YASMEEN.

De JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... Mai multe

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 31-32✍🏼

Page 29-30✍🏼

19 2 0
De JannatMN


*༺•⚘🌺YᎪᏚᎷᎬᎬN🌺⚘•༻*
             *1442H/2020M.*

   

®☄
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ✍*
_{ɢαѕkíчα ɗαчα cє dαgα ƙíntα ѕαí ɓαtα, burínmu mu fαɗαkαr dα αl'ummα dσmín ríbαntαr duníчα dα kumα lαhírα.}_

         '''🎐ɢ•ᴡ•ᴀ🎐'''
*_ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴅᴏᴋɪɴ ᴋᴀʀғᴇ•_*🏇🏼


*ɴᴀ ᴍᴀʀᴜʙᴜᴄɪʏᴀ:-*
*Ꮣαnnαt  ᴍ. ɴαѕír✍🏼*
*ᴡαttpαd_@Ꮣannatмɴ*

*sᴀᴅᴀᴜᴋᴀʀᴡᴀ ɢᴀ :-*
*ᴍч  вlσσd  ѕíѕtєrѕ*
*ᴍαrчαm  ᴍ. ᴍαѕír(ᴍαnαв Ƴαr вαbα )*


ᴡᴀᴛᴛᴘᴀᴅ:- *ɢαѕkíчαᴡrítєrѕᴀѕѕσ.*
ɢᴍᴀɪʟ:-gαkíчαwrítєrѕαѕѕσcíαtíσn@gmail.cσm
ʏᴏᴜᴛᴜʙᴇ ᴄʜᴀɴɴᴇʟ:- *ɢᴀsᴋɪʏᴀ 24ᴛᴠ .*
ғᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ  ᴘᴀɢᴇ:- httpѕ://www.fαcєвσσk.cσm/ᴅσkínkαrfє2019/
ʙᴀᴋᴀɴᴅᴀᴍɪʏᴀ:-
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ's ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ.*

   
                 *😭ᴋᴜᴋᴀɴ  ᴋᴜʀᴄɪʏᴀ.....🕊(9)*

     _Ƴan uwa haƙuri iri biyu ne. Na farko haƙuri abin da kake so idan baka same shi ba. Na biyu haƙurin abin da baka so idan ya sa meka. Samu da rashi duk na Allah ne ƴan uwa, kuma ita duniya ba matabbata ba ce, yau gareka gobe ga waninka, sai ana kai zuciya nesa sannan ake samun cigaba a rayuwa. Ƴan uwa mu kasance masu haƙuri a kowane hali muka tsinci kanmu. Allah yasa mu dace, Ameen Ya Allah 👏🏻_

    

*sʜᴀғɪ ɴᴀ 29-30📑*

  
   
*__________📖* Idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir tsabar tashin hankalin da ya shiga har ƙwalla suka fara kawowa.
   
   
          Ayman da Aymana ma kanta sukayi suna kiran, "Umma! Umma! Ki tashi dan allah, meke damunki? Daddy me ya samu Ummanmu?" Banza yayi musu dan be san me zai ce musu ba, tashi yayi a matuƙar tashin hankali ya nemo ruwa me sanyi ya yayyafa mata shiru bata ko motsa ba, ganin haka yasa hankalinsa ya ƙara tashi, bai yi wata-wata ba ya sureta yayi waje ya sata a mota ya fice a guje sai asibiti.
   

          Bai wani ja dogon lokacin yana gudu akan titi ba ya ƙarasa asibitin dake kusa da su, cikin gaggawa aka shiga bawa Umma taimakon gaggawa likitoci ne burjit akanta sunfi awa biyar akanta, amma basu yi nasara samun sun farfaɗo da ita daga doguwar sumar da tayi, kuma a iya binciken da suka yi basu gano meye musabbabin kawo mata wannan cutar, haka suka kaita ICU ba tare da ta farka ba.

