A SANADIN SOYAYYAR MINTI

By JameelarhSadiq

6.1K 164 14

Lanarine wanda ya kunshi soyayya da makirci ban tausayi abubuwa da yawa fa More

A SANADIN SOYAYYAR MINTI
3&4 kuyi vote and comment pls
5&6
7&8
9&10
11&12
13&14
Sau biyu nasa 13&14 nayi mistake
15&16
17&18
19&20
21&22
23&24
25&26
27&28
29&30
31&32
33&34
35&36
37&38
39&40
41&42
43&44

47&48

208 11 3
By JameelarhSadiq

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 47⏩48

*Sannunku da kokari myreal fan's, kuna nuna man kauna wajen karanta wannan buk din gami da yi man comment, sannan kuma shi comment dinku maganar gaskiya yana sani farinciki sosai da Sosai, fatana dai Allah ya bar kauna ta fissabilillah, dan kuwa ina maku son fissabilillah 💜*

*Tom page din yau sai dai ayi hakuri, dan dole a samu winner da kuma loser tsakanin TEAM UKU, da Team din AMINU sai  Team din Nurandeen sannan kuma Team din Dr Umar🌚, Allah yaba mai rabo sa'a kawai nidai zani ce😊*

Numfasawa Nurandeen yayi sannan yaci gaba da cewa. "Haka muka tafi unguwar su Aziza dan samun wanda Allah zai sa yace ya santa dan, dan kuwa addu'a tun ina wanda na sani har sai da yakai da ina yin addu'a kawai amman bansan abunda nike cewa ba tsabar shiga tashin hankali da nayi a ranar, cikin ikon Allah muka isa unguwar majoji nan muka raba ƙafa kowa da hoto a hannunshi muka fara nuna ma mutane ko sun san wannan baiwar Allahr, amman ansa ɗaya a'a bansan sanda kuka ya ida ƙwaceman ba saboda shiga ruɗu da nayi nidai bani ansa gawar Aziza saboda gidanmu ba'a santa , idan n kaita mai zance masu game da ita? Ita ba accident tayi ba balle na kaita gidanmu nace ba'a san danginta ba su taimakaman ayi mata sutura akaita gidanta na gaskiya, amman a hotel ta mutu suna zina, kinga dole mutuwarta tayi suna a faɗin nigeria Khadija, nidai bansan ina nike takawa ba kawai jefa ƙafa nike, sannna duk wanda na gani sai na nuna mashi picture dinta koda kuwa ƙaramin yaro ne wanda baisan kowa ba a unguwar, cikin ikon Allah naga wani matashin saurayi kamar ni koda ya girmeni ba zai wuce ya girmeni da shekara ɗaya ba, amman bada shekara biyu ba, zaune yake bakin wani shago a unguwar ga dukan alamu shagon nashi ne ma, ida zuwa nayi wajen shi na nuna mashi picture din nace ko ya santa, kallona ya tsaya yi sannan yace man ina na samu wannan picture din? Ce mashi nayi gidansu yarinyar ake nema a unguwar nan, dan Allah idan ya sani ya taimaka ya gayaman dan ana son gani iyayenta ne, girgiza kai mutumin yayi sannan yace ai na santa karka damu bari na kulle shagon na kai ka har gidansu, ai bansan sanda na rungume shi ba,na kuma fashewa da sabon kuka, kallona yake yana mamaki sannan yace kukan mai kakeyi ne bawan Allah, girgiza mashi kai nayi sannan nace nidai dan Allah abokina ka kulle shagon ka kaini gidansu kaji komai maiye idan muje, muna cikin magana muka hadu da mutumin da mukazo dashi , kallona yayi sannan yace fatan kai ka dace ka samu wanda ya santa ko? Bansan sanda Murmushi ya kauceman ba, na ɗaga mashi kai ina nuna mashi mai shagon nan, shima zuwa yayi yace mu tafi."


