3&4

15 0 0
                                    

💓💔💓💔💓💔

        *SON ZUCIYA NE*

          💓💔💓💔💔
(A hrt touching story)

BY
*RABI'ATU AHMAD MU'AZU* ( _Rubby_)



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Sadaukarwa ga:anty haleema (Mrs basheer )
         &
Zahra Abdul (momyn ahlan\in law)
Allah ya bar zumunci da kana,na gode.

  Wannan shafin nakine anty fauzah(Yar amana) na gode kwarai da gaske abisa kauna da karamcin da kika gwada min, thank u so much.
#one luv.

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_Page 3 & 4_

Na dade a tsaye ba tare da na fita ba duk da nasan hakan ma wani laifin nake kara ma kaina,amma ZUCIYATA sai lugude take kamar tana injin niƙa.
Nasan ina son KB kuma ina masifar tsoron shi amma fa hakan be hana kaina hayaki ba kuma ina tare da wasu samarin saboda yadda ake fasa min kai cewar ni MATAR MANYA CE, ajiyar zuciya na sauke tare da dauko hijabi na ash colour da flat shoe shima ash na saka tare da fesa turare na fice.
 
"Ummynah zan tsaya a waje tukunnah kafin na karasa gidan Atikan saboda kabeer ya zo" washe baki tayi tare da fadin.
"To Najlata sai kin dawo"  ficewa nayi tare da nufar waje kirjina yana dukan uku-uku, kai tsaye inda motar shi take na nufa na bude, Shiga nayi tare da yin sallama amma bai amsa ba saima wata harara daya galla min hakan ne yasa nayi saurin jawo kofar motar na rufe.
    "Najla me yasa Idan na fada miki magana bakya ji? kin raina ni ko?" girgiza kai nake ba tare da nace komai ba, cigaba ya yi da fadin.
"Duk abin da kike kallon ki kawai na ke yi, kuma wlh zanyi maganinki, sau nawa zan fada miki ki karna sake ganin ki da Mahmoud amma bakya ji saboda kin mai dani dan iska koh?"
"a'a wlh cwthrt ka fahimce ni Mahmud ba wajena ya zo ba,ya zo wajan Asma'u ne amma kawai ka yanke danyan hukunci"
"Shihhh!!" ya fada alamun na masa shiru ai kuwa na ja bakina na tsuke tare da jinkina da seat din motar ina fata Allah yasa ya yarda da karyar dana masa duk da nasan abune mai wuya dan yana da saurin dagoni.
"hmmmm Najla ke nan, wato bayan rainani ma da ki ka yi har sakarai na koma ko? to fita min a mota tun kafin ranki ya baci!!" fashewa nayi da kuka ina cewa.
"dan Allah kayi hakuri,karka hukuntani,kasan bazan iya jure fushinka ba, naji nayi laifi amma bazan sake ba I promise u"  na kara sakin wani marayan kuka Wanda nasan shi kadai ne zai sa shi sakkowa tun da baya son kuka na ai kuwa rudewa ya yi tare da fadin.
"To shikenan kiyi shiru ya wuce amma wlh kika kuma sai na zaneki kuma kin San zan iya koh?"  share hawayena nayi ina kara janyo hijabi na dan ya rufe min kafafu dan bana so ya ga kayan da suke jikina.
"Ina Ummynah?"
"Tana gida" na ba shi amsa.
"OK to dama gobe Idan Allah ya kaimu zan tafi Kaduna meeting kina bukatar wani abu ne?"
" a'a bana bukatar komai amma dan Allah karka dade Idan kaje"
" no bazan dade ba I think zan yi kamar 2to3 days ne haka"
" OK to Allah ya tsare ya bada abin da aka je nema"
ameen ya fada tare da sakin wani murmushi, dariya nayi na ce.
"cwthrt bari naje aika gidan Anty Atikah"
"OK to bari na sauke ki a gidan in ya so daga nan sai na wuce ko?"  bai jira amsa ta ba ya tada motar tare da gangara wa dan gidan yana bayan layin mu ne, koda muka isa kudi ya zaro a aljihu ya bani, ga wannan ki rike su kafin na dawo zan tafi gida dan yunwa na ke ji, rau rau nayi da idanuna na ce.
" haba dan Allah sai ka dinga barin kanka da yunwa bayan kasan bana so?"
"ya hakuri, to ai bacin raine yasa na kasa cin komai amma ina komawa zan sha tea"
"tea kuma? tabb ni kam ban yadda ba Alaji ka nemi abinci kawai kaci ko kuma na maka kuka"
"Ya  hakuri Rabin rai kar ki yi zan ci to, kinsan bana son ganin hawayen ki" gya ɗa kai nayi tare da ce masa na gode Allah ya saka da alkhairi kuma Allah ya kara maka budi sai ka dawo,fita nayi  ina daga masa hannu, sai da ya ga shigarta gidan sannan ya juya ya tafi.