         Fitowa suka yi suka samu Daddy a bakin ƙofa ya haɗa kai da gwiwa ya rasa inda zai sa kansa, tsoronsa ɗaya kada ya rasa Umma kamar yadda ya rasa tsohuwar matarsa Amina, a lokacin da yake matsanancin buƙatarta, duk da yaso Amina sosai a baya, amma son da yakewa Umma yanzu yafi son da yakewa Amina, dan yanawa Umma so mafi soyuwa a rayuwarsa.

        Duk maganar da Dr. Mahmud ke yiwa Dadday bai jisu ba, domin ya daɗe da lulawa a cikin duniyar tunani, dafasa Dr. Mahmud yayi yace, "Alhaji!" A firgice Daddy ya farka daga duniyar tunanin da ya shiga, a ruɗe  ya shiga jero masa tambayoyi, "Dr ya matata take? Tana ina? Ta farka kuwa? Wane ɗakinta aka kaita?"

         Shiru Dr.Mahmud yayi ya rasa ta ina zai fara yiwa Daddy bayanin abinda ke faruwa, dan ya lura a matuƙar ruɗe yake, muddun ya faɗa masa abinda yake faruwa kai tsaye, to komai zai iya faruwa.

        Wani tunanin ya faɗo masa ya ɗan sashi murmusa tare da yin hamdala a cikin ransa, sannan ya ƙara duban Daddy a nutse yace, "Alhaji ka biyoni office zan yi maka bayani."

  
          Dum-dum Daddy ya ji zuciyarsa na bugawa tare dare da faɗuwar gaba lokaci ɗaya, jiki a sanyaye ya bi bayan Dr. Mahmud har zuwa office ɗin sa, kujerar da Dr.Mahmud yayi masa nuni da hannu alamu ya zauna a kanta ya zauna, yana fuskanta Dr ɗin zuciyarsa na ɗauke da fargaban abinda Dr.Mahmud zai gaya masa.

        Sai da Dr.Mahmud ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara yiwa Daddy ƴar nasiha akan karbar ƙadadda a duk yadda ta zo maka, da kuma yi masa tuni akan yin tawakkali akan duk abinda ya samu bawa, da ƴan abinda ba za a rasa ba sannan ya ɗan yi shiru yana kallan wane irin yanayi Daddy yake ciki a wannan lokacin.
   
   
         Hamdala yayi a cikin ransa ganin tsoro da ruɗun da yake ciki ɗazu ya ɗan kau, kuma ya hango tsantsar nutsuwa yanzu a cikin idanuwansa, hakan ya tabbatar masa da ɗan tunin da nasihar da yayi masa sun shigesa, kuma sunyi tasiri akansa.
   
   
        Gyara zamansa yayi yace,  "A gaskiya Alhaji matarka tana cikin wani mawuyacin hali, dan har yanzu ba mu yi nasarar farfaɗo da ita ba, kuma a iya binciken mu bamu ga abinda ya zama silar shigarta cikin wannan yanayin ba. Haƙiƙanin gaskiya a yadda nayi duba da wannan yanayinta, mu likitoci bamu da maganin da zamu bata ta dawo dai-dai, domin dukan alamu sun bayyana wannan yanayin da take ciki yafi kama da ƙirƙirare ne, ma'ana sihiri ke aiki akanta, duk asibinta da zaka kaita cin kuɗinka zasu yi kawai, amma ba zasu iya yi mata maganin ba. Roƙon Allah zaku koma, da neman mata maganin karya sihiri, da kuma taimakon Mallamai shine mafita kawai, indai har kana san samun lafiyar matarka, amma indai kace likitoci zaka rinƙa bi ina mai tabbatar maka ɓata maka lokacin kawai zasuyi ta yi, yanzu dai mun kaita ICU mun kwantar da ita, a duk lokacin da kuka shirya karɓar sallama zan baku, domin kuje ku fara yi mata roƙon Allah da karɓar mata taimakon Mallamai."
   
   
    Kallan Dr.Mahmud kawai yake yi ba ƙyafta ido, bakomai yake tunawa ba face shekaru shidda da suka wuce lokacin da ya fara haɗuwa da Umma, haka likintan da ya kaita asibitin ya gaya masa irin wanda likitan nan ya gaya masa yanzu.
   
