Page 22&23✍🏻

Start from the beginning
                                    

       Hannuta shima ya kamo ya duba damtsen hannuta sai ga irin abinda ke damtsen hannusa sak a damtsen hannuta.

       "Kabir wallahi itace Yasmeen ɗinta, ka tuna wannan baƙin abin da muka taɓa tambayar Umma na menene? Har kake tambayarta me yasa Yasmeen take da shi nima nake da shi amma kai baka da shi, taya dariya tace saboda mu gada muka yi a wajenta, ita take da shi shiyasa baka da shi, ka tuna har ta nuna mana nata shima a dai-dai inda namu yake?"

 
     "Na tuna ɗan uwa, Allah sarki Ummanmu ko tana ina? Yanzu ga Yasmeen ta bayyana itama Allah ya bayyanar mana da ita."

      Gaba ɗaya suka amsa da, "Ameen Ya Allah." Suka saka Yasmeen a tsakiyi, suka rugumeta suna farin cikin ƙara haɗuwa da abin sansu.

   
     Sun jima a haka babu wanda yace mu ƙala, su kuma tuni suka manta da wasu mutane a wajena idansu ya rufe tsabar murna.

     
       Yasmeen ce ta zame jikinta, ta tashi ta nufi wajen da Daddy yake zauna, ta tsuguna tare da haɗa hannayenta biyu tace,
   
   
       "Alhaji dan Allah ka yi haƙuri ka barni da ƴan uwana mu cigaba da rayuwa tare da su, kamar yadda aka gaya min komai tare muke yi da su, basa yin nisa da ni sai in makaranta za su je, suna dawowa zamu cigaba da kasancewa tare, dan Allah ka barni da Yayyena, bani da kowa sai su yanzu a duniyar nan Babanmu ya kore ni daga gidansa, yace kada na sake na ƙara dawo masa gida, yace ko a hanyar gidan mu ya ƙara ganina sai ya yankani da raina, dan Allah ka barni na zauna da su, na gaji da wahalar da Mama take bani da dukan da Yaya Jafar da Yaya Adam suke min, kullum sai sun dake ni jikina duk shatin dukansu bari ka gani."
   
   
         Rigarta ta zame, sai ga tabbunan duka manya-manya a bayanta sun bayyana, wani ma taɓan ana hango namanta tsabar dukan da ta sha, kansu suka ɗauke da ganin tabbunan dake jikin Yasmeen, a ransu tausayin yarinyar ne ya kamasu.

       Safnat sarkin kuka tuni ta fara zubarwa da Yasmeen ƙwalla, su kansu sauran sai da ƙwalla taso zubowa musu, dan ko ba a faɗan musu ba sun san ta wahaltu sosai, gata yarinya ƙarama ko shekara sha ɗaya bata cike  ba, wahalhalun da ta ɗauka sun fi ƙarfinta, bai kamata a ace ƙaramar yarinya kamarta ta fuskanci wannan ƙalubalan ba a rayuwarta.

      Hankalin Yassar da Kabir ne ya tashi ganin tabunan dake jikinta, mamaki ne ya kama Yassar a cikin ransa yace, _Dama da wannan baƙaƙe tabunan a jikin ƙanwata? amma me yasa ban kula ba rannan da na gyara mata jiki?_ Ita kanta Safnat sai yanzu ta lura da wannan tabunbunan na jikin Yasmeen.

    "Ka gani ko? Wallahi na koma wajen su abinda zasu yi min sai yafi wannan, dan Allah ku barni da Yayana."
   
   
    Kamota ya yi ya gyara mata rigarta yace, "Yi shiru ki daina kuka ƴata, ba zan rabaki da Yayanki ba kin ji."
   
   
    "Dan Allah da gaske zaka bar ni da Yayana?"
   
   
      Yana murmushi ya gyaɗa mata kai alamun eh da gaske yake.
   
   
       Murna ta shiga yi tace, "Na gode Alhaji Allah ya saka maka da alheri..."

      Dakatar da ita ya yi da cewa, "Daga yanzu karki ƙara ce min Alhaji, ki kirani da Daddy kamar yadda kija ji ƴan uwanki na faɗa."

    
       Ya nuna mata Momy yace, "Itama daga yanzu ki ɗauke ta a matsayi mahaifiyarki, ni kuma mahaifinki, daga yanzu mu ahali ɗaya ne kuma zaki zauna a wajen Yayanki."
   
   
    "To..! Daddy Insha Allah zan ɗauke ku a matsayi iyayena."

    Murna kowa ya shiga yi da jin haka musamman Yassar da Kabir, ganin an karɓi ƙanwarsu a halin nan mai albarka da hannu bib-biyu, kamar yadda suma aka karɓe su lokacin da suka haɗu da Nabil.

       Momy ce ta jawo Yasmeen a jikinta ta rugumeta, dan tun ranar da ta je dubata a asibiti taji ta shiga ranta sosai.
   
   
    Daddy ne ya gyara zama yace, "Yassar Kabir ku matso mu yi magana."

YASMEEN.Where stories live. Discover now