"Nan muka tafi mu dukanmu ba wanda yake  magana, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyarshi Khadija, wani babban gida muka iso, dan gida yana da kyau ba laifi tsayawa mukayi bakin gate wannan mutumin ya shiga ciki bai jimaba sai gashi yace mu shigo, tare muka shigo dan harda police muke ni ban ma lura da wasu police ba sai lokacin da zamu shiga cikin gidansu, muna shiga aka kaimu part din baƙi nan muka zauna munyi jiran kusa ten minutes sai ga wannan mai shago ya shigo mana da ruwa da lemu yace kuyi hakuri mun barku zaune, ga Baban nan zuwa yanzun ya dawo baya gida, amman na kira shi waya yama shigo ya shiga part din shi dan ya rage kayan jikinshi, da sauri na ɗago kaina aiko muka haɗa ido biyu da wannan mutumin nan naga yana yar'kama Aziza, sauke kaina nayi kasa ban sake ɗagowa ba, can sai ga Babanta ya shigo da sallama a bakinshi, ansawa mukayi sannan muka bashi hannu aka gaisa, bayan an gama angaisawa aka fiddo picture din Aziza aka nuna mashi aka wannan yarinyar ƴarka ce."?

"Allah sarki ɗaga kai yayi kawai amman baiyi mana magana ba, kuma na lura tunda aka nuna mashi picture din Aziza fuskarshi ta chanza ta tashi daga walwala ta koma rashin walwala, tunda muka lura da yanda yanayin shi ya koma sai muka kasa yi mashi bayanin abunda ya kawo mu, daurewa wannan mutumin yayi sannan yace Alhaji hannunka ba zai ruɓeba ka yanke ka yada, duk abunda Aziza tayi maka ya wuce dan Allah ka yafe mata, dan yanzun ba abunda Aziza take bukata a wajen ku idan ba wannna yafiya ba, sannan kuma addu'a idan har kuka yi mata haka to kun gama mata komai kuma kunyi mata abunda ita ta kasa yi maku, dan Allah Alhaji karkace ba zaka yafema ƴarka ba ƴarka ce ta cikinka komai tayi maka ayi hakuri kar a tuna baya a yafe mata."

"Tunda ya fara maganar Baban Aziza yake kallonshi har ya gama, sannan shima yace Bawam Allah ai Aziza da bakintaa tace ni ba ubanta bane, sannan kuma tace man na manta da na taɓa haihuwar wata mai suna Aziza kuka ya fashe dashi ya cigaba da cewa yarinyar nan ta zaɓi wata gurba marar kyau nida yan'uwa ba yanda bamuyi da ita ba akan tabar wannan ƙazamar rayuwa amman tayi kunnan uwar shegu damu, kaga wannna har aure sai da na daura mashi da ita, ranar da aka daura masu aure a ranar ta gudu daga nan bamu sake ganinta ba, koda kuwa labarinta ban sake ji ba sai yau ku da kuka zo mana da labarinta, daman ai haka bariki take angama yayinta shine aka dawoman da ita ko? To wallahi bani ansarta taje ta cigaba da rayuwar da ta ga itace ta dace da ita."

"Dafashi wani police yayi sannan yace hakuri zakayi Alhaji dan yanzun haka Aziza bata bisa doron duniya, Allah S. T.W ya anshi rain Aziza dan kuwa yana hannunshi sai dai mai Aziza ta mutu ta hanyar da mai kyau ba dan kuwa a hotel ta mutu suna aikata *Zina* da wani wanda ba ma addininsu ɗaya ba, a haka rai yayi halinsa da akazo gyara room aka tadda gawarsu sai muka kira wannan bawan Allah ya nunani sanna ya cigaba da cewa munsa matarshi ce dan tayi saving din sunanshi da *Mijina* koda yazo yaga gawarta ya tsorata sosai kuma har yanzun bai daina kuka ba, yace mana baisan tana wannan harkar ba shi dai yana soyayya da ita suna shirin auren juna, sai yace mana ta taɓa ce mashi ita yar majoji ce, amman bai taba zuwa gidansu ba shine muka shigo majoji dan nemo gidansu yanzun haka gawarta ta hanya dan anraba gawar anba ancan nasu kuma mun bada address za'a kawo maku taku."