   
    "Hmmm!" Wata nannauyar ajiyar zuciya Daddy ya sauke tare ambatan Allah a cikin ransa domin ya samu sassauci daga abinda yake ji sannan yace, "Dr na gode insha Allah zamu dage da roƙon Allah, da neman taimakon Mallamai a game da halin da take ciki, hakan ba baƙon abu bane, dan ta taɓa shiga irin wannan yanayi shekaru shidda sa suka wuce, kuma abinda ka gayan yanzu shi aka gaya min a baya, da muka yi mun ga ta samun sauƙin, na gode sosai Allah ya saka da alheri yanzu ka bamu sallamar kawai."
   
   
    Dr.Mahmud ba ƙaramin jin daɗi yayi ba ganin Daddy ya karɓi ƙaddarar da ta afkawa matarsa da hannu bibbiyu kuma yayi tawakkali, kai kawai ya jinjina sannan ya bawa Daddy sallama, taimaka masa sukayi suka saka masa ita a mota ya koma da ita gida a sumen.
   
   
     Ɗakinta ya kaita ya shimfiɗe ta a saman rantsatsan gadonta, Ayman da Aymana ne suka shigo ɗakin, zasu fara tambayarsa me ya samu Ummansu ya yayi musu nuni da su fita, fita suka yi suna kuka ganin haka ne yasa ya ƙara jin tausayin yaran nasa, gashi lokacin da suke buƙatar kulawa mahaifiyarsu ita kuma ba zata iya taɓuka musu komai ba, tsoronsa ɗaya kada abinda ya faru a baya ya sake maimaituwa, addu'a da roƙon Allah ya shiga yi a cikin ransa na kada hakan ya tabbata.

    Tashi yayi ya fito daga ɗakin ya jawo mata ƙofa, ya nufi ɗakinsu Ayman yana shiga ya tarar da Salma na rarrashin su, suna ganin sa suka yi kansa cikin kuka suke cewa, "Daddy dan Allah me ya samin Ummanmu? Ba ta mana magana kuma bata buɗe idonta, dan Allah Daddy me yasa Umma take mana wannan wasan?" Ƙanƙamesu yayi a jikinsa yana lallashinsu da suyi haƙuri suyi shiru, babu abinda zai samu Ummansu Insha Allah zata tashi lafiya ƙalau, sannan ya shaida musu Ummansu bata da lafiya ne su tayata da addu'ar Allah ya bata lafiya."
   
   
    Amsa masa suka yi da to, sannan yace musu kada su sake suyi hayaniya idan sunje wajenta saboda yin haka zai dameta, kaɗa kai sukayi alamun sunji duban Salma yayi yace, "Yanzu kin ga abinda ke faruwa da uwar ɗakin taki, shin zaki iya zama ki cigaba da aikin ko kuma tafiya zakiyi? dan komai nufi ne na Allah kuma bamu da tabbacin yaushe zata dawo hayyacinta." 
   
   
    "Ba zan guji Umma ba a yanzu da take buƙatar taimakona, Umma tayi min abinda ko uwar da takawo ni duniya ba tayi min shi ba, ta ɗauke ni tamkar ƴar da ta haifa da cikinta, zan zauna na kular mata da yaranta kamar yadda ta kula da ni har Allah ya bata lafiya."
   
   
    Tabbas Daddy ya ji daɗin kalaman Salma farin cikin ne ya bayyana akan fuskarsa ƙarara, domin yasan mudun Salma ta gujesu bai san ina zai saka ransa ba, saboda su twin's ban da Ummansu da Yayansu da kuma shi babu wanda suka saba da shi suke rayuwar jin daɗi da shi sama da Salma, gashi yanzu ba Umman nasu ba kuma Yayansu shi kuma ba zai iya kula dasu yadda ya kamata ba, kuma bayan Ummansu ita kaɗai ce tasan me suke so meye basa so, godiya ya shiga da yi mata sannan yace "Dan Allah ki kula min da yaran nan kamar yadda Ummansu ke kula da su na baki amanar su, kuma zan linka miki abinda Hajiya take baki a wata kin ji."
   