"Asma'u kuwa tana komawa gida ta shiga dakin su ta tarar duk Ƙannenta basa nan ,zama tayi tare da fadin.
"Najla wlh bazan bari ki auri KB ba domin shi din ZUCIYATA ce ina son shi,ina kuma kaunar shi inda na miki zarra shine ni na iya boye soyayya amma ke nunata kike a fili dan haka koda tsiya koda arziki sai na mallaki KB dan kuwa dani ya dace bake ba, wahallaliya kawai. ai zan ta hada miki tarko ne Wanda KB zai ta wulakanta ki a idon mutane ,dan ni Marin da ya miki yau ya min sugar" ta fada tana kwashewa da dariya tare da yin kwafa ta ce.
" yanzu aka fara muje zuwa za ki san ko ya kalar makircin Asma'u yake."

Ban koma gida ba sai wajan 8:30 na tarar Ummynah tana ninke kayanta sallama nayi na shiga.
"Ummynah na dawo"
"To Najlah ta sannu da dawowa"
"yauwa Ummynah, na kai mata kuma tace na gaisheki"
" to ina amsa wa,
Kabeerun ya tafi ne?"
"Eh ya tafi Ummynah sbd gobe zai tafi Kaduna ga wannan kudin ma ya bani yace na rike kafin ya dawo"
"to Allah ya saka masa da alkhiri amma Najla ki nutsu ki rike maraicin ki dan Allah ki rage rawar kai kin ga yaron nan dai yana sonki amma kike raba kafafuwa"
" to Ummynah" na bata amsa ina mikewa ,dakina na tafi na cire hibajin na kwanta dan yau ina period ba sallah zanyi ba ,wayata  na kunna data na fara chatting aikuwa sai ga kiran Asmeey a wayata dagawa nayi nasa a kunne.
"Hello habibty" ta fada na ce .
"na'am ya aka yi"
"Kalau wlh kin gama kukan akan namiji?"
"eh ina ruwanki?"  na bata amsa
"ai in fada miki har ya sauko tun da yasan ba zai iya fushi dani ba" damm!! gaban Asma'u ya fadi ba haka ta so ba amma saita fuske ta ce.
"to shikennan sai ki ci gaba da haukar ai"
"Eh din ina ruwanki? wlh Asma'u ki dai na ce min mahaukaciya tammm"
"An fada din" zata fara hayaniyar tata na kashe wayata, tsaki na ja ina turo karamin lips dina na ci gaba da charting dina hankali kwance.

Yana kwance akan gadonsa na alfarma yana tunanin hmmmm son ma so wani fa na ke yi,sai yaushe Najla zata dai na son  KB ne? hmmmm wlh ina sonki kuma ba zan taba bari ki auri Kabeer ba dan nima ina jinki a ZUCIYATA, Mahmud ne ya ke ta fadar wannan maganar, ni kuwa nace anya Mahmud dan na ga Najla ta afku da yawa.

     "Asma'u me yasa za ki bari Najla ta miki zarra? Idan kika bari ta auri Kabeer fa kinci baya dan wlh samun irin su ba karamar sa'a bane"
" to yanzu ya zanyi Deejerh?"
" hmmmm ki bari zan fada miki yadda za ki yi,kawo kunnenki ki ji" matsowa Asma'u ta yi ai kuwa ban San me ta rada mata ba suka kwashe da dariya.
"hmmmm Ƙawata kina da basira fa, amma wlh kin kawo shawara za ta ci ubanta ne ai"


@@@@@@

Comments

And

Share

By (Rubbyy)

💕💔SON ZUCIYA NE💔Where stories live. Discover now