"Tashi tsaye Babansu yayi sannan yace inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Aziza tabbas kinyi mutuwar asara sai dai muna rokan Allah ya yafe maki nidai ko na yafe maki ƴata na yafe maki har abada inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Asiya Allah ya baiyanaman ke cikin aminci tabbas alhaƙin Asiya shine yake biyayarmu a gidan nan, alhakin marainiyar Allah shine yake biyayarmu Allah na tuba, tabbas na kasance uba marar kyautatama iyalansa, kallonshi muka fara yi sannam akace wacece Asiya? Ce mana yayi Asiya ɗiyarshi ce ta cikinshi mahaifiyarta ta rasu ta barta cikin matanshi suka matsa mata bata da gata sai su Aziza da suke da uwa a cikin gida ba soyayyar da bai nuna ma su Aziza ba da iyayensu amman banda Asiya da tazama baiwa a gidansu Aziza dan duk wani aikin bauta Asiya ce take yinshi lokacin da suna zaune a kunya chemist ɓarayi suka shigo gidansu nan sukayi ma Asiya fyaɗe yace mana yayi kuka a lokacin daga baya matanshi suka zugashi akan Asiya ta samu hanya tana bin maza tunda taga ɓarayi sunyi mata hanya, da bani yarda sai daga baya na fara yarda sai kuma ga ciki ya baiyana a jikin Asiya ni kuma ido ya rufe sai nace wajen iskanci ta samaishi dan daga yi mata fyaɗe rana ɗaya ciki ba zai shiga ba, da bakina da kaina na kori Asiya a gidana haka ta tafi tana kuka, ni kuma a lokacin ko a jikina dan gani nike ba zan yarda ba a haifa man shege a gidana ba, haka ta tafi muka cigaba da rayuwar mu cikin gidanmu muka manta da Asiya, bamu damu da wani hali take ciki ba sai ga Aziza ta bullo da halin bin maza na girgiza sosai tana level one a university ba faɗan da banyi mata ba, karshe na aure mata aure da Kamalu gashi nan ɗan ƙanenane amman sai ta gudu, bayan ta gudu kuma ƙanwarta ita kuma take neman mata😭, yanzun haka sana'arta kenan bin mata take dan itama ta tashi ta barman gidan tana zaman kanta, in kaiku karshe yanzun haka baki ɗaya yarana bana maijin magana daga mai shaye shaye sai mai yi ma ciki, yaran Amarya tane kawai masu ji su biyu ne suma ba wani girma sukayi ba sosai balle nasan ya nasu girma zai zo masu, inalillahi wa'inna'alaihirajiun 😭, wallahi Khadija sosai labarin Baban Aziza ya samu kuka muna cikin kukan akazo da gawar Aziza nan kuka ya zama sabo, haka aka gaya ma matan gida kamar anbusa isul haka unguwar ta kaure da rasuwarta haka muka hadu muka sallaci gawar Aziza muka rakata gidanta na gaskiya, bayan mutuwar da kwana uku nabar zuwa gidan su Aziza, kinji yanda karshen Aziza yazo Khadija dan Allah Khadija ki yafema Aziza na rokeki ki yafe mata dan al'farma Annabi Muhammad S. A. W."

Shiru nayi kawai ina hawaye dan har ga Allah naji mutuwar Aziza sosai, duk da ta bada gudumuwa wajen lalacewar rayuwata amman nasan harda laifina ba laifinta bane dan nice na bata fuska har ta sani a hanya, nayi mamaki da naji Aziza ƙanwar Aunty Asiya ce ji yayi shirun yayi yawa naji yace.

"Khadija ya naji kinyi shiru say something please Khadija." Nima ajiyar zuciya nayi sannan nace "tabbas naji mutuwar Aziza sosai Noor, na yafe mata balle ma batayi man komai ba, tunda komai ya faru dani bata sani nayi dole ba, asalima iyakacinta dai kawai ta bani shawara nice nan mai laifi da na biyema son zuciyata na aikata aikin da nasani, kuma da nasani ance ƙeyace kuma kuskure na riga na aikata sai dai mu roki Allah ya yafemana baki ɗayan mu, ita kuma Allah ya kyauta makwancinta Amin."