   
    Girgiza kai tayi alamun a'a tace, "Bana buƙatar kuɗi wajen kula da Umma da su Ayman, ina karɓi kuɗinka Daddy kamar na aikata butulci ne a rayuwata, domin Allah zan yi wannan kuma insha Allah zan riƙe amanar da ka ban, kuma na kula da ita fiye da yadda zan kula da kaina." Godiya yayi mata sosai yace mata zai je ya dawo ta kula masa da yaran, amsa masa tayi da yi masa a dawo lafiya.
   
   
    Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan mahaifiyarsa ya shaida mata abinda ke faruwa, a matuƙar tashin hankali ta shiga haɗa kayanta suka baro gidan sai gidan mallamin da ya taɓa taimakonsu a shekarun baya Umma ta warke da izinin Allah.
   
   
    Suka shaida masa abinda ke faruwa girgiza kai kawai ya rinƙa yi, yace suje ya ga halinsa take ciki sannan sai a san ta inda za a ɓullowa lamarin, haka suka ƙara ɗugunzumowa suka dawo gidan, har ɗakin da take kwance Mallamin ya shiga ya ganta, haƙiƙa babu wanda bai tausayawa Umma ba, domin har kamaninta sun fara janzawa duk tayi wani baƙi, ruwa yace a bashi a kofi a gurguje Salma ta je ta samo ruwa a ƙofi ta kawo masa, karɓar yayi yarinƙa karanta addu'o'i da ayoyin Alkur'ani yana tofawa a ruwan da ke cikin ƙofin, ya ɗauki lokaci yana haka sannan ya miƙawa Daddy ƙofin yace, "Buɗe bakinta ka zuba mata wannan ruwan addu'ar, sannan ka shafe mata jikinta da sauran mu jira ikon Allah." Yadda Malam yace yayi haka yayi a takiyanke, ya koma gefe yana kallanta kowa na san ya ga me zai me zai biyo baya, miti goma har zuwa ishirin babu abinda ya faru har sun fara sarewa da samun nasara, minti talatin ma shiru har Mallam ya miƙe zai tafiya gida yayo mata rubutu, sai Allah ya nuna musu ikonsa akanta, idonta ta buɗe tana kallan silin ɗakin hamdala suka shiga yi Hajiya tsohuwa har da ƙwallar farin ciki.

   
     Sauke idanta ta rinƙa yi akan mutan dake  ɗakin kallansu take ɗaya bayan ɗaya alamun bata gane kowa a cikinsu ba, ganin irin kallan da take musune yasa zuciyar Hajiya tsohuwa da ta Daddy bugawa da ƙarfi, zuciyoyinsu na ayyana musu shikenan ta faru ta ƙare abinda suke gudu ya tabbata.
   
   
    Sannu suka shiga yi mata amma babu wanda ta iya amsawa sai dai akwai ta bi duk wanda yace mata sannu da idanuwa, tashi take san tayi amma ta kasa motsa duk wata gaɓar dake jikinta, bakin nata ma tana san tai magana amma ta kasa buɗe shi, Mallam duk ya fahimci abinda ke faruwa da ita sai ya miƙe yace su biyosa falo.
   
   
     Gaba ɗayansu suka biyosa falon dan jin meke faruwa, suna zuwa yace musu, "Shekarar baya ce ta sake maimaita kanta, amma wannan karan da wani sabon salo tai maimaituwa, yanzu haka ta manta abinda ya faru da ita amma ba kamar a da ba, dan a yadda na kalli yanayinta zata iya tunawa da ku, domin rayuwar da kuka yi da ita bata manta ita ba har cikin kanta, zata iya tunawa da ku a hankali idan kuka rabu da ita baku ƙara takura mata ba, kuma ba zata iya motsa gaɓobin jikita ba ballantan ma tayi magana." Ya kuma gargaɗe su da kada su kuskure su ce zasu yi ƙoƙarin tuna mata da wani abinda ya faru da ita a baya, ya kuma kara musu da cewa, " Yin hakan yana iya ƙara jefata cikin mawuyacin hali, wanda na tabbata yanzu ma wani abinda ya shafi rayuwarta ta baya aka gaya mata, ta fara tunani akansa shiyasa ta shiga cikin wannan halin."

