to night school so he can work and get his degree. Keith however, he's a bad boy, someone even...