Ajiyar zuciya naji yayi sannan yace "Alhmdullh Allah abun godiya tabbas Khadija keɗin ta daban ce kina da kyawkywan hali, wallahi halinki mai kyau ne wallahi Khadija ina sonki ba zan iya rayuwa babu ke ba dan Allah Khadija ki yafeman mu auri juna mu rufama junanmu asiri Khadija, ki tuna son da kika nunaman a baya ki maidoshi wallahi zan kula dake sannan kuma zan baki kulawa ta mussaman wanda ba zakiyi tunani ba Khadija, kin... "Ya isa haka enough please Noor, har da sauran soyayya a tsakanin mu daman? Har kana da bakin da zaka dawoman da soyayyarka a cikin zuciya ta? Kayi hakuri Noor tabbas ka faɗi gaskiya da na soka so wanda na sani har na mutu ba wanda zan ƙara yi ma irinshi sai dai yanzun kayi hakuri ba zan iya aurenka ba, ina maka fatan Allah ya baka wanda ta fini." ina gama faɗa mashi haka ban barshi yayi magana ba na kashe wayar baki ɗaya na kalli su Aunty Asiya da suka zuban ido tunda na fara wayar cewa nayi.

"Daman bakuyi bacci ba."? Ɗaga man kai kawai Dejja tayi sannan tace. "Taya zamuyi bacci, bayan munji kinata salati harda kuka, mai kuma shi Nurandeen ɗin ya gaya maki."? Murmushi na ƙalilo mai ciwo sannan nace. "Aunty Asiya ina tambayeki mana."? Nayi mata maganar ina murmushi na samu na kauda damuwar da ke raina dan bansan na tada mata hankali duk da inajin ɗaci da ciwo na mutuwar Aziza, itama murmushin tayi sannan tace "tambayarni ina jinki Khady." kallonta nayi sannan nace. "Daman da kukaje kano kai da su Mama bakuje kuka gaida su Baba ba da matanshi."

Chanza fuska ta ɗan yi alamun tambayar bata yi mata dadi ba, kallon juna mu kayi da Dejja tayi man alamun mai yasa nayi mata tambayar sai na nuna mata ba komai, maida kalona nayi gareta nace. "Yi hakuri Auntyna bansan tambayar zata ɓata maki rai ba da banyi maki ita ba." kamo hannuna tayi tana murmushi sannan tace. "Ko ɗaya Khady, kawai dai nayi mamakin tambayar ne, ai ni bani zuwa gidanmu har abada, Baba da bakinsa yace na bar mashi gida, kinga kenan da hannunshi ya yankan man ticket din shiga duniya, Kinga kenan banga amfanin komawa wajen shi ba tunda ni yar'iska ce ina neman maza har sunyi man ciki, Khady ba amfanin komawa karda na koyama yaranshi bin maza."

Girgiza mata kai nayi sannan nace. "Dan Allah kiyi hakuri ki sasanta da Baba, nasan yayi nadamar abunda yayi maki Aunty kin manta kece kika maidoni gida? Maiyasa ke ba zaki sasanta da Baba ba ki maida komai ba komai ba please Auntyna." murmushi tayi sannan tace. "Zan koma gida saboda ke Khady, amman ba yanzun zan koma ba sai nayi aure may be har haihuwa sai nayi sannan zan koma masu da mutuncina, su san na cigaba ba baya ba."murmushi nayi sannan nace. "To fatan ankusa auren ko."? Dariya tayi sannan tace. "Ai naso gaya maku tunda kuka dawo sai naga kina cikin damuwa shiyasa ban gaya maku ba."

Dariya Dejja tayi sannan tace. "Wallahi Aunty ni nasan zakiyi aure kuma nasan Baba zaki aure." kallon Dejja nayi cikin surprise nace. "Ke wai wane Baban? Ba dai Yaya Jamilu ba."? Cewa tayi."ehmana shi, kiji Aunty Auta daman ina da wani Baban bayan shi."? Girgiza mata kai nayi ina dariya dan naji dadin yanda Yaya zai auri Auntyna, kallanmu tayi taga yanda muke ta farinciki tace. "Ku yanzun bakuji haushi ba? Bama kamar ke Dejja da za'ayi ma Mamanki abokiyar zama."? Girgiza kai Dejja tayi sannan tace. "Wallahi ba abunda mukeji harda Momy dan Momy ta gayaman yanda akayi har ƙin yarda da kikayi sai da aka sha wuya ai mun zama ɗaya Aunty kuma da zuciya ɗaya muke zaune dake, da yaje ya auro wata wanda bamu sani ba fa? Ai kinga gwara ke mudai fatanmu Allah ya bamu zaman lafiya."