         A matuƙar tashin hankali Daddy, Hajiya tsohuwa da Salam suka kalli mallamin, wannan karan Daddy kasa riƙe kansa yayi sai da ya fashe da matsancin kuka mai tsuma zuciyar me sauraro, a ranshi yana tunani wanene wanda ya aikata masa wannan mumunan laifi da zai gaya wa matarsa abinda ya shafi rayuwarta ta baya, da ace zai ga wanda yayi masa haka da babu abin da zai hana bai ɗauresa ba.

       Cikin tausayawa ɗan nata Hajiya tsohuwa ta jawo shi jikinta, Lallaishinshi ta shiga yi tana mai bashi haƙuri, tare da yi masa tuni da yarda da ƙaddara, duk da itama ɗaurewa kawai take amma idanuwanta basu daina zubar da hawaye ba, sallama Mallam yayi musu tare da ƙara gargaɗarsu akan su kiyaye abinda yace musu, sannan yace zai je ya fara shiryawa lamarin Ummu, ya kuma ce musu suma su dage da addu'a da roƙon Allah lamarin nata sai da roƙon Allah. Kai kawai suka kaɗa masa, babu wanda ya iya ce masa ƙala saboda halin da suke ciki ba zasu iya masa magana ba.

 
    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu ba daɗi har tsawon wata uku, domin al'amarin Umma ya fara basu tsoro dan yanzu halittuta ke rikiɗewa daga safe zuwa dare, duk da kalar da take komawa kuma bata iya cin abinci sai dai a ɗura mata shima mai ruwa-ruwa, kuma ana ɗura mata rabi na shiga rabi na dawowa komai su Salam ke yi mata, kula da su Aymana kuwa shima yi take ba dare ba rana, Hajiya tsohuwa ma ta dawo gidan da zama domin su rinƙa kula da ita tare, duk daren Allah Ayman da Aymana da Daddy a gefen Umma suke kwanaciya suyi barcin su har safiya, babu wanda yake yin yikurin tuna mata shi ko waye a wajenta hatta su ma Aymana kuwa.
   
   
     Lamarin Abdallah kuwa Daddy ya hana kowa ya faɗa masa meke faruwa da Ummansa, a kullum ya tambayeta sai suce masa tana wani uzuri ne bata kusa, ko ya tambayi su Aymana basa cewa komai sai dai su ƙara maimaita masa abinda ake gaya masa, tun yana damuwa akan rashin gaisawarsa da Ummansa har ya daina dan Daddy yace masa bai yarda ya tako ƙasar Nigeria ba muddun ba kammala karatunsa yayi ba.
   
   
     Suna cikin wannan hali ne har tsawon wata bakwai kullum basa gajiya da nemon mata roƙon Allah, a cikin wata na takwas ne Umma ta fara tuna rayuwarta da su, yanzu kowa ta kalla ta sansa dan an ƙara samun cigaba tana yiwa wanda suke gewaye da ita murmushi, amma bata iya buɗe baki tayi magana kuma bata tafiya sai an kwantar an tayar....

   

  
_*See me next page✍🏻*_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   




   
*©JANNAT M. NASIR•*

Continuă lectura

O să-ți placă și

264K 10.3K 32
""SIT THERE AND TAKE IT LIKE A GOOD GIRL"" YOU,DIRTY,DIRTY GIRL ,I WAS TALKING ABOUT THE BOOK🌝🌚
233K 27.3K 120
Genre- Drama Fantasy Historical Romance Slice of Life Author(s)- 静似骄阳 Associated Names- 穿书七零:我的炮灰丈夫十项全能 Eng Name- Transmigrating into a Novel: My Can...
75.1K 1.9K 69
"mom, dad, Im married!" lahat ng relatives namin ay nagulat sa announcment ko. Sino ba naman kasi ang mag aakala na ang unica ija ng pamilyang Letpr...
192K 4.7K 110
As the Maid of Evil, Y/n sacrifices her life for her twin brother. As the Mist Hashira, Y/n sacrifices her life for humanity. But not anymore will Y...