"Amin ya Allah."nace dan kuwa Aunty kasa magana tayi, kallon su na sake yi sannan nace. "Dejja kinsan kuwa Aziza ta mutu."? Kallona tayi sannan tace. "Taya zan sani Aunty Auta? Allah ya jikanta da rahama muma Allah yasa mu cika da imani."
Banji dadin yanda Dejja ta nuna rashin damuwarta ba, akan mutuwar Aziza sai dai kawai nayi murmushi nace. "Amin, ni zan kwanta sai da safenku."
Haka na kwanta ina tuna da nawa da Aziza kuma ina mata addu'ar dace wajen maiduka.

*Some weeks letter*

Washe gari da safe muka shirya mukaje gidan Aunty Fatima mun daɗe sosai, nidai ina cikin damuwa sosai akan masoyana guda uku, dan har ga Allah duka nike sonsu duk wanda na aura ina so, to taya zan fidda indan akace na fidda wanda ya dace da ya zama abokin rayuwata? Idan na tuna abun yakan sani cikin damuwa dan Yau da safe Mama tace mu fara shirin fidda miji dan aure za'ayi mana mun ida karatun a gidan mazajenmu, kuma Yaya Jamilu ya yarda da shawarar Mama yace ana gama bikinshi da Aunty muma za'ayi namu, hakan ya saman damuwa sosai.

Kallona Yaya Fatima tayi sannan tace. "Wai Auta mai ke damunki naga baki cikin wata walwala sai kace an gaya maki sakon mutuwa."? Murmushi nayi na kwantar da kaina bisa ƙafaɗarta sannan nace. "Bakomai kawai ina tunanin wa zan fidda cikin masu sona guda uku shine kawai damuwar Yaya." ɗago da kaina tayi tana kallona sannna tace. "Ikon Allah bangane masoya guda uku ba? Daman kina da wanda ya dace ki aura inba Aminu ba."?

Banyi mamakin tambayar Yaya Fatima ba, dan nasan su duka Aminu suke so na aura bayan kuma bashi ya dace ya zama miji a gareni ba, tabbas Aminu masoyina ne kuma masoyi na gaskiya sai dai ina tsoran ranar da zaiyi man gora akan rashin bashi kyautar budurci, amman idan na auri Nurandden shikenan ba batun gori danshi ya fara sani na, murmushi kawai nayi sannan nace. "Ehmana Yaya Fatima akwai Dr Umar da kuma Nurandeen, kuma duka suna zuwa gida."

Murtuƙe fuska tayi sannan tace. "Daman ke har yanzun baki san ciwon kanki ba Auta? daman baki kishin ƙanki ban sani ba? Taya za'ayi ace kina kula wanda ya lalata maki rayuwa har yanzun? Kina sashi a jerin masoyanki Khadija? Wai Khadija yaushe zakiyi hankali kinsan inda yake maki ciwo? Wai... "Amman Yaya Fatima fissabillah ya kamata ki duba wani shine ya ɓataman rayuwa shine ya dace na aura dana auri wani yazo daga baya yanaman gori ko."? Na ida maganar ina shirin yi mata kuka, dan nasa araina bani auren Dr da Aminu dan basu suka dace da su aureni ba, Nurandden shine ya dace ya aureni ya zama miji a gareni, kallona kawai tayi sannan tace. "Tashi ki barman gida dan ubanki tun kafin ranki ya ɓaci kuma ki sani ba wanda zamu aura maki idan ba Aminu ba, ki rubuta ki ajiye shasha wanda bata san maiye rayuwa ba." tashi nayi ina gunguni, itama Dejja tashi  tayi ranta ɓace dan duk taji abunda mukace da Yaya Fatima haka tasa driver ya maidomu gida bamuyi rabuwar arziƙi ba.

Itama Dejja bata ce man komai ba, koda muka koma gida da yake mutane sun fara zuwa ana hidimar bikin Aunty da Yaya dan sauran kwana biyu daurin aure, wanka mukayi muka huta Dejja ta dauko mana abinci mukaci, kallona tayi sannan tace. "Yanzun Aunty Auta da gaske Noor zaki ba dama ba Uncle Aminu ba."!? Cikin tsoro da tarin damuwa a fuskarta tayi man magana, itam Aunty Asiya da saura ta ida isowa wajenmu ta sama room din key tazo ta zauna ta zubaman ido tana jiran ansar da zan ba Dejja, su duka na kalla naga suna cikin damuwa girgiza kai nayi dan nasan nafisu damuwa dan kawai ni ta zama jinin jikina ne shiyasa, cewa nayi. "Insha Allah Dejja, Noor zan aura da yarda Allah." tashi tayi zauna tana girgiza kai tace. "No! No!! No!!! Impossible wallahi Aunty Auta, anya kuwa kina cikin hankalinki kodai Noor asiri yayi maki yasa kika fita cikin tunaninki Khadija Bello."!? Cikin masifa Dejja tayi man tambayar, nima tashi nayi nace mata. "Tabbas ina cikin hankalina kuma nasan abunda nike ba asiri Noor yayi man Khadija Jamilu Bello."

Tashi Aunty Asiya tayi taga faɗa yana shirin kaurewa tsakanina da Dejja, kallona tayi sannan tace. "Bamai yi maki dole Khady, amman kuwa kina da hankali a yau ɗinan? Shin Khady a barshi kina cikin hankalinki to mai yasa zaki auri wanda ya wulakanta maki rayuwa yaci maki mutinci gaban Dejja kodai kin manta abubuwan da yayi maki? Idan kin manta zauna mu sai mu tuna maki Khady."

Murmushi nayi sannan nace. "Tabbas ban manta abunda Noor yayi man ba, dan kuwa har na mutu ba zan manta da abunda yayi man ba, sai dai ku sani zan aureshi saboda na cika wani burin nawa a kanshi,  kuma wallahi sai na aureshi ni kaɗa nasan abunda yasa zan aureshi kuma ba zan gaya maku ba, sannan karku matsaman na roƙeku Allah yaba Aminu wanda tafini, amman ku sani babu rabon aure tsakanina dashi."

Su duka shiru sukayi ba wanda tayi man magana, nocking din ɗakinmu akayi na tashi na buɗe abun har mamaki ya bani ganin su Yaya Fatima su dukansu sukazo kuma nasan aikin Yaya Fatima ne dan ta iya haɗa meeting din cikin yan lokaci shigowa sukayi suka kulle kofa Yaya Amina ce ta fara magana tace. "Sannu uwar masu hankali, wallahi Auta yau na ida yarda da baki da hankali mai zakiyi da wanda ya wulakanta maki rayuwa yaci maki mutinci ya rabaki da martabarki."? Kuka kawai na fashe dashi sannan nace. "Haba dan Allah ya dace kuyi man uzuri ku barni na auri Noor shi Aminu yayi hakuri haka Allah ya kaddara." Yaya Aisha ce tace. "Kika dai kaddara ma kanki Auta, ya kamata ki duba Auta wallahi Aminu shine masoyinki na gaskiya ba Nurandeen ba Auta kinji yar'autar Mama." murmushi nayi sannan nace tabbas nasan Aminu shine masoyin na gaskiya amman a haka zan hakura dashi na auri Noor dan kawai na ida wani buri na a kanshi."

"Wai wani buri ne har haka Auta."? Kallon Yaya Fatima nayi sannan nace. "Zaku ganshi idan na cikashi, yan'uwa kuyi hakuri nasan yau na ɓata maku amman haka Allah Ya kaddara karki damu." cewa sukayi a tare. "Allah ya zaɓa maki alkhari Auta mu zamu tafi."
"Amin." nace na kwanta su kuma suka kama gabansu a daren na shedama Nurandeen yazo gobe inason ganinshi haka a daren na shedama Aminu shima ya shigo gobe inason gani magana dashi, sannan na kashe waya na kwanta bacci.

Washe gari da safe na shirya ma zuwan nasu cikin ikon Allah Aminu ya fara zuwa bai jima da zuwa ba sai ga Noor shima yazo, tare  na anshesu na kaiku ɗakin baƙi bayan sun gama shan ruwa na shigo kallonsu nayi sannan nace....


Share
Comment
And
Vote

Continue Reading

You'll Also Like

333K 10K 81
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
80.6K 3.6K 164
Mo Chen traveled to the Collapse World and obtained a character strategy simulator. In simulation after simulation, he conquered the conquerable char...
39.6K 3.6K 10
Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan ๐Ÿ’—